Page 51
*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***
Domin shiga comment section kuma ki danna wannan link ɗin👇🏼 *** *_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining link ɗin da ke sama domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜
_*💃🏻💃🏻 _Kuna ina 'yan uwana matar aure da 'yan mata? Shela nake ko wacce ta fito domin kuwa yau na zo maku da albishiri! Kun san matar Sayyadee ta ku ce ba ta samun abun ƙaruwa ta yi shuru domin ta ƙaru ita kaɗai._💃🏻💃🏻
💐💐🌼🌼_Magana ake ta ƙamshi. Toohwa! Mai ya hwaru?_ 🤔 🌷🌷🌸💮
*To maza ku marmatso ga sirrin nan. Shahararriyar nan wacce ke inganta soyayya tsakanin ma'aura wato Fatima Zaransalaty inkiya Queen Zarah ce ta taho mana da wani ƙamshim domin cika hancinar mazajemu da ƙamshi*. _INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_ _TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA KUJI 💃🏻
_Zaran Salaaty ta yi tafiya miƙaƙƙa har Sudan domin farnata ranmu da na mazajenmu ta kawo mana Sudanese perfume👌🏻 wanda idan har kika shafa shi a jikinki ko kin yi wanka ƙamshin bai barin jikinki. Tested and Trusted ƴaruwa. Zaransalaty ba iya sudanese perfume ta kawo maku ba, akwai kayayyaki masu matuƙar inganci na gyaran HQ (kun san dai ba a wasa da headquarter) akwai kayan gyararrakin jiki kala-kala na ƴan mata da matan aure. Sannan Zaransalaty tana sai da Decoration na kayan ɗaki iri-iri wanda baki taɓa ganinsu._
_KAR IN CIKA KI DA SURUTU, KE DAI NEMI ZARANSALATY A NUMBERS ƊINTA KAMAR HAKAA_: *** Or ****
*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_nfection_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_
_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ ***** *****
_DENMARK_ Zuba masa idanu ta yi tana kallonsa babu kyaftawa, can kuma ta shiga yawo da idanunta a cikin ɗakin kamar wacce ke sabon duniya. Ta fi mintuna goma a haka kamun mayar da kallonta kan Jawaad da ya zabga tagumi yana kallonta.
"Wacece ni, me nake yin a nan, kai wanene?" ta faɗi maganar kamar mai koyon karatu don daki-daki ta ke furta ko wacce kalma.
"Ke ɗin ƙanwata ce. Sunanki Zeenat, ni kuma sunana Hamma Jawaad. A cikin jirgi na fara ganin ki za ki dawo Nigeria daga Dubai, sannan kuma na sanki a garin Lagos. Tun da na fara ganin ki ƙaunarki ta soki nan ɗina" ya ƙarisa maganar yana nuna saitin zuciyarsa.
Kallonsa ta yi na tsayin mintuna biyu kamun ta ce, "Ban san ka ba, ban tuna komai ba."
Shuru ya yi yana kallonta kamar yanda ita ma take kallonsa. Ajiyar zuciya ya saki mai ƙarfi kamun ya kuma furta, "Kar ki damu a hankali za ki tuna komai In sha Allah. Nan da sati ɗaya za ayi discharging ɗin mu. Zan ɗauke ki na mayar da ke gidana, za ki zauna?"
Shuru ta yi kamar mai tunani kamun ta gyaɗa kai a hankali. Duk ta zama wani irin kamar ƙaramin yaro mai koyan sabon abu.
"Ina jin fitsari fa!" ta faɗi har da turobaki kamar yarinya.
Murmushi ne ya suɓuce masa tare da faɗi ƙasa-ƙasa, "Hmm wato dai komai ya goge amma banda rigimar!"
"Me ka ce? Ni faAllah zan yi a kan gadon." ta faɗi seriously.
Ɗan waro idanu ya yi tare da faɗin, "Wai dagaske? To gwada mu gani!" ya faɗi yana dariya ƙasa-ƙasa.
"Allah ni dai ka fita, a gabanka ne zan ɗaga riga na yi fitsarin?" ta faɗi tana turo baki waje.
Wani irin sanyin daɗi ne ya mamaye shi jin abunda ta furta, "Ke nan haka na nufin ta san tsiraici abu ne da ake ɓoyewa, Alhamdulillah!" ya faɗi cikin zuciya tare da miƙewa ya fita ya turo mata ƙofar.
Tana ganin haka ta yi wuff! Ta miƙe tare da shigewa bayihar ƙafarta na buguwa da ƙarfen gadon da take kai kasancewar fitsarin ya ƙulle mata mara kuma gab yake da zubowa.
Jawaad kuwa har ya fice daga ɗakin fuskansa ba ta bar murmushin jin daɗi ba. Bayan kaman mintuna sha biyar ya yi knocking sannan ya murɗa handle ya ɗan leƙo. Ganin kwance a kan gadon har da jan lulluɓi ya bashi damar kutsa kai sannan ya mayar da ƙofar ya rufe tare da ƙarisowa ya zauna a kan kujerar da ya tashi bayan ya ɗan matsar da kujerar kusa da gadon.
"To yanzu me ke miki ciwo?" ya jefa mata tambaya yana kallonta.
Idanunta a rufe ta ce masa, "Kaina ke ɗan min ciwo kaɗan-kaɗan. Ina jin kamar ina son inyi tunani amma da zarar na yi forcing kaina sai na ji kaina na sara min."
Hannu ya ɗaura a kan kadon sai dai bai yi kuskuren kaiwa jikinta ba ya furta, "Kina ji ko, kar ki riƙa rakurawa kanki akan dole sai kin tuna pass ɗinki. In sha Allah a hankali komai zai dawo miki cikin ƙwaƙwalwarki."
"Ɗazu na ji ka ce gidanka zan koma idan an sallame ni nan da sati ɗaya ko?" ta faɗi bayan ta tashi zaune daga kwancen da take tana kallonsa.
Gyaɗa mata kai ya yi tare da faɗin, "Ko bakya son zama dani ne?"
Ɗan turo baki ta yi tare da faɗin, "To ni da wa zan zauna a gidan? Ni gaskiya ba zan zauna ni kaɗai ba."
Dariya ya yi tare da faɗin, "Dama wa ya faɗa miki ke kaɗai za ki zauna? Ai matata na gidan."
"Kana da mata dama? Shine ɗazu ka ke wani cewa kana sona, caɓ!" ta ƙarisa maganar tana harararsa.
Dariya kawai ya yi tare da miƙewa ya ce, "Zan je in dawo. Maybe kamun na dawo Khairiyyah za ta riga ni zuwa da abincinki."
"Wacece haka?" ta faɗi tana kallon kwayar idanunsa.
"Matata mana!" ya bata amsa shima yana kallon cikin idanunta.
"Caɓ! Kuma ka faɗa mata ni kana sona?"
"A'a ban faɗa mata ba, sai dai idan yanzu kin ba ni izini sai in faɗa mata idan na koma gida."
Hannu biyu ta ɗaura a kan bakinta tana girgiza kai tare da faɗin, "A'a don Allah! Ni Allah ma na fasa zama a gidan naka." ta ƙarisa maganar tana marairaice fuska.
"To ki haƙuri kar ki fasa, na ji ba zan faɗa mata ina sonki ba, amma to ke kina sona?"
Watsa hannu ta yi tare da faɗin, "Ni ban sani ba, ban san menene so ba. Ban san ko ina sonka ko ban sonka ba!" ta ƙarisa maganar da iyakacin gaskiyarta.
Kallonta ya yi na kusan mintuna uku kamun ya furta, "Za ki sani very soon!" yana gama faɗin haka ya juya zai bar ɗakin.
Da sauri ta yi gyaran murya alamar akwai abunda ta ke son faɗa. Juyowa ya yi tare da faɗin, "Akwai abunda kike so ne?"
Turo baki ta yi tare da faɗin, "Please ka daina saka turaren nan, ƙamshinsa na sakawa ina jin wani abu a cikin kaina. Sai kaina ya riƙa min duuum haka!" ta ƙarisa maganar tana mai riƙe kanta.
Kallonta ya riƙa yi sosai kamun ya ce, "Ni kuma ina son ƙamshin nan sosai. Ɗan uwana ne ya ba ni matsayin gift ɗin aurena da Khairat saboda ya san ina sonsa. Amma tunda gimbiyata ba ta so, daga yau an daina sakawa!" ya ƙarisa maganar yana kashe mata idanu.
"To ai ni ma ban ce turaren bai da daɗi ba, kuma ban ce ka daina sakawa ba. Kawai dai......" sai kuma ta yi shuru.
"Zee, mai ƙarya fa ɗan wuta ne! Yanzu fa kika ce min don Allah kar in ƙara sakawa amma kuma kika canza maganarki da ƙarya wai baki ce haka ba. To kawai dai me? Sai kin ƙarisa maganar." ya faɗi da alamar zaulaya.
Kai tsaye ta ce, "Kawai dai turaren na da daɗi da saka sanyi a zuciya. Amma ni ban san mai yasa idan na shaƙa gabana ke faɗuwa ba kuma kaina sai ya min duuum haka."
"Zan bari in sha Allah, kin ji? Yanzu ki samu ki kwanta ki huta. Bari na je na dawo, ko kina buƙatar wani abu?"
Girgiza kai ta yi tare da faɗin, "Ban buƙatar komai, I just want to have some rest."
"Ok, tom ki huta sai na dawo."
Gyaɗa kai ta yi tare da zamewa ta kwanta ta lumshe idanu. Shi kuma ya fice tare da jawo mata ƙofar a hankali.
A hankali ya ke murza kan motar yana tunanin ta yanda zai fara yiwa Khairat bayani don fisabilillahi yana matuƙar jin kunyarta duk da ya na da yaƙinin ba za ta ƙi amincewa Zeenat ta zauna da su ba, sai dai kuma still wani ɓangare na zuciyarsa na masa tuni da wannan halin na mata wato kishi.
Mintuna ashirin ne zai kai sa gida daga asibiti, amma sai ga shi ya ɓuge da kwasar mintuna talatin har da biyar. Gate ɗin a buɗe yake hakan ya bashi damar kutsawa ya yi parking wajen aje motoci. Number 18 shine number ɗin gidansa, sama da ƙasa ne gidan. Hango Khairat ya yi ta can saman gidan tana shanya jikinsa sanye da hijjab har guiwarta. Karaf suka haɗa idanu ta sakar masa murmushi tare da saurin ƙarisa shanya rigar da ke hannunsa sannan ta juya domin saukowa.
Ko da ya isa ƙofar bai danna door bell don ya san ta riga ta ganshi za ta ƙariso ta buɗe masa. Aikuwa ko mintuna biyu bai yi ba sai gata ta buɗe ƙofar.
Hannun ya ware mata alamaar ta ƙariso gare shi ta rungume shi. Cike da kunya ta ƙariso ta shige jikinsa ta yi luff. Sun jima a haka kamun ya ɗago kanta ya sumbace ta sannan ya kama hannunta zuwa cikin parlourn.
"Ban yi tsammanin ganinka ba da wuri haka." Khairat ta faɗi.
Lumshe idanu ya yi sannan ya buɗe tare da faɗin, "Ko in koma ne?"
Da sauri ta girgiza kai tare da faɗin, "Ni dai ban ce ba wallahi!"
Da serious face ya kalleta alamar yana son magana mai mahimmanci da ita. Hannunta ya kamo tare da furta, "Khairaat!"
Sai da tsikar jikinta ta miƙe saboda yadda ya kira sunanta, "Uhiym!" ta amsa kanta a ƙasa.
"Ina son neman wata alfarma a wajenki, ban san ko za ki iya taimaka min ba, sannan ban san ta yadda za ki fassara abunda zan faɗa miki ba."
Ɗan ɗagowa ta yi kaɗan ta kallesa gabanta na faɗuwa, amma sai ta yi ƙarfin faɗin, "Hamma ka yi umarni kai tsaye, idan har bai shiga hurumin ubangiji zan yi maka shi. Ai ni mallakinka ce."
Hannunta ya riƙa murzawa yana jin sonta na huda zuciyarsa. Amma kuwa kunyarta sosai yake ji. Can ya daure tare da faɗin, "Kalle ni Khairiyya!"
Ɗagowa ta yi a hankali ta kallesa cikin ido duk da matsanaicin kunyarsa da take ji.
"Baki taɓa tambaya inda nake zuwa ba tun da muka sauka a Denmark, mai yasa?" ya jefa mata tambaya.
"Hamma, ai ba hurumina bane hakan. Ni ce dai idan zan fita ya zama wajibi ka san inda zani har ma lokacin dawowata."
Gyaɗa kai yi kamun ya ɗauki tsayin sakwanni kamun ya furta, "Asibiti na ke zuwa, Khairta."
Da sauri ta damƙi hannunsa tare da faɗin, "Asibiti Hamma? Mai ke damunka?"
Girgiza kai ya yi tare da faɗin, "Kwantar da hankalinki babu abunda ke damuna, wata ce ke kwance a asibiti, kuma ni na kawo ta nan ƙasar domin a duba lafiyarta. Ta samu matsala a ƙwaƙwalwarta ce shine na taimaka na kawo ta akai mata aiki, sai dai sanadiyar aikin ta kuma kamuwa da wata matsalar ta shafewar tunani. Ta mance duk wani abu da ya taɓa faduwa da ita a bayaa, hatta sunanta ba ta sani ba. Shine na ke son ki taimaka min ki haƙuri ta zauna damu a nan gidan kamun tunaninta ya dawo. Amma fa idan har baki amince ba sai in nema mata wani wajen ta zauna."
Murmushi ne ya faɗaɗa a fuskan Khairta wanda har sai da ya ba Jawaad mamaki matuƙa.
"Kai Alhamdulillah! Alhamdulillah ni ma zan samu abokiyar hira. Don Allah yaushe za ka kawo ta? Allah sarki Allah ya bata lafiya."
Kamar statue haka ya tsaya yana kallonta har sai da ta girgiza shi don bakinta da ke motsi kawai yake kallo amma bai gane abunda take cewa tun bayan furucin farko da ta yi. Kawai ji ta yi ya mata wata wawuyar runguma yana ajiyar zuciya. Sun jima a haka kamun ya furta cikin kunnanta, "Allah ya miki albarka sweetheart!"
Da "ameen" ta amsa tana ƙara rungume sa.
Sungum ya ɗauke ta zuwa bedroom suka more yaruwarsa tare da tsaftace jikinsu sannan suka shirya. Sharp-sharp Khairat ta dafa pasta with vegetables, ta sakaa na Zeenat cikin cooler, a plate ɗaya kuma ta zuba nata da na Jawaad ta kai dinning.
Bayan sun ci sun ƙoshi ta koma ɗaki ta saka abaya tare da yane jikinta da mayafin abayar ta fito, lokacin tuni har Jawaad ya kai wajen mota ya saka basket ɗin abincin a ciki.
"Kin yi kyau sosai, matata!" ya faɗi tare da jan kumatunta bayan ta ƙariso kusa da shi. Shi ya buɗe mata murfin gaba ta shiga sannan ya zagaya ya shiga mazaunin driver ya jaa motar.
_Arɗo Barkinɗo Estate_
Huɗu daga cikin ƴaƴan Babiyo shiga su kai ta alfarma domin zuwa Kaduna garin gwamma kai kuɗin auren ƴar tsohon gwamnar jahar da Jawaad zai aura. Daga ciki akwai Baffa Jibrilla, Baffa Gidaɗo, Baffa Modibbo da ya zo takanas tun daga Lagos sai Baffa Chubaɗo.
Babiyo sai murmushin jin daɗi ya ke, hakan kuwa ba ƙaramin ƙona ran baffa Jibrila ya yi ba, sai makawa Babiyo harara ya ke yi a faƙaice.
Gaba ɗaya a zaune a parlourn babiyo suke suna jiran Hafiz domin ya kai su. Kowa ya san Hafiz Babiyo kawai ya ke tuƙawa, amma kasancewar kuɗin auren ɗan gwal (su baffa Jibrilla suka faɗa ba ruwan matar Sayyadee😂) za su je kaiwa, sai Babiyo ya ce su dakata Hafiz ɗin zai kai su.
Bayan shigowar Hafiz, Babiyo ya shiga kwararo addu'a ga dukkansu akan Allah ya kaii su lafiya ya kuma dawo da su lafiya. Don a son babiyo ana ɗaura auren Abdul-Hameed yau, to sati mai zuwa a rantsar da shi matsayin Ministern Abuja.
"Hafizu, don Allah kai min motata gida tunda ba da ita za muyi amfani ba." faɗin baffa Jibrila yana miƙawa Hafiz makullin mota.
Cikin sauro Hafiz ya amshi key ɗin tare da fita daga ɗakin. Kai tsaye wajen motar ya nufa tare da buɗewa ya shiga, sai dai kamar an ce ya juya, sai idanunsa suka sauka a kan wasu ducument har huɗu. Saurin yiwa motar key ya yi tare da barin farfajiyar gidan babiyo. Sai da ya yi ɗan nisa sannan ya kai hannu ya kwaso document ɗin ya shiga dubawa. Abubuwa ya ci karo da su sosai game da sabon kamfanin d suke shirin buɗewa tare da saka hannun wasu manya share holders na kamfanin babiyo, na ƙarshen ne kuma ya ci karo da takarun kamfanin da Ɓaleri ya ce ya kawo masa. Jikinsa har rawa yakee wajen kwasar biyu daga cikin documents ɗin.
#Jawaad #Zeenat #Khairat #Babiyo #Abdul-Hameed #Kaduna #Baffa Jibrila #Hafiz Informer #My Destiny #Matar Sayyadee *** [8/10, 4:18 PM] ***: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)
*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee
☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`