My Destiny (Ƙaddarata)

Page 52

by @matarsayyadee3

*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***

Domin shiga comment section kuma ki danna wannan link ɗin👇🏼 *** *_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining link ɗin da ke sama domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜

_*💃🏻💃🏻 _Kuna ina 'yan uwana matar aure da 'yan mata? Shela nake ko wacce ta fito domin kuwa yau na zo maku da albishiri! Kun san matar Sayyadee ta ku ce ba ta samun abun ƙaruwa ta yi shuru domin ta ƙaru ita kaɗai._💃🏻💃🏻

💐💐🌼🌼_Magana ake ta ƙamshi. Toohwa! Mai ya hwaru?_ 🤔 🌷🌷🌸💮

*To maza ku marmatso ga sirrin nan. Shahararriyar nan wacce ke inganta soyayya tsakanin ma'aura wato Fatima Zaransalaty inkiya Queen Zarah ce ta taho mana da wani ƙamshim domin cika hancinar mazajemu da ƙamshi*. _INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_ _TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA KUJI 💃🏻

_Zaran Salaaty ta yi tafiya miƙaƙƙa har Sudan domin farnata ranmu da na mazajenmu ta kawo mana Sudanese perfume👌🏻 wanda idan har kika shafa shi a jikinki ko kin yi wanka ƙamshin bai barin jikinki. Tested and Trusted ƴaruwa. Zaransalaty ba iya sudanese perfume ta kawo maku ba, akwai kayayyaki masu matuƙar inganci na gyaran HQ (kun san dai ba a wasa da headquarter) akwai kayan gyararrakin jiki kala-kala na ƴan mata da matan aure. Sannan Zaransalaty tana sai da Decoration na kayan ɗaki iri-iri wanda baki taɓa ganinsu._

_KAR IN CIKA KI DA SURUTU, KE DAI NEMI ZARANSALATY A NUMBERS ƊINTA KAMAR HAKAA_: *** Or ****

*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_nfection_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_

_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ ***** *****

Ko kamun ya koma gidan Babiyo ya ɗauki su Baffa zuwa Kaduna, sai da ya turawa Ɓaleri message akan ya samu nasarar ɗauko takardun kamfanin da Mamiyo da 'ya'yanta suke son buɗewa har ma da wanda shi Ɓalerin bai saka shi ya ɗauko ba. Gajeran saƙo Ɓalerin ya tura masa.

_Ka kyauta, zuwa da daddare zan zo na karɓa, sannan shi ma na Babiyon ka tabbatar ya shigo hannunka kamun wa'adin da na baka su cika!_

Yana kammala karanta saƙon ya goge tare da shiga farfajiyar gidan Babiyon, inda a nan ya iske duk su Baffa a waje har da Babiyon suna jiransa.

"Ma sha Allah, gashi ya iso sai ku yi haramar tafiya. Allah ya kiyaye hanya, ku gaishe min da Sulaiman ɗin kuma ku faɗa masa musamman zan zo na kawo masa ziyara, in sha Allah."

Baffa Jibrila sai kallon Babiyo ya ke yi a kaikaice cike ɗumbin mamaki ganin irin fara'ar da ke kwance samar fuskansa, kuma wai shine da yi masu rakiya don kawai za su ce kai kuɗin auren Abdul-Hameed. Wani tuƙuƙin baƙin ciki ne ya cunkushe zuciyarsa tare da yin kicin-kicin da fuska.

Babiyo bai bar tsakar gidan ba har sai da ya ga motarsa sabuwa da ko sati bata yi ba, ta fice daga gidan sannan ya juya. Cak! Ya tsaya bayan ya ɗaga idanunsa kaɗan ya kalli windown sama ta yadda ba kowa zai fahimci hakan ba sai shi da ya yi. Faɗaɗɗiyar murmushi ya saki tare da shigewa katafaran falonsa bayan ya tabbatar da wacce ya gani tsaye jikin window tana leƙe.

Zama ya yi yana kaɗa ƙafafun, cikin mintuna guda ya dawo da asalin yanayinsa a kan fuskansa na ɗaure fuska da nuna isa da taƙama.

Waya ya zaro tare da kai sa saitin bakinsa sannan ya furta cikin turanci tamkar baturen Ingila (England) ya furta, "Call Belɗo".

Nan ta ke wayar ta kira masa wanda ya furta ta kiran. Ringing biyu Baffa Belɗo mahaifin Abdul-Hameed ya amsa kiran cike da tsan-tsan biyayya tamkar yana gaban Babiyon.

"Ka zo gida yanzu ka same ni!" yana kammala faɗin haka a dake ya katse wayar tare da ajiye ta a kan glass table ɗin da ke kusa da shi.

Daidai nan Mamiyo ya shigo falon hannunta riƙe da wata kyakkyawar ƙwarya mai ɗauke da damammiyar hura da nono mai sanyi don har ƙananan ƙanƙanra ne a ciki. Fuskannan tamkar gonar auduga, amma can cikin zuciyarta balbalin bala'in baƙin ciki ne cunkushe.

Kallo ɗaya mata ya ɗan saki murmushi kaɗan sannan ya kuma mayar da fuska ya ɗinke.

Mamiyo bata damu da ɗaure fuskarsa ba, don idan da sabo ya saba, asiri kuwa ta yi iri-iri akan samun kan Babiyo a hannunta sai yadda ta so amma sam bai aiki, don ko ya yi aikin ma bai wuce na wata ya saki. Dole ta shigo da kissa da maƙirci a cikin lamuranta wanda hakan ɗin ne ya saka ta ke watayawarta yadda taso a cikin gidan.

"Ranka shi daɗe Arɗona, Arɗon Lauratu ita kaɗai tak!" ta faɗi tana ƙoƙarin zama a kusa dashi. Sai dai furicin da ya furta ya saka ta yi suman wucin gadi don ta kusa mintuna biyu kamun ta iya kai ɗuwawunta kan kujera wasu zufan tashin hankali na kwaranyo mata har ta tsagun mazaunanta.

"Point of correction Hajiya Lauratu! Ai Arɗon ba na ki bane ke ɗaya. Abunda ya kamata ki kara cewa shine, Arɗon Maimuna angon Lauratu kuma na Laɗifa da Karime."

Ya faɗi hakane tare da sakar mata wani murmushi da shi kaɗai ya san ma'anarsa sannan ya karɓi ƙwaryar da ke hannunta ganin tana neman sakinsa a ƙasa ba tare da ta ankara ba. Bata gama dawowa daga shock ba ya kuma sakar mata maganar da ta ji ta tamkar saukar guduma a tsakar ka.

"Jiya na yi mafarkin Maimunatuna, cikin ɓacin rai ta ke faɗamin ban mata adalci ba sabida na ga babu ita a duniya, ta ce na banzatar mata da 'ya'yanta wanda hakan na ta haifar da abubuwa mara su daɗi. Sannan ta ƙara da bata yafe min ba idan ban haɗa mata kan 'ya'ya waje ɗaya ba. Me za ki ce game da wannan mafarkin nawa?"

Har ga Allah da gaske Babiyo ya ke faɗi mata ya yi mafarki, don tun da ya farka ƙarfe biyun dare bai kuma runtsawa ba.

Tsuru-tsuru ta yi gabanta na wani irin harbawa tamkar za ta faso zuciyarta ta fito, kuma sai yanzu ta ke ƙara tabbatar da maganar Mala mai huluna da ya ce Maimunatu ba ƙaramin asiri ta tafkawa Babiyo ba kamun ta bar duniya ta yadda ko bayan ranta ba zai iya kataɓus ba. To amma kuwa abunda ya matuƙar tada hankalinta, Malam mai huluna ya faɗa mata ya yi wa Babiyo asirin dahar abada ba zai ƙara kallon ko tuna Laɗifa da Karime matsayin matansa ba, sun riga sun zama jinginannu. Sai kuma ga shi yau ya ambace su. Mai hakan ya ke nufi, kuma mai ke shirin faruwa da ita?

Murmushi Babiyo ya yi mai sauti har hakan na bayyanar da haƙoransa farare tas da ko guda ɗaya bai fita ba duk tsufansa.

Nan da nan hankalin Mamiyo ya dawo jikinta ta shiga bin Babiyo da idanu ganin haƙoransa a waje har wannan lokaci.

"Ki dawo cikin hayyacinki Lauratu kar ki saka zarginki a zuciyar wannan tsohon banzan da mutum bai gane gabas ɗinsa?" ta faɗawa kanta kamun nan ta aro wani fara'a da murmushi a kan fuskanta.

"Ka ganni na faɗa dogon tunani akan rayuwarmu da mamansu Ɓaleri, mutuwa mai shiga tsakani!" tana kawowa nan ta fashe da kuka mai sauti wanda ba na komai bane sai na baƙin ciki kuma da ma maƙale yake jiran makafa kawai take yi ta sake shi ko ta ɗan ji salama.

"Menene abun kuka kuma? Ai ta su ta yi kyau sai dai jiran ta mu mu 'yan baya. Maimunatu ai 'yar aljanna ce in sha Allah. Don ni na riga na ɗaga ƙafa in dai har a ƙarƙashin ƙafata aljannarta take. Sai dai mu yi mata fatan rahamar ubangiji."

"Hakane kam!" Mamiyo ta faɗi tana yaƙe tamkar zararriya. Duk wanda ya kalleta ya san natsuwarta ta bar jikinta.

"Ki shirya tarbar 'yan ƙannan naki yau, don zuwa bayan la'asar miji zai bar hannunki zai koma wajen ƙanwarki Karima don tare suka taho nan ɗin ita da Modibbo a bisa umarnina. Ita ma bayan kwana biyu za ta bai wa 'yar uwarta Laɗifa, idan aka kuma kwana biyu sai girki ya dawo kanki!"

Wannan karan furucin Babiyo kaɗan ya rage ya tarwatsa zuciyar Mamiyo don hatta idanunta sai da suka rine suka koma jazir.

Daidai nan Ɓaleri ya yi sallama ya shigo falon. Lokaci ɗaya Babiyo da Mamiyo suka ɗago suka kalle shi. Wani irin harbawa zuciyarta ya yi don sai ta ga ma kamar wani irin mummunar kallo ya ke watsa mata.

Tun da ta yi sanadiyar barinsa Arɗo Barkinɗo ba ta ƙara saka shi a idanu ba kusan shekaru sha takwas. Wani irin haske, cika da kyau da kuma kwarjini ta ga ya mata.

Har ƙasa ya ɗuka tare da faɗin, "Awallidjam, Babiyo," ita ma Mamiyo ya juya ya ce mata haka.

Da ƙyar Mamiyo ta iya haɗiye miyau ta amsa masa gaisuwa, can kuma ta miƙe ta yi excusing ɗinsu ta koma ciki.

Tana shiga cikin ɗakin ta yo watsi da kayan da ke gaban madubi da ƙarfi duk suka watse a ƙasa sannan ta saki wani irin ihun baƙinciki tamkar wata zararriya.

Can kuma ta rarumi waya ta dannawa malam mai huluna kira. Sai da ya yi ringing kamar zai yanke sannan aka ɗaga.

"Wani irin shashanci ne wannan? Ni za ka lalatawa aiki malam? Ni za ka wulaƙanta a idanun Arɗo Barkinɗo. Ya muka yi da kai? Ba ka faɗa min Arɗo ba zai taɓa kula Laɗifa da Katima ba? Ka faɗamin yanda ya mance da taste ɗin nonon mahaifiyarsa haka ya mance da su! Amma kuma yau Arɗo ya zo min da zancen banza wai yau zan ba wa Karima girki. Sannan yanzu hakaa ga Belɗo can a falo kuma uban ne ya kira shi don idan har ba shi bane Belɗo bai isa ya tako ƙafafunsa cikin falon ubansa ba. Wai me ke shirin faruwa da ni ne, Malam?"

Wani murmushi malam ya yi sannan ya ce, "Shekaru nawa kina tare da mu muna miki aiki baki taɓa ganin matsala? Kar ki garaje, sakamakon aikin ki zai iske nan ba jimawa. Ai mun riga mun gama magana tun lokacin d kika ce na warware sihirin farra'u da na yi wa Abdul-Hameed da katuwarsa. Don haka ki cigaba da sauraran sakamako kawai."

Ajiyar zuciya Mamiyo ta sauke tare da faɗin, "Kenan idan na fahimce ka in kwantar da hankalina komai zai yi daidai?"

Wani dariya ya kwashe da shi cikin zuciyarsa tare da faɗin, "Ai kin warware komai da kan ki, don kifi na ganinki mai jar koma!"

Amma a zahiri sai ya ce, "Kwarai kuwa, ki je ki jira kawai sannan kar ki ƙara tambaya ko tada hankali idan ba haka ba komai na ki zai rushe."

Ƙit ta katse wayar tare da watsa shi a kan gado sannan ta zauna jagwab a kan dagon tana imagining ga ta ita da 'ya'yanta a wulaƙance.

"Inaaaa! Ba zai taɓa yuwuwa ba wallahi!" ta faɗa tare da lalubar wayarta ta shiga neman wata number.

Gyara zama Babiyo ya yi yana kallon Baffa Belɗo da kansa ke a ƙasa yana murza hannunsa.

"Uh-uhm" Babiyo ya yi gyaran murya still yana kallon Belɗo da idan ka ƙura masa idanu za ka ga kamar jikinsa rawa ya ke yi don shakka da tsoron Babiyo a jininsa ya ke.

"Abdul-Azeez!" Babiyo ya kira asalin sunansa cikin kakkausar muryar da ya saka hantan cikinsa ya kada.

"Na'am, Baffa!" ya amsa muryansa a raunane sosai.

"Ka faɗa min gaskiya tsakaninka da ubangiji mahaliccin sammai da ƙassai. Menene gaskiyar abunda ya faru shekaru sha bakwai zuwa sha takwas da suka wuce!" yana gama faɗin hakaa ya rumtse idanunsa.

A hankali Belɗo ya ce, "Na rantse da ubangijin sammai da ƙasai, ubangijin da ke saukar da ruwan samaa, ubangijin da ke fitar da tsirrai, ubangijin shaiɗan da Aljan, ubangiji dukkan halittun duniya ban aikata ɗaya daga cikin abunda ake tuhumata da su ba, ban taɓa kai ko karan sigari bakina ba balle na ɗaga kwalbar giya, haka ban taɓa zina ba. Wallahi, tallahi, billahil azim su zama shaida a gare ni idan ƙarya na faɗi." ya ƙarisa maganar yana fidda hawayen baƙin ciki don hoton ranar dawo masa ya yi a idanunsa.

Wata wawuyar ajiyar zuciya Babiyo ya faɗi kamun ya buɗe hannayansa ya yi wa Belɗo alama da ya taho ya rumgume sa. Da sauri Belɗo ya miƙe ya faɗa kan Babiyo ya rungumesa sosai yana mai fashewa da kuka. Hannu Babiyo ya saka yana bubbuga bayansa.

"Ƙundun ubancan kayyasa!" faɗin Mamiyo a kan laɓɓanta daidai ta ɗaga labule kenan ta hango abunda ke faruwa. A hankali ta saki labulen ta koma da baya don wannan karan ba za ta iya jurewa tabbas. Idan har ta isa tsakiyar falon za ta iya shaƙesu su duka su mutu ko kuma ta tuttura masu kwandon ashariya.

Bayyananniyar murmushi Babiyo ya saki bayan ya kau da kallonsa ga Mamiyo da ta juya. Don duk abunda ya faru akan idanunsa ne ta ƙasa-ƙasa ta yadda ita kanta Mamiyon ba za ta fahimta ba.

"Allah ya maka albarka!" faɗin Babiyo bayan ya ɗago Belɗo daga jikinsa.

Komawa wajen zamansa ya yi tare da tanƙwashe ƙafa ya soma magama a hankali.

"Babiyo, don girman Allah kamar yadda ka yafe min ka dawo dani gare ka, ka tausaya ka dawo da Hamma Ɓaleri don shi ma na tabba bai aikata abun......."

Hannun da Babiyon ya ɗaga masa ne ya saka shi yin tsit ba tare da ya ƙarisa maganar da ya soma ba.

"Ka tashi ka je. Ban so ka ƙara kawo min maganar ɗan uwanka a gabana!"

"In sha Allah!" faɗin Belɗo yana kallon tiles idanunsa cike da hawaye.

"Ka je sai na neme ka" faɗin Babiyo yanaa mai lumshe idanu.

Miƙewa ya yi tare da faɗin, "Na barka lafiya, Baffa."

Gyaɗa kai kawai Babiyo ya yi tare da ɗaga masa hannu idanunsa a rufe yana wani tunani a zuciyarsa.

Bayan magrib su baffa Jibrila suka dawo daga Kaduna. Da kyakkyawar sakamako suka je wa Babiyo na irin tarbar mutuncin da akai masu, sannan kuma an saka bikin Sati biyu masu zuwa wanda ya yi daidai da ranar da shugaban ƙasa zai fitar da sunan wanda zai kasance Ministern Abuja. Kuma sunan mutane biyu ne a hannun shugaban ƙasan, a ciki shugaban zai tantance guda ɗaya.

#Babiyo #Mamiyo #Ɓaleri #Belɗo #Abdul-Hameed #The wedding #Up comimg Minister #My Destiny #Matat Sayyadee *** [8/10, 4:18 PM] ***: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)

*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee

☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`