Page 53
*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***
Domin shiga comment section kuma ki danna wannan link ɗin👇🏼 *** *_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining link ɗin da ke sama domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜
_*💃🏻💃🏻 _Kuna ina 'yan uwana matar aure da 'yan mata? Shela nake ko wacce ta fito domin kuwa yau na zo maku da albishiri! Kun san matar Sayyadee ta ku ce ba ta samun abun ƙaruwa ta yi shuru domin ta ƙaru ita kaɗai._💃🏻💃🏻
💐💐🌼🌼_Magana ake ta ƙamshi. Toohwa! Mai ya hwaru?_ 🤔 🌷🌷🌸💮
*To maza ku marmatso ga sirrin nan. Shahararriyar nan wacce ke inganta soyayya tsakanin ma'aura wato Fatima Zaransalaty inkiya Queen Zarah ce ta taho mana da wani ƙamshim domin cika hancinar mazajemu da ƙamshi*. _INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_ _TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA KUJI 💃🏻
_Zaran Salaaty ta yi tafiya miƙaƙƙa har Sudan domin farnata ranmu da na mazajenmu ta kawo mana Sudanese perfume👌🏻 wanda idan har kika shafa shi a jikinki ko kin yi wanka ƙamshin bai barin jikinki. Tested and Trusted ƴaruwa. Zaransalaty ba iya sudanese perfume ta kawo maku ba, akwai kayayyaki masu matuƙar inganci na gyaran HQ (kun san dai ba a wasa da headquarter) akwai kayan gyararrakin jiki kala-kala na ƴan mata da matan aure. Sannan Zaransalaty tana sai da Decoration na kayan ɗaki iri-iri wanda baki taɓa ganinsu._
_KAR IN CIKA KI DA SURUTU, KE DAI NEMI ZARANSALATY A NUMBERS ƊINTA KAMAR HAKAA_: *** Or ****
*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_nfection_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_
_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ ***** *****
Cike da farinciki Babiyo ya ɗaga waya ya kira Abdul-Hameed da fita ta zame masa tamkar ana yankan naman jikinsa. Tunda Nenne ta yi masa wannan furucin a kan Zeenah ya jj gama ɗaya duniyar ta daina masa daɗi. Abinci ya zama abokin gabansa, fara'a kuma ta zama maƙiyiyarsa. Hatta iyayan nasa sum dai na ganin walwala a fuskansa, kulluma dai yana zuwa gaishe su da safe da kuma dare, bayan nan babu abunda ke kai shi falon.
Tun abun bai damun Nenne har ya soma taɓa ta. Don sosai take jin ɗan nata cikin zuciyarta. Sai dai ta yi alƙawarin ba za ta taɓa faɗa masa ta janye maganar da ta yi wancen lokacin ba har sai an ɗaura aurensa da Asma'u tukun. Duk da tun a ranar da ta yi wannan furuci Baffa Belɗo ya gwada mata ɓacin rai sosai tare da nuna mata illar harshe uwa a kan 'ya'ya, sannan kuma ya bata umarnin janyewa. Take kuwa ta janye sai dai ta roƙi alfarmar kar ya sanar da Abdul-Hameed ɗin har sai an ɗaura masa aure gudun samun matsala daga wajen Babiyo.
Ringing ɗin wayarsa ce ta dawo da shi cikin hayyacinsa kasancewar ya faɗa dogon tunani akan rayuwar da su ka yi da Zee-meed ɗinsa, sannan gefe guda kuma yana tunanin mai ya sa ya mance da ita tsayin shekaru haka, kuma mai yasa ita ma bata ne me shi ba.
Kallon wayar da ta kusa katsewa ya yi tare da ɗan sakin siririn tsaki sannan ya ɗaga wayar ya kara a kunne tare da yin cikakkiyar sallama cike da rashin fara'a.
"Our up coming young minister! Ya na ji muryarka tamkar baka cikin farinciki? Wa ya taɓo mana Ministern mu na gobe ne wai?" Babiyo ya faɗi cike da barkwanci wanda a cikin kafatanin jikokin nasa da Abdul-Hameed kawai ya ke wasan jika da kaka. Don sauran jikokin nasa tamkar yanda ya ke wa 'ya'yansa haka ya ke musu. Shiyasa ko da wasa ba su taɓa gigin jansa da wasan jika da kaka ba don ba su ga fuska ba. Ko shi kansa Abdul-Hameed ɗin ba ko da yaushe ya ke wasan da shi ba, kuma ko da zai yi sai sun kasance su kaɗai ne a wajen.
Shuru Abdul-Hameed ya yi ba tare da ya bashi amsa tambayansa ba, sai dai duk suna sauraren juna.
Bayan shuru ya ɗan ratsa, sai Babiyo ya ce, "Ka zo gida ina neman ka!" yana gama faɗin haka ƙit ya kashe wayar.
Ba don ya so ba ya miƙe daga kan gadon daga shi sai gajeran wando, farar jallaniya kawai ya zura tare da kifa hula shafa ka ji hadisi sannan ya zura takalmi ya ɗau wayarsa ya saka a aljihu sannan ya fito daga ɗakin. Kiciɓis su ka yi da Baffansa shi ma zai fita.
Murmushi Baffa Belɗo ya yi ganin fuskan Abdul-Hameed ɗin kicin-kicin tamkar zai fashe. Da hannu ya yafito shi bayan ya ɗan kalli bayansa kaɗan. Ƙarisawa inda ya ke Abdul-Hameed ɗin ya yi tare da ɗan risinawa ya gaida shi. Maimakon Baffa ya amsa, sai ya riƙo hannunsa tare da soma magana ƙasa-ƙasa.
"Tuntuni na ke faɗa maka ka kwantar da hankalinka Lover boy. Nennenka fa ta riga ta janye maganarnan tuntuni. Munƙi faɗa maka ne sabod ba ma son ka botsare mana ka jama fushin Babiyo. Bari ma in kunna maka recording ɗin ka ji domin ka tabbayar."
"Uhh-uhhm!" Nenne da ke bayansu ta yi gyaran murya don tun da Baffa ya soma magana ƙasa-ƙasa ta leƙo daga kitchen ta tsaya a bayan labule.
"Yauwa kana ji ko yaron kirki, yanda ka yi ɗin shine daidai! To menene amfanin rashin bin maganaar iyaye? Sam bai da amfani." faɗin Baffa cike da borin kunya. Can kuma ya ce, "Yauwa Nenne, kin gan shi nan zuwa ya yi yana bani baki harda 'yar ƙwallarsa wai na raka shi yaje ya baki haƙuri shi ya amince zai bi umarninki." ya ƙarisa maganaar yanaa kallon Abdul-Hameed tare da kyafta masa idanu.
Shikuwa Abdul-Hameed sai ƙumshe dariya ya ke yi yana jin wami mugun farinciki na ziyartarsa.
"Kunna masa recording ɗin" Nenne ta faɗi tana ɗan ɗaure fuska duk da a bayyane ya ke itama dariyar ne ke son kufce mata.
Aiko kamar an kunna Abdul-Hameed da remote ya fashe da dariya har yanaa riƙe ciki ganin yadda Baffan nasa ya yi tsuru-tsuru.
"Haka muka yi da kai ko? Hakaa mu ka yi ko?" Nenne ta faɗi tana nuna Baffa da Ludayin da ke hannunta.
"Zo ko ji mana Nannenaaaa!" ya faɗi shima yana dariyar.
"Ban ƙara sirri da kai!" Nenne ta faɗi tana dariya tare da komawa kitchen Baffa ya bi bayanta.
Abdul-Hameed kuwa ficewa ya yi yana jin wani relief a cikin zuciyarsa. Wayarsa ce ta yi ƙara, hannu ya saka ya fiddo bayan ya zauna a cikin mota. Ganin mai kiransa ya yi saurin ɗagawa tare da karawa a kunne, "Ango! Ango!! Ango!!! Mutanen Denmark. An samu duniya an mance da Hamma Hameed ko?"
Daga can ɓangaren Jawaad ya ce, "Daɗina da kai tsinannan son girma. Duka duka watanni ne tsakanin mu?"
"Ko da ina fitowa ka fito na dai riga ka shan iskan duniya kuma dole a cewa mijin Iya baba!"
Hararar wayar Jawaad ya yi tare da faɗin, "Ka dai ji da shi. To ya mutanan Naija?"
"To Alhamdulillah, ga su nan!" ya bashi amsa.
"Ɗazu Babiyo ya kirani wai nan da six months zan dawo Nigeria. Ni wallahi ban san inda wannan tsohon ya dosa ba. Ya kawo ni cikin tsinannu ya aje, ni babu wani abu abunda na ke tsinanawa sai kwanciya from edge to edge ɗin gado."
Wata muguwar dariya Abdul-Hameed ya kwashe da ita har da buga steri sannan ya ce, "Lallai sai yanzu na fahimci wannan tsohon yasin! Honeymoon ya tura ku domin ɓarje amarcin ku. Ka ga yanzu ya kira ya ce maka za ku dawo nan da six months, ka ga idan an haɗa da one month ɗin da kuka ci ya kama exactly 7months kenan. Tsoho na nufin ka tabbatar ka yi noma da kyau domin idan kun dawo ya ga amfanin gona ya fito har ya fidda iri girbi kawai ya ke jira."
Rintse idanu Jawaad ya yi yana dariyar shima sosai kamun ya ce, "Aikuwa ba lusarin jika ya ke da shi ba, in sha Allah da tsabar twins za mu duro ƙasar Nigeria!"
"Ɗan iska abokina! Ka ce ka kashe bosss!" sai da ya ja S ɗin wajen faɗin Boss ɗin.
Ƙit Jawaad ya kashe wayar yana dariya saboda fitowar Khairat daga bathroom ɗaure da towel kasancewar su dare ne a can ƙasar Denmark.
Hannu ya miƙa mata tare da faɗin, "Taho nan kiji 'yar ƙanwata kuma matata sanyin idaniyataaa!"
Maƙe kafaɗa ta yi tare da faɗin, "Naƙi wayan, ka bari in shirya na je na dubo aunty Zeenah sannan na dawo."
Komawa ya yi ya kwanta yana kallonta ƙasasa, "Gaskiya familynmu ba dai kyau ba. Idan ana maganar kyau aka shigo Arɗo Barkinɗo an zo last bus stop!" ya faɗi cikin zuciyarsa yana ƙara kallon tsantsan kyawunta.
Sai da ta gama shiryawa kaf ta saka kayan bacci tare da ɗaura after dress a kai sannan ta juyo ta kallesa tare da faɗin, "Hamma bari na je na dawo."
Gyaɗa mata kai ya yi still yana kallon fuskanta da ta tsantsawa kwalliya. Murmushin jin daɗin yanda ya ke bin ta da kallo ta yi sannan ya fice daga ɗakin.
Kitchen ta fara zuwa ta haɗa mata coffe ɗin da kullum take yi mata tun da ta dawo gidan yau kusan sati biyu. Juyewa ta yi a wani kyakkyar mug sannan ta nufi ɗakin da Zeenat ɗin ta ƙwanƙwasa.
"Yes, come in!" Zeenat da ke zaune a tsakiyar gado riƙe da kai ta amsa.
Tura ƙofar ta yi ta shiga fuskan nanzzz nata ɗauke da murmushi. Ganinta riƙe da kai ta yi saurin aje mug ɗin a kan side drawer sannan ta ƙarisa kan gadon tare da faɗin, "Aunty Zee lafiya? Kan ne? Ko in kira Hamma Jawaad mu je asibiti?" ta jero mata tambayoyin tana tattaɓa jikinta.
Girgiza kai Zeenat ta yi tare da faɗin, "Ba wani ciwo ya ke mun ba, kawai duum haka yake min. Na ji ƙamshin coffee, yana ina?" Zeenat ta faɗi bayan ta cire hannu a kai.
Sauka Khairat ta yi tare da ɗauko Mug ɗin ta miƙa mata. Amsa ta shiga sipping a hankali don sosai cappucino ɗin ya ke mata daɗi tare da jin kamar ta san taste ɗinsa amma ta kasa tuna yaushe, kuma a ina ta taɓa sha.
"Kin tabbata babu komai zan iya tafiya?" Khairat ta faɗi cus she's eager to go back to her husband.
Jinjina kai Zeenat ta yi tare da faɗin, "Alhamdulillah, ki tafi abunki wajen mijinki.
Dariya Khairat ta yi tana ɗan sosa kai alamar kunya. Ita kuwa Laushi bata san ma Khairat ɗin na yi ba don ta faɗa tunanin da ita kanta bata san ko na menene ba.
"Sai da safe, Allah ya ƙara miki lafiya!" Khairat ta faɗi tana mai sauka daga kan gadon ta fice tare da rufo mata ƙofa.
"Har kin dawo?" Jawaad ya faɗi yana tsane jikinsa kasancewar shi ma yanzu ya fito daga wanka.
"Eh, na je na same ta riƙe da kanta kum......." cak ta tsayar da abunda take shirin faɗa ganin wani irin zabura da Jawaad ya yi daga kawai ta ce masa Zeenah na riƙe da kanta. Zuba masa idanu ta yi don haka kawai ta ji wani abu ya soki zuciyarta ganin yanda ya nuna damuwa da firgici a kan wata macen da ba komai tasa ba. Ita sai yanzu ma wani abu ya zo mata a rai na rashin tambayarsa ita Zeenar wacece kuma menene alaƙarsa da ita, ina iyayanta kuma ya akai ya kawo ta ƙasar.
Ganin irin kallon da ya ke mata ya saka ya yi saurin saisaita kansa tare da faɗin, "kumburin raunanniyar jijiyar jinin ƙwaƙwalwa ta ke ɗauke da shi, kuma kumburin ya fashe wanda ya saka akai mata aiki ta cikin jijiyar jinin ƙwaƙwalwar wanda hakan ya yi sanadiyar ta mance duk wani abu da ya faru da ita a baya, to kuma sam masu irin wannan cutar ba a so suna ciwon kai shiyasa ki ka ga na razana.
Jikinta ne ya yi sanyi da jin bayanin da ya yi mata. Hakan ya saka ta ɗanji kumallon na mu na matan da ya ɗan motsa mata ya lafa. Sai cewa ta yi, "Allah sarki! Allah ya ba ta lafiya. Amma don Allah Hamma wacece ita?"
Ɗan jimm ya yi kamun ya zauna a bakin gadon ya kamo hannunta sannan ya soma faɗin, "Matar wani abokina, iyayanta ba sa son sa da ita amma ita kuma ta nace sai shi, hakan ya sa suka fiddo mata miji suka saka ranar aure. Ita kuma ana gab da auren ta gudu suka haɗu da shi abokin nawa kamar yanda suka tsara ita da shi suka gudu su kai aure. Sai dai kuma ko wata uku ba su yi da aure ba wannan cuta ta bayyana a jikinta, haka su kai ta wahalar zuwa asibitoci har abun ya lafa. Suna cikin wata shidan aurensu aka tura shi somalia kasancewar shi soja ne, to ina faɗa miki dawowar da har yanzu bai yi ba kenan, shi ba a ga gawarsa ba, shi kuma bai nemi kowa ba. Yanzu dai ba a san ko yana mace ko a raye ba. Hakane ya tada hankalinta har cutar ta dawo sabuwa, gashi ni kaɗai ta sani a abokansa. Ko iyayansa bata sani ba don asalinsa ɗan Ghana ne. Sai kula da ita gaba ɗaya ta dawo kaina, gashi kuma Babiyo ya turo ni nan ƙasar, hakan ya saka ita ma na yi mata Visa muka taho nan tare na kaina asibiti don ko da muka zo nan ɗin bata san wa ke kanta ba. Sanadiyar aikin da aka mata ya saka ta mance komai na rayuwarta. Kuma dama burina shine idan ta samu lafiya na miƙa ta ga danginta bayan na masu bayanim komai tare da, ba su hakuri. To kuma ga shi ta samu memory lost, kuma wallahi ni ban san kowa nata ba, ko sunan garinsu ban sani ba. Hakan ne ya saka na roƙi alfarmar ki a kan ta ɗan zauna da mu a nan kaun ta warke mu san abun yi." ( Shafi'uuuuu! Gaskiya Jawaad ka iya zubo ta🤔😂 Caɓ! Ashe haka ka iya zubabo shaharamansin haka?)
Sosai tausayi ya lulluɓe Khairat har da hawayenta ka mun ta furta, "A gaskiya Hamma abokinka sam bai kyauta ba kuma bai yi amfani da ƙwaƙwalwa ba. Menene amfanin ɗauke 'ya a gaban iyayenta ya gudu da ita ya aurenta? Yanzu fisabilillah kalli yanda komai ya kwaɓe! Har na ji tsoron a ce iyayanta irin Babiyo ne. Wannan abunda ya same ta ma Allah zan iya cewa alhakin iyayanta ne don bata musu adalci ba sam. Kuma sun yi hanzari ne, don tunda har su kai aure yanzu, da sun haƙura sun duƙufa addu'a wallahi sai Allah ya yayyafawa iyayan nan salama sun amince don an riga an rubuta ita ɗin matarsa ce. Amma tunda komai ya riga ya faru sai a tari gaba kuma a yi ta addu'a. Allah ya bata lafiya, shi kuma idan bai mutu ba Allah ya bayyanar da shi, idan kuma ya mutu Allah ya gafarta masa."
Da ameen ya amsa, amma can cikin zuciyarsa wata irin kunyar ƙarya da ya shafto ya ke ji, don shi kansa mamakin irin ƙaryar da ya yi ya ke don ya san komin daren daɗewa gaskiya za tai halinta. A wannan lokacin ne kuma har ga Allah bai san da wani idanu zai kalli Khairat ɗin ba. Don ya san mutuncinsa zai zuɓe a idanunta, uwa uba kuma auren Zeenat ɗin da shine burinsa. Ji ya yi gaba ɗaya jikinsa ya yi sanyi.
Ita ta taimaka masa ya idasa shiryawa sannan su kai raka'a biyun da suke yi ko wani dare kamun kwanciya bacci sannan suka kwanta.
Ya na jin saukar numfashin Khairat a kan hannunsa da ke nuni da ta jima da yin bacci, shi kuwa abun duniya duk ya dame shi ya ma kasa bacci. A hankali ya lalubi wayarsa ya duba agogo. Ƙarfe biyu da mintuna arba'in ya gani, a hankali ya sauke kan Khairat da ke kwance a kan cinyar hannunsa sannan ya sauka a kan gadon cikin sanɗa gudun kar ta ji motsi ta farka.
Haka ya dunga sanɗa har ya isa ƙofar ɗaki ya murza key a hankali ya buɗe sannan ya rufo a hankali ta yadda ba zai yi ƙara ba. Kai tsaye ɗakin Laushi ya nufa don tun da Khairat ta faɗa masa ta riƙe kanta ya kasa sukuni ya na son duba ta amma bai son Khairta ɗin ta zarge shi ko kuma ya sosa ranta don fisabilillahi tana da wani irin matsayi da ƙima a zuciyarsa.
Addu'a ya yi sannan ya murɗa kofar, aikuwa ya taki sa'a a buɗe take sai dai ɗakin mamaye ya ke da duhu. Fitilar wayarsa ya kunna don ya,san yana kunna na ɗakin za ta farka. Can tsakiyar gado ya hangeta ta duƙunƙune waje ɗaya tana bacci kuma ga dukkan alamu bata jima da yin barcin ba.
Ya fi ƙarfi mintuna goma yana kallonta kamun ya ƙarisa ta gefen da take ya kai hannu saman goshinta, jinsa rauu ya saka ya maida hannu zuwa wuyansa. Motsi ta yi wanda ya saka ya yi saurin janye hannu tare da rufe hasken wayan da tafin hannunsa.
Bayan mintuna biyu ya ƙara haskawa ya kuma taɓa wuyanta, rauu shima ya ke. Hakan ya sa ya fahimci akwai zazzaɓi a jikinsa. Bargo ya ja mata sannan ya kashe AC sannan ya tofa mata addu'a tare da fita ya jawo mata ƙofar ransa a jagule sabida zazzaɓin da ya taras tana fama da shi kuma mai zafi.
Da sanɗan ya kuma komawa ɗaki ya rufe ƙofar a hankali sannan ya hau gadon tare da gyarawa Khairat kwanciya ya mayar da kan nata a kan cinyar hannunsa sannan ya lumshe idanu ba don yana jin bacci ba.
_NIGERIA_ Tada motar ya yi tare da reverse ya bar gidan domin amsa kiran Babiyo. Tafiya ya ke yana jin nishaɗi don har waƙa ya kunna ta Celine Dion _Titanic_ ya na kamar haka;
Every night in my dreams I see you, I feel you That is how I know you go on Far across the distance And spaces between us You have come to show you go on Near, far, wherever you are I believe that the heart does go on Once more, you open the door And you're here in my heart And my heart will go on and on Love can touch us one time And last for a lifetime And never let go 'til we're gone Love was when I loved you One true time I'd hold to In my life, we'll always go on Near, far, wherever you are I believe that the heart does go on (why does the heart go on?) Once more, you open the door And you're here in my heart And my heart will go on and on You're here, there's nothing I fear And I know that my heart will go on We'll stay forever this way You are safe in my heart and My heart will go on and on.
A farfajiyar gidan Babiyo ya yi parking sannan ya buɗe murfin motar ya fito ya nufi cikin gidan.
(Kai mu haɗe gobe kawai🙄 yau typing ɗin a gantale na yi sa. Wata ta tura ni ta bayaa na faɗa kan katifa na dumuimuyi laushi 🥱)
#Jawaad #Khairat #Zeenah #Abdul-Hameed #Babiyo #Mamiyo #My destinye #Matar Sayyadr #Gantalewa 😂 *** [8/10, 4:18 PM] ***: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)
*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee
☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`