My Destiny (Ƙaddarata)

Page 58

by @matarsayyadee3

*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***

Domin shiga comment section kuma ki danna wannan link ɗin👇🏼 *** *_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining link ɗin da ke sama domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜

_*💃🏻💃🏻 _Kuna ina 'yan uwana matar aure da 'yan mata? Shela nake ko wacce ta fito domin kuwa yau na zo maku da albishiri! Kun san matar Sayyadee ta ku ce ba ta samun abun ƙaruwa ta yi shuru domin ta ƙaru ita kaɗai._💃🏻💃🏻

💐💐🌼🌼_Magana ake ta ƙamshi. Toohwa! Mai ya hwaru?_ 🤔 🌷🌷🌸💮

*To maza ku marmatso ga sirrin nan. Shahararriyar nan wacce ke inganta soyayya tsakanin ma'aura wato Fatima Zaransalaty inkiya Queen Zarah ce ta taho mana da wani ƙamshim domin cika hancinar mazajemu da ƙamshi*. _INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_ _TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA KUJI 💃🏻

_Zaran Salaaty ta yi tafiya miƙaƙƙa har Sudan domin farnata ranmu da na mazajenmu ta kawo mana Sudanese perfume👌🏻 wanda idan har kika shafa shi a jikinki ko kin yi wanka ƙamshin bai barin jikinki. Tested and Trusted ƴaruwa. Zaransalaty ba iya sudanese perfume ta kawo maku ba, akwai kayayyaki masu matuƙar inganci na gyaran HQ (kun san dai ba a wasa da headquarter) akwai kayan gyararrakin jiki kala-kala na ƴan mata da matan aure. Sannan Zaransalaty tana sai da Decoration na kayan ɗaki iri-iri wanda baki taɓa ganinsu._

_KAR IN CIKA KI DA SURUTU, KE DAI NEMI ZARANSALATY A NUMBERS ƊINTA KAMAR HAKAA_: *** Or ****

*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_nfection_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_

_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ ***** *****

"Wannan wacce irin ƙazamar rayuwa ce, ni Abdul-Hameed? Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Allah kai ka san dalilin da ya sa ka ɗaura min ƙaunar baiwar Allahn nan a zuciyata. Allah idan har alkhairi ce a rayuwata ka bani haske domin sanin inda take da abunta ta haifa. Idan kuma ba alkhairi bace, ka fitar da ita a cikin zuciyata in samu salama. Ina son ganin abunda Zee-meed ta haifa, ina son ganin 'ya ko ɗana." Abdul-Hameed ya faɗi a bayyane yana mai riƙe kansa.

"Hamma Hameed!" Ramadan ya yi kiran sunansa da tun lokacin da ya buga waya a jikin bango ya shigo ɗakin amma shi Abdul-Hameed ɗin bai lura da shi ba kasancewar hankalinsa ba a jikinsa bace.

A firgice Abdul-Hameed ya juya ya kalli Ramadan wanda ke nuna alamum ya ji duk abunda ya ke faɗa saboda irin kallon da ya ke masa.

"Ramadan mai ka ke min a ɗaki with out my permission? Kana hauka ne za ka shigo ba tare da knocking ba?"

"I'm sorry, na ji ƙarar faɗuwar abu ne da ƙarfi shine na shigo duba ka, I'm just worried about you." Ramadan ɗin ya faɗi yana wa yayan nasa wani irin kallo mai tafe da zargi.

"I'm I a kid? Dallah malam get out of my room!" ya faɗi da ƙarfi yana nuna masa ƙofa.

Juyawa Ramadan ɗin ya yi zai fice daga ɗakin, sai kuma Abdul-Hameed ya yi gyaran murya tare da faɗin, "Come and sit, I want to talk to you."

Kamar Ramadan ɗin ba zai juyo ba, amma sanin cewar babu burbushin raini a tsakaninsu ya saka ya dawo ya zauna a inda Abdul-Hameed ɗin ya nuna masa, sai dai sam fuskansa babu annuri.

Shima Abdul-Hameed ɗin zama ya yi kusa da Ramadan ɗin tare da ɗan yi gyaran murya sannan ya furta, "Sorry what I did to you earlier, I was upset ne shiyasa."

"Never mind!" Ramadan ya faɗi ba tare da ya kalle sa ba, asali ma ƙasa ya ke kallo gabansa na faɗuwa saboda abunda kunnensa ya jiye masa. Don ya san idan har hasashensa gaskiya ne to fa ahalinsu sun kaɗe a wajen Babiyo. Duk zuri'a sai sun san mai ke faruwa kuma sannann kuma a kum musu koren kare, kuma dama yaushe suka dawo gidan.

"Don Allah abunda ka ji ya zama sirri a tsakaninmu!" Abdul-Hameed ya faɗi bayan ya kawas da fuskansa daga kallon Ramadan ɗi don wani kunyansa ne ya lulluɓesa.

"Hamma yanzu kenan dagaske 'ya gare ka a waje ba tare da aure ba? Kenan kar in ƙaryata kunnena? Haba Hamma! Mai yasa za kai haka bayan ka san irin bala'in da hakan zai iya jawo mana musamman ba ga Baffanmu idan Babiyo ya samu wannan labarin. Kuma kai ma ka san yadda idanun Babiyo ke akan motsin ko wani ɗa da jikansa dole ne wata rana ya binciko wannan abu. Hamma da girmanka, ilimi kuma da hankalinka! Garin yaya hakan ta faru?"

Shuru Abdul-Hameed ya yi na kusan mintuna biyar tamkar ba zai kuma furta komai, wanda ba komai ya jawo shurun ba face kukan da yake yi kuma bai son sautin ya fito. Hawayensa har ɗiga suke yi a ƙasa. Sai da ya ɗan natsu sannan ya soma magana.

"Ramadan wallahi ni ba fasiki bane! Ban taɓa jin sha'awar aikata zina ba a rayuwata. Ban san ko hakan na daga ciki ƘADDARATA bane. Don ko da na fara ganin Zeenatu a rayuwa a garin bauchi, haka nan Allah ya ɗaura min ƙaunarta a kallon farko. Ban san ko haka na da nasaba da kamannin familynmu da na gani a tattare da ita ba duk da kuwa na san ita ɗin ba zai taɓa yuwuwa a ce ƴar nan gidan bace. A fizge ma wallahi kamanni ta ke min da Babiyo da kuma Baffa Ɓaleri yayan Baffanmu, sai dai na san ko giyan wake nasha ba zan taɓa tunanin 'yar wan baffanmu zaune gidan karuwai tana karuwanci ba."

"Karuwanci! Karuwa ce ma kenan? Lallai caɓ! Aikuwa ba dai 'yar baffa Ɓaleri ba. Zan iya yadda 'yar da Babiyo ya haifa da cikinsa za ta iya karuwanci amma ba dai 'yar baffa Ɓaleri ba. Wallahi sai ya kwantar da ita ta kalli gabas sannan zai dadara wuƙa a cikinta a irin dai halin baƙar zuciyarsa da Baffanmu ya ke bamu labari duk da ni ban wani waye sa ba." Ramadan ya faɗi.

"Ni ai ba cewa na yi 'yarsa bace. Ita sunan mahaifinta ma Ayuba. Kuma shi ɗin ba bafullace ba ne, tsakanin bazamfare da basakkwace ne shi. Kawai dai kamanni ne. Ka san dai ni ma a hoto na wayi Baffa Ɓalerin don tun muna yara ya bar estate ɗin nan."

"To amma kai Hamma mai ya kai ka kula karuwa da mutuncinka?" Ramadan ya faɗi.

"Hmm! Duk yadda zan kwatanta maka ba za ka gane ba Ramadan don baka san mai ake kira da so mai zafi ba."

Taɓe baki Ramadan ya yi tare da faɗin, "Ni kam ban ga abun so a jikin karuwa ragowar titi ba!"

Sosai Abdul-Hameed ya ji zafin abunda Ramadan ɗin ya ce, amma sai ya fuske tare da cigaba da magana, "Na yi nasarar gyara rayuwar Zeenah har ta tuba ta daina bin kwalta. Ni kuma na yi mata alƙawarin aurenta idan ta gama istibura'i, sai dai a wani dare na rusa komai da hannuna. Ban sai mai fizgeni ba har na aikata zina da ita, wanda bayan afkuwar komai hankalinmu ya dawo jikinmu, mun yi kuka tamkar ba gobe saboda abunda muka aikata. Mun yi nadama tare da roƙon ubangiji yafiya. Sai dai ban san mai ya faru ba, tun daga wannan ranar da na bar Bauchi, ban kuma tuna wata halitta wai ita Zeenatu cikin zuciyata sai a asibiti bayan na farfaɗo daga suman da na yi lokacin da aka buga min ƙarfe a kai."

Tsit ɗakin ya ɗauka. Abdul-Hameed na hawaye, yayin da Ramadan ya faɗa wani tunani can yana saƙa da warwara.

"To amma Hamma, kai da ka kusance ta sau ɗaya tak kuma ba ka sake waiwayanta ba, ya akai ka san ta haihu kuma har kake danganta abunda ta haifa da kai?"

Ajiyar zuciya Abdul-Hameed ya saki tare da faɗin, "Na koma garin Bauchi domin bincike. A nan na samu labarinta."

"Sai kuma aka faɗa maka cikinka ne ta haifa ko?" Ramadan ya faɗi ba tare da ya wani ji a ransa cikin budurwar na hammansa bane.

"To cut the long story short Ramadan, yanzu haka babu wanda ya san inda Laushi ta ke, ance tabar garin Lagos ita da ƙawarta Ladi Katifa da kuma wata wai ita Salma nice."

Miƙewa Ramadan ya yi don shi haushin labarin da wan nasa ya ke ba shi ya ke ji. Don shi har ga Allah bai ga inda cikin jikin wata wai ita Laushi ya zamaa na Hammansa ba daga yi sau ɗaya. Bugu da ƙari ma kuwa ita budurwar ya furta da bakinsa karuwa ce. Can dai ta samo cikinta a wani wajen.

"Your secret is safe with me Hamma, amm ni fa har ga Allah ban amince abunda aka haifa cikinka bane. Ka kwantar da hankalinka kawai."

Ƙala Abdul-Hameed bai ce masa ba, don ya fahimci babu abunda Ramadan zai fahimta game da abunda ake kira ƙauna.

Kusan kwanaki uku Abdul-Hameed bai bacci sai raya dare da sallah da kuma neman zaɓin ubangiji. Ga bikinsa sai daɗa matsowa ya ke yi shi ko ta kan amaryar ma bai yi. Yana dai daurewa yana amsa kiranta da take damunsa da shi duk dare. Wani lokacin ma kashe wayaar ya ke yi saboda ita.

Wani irin juyi Mamiyo ta yi a tsakiyar falo saura kaɗan ta faɗi ƙasa wanda da hakan ya faru babu abunda zai hana ta zaman 'yan bori a ƙasa. Idanuwa gaba ɗaya a waje ta liliyo wani mugun ashar ta zabgawa Baffa Jibrila tare da faɗin, "Gidan uban wa ka aje takardun? Takardun kamfanin da na samu nasarar ginawa kusan tsayin shekaru talatin ka ɓatar! Jibrila yau ba gobe ba sai na tsine maka albarka idan har baka fita ka ɗauko min takardun nan ba ka kawo shi nan a gabana ba." sai kuma ta fashe da wani irin kuka da ya kaɗa hanjin gaba ɗaya 'ya'yanta da ke zaune sun y jigum-jigum.

_For days before the wedding_

"Wallahi kin ji na rantse miki da Allah a cikin mota na aje. Kuma babu wanda ya ke shiga motata idan ba ni ba. Dole akwai wanda ke mana kutse cikin lamuranmu. Don idan ba mu ɗinnan ba babu wanda ya san komai game da sabon kamfani." faɗin Baffa Jibrila.

Wani kallon banza Mamiyo ta watsa masa tare da faɗin, "To tunda babu uban da ke fita da motarka, uban wanene kenan ya ɗauki takardun?"

Shuru Jibrila ya yi yana tunani, can ya yi saurin ɗagowa ya kalli Mamiyo tare da faɗin, "To wallahi ba kowa zai ɗauki wannan takardun ba sai Hafizu drivern Babiyo, don shi kaɗai ya yi amfani da motata ranar da za mu je kai kuɗin auren ɗan iskan yaron can Abdul-Hameed."

Wani irin tsam, Mamiyo ta yi tare da zama jagwab a kan kujera riƙe da kai tana girgiza ƙafa. Sai kuma ta yi saurin rarumar waya ta dannawa Hafizu informer kira. Sai da ya kusa katsewa Hafizu ya ɗaga kiran tare da ƙoƙarin fara gaishe ta amma sai ta dakatar da shi wajen faɗin,

"Ka zo gida yanzu ka same ni!" tana gama faɗin haka ta katse kiran.

Cikin mintuna talatin sai ga Hafiz yana knocking. Kallon Baffa Mahmuda ta yi tare da yi masa alama da hannu akan ya buɗe ƙofar. Yana buɗe ƙofar su kai idanu biyu da Hafiz wanda ya ɗan duƙar da kai tare da gaishe sa. Ba tare da ya amsa gaisuwar ba ya bashi hanya ya shigo sannan ya mai da ƙofar ya rufe har da murza key.

Duƙawa ƙasa ya yi tare da faɗin, "Barka da rana, uwar ɗakina."

Maimakon Mamiyo ta amsa gaisuwar sai ta miƙa masa hannu farar fuskan nan nata a mugun murtuke.

Da idanu Hafiz ya bi hannu sannan ya kai ƙwayan idanunsa akan Mamiyo tare da faɗin, "Ranki shi daɗe mai zan baki?"

Maimakon jin amsa sai saukar sawayen Mamiyo ya yi a fuskansa hagu da dama sannan a kausashe ta furta, "Ban takardun kamfanina da ka ɗauka a motar Jibrila!"

A razane ya kuma kallon Mamiyo tare da faɗin, "Takardu kuma? Ni kuwa mai zan yi da takardun kamfaninki ranki shi daɗe?"

Wani murmushin baƙin ciki Mamiyo ta saki, domin da zargi take amma ganin reaction ɗin Hafizun ya tabbatar mata da shine wanda ya ɗauki takardun a motar Jibrilan.

"Hafizu kenan! Wato na ɗauko ka daga rana na kawo ka inuwa shine za a haɗa kai a ci dunduniyata ko? To ka sani a tafin hannuna kake, kuma cikin saƙon ɗaya zan iya loma da kai tamkar yanda na ke haɗiyar lomar tuwo. Wa ka ke wa aiki Hafiz!?" ta faɗi a matuƙar kausashe fiye da ɗazun.

"Na rantse miki da Allah Mamiyo ban ci amanarki ba, ki yarda dani. Ke kaɗai na ke wa aiki a cikin gidan nan."

"Ku banƙare min shi in tura shi barzahu kuma in binne gawarsa har abada kuma babu wanda zai san mai ya faru. Kuma ko gawarsa ba zan bari a gani ba." ta ƙarisa maganar tana wasa da wuƙat da yake yanka apple wanda ta ɗauke shi a kan Center table ɗin dake kusa da ita.

Cikin ƙanƙanin lokaci su Baffa Jibrila, Baffa Tukur da Baffa Mahmuda suka yi yadda Mamiyo ta ce. Zai kwarma ihu Baffa jibrila ya toshe masa baki.

Cike da isa Mamiyo ta tako har inda ya ke tana wasa da wuƙar hannunsa tare da yin wani mugun murmushi sannan ta yiwa Baffa Jibrila alama da hannu a kan ya saki bakin Hafiz ɗin.

Wanh ajiyar zuciya Hafiz ya saki tare da fashewa da kuka. Da sauri ya gimtse sakamakon ɗaura yatsa da Mamiyo ta yi a baki tare da furta "Sssh!"

Babu abunda Hafiz ke yi sai zazzare idanu yana jin tamkar zai saki zawon tashin hankali, don fitsari ma ba a magana don tuni ya jiƙa wandonsa.

"Wa ya saka ka ɗaukar takardun kamfanina?" ta kuma watsa masa tambaya babu alamar wasa a fuskanta.

Bakinsa na rawa ya shiga faɗin, "Ki min rai ranki ya daɗe. Ki bani dama na yi maki bayani dalla-dalla."

Nuni ta yiwa su Baffan Jibrila da su sake shi. Take suka watsar da shi a tsakar ɗaki, Baffa Jibrila har da shurunsa da ƙafa duk da kuwa Hafizun ya girme shi don shi Hafiz sa'an Baffa Tukur ne.

Zama Mamiyo ta yi tana girgiza ƙafafu tare da ƙanƙance idanu tana kallon Hafizun.

"Hamma Ɓaleri ne ya saka ni ɗauko takardun bayan ya yi min barazana da tona asirinmu wajen Babiyo tare da ɓatar da iyalaina. Kuma idan ba ki manta ba, wasu watanni can da suka wuce na faɗa miki na ganshi da idanuna a cikin Arɗo Barkinɗo."

Ba Mamiyo kaɗai ba, hatta su Baffa Jibrila sai da suka yi wata muguwar razana jin furucin Hafizu.

"Ɓaleri ka ce? Ya akai ya san da kamfanin?" Mamiyo ta faɗi a rarrabe saboda tashin hankali.

"Akwai abunda na ɓoye miki bam faɗa ba, ko kuma ince tsoro ya hana ni faɗa miki." Hafiz ya faɗi.

"Menene wannan baka faɗa min ba Hafizu? Faɗa min shi yanzu!" kallo daya za kai wa Mamiyo ka fahimci a matuƙar razane take.

"Wannan yarinyar budurwar Abdul-Hameed ba wata bace illa ɗiyar Abubakar Ɓaleri!"

Wannan karan wani irin mugun tari ne ya sarƙe Mamiyo ta shiga yi babu ƙaƙƙautawa har sai da Baffa da ya kafa fahimtar abunda Hafizun ya faɗa ya rarrafa tare da buɗe firji ya ɗauko mata ruwan gora ya miƙa mata bayan ya ɓalle murfin goran.

Kafa kai ta yi ta dunga kwankwadar ruwan tankat raƙuma. Sai da ta shanye tass sannan ta yi wurgi da goran wani irin zufn tashin hankali na kwaranyo mata. Sai da ta kwashi mintuna goma tana haki tamkar wacce ta yi tsere da jirgin ƙasa sannan ta furta, "Sa....ke...mai...maita abunda.... Ka ce ha..fizuu!" a rarrabe ta yi maganar saboda hakin da take yi.

#Abdul-Hameed #Laushi #Mamiyo #Hafizu #Ɓaleri #Family Saga #My destiny #Matar Sayyadee *** [8/18, 10:47 PM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)

*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee

☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`