Page 55
*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***
Domin shiga comment section kuma ki danna wannan link ɗin👇🏼 *** *_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining link ɗin da ke sama domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜
_*💃🏻💃🏻 _Kuna ina 'yan uwana matar aure da 'yan mata? Shela nake ko wacce ta fito domin kuwa yau na zo maku da albishiri! Kun san matar Sayyadee ta ku ce ba ta samun abun ƙaruwa ta yi shuru domin ta ƙaru ita kaɗai._💃🏻💃🏻
💐💐🌼🌼_Magana ake ta ƙamshi. Toohwa! Mai ya hwaru?_ 🤔 🌷🌷🌸💮
*To maza ku marmatso ga sirrin nan. Shahararriyar nan wacce ke inganta soyayya tsakanin ma'aura wato Fatima Zaransalaty inkiya Queen Zarah ce ta taho mana da wani ƙamshim domin cika hancinar mazajemu da ƙamshi*. _INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_ _TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA KUJI 💃🏻
_Zaran Salaaty ta yi tafiya miƙaƙƙa har Sudan domin farnata ranmu da na mazajenmu ta kawo mana Sudanese perfume👌🏻 wanda idan har kika shafa shi a jikinki ko kin yi wanka ƙamshin bai barin jikinki. Tested and Trusted ƴaruwa. Zaransalaty ba iya sudanese perfume ta kawo maku ba, akwai kayayyaki masu matuƙar inganci na gyaran HQ (kun san dai ba a wasa da headquarter) akwai kayan gyararrakin jiki kala-kala na ƴan mata da matan aure. Sannan Zaransalaty tana sai da Decoration na kayan ɗaki iri-iri wanda baki taɓa ganinsu._
_KAR IN CIKA KI DA SURUTU, KE DAI NEMI ZARANSALATY A NUMBERS ƊINTA KAMAR HAKAA_: *** Or ****
*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_nfection_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_
_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ ***** *****
Jin da ya yi ƙafafunsa na neman kada shi sai ya yi saurin dafe mota ya kai ƙasa tare da tsugunawa ya riƙe kai. Can kuma ya fashe da wani matsanaicin kuka har jikinsa na kakkarwar tashin hankali sannan kuma haƙoransa na haɗuwa da juna tamkar wanda ke zaune cikin dusar ƙanƙara.
Ya fi ƙarfi mintuna talatin a duƙe har sai da cinyoyinsa suka sage kamun ya miƙe ya na mai dafa motar ya buɗe ya shiga sannan ya kuma haɗe kai da steri hawaye na cigaba da masa ambaliya.
Ɗin-ɗin! Karar shigowar saƙo ya shigo wayarsa har sai da ya wani zabura kamar wanda ya ga abun tsoro. Kamar wawa haka ya riƙa kallon gaban aljihun nasa kamun ya kai hannu ya zaro wayar. Ganin number Ɓaleri sai da hantar cikinsa ya kaɗa don har wani zawo-zawo ya ji yana son kufce masa.
_Idan ka yi kuskuran barin Arɗo Barkinɗo Estate domin samun makafa, to ka sani gunduwa-gunduwa zan yi da namar jikinka domin idanuwana na a duk inda ka ke kai da iyalanka! Kuma ka yi ƙoƙarin ɗauko min takardar kamfani kamun cikar wa'adi._
"Ni Hafizu yau na shiga tara na lalace! Menene wannan kuma hakaa? Wani bala'i ne wannan ke tunkaro ni? Anya ba zan tafi kai tsaye wajen Arɗo na warware masa komai da na sani ba kuwa?"
"Kana hauka ne Hafizu? Idan Ɓaleri gunduwa-gunduwa zai yi da kai, shi Babiyo markaɗeka zai yi da ranka!" wata zuciyar ta faɗa masa haka. Sai kawai ya ɗaura hannu a kai ya rusa ihu. Allah ya so inda ya ke shi ɗaya ne kuma cikin mota a kulle da babu abunda zai hana mutane jiyo muryansa.
Ɓangaren Abdul-Hameed kuwa, ji ya yi tamkar ya ɗauki hanyar Bauchi domin ji daga magajiya ko ta samu wani makama, amma ya danne zuciyarsa ya taho Abuja kai tsaye.
Gidansu ya wuce kai tsaye ya yi parking a harabar gidan sannan ya fito ya shiga ciki. Knocking ya yi sannan ya murɗa handle ya shiga. Babu kowa a parlour sai dai ya ji motsi a kitchen. Ramadan ne ya fito hannunsa riƙe da plate ɗin abinci ya na ci daga tsaye.
"Welcome back up coming Minister!" Ramadan ya faɗi ya na kai spoon ɗin abinci baki.
"A tsaye? Babu manner a wannan cin abinci naka, your better get a seat and sitdown." ya faɗi shima ya zama a ɗaya daga cikin kujerun falo tare da cire takalminsa sau ciki yana ƙoƙarin zare socks ɗin ƙafarsa.
Zama Ramadan ya yi kusa da shi tare da faɗin, "Na zauna to."
"Better!" Abdul-Hameed ya faɗi yana zare ɗayan socks din ƙafar hagu.
"Shine ko ka min magana in raka ka domin na riga ganin kowa na gidan nan amaryar taka." Ramadan ya faɗi.
Maimakon Abdul-Hameed ya ba shi amsa sai cewa ya yi, "Ina Nenne?"
"Tana gidan Mama Halima" ya bashi amsa yana kuma kai spoon baki.
"Ok!" ya faɗi a taƙaice tare da tattara safuna da takalmarsa ya nufi hanyar ɗakinsa.
Da kallo Ramadan ya bisa ya na dariya don ya san sam ɗan uwan nasa bai ƙaunar wannan aure da Babiyo ke sab ɗaura masa.
_GIDAN BAFFA GIƊAƊO_ "Wai Marwanat ce na ke gani a nan gidan ko kuwa idanuna ne? Mutanan Lagos, to ina Hamma Modibbon, ko tare kuka zo?" Nenne da shigowarta falon kenan ta faɗi haka.
Gaba ɗaya su Wasila suka nufi 'yar mahaifiyar tasu suka rungume suna mai jin daɗin ganinta. Ɗaya-bayan-ɗaya suka gaishe ta ta amsa cike da jin daɗin ganinsu suma.
Mayar da kallonta ta yi ga Marwanatu tare da sake faɗin, "Kin zo ziyara kenan, to ya mijin naki da yaranki?"
Maimakon Marwanat ta ba ta amsa sai ta taho da gudu ta rungumeta tare da fashewa da matsanaicin kukan da ya tada hankalin Nennen ta shiga tambayanta ko lafiya. Ganin ta ƙi bataa amsa sai ta kama hannunta suka nufi ɗakin Mama Halima.
Mama Halima kuwa jin kuka na tunkaro ɗakinta sai ta yi wuff ta miƙe ta yo waje, kiciɓis suka yi da Nenne da Marwanat ɗi da ke kuka.
"Kai jama'aaa! Wai Marwanatu ba na hana ki kukan nan ba? Shin kukan ne zai miki magani abunda ke damunki? Ki gode wa Allah ma da Babiyo bai tura ki Mayo-Belwa ba. Ke akwai wata mai laifin da ta samu gatanki ne a kaf cikin Arɗo Barkinɗo? Kin san wani hukunci Babiyo ya ke wa duk wanda ya yi yunƙurin yin kisan kai kuwa? Hmm thank God ga Nenne nan a gabanki, na san za ta baki tarihin gidan nan tunda ke haihuwa kuma rainon Lagos ce. Ba ki san komai game da gidan nan ba kuma ba ki san wanene Babiyo da abunda zai iya aikatawa ba. Tun jiya na ke baki baki amma kin ƙi saurarata. Ai sai ki je ki yi ta kukan!" faɗin Mama Halima tare da zabga tsoki ta juya ta shiga ɗaki ta cigaba da mayar da kayan da ta fiddo a cikin wardrobe.
Hannun Marwanatu Nenne ta kama tare da shiga ɗakin fuskanta ɗauke da wani irin tashin hankali ta furta, "Halima, wacece ta yi yunƙurin kisa? Ba dai Marwan ba ko?"
Ba tare da Mama Halima ta kalli Nenne ba ta furta, "Aikuwa ita! Ga ta nan sai ta miki bayanin abubuwan da suka faru a can Lagos ɗin."
Nenne mayar da kallonta ta yi izuwa ga Marwanat ta furta, "Ki ƙaryata kunnuwata yanzun nan! Ki faɗa min ba ki yi yunƙurin kashe kowa ba."
Ƙara sautin kuka Marwa ta yi tare da soma magana amma sai Nenne ta daka mata tsawa tare da faɗin, "Ki shanye kukan nan ki min magana ta yadda zan fahimci mai kike faɗa!"
Haɗiye kukan Marwanat ta yi tare da soma magana, "Nenne, Nura ne ya sake ni kuma ya ƙwace 'ya'yansa duka. Yanzu haka ma ya ƙara aure ance matar ma ta kusa haihuwa!" ta ƙarisa maganar muryanta na rawa kuma zuciyarta na mata suya.
"Nura ya sake ki! To akan me? Me kika masa har ya sake ki?" Nenne ta jeho mata tambayoyi tana jin ranta na ɓaci.
"Akan karuwarsa ya sake ni!" ta faɗi tana mai rushewa da kuka.
"Akan karuwa? Akan katuwa fa kika ce Marwantu! Da hankali da mutuncin Nuran ya yi hakan?" Nenne ta faɗi out of anger.
"Ke! Ki fito ki faɗa mata labarin gaskiya ki daina kwana-kwana." Mama Halima ta faɗi.
A tsawace Nenne ta furta, "Idan ita ba za ta faɗa min gaskiya ba, ke ki min bayani mana!"
Rufe wardrobe Maman Halima ta yi tare da zama a bakin gado sannan ta ce, "Kin ga wannan yarinyar da ke kusa da ke, wallahi a kan kishi zararriya ce, babu abunda wawuyar ƙwaƙwalwarta ba zai iya faɗa mata ta yi ba, kuma sai ta aikan za ta ji daɗi a zuciyarta. Ba kwanan tsawon shekaru shiyasa ba za ki san komai ba, infact ba kya nan a kai aurenta, rabonki da ita tun tana yarinya don bazan mata ba lokaci ɗaya aka haife su da Sa'adatu yar wajen Hafsatun Hamma Ɓaleri. To yarinyar nan lokacin da shi Nura ya fito domin aurenta dakyar Babiyo ya amince. Kin sansa da ƙin bare a cikin zuri'asa, amincewar da ya yi ma don ya yi bincike ne ya gano shi mahaifin Nuran haifaffen Yola ne kuma jinin fulani. Yaron nan Nura mu kam mu da ba gari ɗaya muke da su ba mun shaida irin ƙaunar da ya ke wa Marwanatu. Ita kuma da ta fahimci hakan sai ta yi amfani da hakan wajen muzguna masa. Ga tsinanmam kishin hauka. Sau shida tana lalata masa auren da ya ke shirin ƙarawa. Ance akwai wani auren da ya ke nema ta je ta faɗawa dangin yarinyar wai tana da ƙanjamau kuma wai Nuran ne ya saka mata. In taƙaice miki dai haka aka fasa wannan aure. Shi kuma ya gaji, ta hana shi aure kuma ta kasa ba shi farinciki a cikin gidansa. Shi kuma raunanniyar zuciyarsa ta jefa sa a cikin halakar neman mata. Shine yarinyar nan ta yi bincike ta gano yarinyar da ya ke neman ta kwashi ƙawaye suka tafi har gidan karuwai inda yarinyar ta ke su kai ta ɗiban albarka. To ni dai ban san yadda akai ba sai ji na yi ta soki mijin da wuƙa a ciki bayan zugan wawuyar yarta ta yi mata. An ce zage-zage su ka yi da yar tata da shi Nuran, san........"
"Wallahi Mama Halima ba haka ya faru ba! Duk wanda ya ba ki wannan labarin ƙarya ya ke yi!" faɗin Marwanatu.
Kif! ta kifa mata mari a baki tare da faɗin, "Inna Ƙarama (Karima matar Babiyo kuma mahaifiyar Baffa Modibbo) za ta miki ƙarya kenan?"
"Dakata! Dakata Halima!! Bar ta ta yi magana" faɗin Nenne tare da juyawa ta kalli Marwanat fuskan nan nata a tamke.
"Nenne a gaban idanuna ya kama hannun karuwa ya saka ta a mota ni kuma ya tura ni ga 'yan sanda. 'Yar sandar nan har ta saka min ankwa, ko mai ya gani sai ya ce ta kyale ni. Allah Nenne da kyar ya bar ni na shiga cikin motar nan kuma a gidan baya, ita karuwar tasa a gaban mota sai lallashinta ya ke har da cewa ta faɗi asibitin da ta ke so ya kaita aduba kanta da na buga mata muciya yake tsiyayar jini. Ita kuma sai narkewa ta ke yi har da kwanciya a kafaɗunsa kuma duk a gabana ina cikin motar. Don Allah Nenne wace mace za ayi wa abunda Nura ya min ranta bai ɓaci ba?"
Girgiza kai Nenne ta yi tare da faɗin, "Idan har abunda kika faɗa hakane to tabbas da wuya a samu macen da za ta shanye. Amma garin yaya ke kika soki shi Nuran?"
"Kama ni ta yi da dambe bayan shi Nuran ya sauke ni a ƙofar gida wai na wuce ciki shi kuma zai juya kan mota ya kai ta asibiti, kuma a daidai wannan lokacin aunty Zubaida ta iso wajen ta taras da abunda ke faruwa shine ta hau yiwa Nura nasiha shi kuma sai ya hau zaginta. Ban ankara ba kawai na ji saukan duka daga ita Karuwan. Allah ya ba ni sa a na kaita ƙasa, shine Nuran ya shigar mata ya hau dukana. Ni kuma allah ya bani sa a na miƙe na yi cikin gida da gudu na ɗauko wuƙa na yi kanta, sai kawai Nura ya shiga tsakina na luma masa a ciki. Wallahi har ga Allah ba da gan-gan na soke sa ba!" ta ƙarisa maganar da kuka."
Haushin duka su biyun ne ya rufe Nenne. Na farko ita kanta Marwan na taka ƙafa da ta yi ta je gidan katuwai har wannan tsautsayin ya afku, na biyu kuma Nura da take ji tamkar ta gansa a gabanta ta yayyafa masa ruwan rashin mutunci. Sai kuma ta ukun ita kanta karuwar da nan take ta ji wata mummunar tsanarta ya soki zuciyarta.
"Ta shi ki koma falo zan ne me ki zuwa anjima kamun na bar gidan nan." Nenne ta faɗi.
Gyaɗa kai Marwanat ta yi tana ɗan jin sanyi a ranta. Ko ba komai yau dai mutun ɗaya ya goyi bayanta kuma bai ganin laifinta.
Bayan fitar Marwanat, Nenne ta kalli Mama Halima tare da faɗin, "Wallahi ta ban tausayi matuƙa. Duk da tana da na ta laifin amma laifin Nuran ya fi yawa. Haba! Ace mijinka ya wulaƙanta ka a gaban karuwa har da saki..... Ai wallahi ta ma yi haƙurin cigaba da zama da shi tun lokacin da ta fahimci yana biye-biyen matan banza. Amma ku na lura gaba ɗaya laifinta kuke gani a gaba ɗaya case ɗin, bayan babu babba ɗan iska irin shi Nuran da 'yar iskar karuwan nasa wacce iyayanta suka tsine mata. To tsinewa mana! Ai sai wacce ta gagara kuma ta ke yawo da tsinuwar iyaye za ta zauna a gidan bariki tana bin mazajen mutane. Allah dai ya wadaran na ka ya lalace!"
"Uhm! Allah dai ya shirya za ki ce Nenne, don 'ya'yan nan dai ga su nan muna da su cike da gida, kuma ka haife su ne ba ka haifi halinsu ba. Nan gashi nan Habibu shine silar da akai min kishiya da ƴar da na raina da hannuna, na ci kashi da fitsarinta don ba matsayin addanta take kallona ba sai uwa. Kuma wa ya ja min idan ba shi Habibun ba garin neme-nemen matansa." Mama Halima ta faɗi.
Waro idanu Nenne ta yi tare da faɗin, "Wanene ya sake auran, kuma wanene ke neme-nemen matan banzan?"
Murmushin takaici Mama Halima ta yi tare da faɗin, "Hmm! Baffansu Habib ne ya sake aure, kuma ba da ko wacce mace ba sai Mardiyya."
"Mardiyya? Mardiyya fa kika ce!" Nenne ta faɗi tare da dafe ƙirji tana zaro idanu.
Nan take komai ya dawo wa mama Halima sabo, ciwon da ya soma ɗan warkewa ya famu. Sai kawai ta fashe da kuka ta faɗa kan 'yar uwarta da itama ta soma hawayen tausayin 'yar uwar tata.
"Nenne ban san ko dan mu ba 'ya'yan cikin Babiyo bane shiyasa ya ke ƙuntata mata. Ko kuwa don ya ga mahaifinmu na matuƙar yi masa biyayya tamkar zai masa sujada ne oho! Wallahi ranar da aka ɗaura auren nan ba ki ga irin mugun wulaƙancin da Babiyo ya min ba a gaban Mardiyyan har yana faɗin ban da tarbiyya na kasa bawa Habib tarbiya shiyasa ya aura Hamma Gidaɗo Mardiyyan sabida ya amince da tarbiyanta kuma yana da yaƙinin za ta saita masa gidansa. Nenne ba ki ga yadda na muzanta ba. A ranar da ba dan Abdul-Hameed da ya taushe ni ba da na bar Arɗo Barkinɗo wallahi!"
Shuru Nenne kawai ta yi tana wani tunani a ranta, can kuma ta ce, "Shi Hamma Giɗaɗon ya canza miki?"
Girgiza kai Mama Halima ta yi tare da faɗin, "Ko kaɗan har ita Mardiyyan. Ko idanu ba ta iya haɗawa da ni, amma kullum sai ta shigo ta ce min Mama ko da abunda zan miki, sai in girgiza mata kai kawai."
Jinjina kai Nenne ta yi kamun ta riƙe mata hannu ta furta, "Ki cigaba da kwantar da hankalinki, in sha Allah komai zai yi daidai. Ni fa wallahi ina zargin Mamiyo sosai a cikin lamuran Babiyo!"
Wani kallo Mama Halima ta mata tare da faɗin, "Wai kina nufin sai yanzu kika fara zarginta? Ai wallahi ko koran da akai wa Hamma Ɓaleri da Hamma Belɗo ita ce silar komai."
"Na san da haka, kuma suma sun san da haka. Akwai wani sirri da na ke so na faɗa miki, don ko Baffansu Ramadan bai san na sani ba, kuma ke ma ina son ki riƙe a cikinki."
"In sha Allah Nenne, faɗa min mai ke faruwa?" mama Halima ta faɗi cike da zaƙuwa.
"Hamma Ɓaleri na zuwa nan cikin Arɗo Barkinɗo suna haɗuwa da baffansu Abdul-Hameed. Kuma wani babban abu suke shiryawa a kan Mamiyo har da su Hamma Jibrila. Na ji hakane a wani waya da suka yi da Hamma Ɓalerin lokacin zan shiga ɗakin na kai masa bottle water, jin maganar da suke yi ya saka na ɗan laɓe. Sai dai ba komai na fahimta ba."
(Nenneeeee, aradun Allah laɓe rahamun ne 🙄)
#Abdul-Hameed #Mama Halima #Ɓaleri #Belɗo #Mardiyya #Baffa Giɗaɗo #My Destiny #Matar Sayyadee *** [8/10, 8:57 PM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)
*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee
☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`