My Destiny (Ƙaddarata)

Page 59

by @matarsayyadee3

*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***

Domin shiga comment section kuma ki danna wannan link ɗin👇🏼 *** *_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining link ɗin da ke sama domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜

_*💃🏻💃🏻 _Kuna ina 'yan uwana matar aure da 'yan mata? Shela nake ko wacce ta fito domin kuwa yau na zo maku da albishiri! Kun san matar Sayyadee ta ku ce ba ta samun abun ƙaruwa ta yi shuru domin ta ƙaru ita kaɗai._💃🏻💃🏻

💐💐🌼🌼_Magana ake ta ƙamshi. Toohwa! Mai ya hwaru?_ 🤔 🌷🌷🌸💮

*To maza ku marmatso ga sirrin nan. Shahararriyar nan wacce ke inganta soyayya tsakanin ma'aura wato Fatima Zaransalaty inkiya Queen Zarah ce ta taho mana da wani ƙamshim domin cika hancinar mazajemu da ƙamshi*. _INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_ _TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA KUJI 💃🏻

_Zaran Salaaty ta yi tafiya miƙaƙƙa har Sudan domin farnata ranmu da na mazajenmu ta kawo mana Sudanese perfume👌🏻 wanda idan har kika shafa shi a jikinki ko kin yi wanka ƙamshin bai barin jikinki. Tested and Trusted ƴaruwa. Zaransalaty ba iya sudanese perfume ta kawo maku ba, akwai kayayyaki masu matuƙar inganci na gyaran HQ (kun san dai ba a wasa da headquarter) akwai kayan gyararrakin jiki kala-kala na ƴan mata da matan aure. Sannan Zaransalaty tana sai da Decoration na kayan ɗaki iri-iri wanda baki taɓa ganinsu._

_KAR IN CIKA KI DA SURUTU, KE DAI NEMI ZARANSALATY A NUMBERS ƊINTA KAMAR HAKAA_: *** Or ****

*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_nfection_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_

_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ ***** *****

Sharfe zufa Hafiz ya yi tare da kuma maimaita mata, "Wannan yarinyar da kika raba tsakaninsu da Abdul-Hameed, wannan dai karuwar da na zo na baki labarin suna soyayya da Abdul-Hameed 'yar Abubakar Ɓaleri ce!"

Hannun Mamiyo kar-kar haka ya soma wani irin rawa tamkar an jona mata electric wears. Da sauri Baffa Mahmud ya nufe ta tare da riƙe ta yana faɗin, "Mamiyo mai ke faruwa, wacece wannan yarinyar da kuke magana akai? Ku yi mana bayani kun bar mu a cikin duhu. Har wacece ita da sunanta zai firgita ki haka?"

Sau huɗu Mamiyo na son buɗe baki ta yi magana amma sai ta kasa saboda yanda bakin nata ke rawa. Can kuma sai ta ɗauke wuta ɗif alamar suma.

A gigice gaba ɗaya 'ya'yan nata suka rufa mata suna jijjiga ganin ta sandare masu.

Shi kuwa Hafiz a wannan ɗan tsukukun ya samu ya fice daga falon ya bar gidan yana wani irin dariyar ƙetar halin da Mamiyon ke ciki.

"Caɓ! Mamiyo ce haka jikinta ke rawa don kawai na faɗa mata Zeenah karuwar Abdul-Hameed 'yar wajen Abubakar Ɓaleri ce. Lallai nan gaba kaɗan zuciyarki bugawa za ta yi." Hafiz ya faɗi yana ƙara kwashewa da dariya har da riƙe ciki tuno yadda hannu da bakin Mamiyo ke rawar ɗarin tsoro.

Wayarsa ya fiddo tare da danna wasu numbers sannan ya kara a kunne tare da faɗin, "Ranka shi daɗe na faɗa mata kaine ka saka na ɗauko maka takardun kamfanin, zo ka ga yadda jikinta ke ɓari. Wallahi daga ƙarshe yanke jiki ma ta yi ta faɗi a sume. Sannan na kuma ƙara mata wani haske akan wanda kai kanka baka sani ba."

Daga can ɓangaren Ɓaleri ya furta, "Wani haske ne wannan kenan?"

Ɗan jim Hafiz ya yi kamun ya furta, "Na faɗa mata gaskiya akan karuwar da Abdul-Hameed ya ke so kuma ya mata ciki ta haihu ba kowa bace face 'yarka ta uku, Zeenatu!"

Wani irin duum tamkar an buga masa guduma a tsakar kai Ɓaleri ya ji. Zuciyarsa kuma ta yi masa wani irin mugun nauyi sakamakon danganta shi da ya yi da Zeenatun wanda shi tuni ya cire ta tare da mance ta cikin sahun 'ya'yansa.

A dake ya furta, "Ba ni da wata 'ya mai suna haka. 'Ya'yana bakwai, Maryama, Sa'adatu, Sajida, Salma, Maimunatu, Zubair da Aliyu. Ban san wata Zeenatu cikin sahun 'ya'yana ba. Kuma idan har bakinka ya kuma kuskuren haɗa ni da wannan ƙazamtacciyar sunan, ni kaina ban san irinabunda zan aikata a gareka ba!" yana gama faɗin haka ƙit ya kashe wayar.

Jiki a sanyaye Hafizu ya sauke wayar a kan kunnensa yana wani tunani cikin zuciyarsa, daidai nan wayarsa ta yi ƙara, yana dubawa ya ga Baffa Jibrila ne ke kiran wayar. Da sauri ya ɗaga yana fatan yaji ya ce masa Allah ya ɗauki abunsa, amma maimakon haka sai ji ya yi ya furta cewar ya dawo yanzu Mamiyo na biɗarshi.

"Shegiyar kaya, har ta miƙe kenan! Wannan tsohuwar akwai taurin kai, amma ki saurara don lokacinki ya kusa na tonon silili. Don walleh zame kaina zan ji daga gare ki har ga shi mai kafiyar wato Ɓalerin. Don wallahi wajen mai gayya mai aiki zan nufa na buɗewa kowa aiki.

Cikin mintuna kaɗan ya isa gidan. Ƙyam ya samu Mamiyo a zaune a kan kujera fuskan nan ciɗi-ciɗi don har wani jaa ta yi saboda ɓacin rai.

"Iyalanka za su kasance a ƙarƙashin kulawata har sai ka gama min da aikin da zan saka ka a yanzu. Idan ka kammala succesfully, fine sai ka zo ka amshe su, idan kuma ka faɗi, na rantse da Allah ko damar ganin gawauwakinsu ba zan baka ba, kuma sai na yi dabgenka cikin tukunyata na bajewa karnuka su cinye banza a banza!"

Wani irin bugawa zuciyarsa ta yi sakamakon arba da ya yi da videon iyalansa cikin wani ɗaki bakunansu a rufe da salatep kuma a ɗaɗɗaure har da ƙaramin ɗansa da bai wuce shekaru bakwai ba. Wasu maƙudan hawaye ne suka shiga kwaranyowa daga idanunsa ya rarrafo tare da kama ƙafafun Mamiyo ya shiga zuba mata magiya akan ta rufa masa asiri ta ƙyale masa 'ya'yansa da matarsa.

Hamɓare shi ta yi tare da ɗan duƙowa ta ɗago haɓarsa sannan ta furta, "Ka kashe Ɓaleri washa garin ɗaurin auren ɗan ƙaninsa wato Abdul-Hameed, sannan shi kansa Abdul-Hameed ɗin a daren washa garin auren nasa nake so kai masa yankan rago!"

Wani irin zabura Hafiz ya yi tare da matsawa baya ya zazzaro idanu alamar furgici da tsoro.

Wani murmushi Mamiyo ta saki tare da faɗin, "Tsoron na menene? Shin wannan kisan da na saka shine na farko? In ce dai kai ne ka kashe ƙanin Babiyo wato mahaifin Mardiyya saboda asirina da ya sani garin bincikensa? Ko ka mance kai ne ka kawo min gubar da na shayar da Maimunatu wanda ya dunga aiki a jikinta ba tare da kowa ya farga ba har ta kwanta dama? Wanene ya tsinke birkin motar Ɓaleri lokacin da ya ke barin gidan nan?"

Zufa ce kawai ke tsiyaya a ilahirin jikin Hafizu saboda tsabar kiɗimewa. Ya kasa ko ƙwaƙƙwarar motsi tsabar shiga tension.

"Ka tashi ka fitar min a ɗaki. Jibi iwar haka ina son jin labarin mutuwar Ɓaleri tare da takardun kamfanina da daddare kuma na Young Minister ya biyo baya. Saura aikin kuma, 'ya'yana za su gama da shi. Ku fitar min da shi!"

Ƙiii! Suka ja Hafiz har ƙofar ɗaki sannan suka watsar. Jibrila ya kalli Mamiyo tare da faɗin, "Amma kina ganin ba zai faɗawa Ɓaleri ba, don alamu ya nuna bakinsu ɗaya."

Murmushi Mamiyo ta yi tare da fad'in, "Ba zai kwatanta wannan shirmen ba don iyalansa suna a hannunmu."

Jinjina kai Jibrila ya yi yana jin gamsuwa a ransa.

Baffa Mahmuda ya kuma kallan Mamiyo tare da faɗin, "To shi kuma boss ɗin ya za muyi da shi."

Hannu Mamiyo ta kai saitin wuyarta tare da ja alamar kisa sannan suka bushe da dariya duka.

A wannan daren Habib, Jawaad, Laushi da Khairat suka duro Nigeria. Sai dai shi Habib ya riga su Jawaad isowa tun shekaran jiya. Tsayawa ya yi a Lagos domin neman Laushi don a tunaninsa Jawaad ɗin bai same ta ba don tare suka bar Nigeria kuma a rana ɗaya. Ganin bai same ta ba kuma ga biki jibi, sai kawai ya kuma hawowa jirgi shi da Amatunsa suka diro Abuja.

Jawaad ya riga Habib shigowa Estate ɗin, sai ya yi maza ya nufi gidansa ya aje Khairat da Zeenah sannan ya fito ya nufo gidan Babiyo kuma a wannan lokaci bold ɗin su Habib ya shigo estate ɗin daga airport.

Babiyo zaune a kan kujeransa ta gado yana amsa waya Jawaad ya shigo. Waje ya samu a ƙasa ya zauna yana jiran Babiyon ya kammala waya. Ya ɗau tsayin mintuna yana wayar kamun ya kammala. Yana aje wayar ya kalli inda Jawaad ɗin ya ke tare da buɗe masa hannu alamar ya taho ya rungumesa.

Ba ƙaramin mamaki Jawaad ya yi ba, amma sai ya miƙe tsam ya nufe sa tare da rungumesan.

"Allah ya yi maka albarka da zuri'arka gaba ɗaya!" Babiyo ya faɗi wanda ya saka Jawaad lumshe idanun farinciki don har ƙwalla sun taru a kwarmin idanunsa.

"Ameen, na yi kewarka sosai Babiyona!" Jawaad ya faɗi.

Jan hancinsa ya yi yana murmushi sannan ya shiga tambayar sa iyalansa, "To ya alkhairin da na haɗa, shin kana jin alfahari da haka?" Babiyo ya faɗi da sigar zaulaya abunda bai taɓa yi ba.

"Har ƙarshen rayuwata ba zan daina godiya ga ubangiji da kuma kai da kai silar wannan ƙulluwan auren ba. Haƙiƙa ne maganar da hausa suke yi na cewar duk abunda babba ya hango yaro ko ya hau rimi ba zai taɓa hangowa ba. Nagode ƙwarai kakana."

Wani irin murmushin ne ya suɓucewa Babiyo har sai da haƙwaransa ya bayyana sannan ya furta, "Je gida jikana ka huta ka yi wanka sannan ka ɗauki matarka ku tafi ku gaida iyayanku."

"Godiya na ke yi," faɗin Jawaad yana mamakin abunda ya hana Babiyo ce masa ya tafi ciki ga gaido da Mamiyo.

Fitarsa bai fi da mintuna talatin ba Habib shima ya shigo. Kamar yadda ya yiwa Jawaad haka shima ya yi masa. Kuma dukkansu ya ji daɗin amsar da suka ba shi. Shima dai umartarsa ya yi da ya je ya huta sannan ya ɗauki matarsa su gaida iyayansu.

Da daddare Babiyo ya yi kiran Meeting tare da umarta kowa ya kasance don duka anan za a haɗu aci abincin dare.

Kowa da kowa, yara da jikokin babu wanda bai ji daɗin wannan walima ba. Don hatta Baffa Belɗo da iyalansa suka wajen. Baffa Ɓaleri ne da iyalansa kawai ba sa wajen. Inna Karima da Inna Ƙarama suna gefen hagun Babiyo, yayin da Mamiyo da babu fara'a akan fuskanta ko kaɗan ke a gefen damansa. Don yanda Babiyon ke raha da jikokin nasa abunda bai taɓa faruwa ba ko cikin mafarki ba ƙaramin ƙona zuciyarta ya yi ba. Musamman ma da Babiyon ke jeho Baffa Belɗo cikin hirarsa.

"Babu komai kai rahar ƙarshe, gata iwar haka matacce ne kai!" Mamiyo ta faɗi a zuciya.

"Ina roƙon alfarma kowa, mada da mata, yara da manya akan mu duka mu azumci alhamis ɗin gobe wato jajibarin ɗaurin auren Abdul-Hameed, kuma a sati mai zuwa ne muke saka ran jin sunansa a matsayin ministern wannan birnin tarayyar. Amma fa ban tilastawa kowa ba, duk wanda ke da ya ga zai takura ba sai ya yi ba. Waɗanda za su ɗau niyya kuma, sai suka saka a ransu za su yi azumin ne da niyyar nemawa ɗan uwasu ko ɗansu zaɓin Allah akan wannan mulkin, idan har ba zai iya sauke nauyin da ke kansa ba na talakawa, kada Allah ya ɗaura shi akai, sannan kuma da niyyar samun zaman lafiya da haɗin kan wannan family da kuma kawar da fitintinu da rabuwar kai. Allah ya ba da ikon yi ya kuma sake haɗamu kamar haka a cikin aljanna firdausi."

Gaba ɗaya ɗakin da ameen aka amsa banda irin su Mamiyo da su Baffa Jibrila.

Bayan rufe taro da addu'a kowa ya yi gidansa tare da matarsa. Jawaad kuwa Allah-Allah ya ke ya isa gida sabida Laushi da suka bari ita kaɗai a gidan.

"Ya kake gudu haka akan titi kamar za mu tashi sama?" Khairat ta faɗa tana kallonsa.

Ɗan tsaki ya yi tare da faɗin, "Duba sha ɗaya ta wuce fa! Mun bar baiwar Allah ita kaɗai a gida."

"Shiyasa hankalinka ya tashi hakaa? Ni fa na lura gaba ɗaya yarinyar nan a zuciyarka ta ke. Bam tunanin ko shi mijin nata zai iya nuna damuwa haka a kanta kamar yadda kake yi."

"A'uzu billahi! Haba Khairiyyah, kar kishi ya rufe miki idanu haka mana. Matar wani ce fa!" ya faɗi yana ɗan rage gudun motar.

"Kuma ai na ga dai ba yarinya bace da za ka damu haka don mun barta ita kaɗai a gida. Ina ga nan gama cikin aljihu za ka riƙa saka ta kana yawo da ita."

Shuru bai ce komai ba har suka iso gida. Don ya nuna mata shi ba zumuɗin ganin Zeenah ɗin ya ke ba, sai kawai ya wuce bedroom ɗinsu ba tare da ko kallo ɗaya ya yiwa ɗakin da Zeena ta ke ciki ba. Kuma hakan ya mata daɗi sosai duk da ita sai da ta leƙa ta ganta kwance tana bacci.

Washa gari mutane da dama sun tashi da azumi a Arɗo Barkinɗo, irin su Mamiyo da 'ya'yanta ne kawai ba mai yi, sai dai kuma su kaɗai suka san haka. Don a wajen sauran jama'a suna yi. Sai kuma wasu daga cikin mata masu lalurarmu ta haila.

Wani ƙaramar ƙwarya-ƙwaryan walima Babiyon ya saka aka haɗa lokacin buɗe baki. Anci ansha kuma anyi raha tare da addua wa Abdul-Hameed da kuma ahalin gaba ɗaya har da su Jawaad da Habib akan Allah ya ba su zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba. Kuma kamun a watse sai da Babiyo ya roƙi yafiyar duk wanda ya ɓata wa rai bayan ya yi maganganu masu tsuma zuciya da ya saka mutane da yawa kokawa. Don hatta mutanan Yola duk sun hallara kasancewar gobe ne ɗaurin aure.

Washa gari kuwa da gagarumin biki aka tashi a estate ɗin. Tun sha ɗayaa motoci su kai zuga suka tafi ɗaurin aure Kaduna.

A gidan Jawaad kuwa, Zeenah ce kawai cikin gidan a rufe a ɗaki don Jawaad sosai ya bugawa Khairat warning akan kar ta kuskura kowa ya ga Zeenah kuma ko waye shi.

Ƙarfe huɗu su Babiyo suka dawo har da amarya da danginta. Kai tsaye Babiyo ya ce a wuce da ita gidan Baffa Belɗo wanda hakan si da ya kusa tsayar da numfashin Mamiyo. Don a al'ada dai wajenta ya kamata a kai amarya. Dakyat ta iya danne hakan a zuciyarta.

Washa gari ma da wani gaggarumin bikin aka tashi, dangin amarya Asma'u ma da su akai shagali, sai bayan la'asar Babiyo ya saka aka mayar da su gida bayan sun kai amarya ɗakinta da ke Abdul-Hameed close.

"Mama Halima, don Allah bari na ɗan je gidan Hamma Habib na kwana can, kin ga nan anyi yawa har yanzu akwai baƙin biki." Marwantu ta faɗi.

Kamar Mama Halima ta ce mata a'a, sai kuma ta ga kamar Marwanatun za ta ji ba daɗi, sai ta gyaɗa mata kai.

Da sauri ta juya ta bar ɗakin duk da kuwa dare ya yi don goma saura mintuna biyar. Wanda zai kai ya ta shiga nema don akwai nisa baza ta iya tafiya a ƙafa ba.

Jawaad ganin Khairat baccin gajiya ya dauketa sosai don tum shigowarsu ta ke gyangyaɗi a falo. Sai ya lallaɓa ya fito ya nufi ɗakin da Laushi ke kwance.

Tura ƙofar ya yi ya shiga, to his surprice idanunta biyu hannunta rike da kai tana hawaye. Bai san lokacin da ya ƙarisa ya kusa da ita ba tare da zube guiwowinsa a ƙasa ya kamo hannunta yana leƙen fuskanta tare da kama hannunta biyu da ke riƙe da kanta ya furta, "Zee! Zee mai ke damunki? Why are you crying?"

Ko kamun Zeenah ta yi magana suka soma jin wani irin tafi a bayansu wanda ya saka Jawaad ya juya a firgice, ita ma Laushi da sauri ta ɗago kai tana kallon ƙofar ɗakin.

Khairat ce tsaye sanye da doguwar rigar bacci fuskanta tamkar an aiko mata da saƙon mutuwa. Da hannu ta nuna su sannan ta ce, "Cin amanar da za ku min kenan? Matar abokin naka kake zagayowa kana fasiƙanci da ita? Ni za kai wa haka Jawaad?" ta ƙarisa maganar wasu irin ƙwallar baƙin ciki na kwaranyo mata daga idanu.

"To wallahi tallahi a yau ɗinnan ba gobe sai ta bar min gidan mijina!" ta kuma faɗi a matuƙar fusace tare da cafko hannun Zeenah tare da soma janta ƙiii tana faɗin, "Sai kin fitar min daga gidan miji karuwar banza da hofi."

Da sauri Jawaad ya bi bayan su yama faɗin, "Khairat ba abunda kike tunani bane, ki tsaya in miki bayani."

Ko sauraransa bata yi ba ta nufi ƙofa da hannun Zeenah tare da buɗe ƙofar wanda ya jawo Marwanaatu da ke shirin yin knocking ta yi sa a goshin Laushi.

Wani irin jaa da baya Marwanat ta yi tare da lailayo wani mugun ashar tare da shaƙo wuyar Zeenah......

A can side ɗin Babiyo kuma, su Jibrila sun shirya tsaf domin kashe Babiyo a wannan daren. Da taimakon Mamiyo suka siɗaɗa suka shiga ɗakinsa. Kwance ya ke akan gadon yana bacci. Duk da wuta a kashe ya ke suna hangosa lulluɓe da bargo. Farin furfuransa fes don babu wulan gadon a kansa.

Baffa Modibbo ya tsaya ta wajen ƙafafu, Baffa Tukur kuma ta daidai tsakiyarsa, sai Baffa Jibrila ta daidai kansa. Gyaɗa masa kai Baffa Tukur ya yi, sai ya ya yi saurin ɗaga filon ya ɗaura a kan Babiyo da ƙarfi tsiya.

Wani irin firgita suka yi su duka sakamakon haske da ya gauraye ɗakin. Tsaye ya ke a daidai inda switch ɗin ya ke hannunsa goye a bayansa yana kallonsu da mugun ɓacin rai.

"Ni kuke shirin kashewa Jibrila? Ni mahaifin na ku?"

(Caɓ! Walleh ban da ta cewa. Na san dai da safe akwai tashin bomb. Mai rabon ganin baɗi ya gani)

#Bomb blast #Abdul-Hameed #Jawaad #Zeenah #Khairat #Laushi #Marwanat #Babiyo #Mamiyo #Baffa Jibrila #Baffa Tukur #Baffa Mahmuda #The battle #My Destiny #Matar Sayyadee *** [8/18, 10:47 PM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)

*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee

☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`