My Destiny (Ƙaddarata)

Page 54

by @matarsayyadee3

*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***

Domin shiga comment section kuma ki danna wannan link ɗin👇🏼 *** *_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining link ɗin da ke sama domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜

_*💃🏻💃🏻 _Kuna ina 'yan uwana matar aure da 'yan mata? Shela nake ko wacce ta fito domin kuwa yau na zo maku da albishiri! Kun san matar Sayyadee ta ku ce ba ta samun abun ƙaruwa ta yi shuru domin ta ƙaru ita kaɗai._💃🏻💃🏻

💐💐🌼🌼_Magana ake ta ƙamshi. Toohwa! Mai ya hwaru?_ 🤔 🌷🌷🌸💮

*To maza ku marmatso ga sirrin nan. Shahararriyar nan wacce ke inganta soyayya tsakanin ma'aura wato Fatima Zaransalaty inkiya Queen Zarah ce ta taho mana da wani ƙamshim domin cika hancinar mazajemu da ƙamshi*. _INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_ _TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA KUJI 💃🏻

_Zaran Salaaty ta yi tafiya miƙaƙƙa har Sudan domin farnata ranmu da na mazajenmu ta kawo mana Sudanese perfume👌🏻 wanda idan har kika shafa shi a jikinki ko kin yi wanka ƙamshin bai barin jikinki. Tested and Trusted ƴaruwa. Zaransalaty ba iya sudanese perfume ta kawo maku ba, akwai kayayyaki masu matuƙar inganci na gyaran HQ (kun san dai ba a wasa da headquarter) akwai kayan gyararrakin jiki kala-kala na ƴan mata da matan aure. Sannan Zaransalaty tana sai da Decoration na kayan ɗaki iri-iri wanda baki taɓa ganinsu._

_KAR IN CIKA KI DA SURUTU, KE DAI NEMI ZARANSALATY A NUMBERS ƊINTA KAMAR HAKAA_: *** Or ****

*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_nfection_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_

_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ ***** *****

A kujerarasa ta gado ya same sa zaune fuskansa sanye da glasses ya na duba abu a waya. Jin sallamar Abdul-Hameed ɗin ne ya saka shi aje wayar tare amsa masa sallamar ya na murmushi.

Zama a ƙasa daidai wajen ƙafafun Babiyon ya yi bayan ya gaida shi. Amsa gaisuwar ya yi tare da shafa kansa sannan ya furta, "Ka sauko kenan?"

Murmushi Abdul-Hameed ya yi tare da faɗin, "Da ma ban hau ba."

"Ja'iri! Na san murmushin nan duk na farinciki ne ko?" Babiyo ya faɗi.

Gyaɗa kai ya yi yana ƙara faɗaɗa murmushin kan fuskar nasa.

"To a faɗa min mana, farincikin mai ake haka? Ko dai har ka samu labarin kuɗin aurenka da aka kai ne? To dai ya kamata ka ban tukuicin don ni ne sila!"

Ɗan taɓe baki Abdul-Hameed ya yi don shi sai yanzu ma ya ke ji a bakinsa. Amma kuma sai ya kalli Babiyon tare da gyaɗa masa kai don ya faranta masa.

Duka Babiyon ya ɗan kai masa a bayansa tare da faɗin, "Ja'iri! Allah dai ya maka albarka. Nan da kwanaki goma sha uku ka zama ango kuma ministern mu, In sha Allah."

Ɗaga kai Abdul-Hameed ya yi ya kalli Babiyon tare da faɗin, "Ina neman wata alfarma a wajenka, amma idan har ka ce baka yarda ba na haƙura (ya faɗi hakane domin samun yardar Babiyon ba kuma don zai haƙura ba idan Babiyon ya ƙi.)"

Gyara zama Babiyo ya yi tare da faɗin, "Ina jin ka, young Minister."

Ɗan jima Abdul-Hameed ya yi tare da faɗin, "Kamun ka zaɓa min mata, akwai wacce muke soyayya da ita har mu kai alƙawarin aure. Amma jin ka zaɓar min mata ya saka na aje wancen maganar a gefe don na san ba za kai min zaɓin tumun dare ba, amma da ƙudurin bayan an ɗaura da wasu ɗan lokaci sai na gabatar maka da nawa zaɓin, amma sai da amincewarka."

"Ko 'yar gidan wacece ita na maka alƙawarin sai na cika maka burinka. Ai ƙara aure sunnah ma'aiki ce, kuma ni ba zan hana ka hakan ba. Allah ya zaɓa abunda ya fi alkhairi. Ka amshi zaɓina da hannu biyu b tare da ko sauya fuska ba, ni kuma son zuciyata ba zai bar ni na hana ka zaɓinka ba. Ka je kana cika shekara da aure ni kuma zan je da kaina wannan karon domin amso maka auren zaɓinka!" Babiyo ya faɗi har cikin ransa.

"Ka yi min alƙawari, Babiyo?" Abdul-Hameed ya faɗi yana riƙe hannun Babiyon.

"Na yi maka alƙawari Abdul-Hameed, kuma ka san Babiyo never go back on his words!"

"Ni shaida ne a kan haka. Nagode sosai kakana na kainaaaa! ya ƙarisa maganar yana rungume sa.

"Ya kamata ka je ka ga amaryar nan ta ka domin ku tattauna," Babiyo ya faɗi.

"In sha Allah, gobe nan zan je."

Ko da Abdul-Hameed ya koma gida, waya ya fiddo ya kira magajiyar karuwan da Zeenat ta fara zamaa a wajenta tare da yi mata tayin rabin miliyan idan har ta binciko masa gidan karuwan da Laushi ta ke zaune a garin Lagos.

Ita kuwa jin zunzurutun kuɗin sai ta ruɗe tare sa shaida masa ita kuma In sha Allah kamun cikar wata guda za ta yi duk iya yinta, idan ya kama ta tafi Lagos ɗin ma sai ta je domin bincike da kanta.

Washa gari ya shirya tsaf tare da escourt domin zuwa ganin amaryarsa. Tarba ta musamman ya samu daga mutanan gidan. Iyayan Asma'u sosai su ke da mutunci da karamci.

A katafaran falon mahaifin Asma'u aka sauke shi tare da cika masa gabansa da nau'ikan abinci kala-kala.

Asma'u kuwa tun da ta samu labarin zai zo ta tsantsara gayu na kece raini. Fara ce tass kuma kyakkyawa, ita ba doguwa bace kuma ba gajera ba. Sannan ba ta da wani jiki, siririya ce sosai tamkar za ta ɓalle. Sai dai kallo ɗaya za kai mata ka san ita ɗin ba mai haƙuri bace sam.

Sanye take ciki riga da skirt na atamfa wanda ya kuma taimakawa siritanta fitowa. A fuska dai akwai kyau, sai dai idan anzo maganar shape to fa zero ne.

Fuskanta sanye da google sai siririn mayafin da ta yafa a kafaɗa. Waya ne a kunnenta tana magana cikin harshen turanci cike da tsantsan kwarewa, masters gareta a fannin English and literature. Don yanzu haka ma ita lecturer ce a Kaduna state University tana karantar da English.

Tun tahowarta ya kalle ta sau ɗaya ya kawas da kai tare da taɓe baki. Don shi ko ta ina bata masa ba, kawai zai yi accepting ɗinta ne a matsayin ƙaddararsa.

Zama ta yi a kujeran da ke fuskantarsa tare da ɗaura ƙafa ɗaya a kan ɗaya still tana waya. Da idanu ya bi jan lallen da ke zane a ƙafanta yana tuno masa Zee-Meed ɗinsa kasancewar ita ma da wuya ka ga hannu da ƙafarta fari, musamman ƙumbunan hannunta kuma ba ƙaramin kyau suke mata ba. Hakan ce ta saka ya zubawa ƙafar tata idanu ta ƙasan ido har ta kammala waya.

"Sorry, I kept you waiting. So ya hanya, ya ka baro mutanan gidan? You haven't eaten, me yasa?"

Sai a lokacin ya ɗago ya kalle ta tare da ba ta amsa ɗaya cikin harshen Hausa, "Kowa na lafiya. Ya kike?"

"As you can see, I am perfectly fine!" ta ƙarisa maganar tana mai zuba masa idanu kasancewar ya mata masifar kyau, sai ta ga ya ma fi kyawu a zahiri akan hoton da aka nuna mata.

"From what I've heard from my parent, you're my future husband in the next coming 13days. Well it's ok by me, but I want you to......."

"Can you please speak to me in your mother tongue? Have heard enough at school. I mean the English spoken language!" ya faɗi a dake.

Ita kuwa ba wai maganar da ya yi bace ta sanƙarar da ita, irin salon da ya yi amfani da wajen yin turanci ne. Sai ta ji tamkar bature ne a gabanta ke yin turanci.

"Alright, by the way...."

"Hausa don Allah! Idan kuma kina jin fulfulde, bismillah nan ma na fi ƙwarewa." ya katse ta.

"Ok... Ok.. I'm sorr, ohh ya haƙuri please." ta faɗi tana ɗan dariya don turanci ya riga ya kama bakinta ta yadda ko da da ɗan ƙauyen-ƙayayau ta ke maganaa sai ta yi turancin nan. A Uni ɗalibanta da dama da Queen Elizabeth ko dictionary suke kiranta.

"Ni fa ina son da na yi wa mutum gyara sau ɗaya ya yi ƙoƙari ya shiga ƙwaƙwalwarsa, don a gare ni kuskure sau ɗaya ake yin sa, idan mutum ya ƙara kuma ya zama ganganci, so please take note!" ya ƙarisa maganar ya na kallonta fuskansa ba a tamke ba, kuma ba a sake ba. Ba dai yabo kuma babu fallasa.

Jinjina kai ta yi tare da faɗin, "Sunana Asma'u Sulaiman, 'ya ga tsohon gwamnar wannan jiha, kuma 'ya mace tilo a cikin gidannan and kuma the last born."

Girigza kai kawai ya yi don ya fahimci ba za ta taɓa iya magana ba ta saka turanci ba.

Cigabaa da magana ta yi, "Na yi primary and secondary ɗina a nan Jihar, sai kuma na tafi England na haɗa degree da masters ɗina a can. Yanzu haka ni seniour lecturer da ake ji da ita ne a Kaduna state university, and also the founder of Nigeria Cambridge Academy in here Kaduna state."

"Hakan na da kyau! Yanzu kin shirya zama house wife kenan?" ya jefa mata tambaya.

Wani murmushi ta saki tare da yin farr da idanu sannan ta furta, "Eh, tom! Amma ba irin wai zan zama kamar sauran matan auren da ka sani bane. Ko da yake na ganka wayayye na kai ma ba mai taushewa mace ra'ayi da haƙƙinta bane. Don gaskiya I can cook ko da yaushe da sauran house chores. Ka san dai wacece matar da za ka aura, well educated wacce za ta iya fitar da kai kunya a ko ina."

Miƙewa kawai ya yi yana duba agogan hannunsa tare da aje mata rafar 1k guda biyar a kan hannun kujeran da take zaune sannan ya ce, "If you need more, just give me a call. Take good care of your self Mss well Educated! Sai na kira ki." yana gama faɗin haka ya juya ya nufi ƙofa.

Da mamaki take ta kallonsa har ya fice, sai kuma ta yi saurin take masa baya har ta isa kusa dashi suka soma jerawa gudun zunɗen dangi da ƙawayenta da ta kikkira domin su ga kyakkyawan mijinta kuma mai jiran kujeran minister. Ta yi kuri da ƙarya kala-kala, don cewa ta yi a UK suka haɗu ya gwada yana sonta ita kuma sai yawo da hankali take masa, don da kyar ta bashi digits ɗinta don sai da ya yi ƙwalla tukun.

Hira ta dunga jansa da shi, shi kuwa daga um si um-um har suka isa wajenconvoy ɗinsa don ko sallama da mahaifinta bai yi ba.

Ko da ta koma ciki sai ta liliyo ƙarya ta antaya wai kiran gaggawa ya samu daga Villa shiyasa ya tafi babu shiri tare da baje masu kuɗin da ya ajiye mata wai ta sakaa kati sannan kuma ta nuna masu wani ATM wai shi ya ba ta ta soma yin duk wani hidimar bikin, idan kuma sun ƙare ta yi masa magana.

Aikuwa duk suka ruɗe don sun yarda ɗari-bisa-ɗari da ƙaryar kasancewar sun san ko su wanene familyn Arɗo Barkinɗo. Kaf Nigeria ma babu wanda bai san su ba (tamkar dai yanda jama'a suka san Ɗangotte yanzu🤣).

Cikin daren nan kamar yanda Ɓaleri ya yi alƙawari sai ga shi cikin Arɗo Barkinɗo suka haɗu da Hafiz a keɓantaccen waje ya ba shi document ɗin da ya ɗauko a motar Baffa Jibrila.

"Kar ka ɗauka zan yaba maka, sam! Babu yabo tsakanina da kai, maciyi amana! Kuma ka sani ka gama min aiki za ka amshi sakamakonka daidai gwargwadon abunda ka aikata tsawon shekaru a cikin gidannan. Daga ciki har da bayanin yadda kuka kashe mahaifiyata kai dai ɗayar azzaluman. Kwanaki na ƙara ja, ina jiran takardun kamfanin mahaifina."

Ɓaleri na gama faɗin haka ya juya ya bar Hafiz a tsaye tamkar gunki. Tashin hankali ya gama dabaibaye shi. Don jikinsa wani irin kakkarwa ya shiga yi yana tsiyayar da zufa ta ko ina a jikinsa. (Tabɗijam! Haaafizuuuu😲 bari dai na yi 🤐)

#Mss Educated #Abdul-Hameed #Hafizu #Ɓaleri #Mamiyo #Babiyo #My Destiny #Matar Sayyadee *** [8/10, 4:18 PM] ***: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)

*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee

☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`