My Destiny (Ƙaddarata)

Page 50

by @matarsayyadee3

*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***

Domin shiga comment section kuma ki danna wannan link ɗin👇🏼 *** *_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining link ɗin da ke sama domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜

_*💃🏻💃🏻 _Kuna ina 'yan uwana matar aure da 'yan mata? Shela nake ko wacce ta fito domin kuwa yau na zo maku da albishiri! Kun san matar Sayyadee ta ku ce ba ta samun abun ƙaruwa ta yi shuru domin ta ƙaru ita kaɗai._💃🏻💃🏻

💐💐🌼🌼_Magana ake ta ƙamshi. Toohwa! Mai ya hwaru?_ 🤔 🌷🌷🌸💮

*To maza ku marmatso ga sirrin nan. Shahararriyar nan wacce ke inganta soyayya tsakanin ma'aura wato Fatima Zaransalaty inkiya Queen Zarah ce ta taho mana da wani ƙamshim domin cika hancinar mazajemu da ƙamshi*. _INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_ _TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA KUJI 💃🏻

_Zaran Salaaty ta yi tafiya miƙaƙƙa har Sudan domin farnata ranmu da na mazajenmu ta kawo mana Sudanese perfume👌🏻 wanda idan har kika shafa shi a jikinki ko kin yi wanka ƙamshin bai barin jikinki. Tested and Trusted ƴaruwa. Zaransalaty ba iya sudanese perfume ta kawo maku ba, akwai kayayyaki masu matuƙar inganci na gyaran HQ (kun san dai ba a wasa da headquarter) akwai kayan gyararrakin jiki kala-kala na ƴan mata da matan aure. Sannan Zaransalaty tana sai da Decoration na kayan ɗaki iri-iri wanda baki taɓa ganinsu._

_KAR IN CIKA KI DA SURUTU, KE DAI NEMI ZARANSALATY A NUMBERS ƊINTA KAMAR HAKAA_: *** Or ****

*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_nfection_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_

_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ ***** *****

Ita kuwa Ladi da ke raƙube a soro wani irin narkakken kuka ta fashe dashi tare da durƙushewa a waje.

Gaba ɗaya jama'ar sai suka nufi soron yuuuu. Wata mace ce ta yi nasarar kamo Ladi dake ɗuke tana kuka ta ɗagota tare da rungumeta itama ta fashe da matsanaicin kuka tana faɗin, "Rakiya ke ce! Inna lillahi wa inna ilaihir raju'una, Rakiya ina kika shige tsayin shekaru haka? Uzaibatu ta yi kuka har ta idanunta sun samu matsala saboda kewarki, sai da aka mata aiki sannann ta fara gani shi ma ba kamar da ba."

Jin haka sai Ladi ta kuma fashewa da kuka tana ƙara ƙwaƙwume wacce ta rungumeta.

Hannunta matar ta riƙe tare da janta zuwa cikin gidan har ɗakin kakarta dake fama da ciwon ƙafa ta kasa fitowa amma kuma sai dirzan kuka take tun da taji an ambaci sunan Rakiya.

"Rakiya taho ki rungume ni in tabbatar ke ɗin ce ba gizo ba!" kakarta ta faɗi tana kuka.

Ƙarisawa Ladi ta yi ta rungume kaka tare da furta, "Baaba Jummala ni ce na dawo. Ina mamata take?"

Wayarta ta laluba ƙirar nokia mara haske ta ciki ta miƙa mata tare da faɗin, "Ungo laluba sunan Uzaibatu ki kirata."

Hannu na rawa ta amshi wayar ta shiga lalubar numbern mahaifiyar tata ta danna mata kira. Duk ringing ɗaya tafiya yake da bugun numfshinta. Sai da ya kusa katsewa sannan muryan mahaifiyarta ya daki dodon kunnanta, "Assalamu alaikum, Baaba!"

"Mamaaaaa!" Ladi ta faɗi tana mai fashewa da wani irin gigitacciyar kuka.

Daga can ɓangaren kuka, ganin kawai aka yi Uzaibatu ta miƙe tsaye hannunta dafe da ƙirji, can kuma ta tafi luuuu ta faɗi ƙasa.

Baaba Jummala duk ta kori jama'ar da suka cika gidan har da na maƙota sannann ta saka aka kai wa Ladi ruwan wanka, bayan ta dawo ta taras da abinci kala-kala cikin tasoshi. Sai dai daƙyar ta iya yin loma biyar ta kwanta a kan katifar kakarta, nan da nan bacci ya kwashe ta.

Washa gari wajajen goma na safe sai ga Uzaibatu ita da mijinta da take aurensa a kano har da ƴaƴa uku wanda ta haifa da su. Tun kamun Uzaibatu ta shigo, Ladi ta yi fitar bindiga ta nufi uwar tare da rungumeta ta fashe da kuwa. Uzaibatun ma kukan fitar hayyaci take don har ta cire rai da ƙara ganin Ruƙayyanta.

Kowa a wajen sai da ya zubar da hawayen tausayin uwa da ƴa. Kan kace kwabo gidan ya ƙara cika maƙwabta 'yan taya murnar dawowar 'yar Uzaibatu.

Ladi Katifa kallon ƙannanta ta riƙa yi su uku. Na farkon Namiji mai suna Nazifi, sai bi masa Salima da auta Fa'izu. Rungume su ta yi tana jin ƙaunarsu har cikin ranta ganin ta samu 'yan uwa yanzu. Ita da Nazifi kamarsu ɗaya, duk da Salima tana fizgar kama da ita amma ba kamar Nazifi ba. Fa'izu ne ya ɗauko babansa sak.

Sai dare can mutane ƴan taya murna suka daina shigowa, kuma a wannan lokacin ne uwa da ƴa suka samu damar zantawa da juna lokacin kowa ya yi bacci daga Uzaibatu, sai Baaba Jummala da ita Ladi Katifar.

"Rakiya ina kika shiga tsayin shekarunan muna ta neman ki? Har Kunya mu kai ta zirya zuwa babu ke babu dalilinki. Ƙannan babanki sun ce guduwa kika yi sabida sun miki aure ke kuma baki son zaman auren."

Wani irin kuka Ladi ta fashe dashi tuno irin izayar da ta sha a hannun ƙannan baban nata da kuma uƙubar gidan miji.

Babu abunda ta rage masu a kan azabar da tasha tub daga hannun iyayan nata har auren da suka mata ta azabtu wajen miji da uwarsa, haihuwarta, sakin wulaƙancin da mijin ya mata, kulawa da nurse ta bata, zuwanta nan ɓagwai da korar karen da mahaifin Uzaibatun ya mata har zuwa sanadiyar haɗuwarsu da wacce ta yi sanadin faɗawarta karuwanci a cikin mota.

Irin kukan da Uzaibatu da Baaba Jummala su ka yi tamkar za su amayar da zuciyarsu. Kuka na fitar hayyaci su ka yi jin wai Ruƙayya ƴar Shafi'u ce da karuwanci.

"Malam ka cuce mu, har da kai ka bada gudunmawar ɓata rayuwar marainiyar Allah!" faɗin Baaba Jummala don ko sau ɗaya mahaifin Uzaibatu bai taɓa faɗa masu Ruƙayya ta zo Ɓagwai ba har ya koma ga Allah. Sun san dai ya yi rantsuwar ba zai riƙe ta ba saboda wulaƙancin da ƴan uwan Shafi'un suka yi bayan mutuwarsa a kan gado.

Washa gari dole aka kai Uzaibatu asibiti domin hawan jininta ya yi sama sosai kusan ɗari biyu da wani abu. Sai da ta kwashi kwana goma a asibiti kamun ta dawo daidai.

Baaba Jummala da Uzaibatu mahaifiyar Uzaibatu sun gargaɗi Ruƙayyah akan bayan su da suka san ta yi karuwanci, kada kowa ya sani cikin dangi.

Mijin da Uzaibatu ke aure a cikin birnin Kano, shi ya yi insisting Ruƙayyah ta bisu kanon ta cigaba da Karunta har Allah ya fito mata da miji ta yi aure. Don shi ma yana da rufun asirinsa daidai gwargwado. Matan biyu kuma kowacce da gidanta.

Haka kuwa ta kasance, ranar da Uzaibatu za ta wuce Kano tare suka tafi da Raƙayya wanda shi mijin Uzaibatun ya so suje Kunya wajen dangin mahaifin Ruƙayyar domin su san tana wajen su, amma fir Ruƙayyah ta ƙi amincewa har da kukanta a kan har abada ba ta son ƙafarta ta kuma takawa zuwa Kunya balle ta haɗa idanu da mutanan da ta fi tsana fiye da mutuwarta.

Bayan komawarsu Kano, mijin Uzaibatu ya biya mata WEAC ta zana kasancewar ana dab da zanawarne kuma aka yi sa a basu kulle karɓan kuɗi ba. Ko da result ya fito, Ruƙayyah tana daga cikin waɗanda na su ya yi kyau. Mijin Uzaibatu bai gaza ma ya nemar mata gurbi a Bayero University kasancewar yana na ƙafa. Environmental science aka bata. Gadan-gadan ta fara karatu bayan nasiha mai ratsa jiki da mijin Uzaibatun ya mata. Kasancewar akwai tafiya sosai tsakanin inda suke da BUK, sai ya nemi ɗan taxi yana kai ta shikuma yanaa biyansa duk ƙarshen wata.

Sosai ya mata ɗinkuna, hijjabai da takalma da jakunkuna. Baba Rufa'i ya ɗauki Ruƙayyah tamkar Salima ƴarsa ta cikinsa, shiyasa bai taɓa gazawa ba wajen kyautata mata musammann ma yadda yake jin daɗin zama da mahaifiyarta. Ita ma kuma Ruƙayyar kallon mahaifi take masa ba mijin mahaifiyarta ba.

*ARƊO BARKINƊO ESTATE* _MAMIYO_ Kaɗa ƙafa kawai take yi tana wani murmushi tare da kallon 'ya'yan nata duk zaune suna kallonta suma murmushin ne a fuskansu.

"Gaskiya Mamiyo ke ɗin tadabance a cikin iyaye. Gashi plan ɗinki ya tafi daidai yanda kika tsara. To yanzu ya za kiyi da batun ɗan iskan yaron can da ke nema hayewa kujerar Minister?" faɗin Baffa Jibrilla.

"Daɗina da kai Jibrila, wutar ciki. Shi ma ina kan plan ɗinne kuma na san zan cimmasa. Ku dai ku kasance a shirye, domin babu yadda za ayi Babiyo ya amince fasiƙi ya hau kujerar Minister. Ni ce nan na shafe tunaninsa akan zancen baya da nasa aka faɗa masa game da Abdul-Hameed ɗin a kan karuwar da yake nema a Bauchi, kuma yanzu ni zan warware wannan cushewar tunanin da na saka malam mai huluna ya masa, amma sai ya rage saura ƙiris! Don so na ke in jefi tsun-tsun biyu da dutse ɗaya!"

Gaba ɗaya tafi ya kaure a parlourn. Ƴaƴanta ne ke tafin suna dariyar jin daɗin plan ɗin mahaifiyar ta su.

_BAFFA GIƊAƊO (Mahaifin Habib)_ Har yau ya kasa sakin jiki da amaryar tasa da aka aura masa kuma ya ke wa kallon ƴa. Ko da yake gwara shi yana sakewa sai dai bai taɓa zuwa mata matsayin miji na a shimfiɗa, amma yana zama kusa da ita tare da jan ta da jira har ta murmusa.

Ita kuwa bayan yin duk wani abu da ta san zai buƙata, ta kasa sakin jikinta. Bata zaman parlour sai dai idan shi ya nemi ta fito. Idan kuma ta fito, za ka ganta da hijjab har ƙasa, wani lokacin ma har da safa da face mark kamar wacce za ta fita. Shi tun abun na bashi dariya har ya koma bashi mamaki. Don shi kam ya fara ji a jikinsa ba zai haramtawa kansa abunda Allah ya halasata masa ba (Maza mutananmu 😂) shiyasa ma ya fara janta a jiki domin ta sake da shi.

Ɓangaren Mama Halima ma dai ta fitar da komai a cikin ranta ganin ita za ta jawa kanta ta faɗi ta mutu ta yiwa ƴaƴanta asara. Haka yasa ta tattara duka lamarin ta miƙawa Allah. Abu guda ɗaya ta saka a gaba, shine tsayuwar dare a kan Allah ya yi gaggawar tona asirin Mamiyo komai ya dawo masu daidai su da ƴaƴansu.

_Hafiz Informer_ Jikinsa har rawa yakee wajen danna numbern da ya yi saving da AB. Ringing biyu aka ɗaga wayar.

"Mai ka samo wannan karan?" muryan Ɓaleri ta daki kunnansa.

"Na gado Mamiyo da ƴaƴanta suna shirin buɗe wani katafaren kampani haɗa kayan ɗaki irinsu gado da kujeru a jihar Bauchi. Kuma tana ƙoƙarin janye share holders ɗin `ARDO BARKINDO GLOBAL COMPANY LIMITED` zuwa wancen companyn nata domin durƙusar da kampanin mahaifinka ya daina aiki. Yanzu haka saura ƙiris ya rage mata!"

Wani sakaryar Murmushi Ɓaleri ya yi tare da faɗin, "Dalilin da ya dawo dani cikin Arɗo Barkinɗo kenan. Na san da zaman wannan kamfanin domin a garin da nake zama kenan. Aikin da zan baka da za ka fara daga yau shine, na farko ɗauko takardun kamfanin `ARDO BARKINDO GLOBAL COMPANY LIMITED` da shi kamfanin nata da take shirin buɗewa. Kwanaki talatin da ɗaya gareka domin, domin tsakiyar watan gaba shine watan da za a rantsar da ɗan ƙanina matsayin Ministern jahar Abuja, In sha Allah. Hafizu, idan waɗannan kwanakin suka cika ba tare da ka kawo min takardun nan ba, hmm!" yana gama faɗin haka ya datse wayar.

Wasu irin mahaukatan zufa ne suka shiga kwanranyo daga kai, wuya, da jikin Hafiz jin gagarun aiki mai matuƙar wuyar da Ɓaleri ya bashi. Kuka ya fashe dashi tare da faɗin, "Kaicona! Kaincon kwaɗayin da ya jawo min shiga wannan halin! Yau ni na shiga uku ni Hafizu!! Wayyoo ni Allah, wayyoo kaina!!!"

_Hmmm Hafizuuuu🤔 lallai dole ka ce wayyo! Yanzu ta ina za ka fara bi domin ɗauko takardun kamfanin Babiyo wanda a wajensa kuma cikin ɗakinsa suke, haka zalika Mamiyo? Tirƙashi!_

#Ladi Katifa Ruƙayyah) #Hafiz Informer #Baffa Giɗaɗo #Baffa Jibrilla #Mamiyo #Babiyo #Company #Abdul-Hameed #My Destiny #Matar Sayyadee *** [8/10, 4:18 PM] ***: *Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee

☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`