Page 56
*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***
Domin shiga comment section kuma ki danna wannan link ɗin👇🏼 *** *_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining link ɗin da ke sama domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜
_*💃🏻💃🏻 _Kuna ina 'yan uwana matar aure da 'yan mata? Shela nake ko wacce ta fito domin kuwa yau na zo maku da albishiri! Kun san matar Sayyadee ta ku ce ba ta samun abun ƙaruwa ta yi shuru domin ta ƙaru ita kaɗai._💃🏻💃🏻
💐💐🌼🌼_Magana ake ta ƙamshi. Toohwa! Mai ya hwaru?_ 🤔 🌷🌷🌸💮
*To maza ku marmatso ga sirrin nan. Shahararriyar nan wacce ke inganta soyayya tsakanin ma'aura wato Fatima Zaransalaty inkiya Queen Zarah ce ta taho mana da wani ƙamshim domin cika hancinar mazajemu da ƙamshi*. _INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_ _TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA KUJI 💃🏻
_Zaran Salaaty ta yi tafiya miƙaƙƙa har Sudan domin farnata ranmu da na mazajenmu ta kawo mana Sudanese perfume👌🏻 wanda idan har kika shafa shi a jikinki ko kin yi wanka ƙamshin bai barin jikinki. Tested and Trusted ƴaruwa. Zaransalaty ba iya sudanese perfume ta kawo maku ba, akwai kayayyaki masu matuƙar inganci na gyaran HQ (kun san dai ba a wasa da headquarter) akwai kayan gyararrakin jiki kala-kala na ƴan mata da matan aure. Sannan Zaransalaty tana sai da Decoration na kayan ɗaki iri-iri wanda baki taɓa ganinsu._
_KAR IN CIKA KI DA SURUTU, KE DAI NEMI ZARANSALATY A NUMBERS ƊINTA KAMAR HAKAA_: *** Or ****
*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_nfection_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_
_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ ***** *****
Waro idanuwa Mama Haleema ta yi tare da faɗin, "Kai haba, Nenne! Lallai tunda har Hamma Ɓeleri ya tako ƙafa cikin Arɗo Barkinɗo kashin Mamiyo ya bushe. Duk zafin zuciya, kafiya, taurin kai da mugun riƙo irin na Hamma Ɓaleri amma ya tako ƙafarsa cikin Estate ɗinnan, caɓ! Wallahi dole akwai wani abu da suke shiryawa kam." Mama Halima ta faɗi tana mai jinjina kai.
"Hmm! Ke dai kawai ki shuru da bakinki. Ni nan na ƙosa a fito da ita kowa ya ganta cikin estate ɗinnan. Shi fa Ɓaleri zarginta ya ke akan kashe Inna Maimu mahaifiyarsu." Nenne ta faɗi.
"Habaa! Ai biri ya yi kama da mutum. Ni fa duk abunda aka ce min Mamiyo ta yi ba zan taɓa musawa ba don billahillazi za ta aika. Kai! Har na hango ranar tonon silili a fadar Babiyo, rigiji gabji!" Mama Halima ta faɗi tana dariyar ƙeta.
"Kin ga, bari na leƙa ɗakin Mardiyya na gano ta, ko ba komai ƙanwa take a gare mu. Kuma bata raina ki ba." Nenne ta faɗi.
"Bata san ma kin zo ba, da tuni kin gan ta a nan ɗin ta zo gaishe ki. Gaba ɗaya ni rausayi ma take ba ni don ta kasa sakin jikinta sai ɗari-ɗari take yi da ni. 'Ya'yan nata ma sai da na ci ubansu (mama Halima na nufin ƴaƴanta wato ƙannen Habib) don ƙiri-ƙiri su ka daina gaishe ta. Sai da na yi da gasken-gasken tukun." faɗin mama Halima.
"Hmm! 'Ya'yan kirki ba, wai taya ki kishi suke." Nenne ta faɗi.
"To ni faɗa musu a kai kishi na ke da Mardiyyan, hu'um caɓ! Ai ragowa na bar mata." Faɗin Mama Halima.
Dariya Nenne ta yi tare da faɗin, "Ƴaƴa huɗu ai ba wasa ba. Ga jika ma yana hanya in sha Allah."
Murmushi Mama Halima ta yi Habib ta faɗo mata a rai, don har yanzu fushi take yi da shi, duk da kuwa babu rana da za ta fito ta faɗi ba tare da sun yi waya ba.
A falo ta taras da Marwanatu da sauran ƴan uwan nata suna cin abinci. Da idanun tausayi ta bi Marwanatun kamun ta fice daga ɗakin.
Sam Nenne ba ta yi tsammanin Baffa Giɗaɗo yana gidan ba, hakan ya sakaa da ta yi knocking sau ɗaya sai da murɗa handle ɗin ƙofar ta buɗe ta shiga. Turus! Ta tsaya tana ji tamkar ta juya ta bar ɗagin ganin Mardiyya ɗare-ɗare akan cinyar Baffa Giɗaɗon sai sinne kai take yi, yayin da shi kuma ya ke lallaɓata tare da kai spoon ɗin abinci bakinta.
Juyowar da Mardiyya za ta yi, sai ta yi arba da Nenne a tsakiyar ɗakin. Wani irin zillo ta yi tare da sauka akan cinyar Baffa Giɗaɗo tana rarraba idanu. Can kuma sai ta fashe da kuka tare da durƙushewa a ƙasa saboda wani irin kunya da ya yi mata ƙawanya.
Shi kuwa Baffa Giɗaɗo sai ya hau borin kunya yana faɗin, "Barka, sannu da zuwa Nenne (tsabar ruɗewar kunya shi ma da Nennen ya kira ta) kin ganta nan tun jiya ba lafiya, na yi na yi ta ci abinci taƙi. Zazzaɓi ne ke damunta." ya faɗi sai washe bakin kunya ya ke yi.
Nenne kuwa basarwa ta yi tamkar bata ga komai ba tare da faɗin, "Ayyaa, Allah sarki! Ai ka san shi zazzaɓi haka yake, sai ya cire wa mutum appetite ɗinsa. Allah ya ƙara lafiya. Ke kuma Mardiyya kuwa ai bai cire raɗaɗin ciwo. Tashi ki zauna mana, ni ma zuwa na yi na duba ta ban ma san kana gidan ba."
"Eh wallahi, na fita ne sai na kira ta awaya na ji gabaɗaya muryanta ma bai fita, shine na dawo domin duba jikin. To kuma da yake ba jimawa zan yi ba, sai na bar motar a can waje, shiyasa ba ku lura ina ciki ba."
Komai Nenne bata ce masa ba, don ita sai suka bata dariya ma. "Ai matarka ce halas malak! More abunka babu wanda ya isa ya ce don me!" A zuciya Nenne ta yi maganar, amma a zahiri sai cewa ta yi, "To na gaishe ku, Allah ya ƙara sauki da afuwa."
Tsabar kunya da tsoro ko ƙwaƙƙwarar motsi Mardiyya ta kasa yi balle ta buɗe baki ta gaishe da Nennen, sai ma jikinta da ke rawa tana addu'a Allah ya sa kar Nennen ta faɗa wa Mama Halima ta ganta a kan cinyar Baffan.
"Ni ma ai yanzu zan shigo ɗakin." Baffa Giɗaɗo ya faɗi ya kasa zaune ya kasa tsaye sai murmushin yaƙe yake.
Juyawa Nenne ta yi ta fice daga ɗakin tana dariya a zuciyarta tare da mamakin halin maza kasancewar Mama Halima ta zayyane mata duk abunda ya faru lokacin bikin da irin boren da Baffa Giɗaɗon ya yi akan shima ba son auren ya ke ba.
"Mazaaaaa, Mutanen mu!" Nenne ta faɗi tana dariya tare da girgiza kai sannan ta nufi side ɗin mama Haliman.
"Na shiga uku yau! Shikenan asirina yau ya gama tonuwa, ni Mardiyya. Sai da na ce maka ka tafi, ka tafi amma ka ƙi wai kai dole sai ka ban abinci na ci, to gashi nan an zo an kama mu ai. Kuma da gangan ka ƙi saka key a ƙofar ai" ta ƙarisa maganar tana rushewa da kuka har da ɗaura hannu a kai.
Ƙarisowa wajenta ya yi tare da kai hannu jikinta, wani irin zabura ta yi tamkar ta ga dodo tare da faɗin, "Wallahi ni dai kar ka sake ka taɓa ni, kuma daga yau ba zan ƙara bari ka shigo ɗakin nan ba. Yau ni na shiga uku idan Mama ta ji na zauna a kan cinyarka!" ta ƙarisa maganar tana kuka wiwi tamkar mahaukaciya.
"Haba, babyna!"(Babyna🤔😂 ikon Allah. Lallai maza a bar su inda aka gan su yasin😂)
"Ni dai ka daina ce min baby wallahi." ta faɗi tana hararar sa.
"Nan da 'yan watanni za su ga abu ya ɓullo a cikinki, kuma su ma sun san tunda dai har aka ɗaura mana dole ne mu rayaa sunna (sunna manya!🤔 baffaaaaa, haka za kai mana mu 'yan uwan mama Halima?Babu komai akwai Allah😢) ta ho nan kin ji matata."
Wani uban tsalle ta kuma dakawa tare da faɗin, "Allah ba zan ƙara bari ka taɓa ni ba, ni ka fita daga ɗakin nan." ta faɗi tana ɗaga murya wanda dole ya saka ya gyara rigarsa inda ta ɗan cukuikuye tare da fita dagaa ɗakin yanaa tsaki. Don bai wuce sati biyu ba kenan da ya fara shawo kanta har ya yi nasarar kashe boss wanda ya sakaa ta ɗan fara sakin jiki da shi kaɗan.
Ganin idan a ɗakinta ya ke sam ba ta sakin jiki da shi in dai da rana ne saboda tana ganin tamkar a idanun Mama Halima suke komai. Hakaan ha saka ya samo dabarar fita bayan ya yi sallama da kowa, sai kuma ya aje motar can bayan gida ya shigo ta ƙofar baya ya hole da amaryarsa sannan ya kuma fita ta bayan ya tafi sabgarsa. (Arrijalukenan😂🤣halinku sai ku).
(Ku ɗan nishaɗantu da wannann ma haɗe da gobe da mai yawa.)
#Baffa Giɗaɗo #Mardiyya #Nenne #Mama Halima #Soyayya sabuwa #Rijalu sai su 😂 #Ƙaddarata #My Destiny #Matar Sayyadee *** [8/11, 8:08 PM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)
*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee
☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`