My Destiny (Ƙaddarata)

Page 57

by @matarsayyadee3

*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***

Domin shiga comment section kuma ki danna wannan link ɗin👇🏼 *** *_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining link ɗin da ke sama domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜

_*💃🏻💃🏻 _Kuna ina 'yan uwana matar aure da 'yan mata? Shela nake ko wacce ta fito domin kuwa yau na zo maku da albishiri! Kun san matar Sayyadee ta ku ce ba ta samun abun ƙaruwa ta yi shuru domin ta ƙaru ita kaɗai._💃🏻💃🏻

💐💐🌼🌼_Magana ake ta ƙamshi. Toohwa! Mai ya hwaru?_ 🤔 🌷🌷🌸💮

*To maza ku marmatso ga sirrin nan. Shahararriyar nan wacce ke inganta soyayya tsakanin ma'aura wato Fatima Zaransalaty inkiya Queen Zarah ce ta taho mana da wani ƙamshim domin cika hancinar mazajemu da ƙamshi*. _INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_ _TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA KUJI 💃🏻

_Zaran Salaaty ta yi tafiya miƙaƙƙa har Sudan domin farnata ranmu da na mazajenmu ta kawo mana Sudanese perfume👌🏻 wanda idan har kika shafa shi a jikinki ko kin yi wanka ƙamshin bai barin jikinki. Tested and Trusted ƴaruwa. Zaransalaty ba iya sudanese perfume ta kawo maku ba, akwai kayayyaki masu matuƙar inganci na gyaran HQ (kun san dai ba a wasa da headquarter) akwai kayan gyararrakin jiki kala-kala na ƴan mata da matan aure. Sannan Zaransalaty tana sai da Decoration na kayan ɗaki iri-iri wanda baki taɓa ganinsu._

_KAR IN CIKA KI DA SURUTU, KE DAI NEMI ZARANSALATY A NUMBERS ƊINTA KAMAR HAKAA_: *** Or ****

*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_nfection_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_

_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ ***** *****

Nenne na shiga ɗakin Mama Halima ko mintuna biyu ba ai ba Baffa Giɗaɗo ya shigo yana gyara malum-malum. Gaba ɗaya yaran da ke ɗakin suka zuba masa idanu tare da faɗin, "Baffa yaushe ka shigo? Ba mu ji ƙarar motarka ba."

Sai da ya kalli Nenne da ke zaune a kujerar zaman mutum ɗaya ta gefen idanu sannan ya ce, "Na ajiye motar a waje ne, yanzu zan kuma fita shiyasa ban yi wahalar shigowa ba." ya faɗi yana zama a kujeran da ke fuskantar Marwanatu.

"Baffa wai da gaske yanzu aunty Marwanatu mamarka ce?" Marwanatu ta faɗi tana jin wani irin kishi na nuƙurƙusarta tamkar ita Mama Halima.

Banza ya yi da ita tamkar bai ji abunda ta ce ba, don idan da sabo ya saba duk ya shigo ɗakin sai Marwa ta yi masa wannan tambayar.

Kallon Nenne ya yi tare da faɗin, "Ba mu gaisa ba Saudatu. Ina yini ya Hamma Belɗo? Har yanzu ba mu samu lokaci mun zanta sosai ba irin na tsakanin ɗan uwa da ɗan uwa. Ina son zuwa ina tsoron kada Babiyo ya fusata."

"Lafiya ƙalau, ka san iyaye dole ne a bisu a hankali ai saboda a rabu da su lafiya." Nenne ta faɗi.

Daidai nan Mama Halima ta fito daga kitchen hannunta riƙe da plate ɗin abinci. Da mamaki ta ke kallon Baffa Giɗaɗo don sam bata ji shigowar motarsa gidan ba.

"Jaɓɓama! (sannu da zuwa)" ta faɗi tana kallonsa da mamaki.

"Kin ganni nan ban jima da shigowa gidan ba, a waje na bar mota ma saboda fitan zan kuma yi. Dama dai 'yarki ce ba lafiya na kawo mata magani." faɗin Baffa Giɗaɗo.

Da kallo Mama Halima ta bi ƴan matanta da ke zaune tare da faɗin, "Wacece ba lafiya a cikin ku?"

Girgiza kai suka shiga yi tare da haɗa baki wajen faɗi, "Lafiyanmu ƙalau Mama."

Sai ta mayar da dubanta gun Baffa Giɗaɗo tare da faɗin, "To wacece kenan?"

"Mardiyya fa na ke nufi!" ya faɗi shima yana kallonta.

Murmushi Mama Halima ta yi tare da faɗin, "To ai wannan ƙanwa ce ba ƴata ba. Kar ma ka sake wannan kuskuren don 'yata babu aure a tsakaninku. Kar ka sake ƙoƙatin ɓata aurenka."

Haɗiye miyau ya yi na kunya tare da miƙewa ya ce, "To ni bari na koma wajen aiki."

"Ka tsaya mana in zubo maka abinci ka ci." Mama Halima ta faɗi tana kallonsa ganin yanaa ta abu tamkar mara gaskiya.

Ita kuwa Nenne sai ƙumshe dariyarta take a zuciya don ba ƙaramin dariya Baffa Giɗaɗon ke bata ba. Yanayinsa kawai ya isa ya ya fallasa shi.

"A'a saurai na ke yi, idan na dawo anjima na ci. Yanzu ma kiran da Mardiyyan ta min ne akan in kawo mata magani ya dawo da ni. Sai na dawo, Saudatu ki gaida gida."

Gyaɗa masa kawai Nenne ta yi bayan ta kawas da kai don ƙiris ya rage ta fashe da dariya.

"To zan shiga ni ma in duba jikin nata. Allah ya ƙara sauki sai ka dawo." Mama Halima ta faɗi tare da nufar Nenne da abincin da ke hannunta ya aje mata.

"Hu'um! Wai mama ba ki lura gaba ɗaya tamkar Baffa bai da gaskiya ba? Allah sai kame-kame ya ke yi. Wa ya sani ma ko ƙaryar Mardiyyan ne da ta ce bata da lafiya kawai ganinsa take son yi don ta ɓata miki rai." faɗin Marwanatu.

"Oh, ni ma kashe min auren za kiyi kamar yadda kika kaso na ki auren? Shi baffan sa'anki ne? Ku tashi ku bar falon nan dukkanku ku wuce ɗakinku." Mama Halima ta faɗi fuska a ɗaure.

Gaba ɗaya suka miƙe suna turo baki tare da ficewa daga ɗakin. Ita kuma Mama Halima ta bi su da harara.

_DENMARK_ Zaune suke a falo suna kalon wani film ɗin america, sai dai Zeenah ce kawai ke kallon. Khairat tagumi ta yi ta zuba mata idanu, don ita dai idan ba gizo idanunta suke mata ba, sai ta ga kamar tana mata kama da Mardiyya (Amaryan Baffa giɗaɗo). Sannan kuma a fizge tana yanayi da Babiyo. Amma da zarar ta tuna da labarin da Hamma Jawaad ya bata sai ta kawas da shirmen da take kawowa cikin zuciyarta.

Wayarta ce ta yi ƙara alamar shigowar kira. A tare ita da Zeenah suka kalli wayar kamun Zeenah ta miƙe ta ɗauko wayar ta miƙa mata kasancewar tana kusa da wayar ne.

Da wani irin farinciki Khairat ke amsa wayar kasancewar da mahaifiyarta ta ke waya.

"Haba! Sati mai zuwa? Hmm lallai, wato da yake Hamma Abdul-Hameed ne ai dole Babiyo ya ce haka." faɗin Khairat tana taɓe baki.

Ita kuwa Zeenah tunda Aka ambaci Abdul-Hameed haka nan gabanta ya faɗi raaas! Sai ta yi ta maimaita sunan cikin zuciyarta.

Har Khairat ta kammala wayar Zeenah na wata duniyar daban na tunanin abunda ita kanta ta rasa ko menene.

Taɓa ta Khairat ta yi, sai ta waigo a firgice tare da zubawa Khairat ɗin idanu. Can kuma ta motsa baki tare da faɗin, "Abdul-Hameed!"

Da mamaki Khairat ta ke kallonta kamun ta ce, "Eh, Abdul-Hameed ne zai yi aure sati mai zuwa. Kin san shi ne?"

Girgiza kai Laushi ta yi tare da faɗin, "A'a ban san shi ba. Amma kuma........." sai ta yi shuru tana mai ɗaga kai samaa kamar tana son tuna wani abu, si ta yi saurin girgiza kai tare da faɗin, "Ban san shi ba."

Ko kamun Khairat ta kuma cewa komai, sai ga Jawaad ya shigo ɗauke da sallama a bakinsa. Amsawa Khairat ta yi tana kallonsa, nan da nan annurin fuskanta ya soma dusashewa ganin wani irin kallo da ya bi Zeenah da shi don sanye take da skirt wanda ya kama ta, sai riga mai hannun vest sannan kuma kanta babu ɗankwali, gashin kanta har kafaɗa sai ƙyalli ya ke yi.

"Welcome!" Zeenah ta faɗi tare da ɗauke kanta daga kallonsa tanaa mai ɗaure fuskanta.

Ajiyar zuciya ya sauke a hankali tare da shafa kansa sannan ya yi kamar zai kulle idanu sai kuma ya yi saurin buɗe su tare da kallon Khairat da sauri kamar wanda ya dawo cikin hankalinsa. Ganin ta yi kicin-kicin sai ya saki murmushi tare da faɗin, "My girl! Ba magana ne?"

Ƙala bata ce masa ba, sai ma miƙewa da ta yi a hankali ta wuce bedroom ɗinsu.

Shi kuwa sai da ya ƙara kallon Zeenah don sosai ta masa kyau sannan ya bi bayan Khairat da ya fahimci kamar fushi take.

Yana tura ƙofar ya ganta zaune a bakin gado ta haɗa kanta da cinyoyinta tana shassheƙar kuka. Jikinsa ne ya yi sanyi. A hankali ya taka ya isa inda take tare da ɗaura hannu a kan kafaɗarta. A hankali ta zame tana mai ƙara sautin kukanta.

Zama ya yi tare da jawo ta jikins gaba ɗaya ya shiga faɗin, "Wa ya taɓa min wife ɗina? Fushin na menene, U'hm?"

Kamar baza ta yi magana ba sai kuma ta turo baki tare da faɗin, "To ba kai bane, kana shigowa ka kafe ta da idanu ko jin sannu da zuwan da nake maka ma baka ji ba. Ni dai yaushe za ta tafi?"

Waro idanu ya yi tare da faɗin, "Ikon Allah! Ashe ana sona haka? Ban da ke da abunki, ina dake wacece za ta burge ni kuma! Ni kin ishe ni a duniyar nan. Kuma fa wancen ɗin matar aure ce fa, ina ni ina matar abokinaaa!" ya ja abokina ɗin har da karyar da kai.

"To ni dai gaskiya zan faɗa mata kar ta sake irin wannan shigar da ta yi don gidan akwai mijin wata." ta ƙarisa maganar har da ƙara turo baki.

"To a dai huce, Jawaad na ki ne ke ɗaya!" (In Allah ya yarda ba amin ba) ya faɗi hakan a zuciyarsa.

"To ni don Allah yaushe za ta tafi ta bar min gidana?" ta faɗi tana kallonsa.

Kallonta ya riƙa yi kamun ya marairaice tare da faɗin, "Haba one and only wife! Na riga na miki bayanin yarinyar nan. Yanzu idan na ce ta bar gidan nan ina za ta nufa da shafaffen ƙwaƙwalwa. Habaa, kar ki zobe ladanki mana. Mu ɗan ƙara jira kaɗan har ta samu lafiya kuma tunaninta ya dawo."

Ɗan shuru Khairat ta yi, sai kuma can ta furta, "Allah ya bata lafiya!"

"Ameen my wife," ya faɗi tare da rungumeta.

"Ɗazu mun yi waya da mamana, ta ce min bikin Hamma Hameed sati mai zuwa, kenan mu muna nan za ai auren?"

Kumatunta ya ja tare da faɗin, "Albishirinki to!"

"Goro fari ƙal!" ta faɗi cike da zaƙuwa.

"To kakanki ya kuma kira na ɗazu wai mu dawo kuma kwana biyu ya bamu kacal domin isowa Nigeria saboda ai biki da mu tare da shagalin murnar Abdul-Hameed ɗin zama ministern Abuja."

Waro idanu Khairat ta yi tare da faɗin, "Har an naɗa su ne?"

Girgiza kai Babiyo ya yi tare da faɗin, "A'a, amma ke ma kin san yadda Babiyo ya ke a wajen mai girma shugaban ƙasa, to babu tantama Abdul-Hameed ya gama zama minister in Allah ya yarda."

Jinjina kai Khairat ta yi cike da zumuɗi tare da faɗin, "Can't wait to see me in my country. To wait, ya za mu yi da Zeenat?"

Ɗan jim ya yi tare da faɗin, "Tare za mu tafi, sai dai ni da ke ne kawai za mu san da zamanta a cikin Arɗo Barkinɗo. Kin min alƙawari za ki riƙe min wannan sirrin matata?"

Jinjina kai Khairat ta yi tare da faɗin, "In sha Allah mijinaa!"

_SWEDEN_ Cike da zallar farin ciki Habib ke haɗa kayansu cikin akwati, Amatul Kareem sai kallonsa take yi cike da mamaki ganin wani irin zumuɗi da farincikin da yake yi.

"Sweetheart wannan farincikin duk na komawa Nigeria ne? Ni zan iya cewa ko daren aurenmu ban ga irin wannan farincikin a fuskanka ba wallahi."

Ɗagowa ya yi ya kalleta, sai kuma ya aje jibgegiyar rigar sanyin dake hannunsa a kan gadon tare da faɗin, "Baza ki gane bane, honey. Amma ni kaɗai na san farincikin da nake ciki. Ni dama tamkar a kan ƙaya nake a wannan ƙasar wallahi. Ki sauri kar mu yi missing flight."

Girgiza kai kawai Amatu ta yi tare da fita daga ɗakin, cikinta ɗan wata uku ya ɗan soma turowa kaɗan.

Fitarta ya saka ya fiddo waya da sauri ya shiga neman wata number ya dannawa kira, buga biyu wanda ya kira ya ɗaga wayar. Cikin sauri Habib ya soma magana, "Kana ji na ko? In sha Allah cikin dare zan sauka a Lagos ni da iyalina, ka tabbatar ka yi duk abunda na umarceka da ka yi."

Daga can aka ɗauki tsayin second uku ana magana sannan Habib ya kuma cewa, "Alright sai mun iso." yana gama faɗin haka ya datse kiran.

_NIGERIA_ Bayan kwana uku da bawa magajiya kwangilar nemo Laushi, lokacin kuma ya yi daidai da saura kwanaki sha ɗaya, bikinsa da Asma'u, sai ga kiran wayarta da daddare lokacin Abdul-Hameed na kwance sai juyi yake yi a kan gado rungume da fulo. Ganin numbern da ya yi saving da magajiyar sheɗanu bai san lokacin da ya yi wurgi da filon da ya rungume ba tare da picking call ɗin har hannunsa na rawa.

"Ban buƙatar gaisuwarki, je ki kai tsaye ki min bayani!" ya faɗi ba tare da ya amsa gaisuwar da take masa ba.

"Na yi nasarar gano gidan karuwan da Laushi ta zauna, kuma na samu bayanai a wajen magajiyar gidan mai suna hajja Lanti da wasu daga cikin karuwan gidan. Laushi ta kwashi kusan shekaru takwas zuwa tara a wannan gidan ya 'yar da ta haifa a gidan mai suna Meema da kuma ƙawarta Ladi katifa. Sai dai kuma ta bar gidan sanadiyar wani faɗa da suka yi da matar saurayinta da ta biyo ta har nan gidan karuwaita nemi tashin hankali da ita akan dole sai ta bar mata mijinta. Faɗa dai ya kai su har da ƙoƙarin kisan kai da ita matar saurayin nata ta yi. Wannan dalilin ne ya saka ta bar gidan hajja lanti ta koma gidan da dadironta ya kama mata. Sai dai ko shekara biyu ba tai a gidan ba suka samu labarin zagaye gidan da 'yan sanda sukai bayan gano ana aje muggan makamai tare da hodar iblis wanda shi saurayin nata ne ke kawo wa. Wasu kuma sun ce ita ce ta masa cinne saboda ta taɓa yiwa wani saurayinta can bayaa har hakan ya kai shi ga zaman gidan kaso. To yanzu dai in taƙaicemaka, Laushi dai ta gudu ita da ƴarta, Ladi katifa da kuma Salma nice kuma babu wanda ya san inda suke."

Wani irin jifa da wayar Abdul-Hameed ya yi sai da ta bugu da bango ta tawarwatse a ƙasa.

(Hmm, readers mai kuke hangowa ne wai? Ga Habib zai diro Nigeria, Jawaad ma haka kuma tare da Laushi, gefe guda kuma ga Abdul-Hameed🤔 ƙaƙa-ƙara-ƙaƙa! Tabɗijam😯)

#Abdul-Hameed #Jawaad #Habibi #Laushi #Khairat #Amatul Kareem #Baffa Giɗaɗo #Mardiyya #Babiyo #Mamiyo #My Destiny #Ƙaddarata #Matar Sayyadee *** [8/12, 3:43 PM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)

*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee

☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`