My Destiny (Ƙaddarata)

Page 60

by @matarsayyadee3

*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***

Domin shiga comment section kuma ki danna wannan link ɗin👇🏼 *** *_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining link ɗin da ke sama domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜

_*💃🏻💃🏻 _Kuna ina 'yan uwana matar aure da 'yan mata? Shela nake ko wacce ta fito domin kuwa yau na zo maku da albishiri! Kun san matar Sayyadee ta ku ce ba ta samun abun ƙaruwa ta yi shuru domin ta ƙaru ita kaɗai._💃🏻💃🏻

💐💐🌼🌼_Magana ake ta ƙamshi. Toohwa! Mai ya hwaru?_ 🤔 🌷🌷🌸💮

*To maza ku marmatso ga sirrin nan. Shahararriyar nan wacce ke inganta soyayya tsakanin ma'aura wato Fatima Zaransalaty inkiya Queen Zarah ce ta taho mana da wani ƙamshim domin cika hancinar mazajemu da ƙamshi*. _INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_ _TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA KUJI 💃🏻

_Zaran Salaaty ta yi tafiya miƙaƙƙa har Sudan domin farnata ranmu da na mazajenmu ta kawo mana Sudanese perfume👌🏻 wanda idan har kika shafa shi a jikinki ko kin yi wanka ƙamshin bai barin jikinki. Tested and Trusted ƴaruwa. Zaransalaty ba iya sudanese perfume ta kawo maku ba, akwai kayayyaki masu matuƙar inganci na gyaran HQ (kun san dai ba a wasa da headquarter) akwai kayan gyararrakin jiki kala-kala na ƴan mata da matan aure. Sannan Zaransalaty tana sai da Decoration na kayan ɗaki iri-iri wanda baki taɓa ganinsu._

_KAR IN CIKA KI DA SURUTU, KE DAI NEMI ZARANSALATY A NUMBERS ƊINTA KAMAR HAKAA_: *** Or ****

*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_nfection_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_

_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ ***** *****

Duk irin zafin zuciya, fushin, da taurin zuciyar Babiyo, yau sai zuciyarsa ta yi wani irin nauyi da kuma sanyi. Raunin sosai ya nuna a jikinsa wanda ya bayyanar da rashin kuzari da sanyin jiki. Idanunsa sun kaɗa sun yi jazur duk da kuwa ƙwalla ba su taru ba. Kallon su ya riƙa yi ɗaya bayan ɗaya. Gaba ɗaya sun ƙame ƙam tamkar gumaka, sai wata uwar zufa ce ke tsiyaya a ilahirin jikinsu.

Baffa Jibrila kuwa tuni ya soma kuka ƙafafunsa na wani irin rawa tamkar zai karye kasancewar shine mai ƙwarin guiwar danna filon ɗin a fuskan Babiyon.

"Saboda dukiya ko? Saboda dukiya ku ke shirin kashe ni ku ci gado ku da uwarku ko? Mai na muku a duniyar nan? Na baku ilimi duka biyu, tarbiyya ma na yi iyakacin gwargwadona, na baku aiki a kamfani tare da yanka muku albashi mai tsoka sannan na baku muhalli tare da yi maku auren. Dukkan ku nan babu wanda na bambamta shi da sauran 'yan uwansa, har da Belɗo da Ɓalerin da ku ke tunanin na fifita su akan ku saboda matsayinsu ya fi na ku a kamfani. Komai ɗaya nake maku ku duka. Idan akwai wanda na tauye ma to Modibbo ne. Shine bai samu gatan da kuka sa mu ba. Na tura shi Lagos ko waiwayansa ban yi shi da uwarsa, kuma a hakan bai taɓa gazawa ba wajen yi min biyayya. Da na ɗaga waya na kira shi ya ke amsa kirana kuma ya yi duk abunda na umarce shi duk irin banzatar masa da uwa da na yi. Kun ɗauka ku kaɗai ku ka iya plan? Kun ɗauka ku da uwarku kawai ku ka iya tsara shiri ya yi aiki? To ku duka a tafin hannuna kuke, babu wani motsinku da ban sani tun shekaru uku baya da suka wuce. Tabbas da uwarku ta yi nasara a kaina tunda har ta iya raba ni da 'ya'yana masu matuƙar yi min biyayya a rayuwa, sai dai idan ita da asubar fari ta fito, ni kuma kwana na yi a hanya." Yana gama faɗin haka ya tafa hannunsa sau biyu, sai ga Baffa Ɓaleri ya fito daga maɓoyarsa yana watsawa 'yan uwan nasa wani irin kallo.

Sake tafa hannu Babiyo ya yi, sai ga CID guda huɗu sun fito, ɗaya daga cikinsu hannunsa riƙe da camera, don tun shigowar su Baffa Jibrila camera ke ɗaukar su hoto duk da kuwa duhu ne a ɗakin hotarsu tar ta fito saboda akwai light a jiki.

Tsiii sai ga Baffa Jibrila na tsiyayar fitsarin tashin hankali. Kallon inda fitsarin ya ke bi Babiyo ya yi tare da yin murmushi mai ƙona zuciya sannan ya amshi takardar da ke hannun Ɓaleri da ke nuna shaidar kamfanin na Mamiyo ne da 'ya'yanta, don sunan kamfanin _Laurat and sons company limited_. Miƙawa Jibrila ya yi, amma sai ya kasa ɗaga ko ɗan yatsarsa har sai da Babiyo ya buɗe hannunsa ya saka masa file ɗin tare da faɗin, "Ka na da courage ɗin danna min filo a fuska ko? To ƙarisa abunda ka ke shirin yi Jibril," ya faɗi tare da kwanciya flat a kan gadon wasu siraran hawaye na gangaro masa.

Saurin sunkuyar da kai Ɓaleri ya yi tare da soma tsiyayar da nashi hawayen don tunda uwarsa ta haifesa bai taɓa ganin ƙwallar Babiyon ba sai yau. Yau da ya gani sai abun ya taɓa zuciyarsa sosai.

Rintse idanu Babiyo ya yi sosai yana tariyo irin tozarci da wulaƙancin da ya yiwa 'ya'yan Maimunatu guda biyu, musamman ma Ɓaleri. Kawai sai ji suka yi Babiyo ya fashe da kuka. Daga Ɓelerin har su Jibrila jikinsu ya fara wani irin karkarwar tsoro da tashin hankali jin fitar sautin kukan Babiyu.

Da hannu Babiyo ya yiwa CID ɗin nan alama da su fita su jira shi a waje don ya kasa motsa bakinsa. Cikin sauri suka nufi ƙofa, sai dai kamun su buɗe Mamiyo ta riga su buɗewa ta shigo.

Ƙam ta ƙame tana mai furta, "Shikenan mun mutu yau!"

Gitta ta CID suka yi tare da fita suka rufo ƙofar da ita a ciki.

Babiyo kuwa jin saukar muryanta si ya yi zumbur ya tashi zaune tare da shanye hawayensa ya kalle ta ido cikin ido sannan ya ce, "Aurenki da na yi na kawo ki cikin gidana bai ƙare ni da komai ba sai musiba da tashin hankali game da aikin dana sani! Ba zan tambayeki abunda ya sa kika gurɓata min tarbiyan 'ya'yana ba, kuma ba zan tambayi menene dalilinki na hakan ba. Sai dai tambaya ɗaya zan miki, kuma ya zamaa dole ki ban amsa! Mai yasa kika kashe min Maimunatuna?" yadda ya ƙarisa maganar a zafafe sai da ɗakin ya yi amsa kuwa.

Waro idanu Mamiyo ta yi tana kallon ɗanta wanda shi ke bi ma Baffa Jibrila, wato Baffa Lawal yana fitowa daga tasa maɓoyar. Duk da ta san shi bai shiga sabgarsu ita da sauran 'ya'yanta, amma bata taɓa kawowa ko cikin mafarki zai iya buɗe mata aiki wajen Babiyo ba saboda tana taƙama da soyayyar da yake mata da kuma biyya kaf cikin 'ya'yanta.

"Auwalu! Auwalu ni uwar da na duƙa na haifeka cikin azaba za kai wa wannan cin amanar? To ka je Allah ya ɗebe maka duk wani albarkar da ke tattare da kai, kuma sai ka yi mutuwar ƙwanƙwalati!" Mamiyo ta faɗi tana nuna shi da yatsa.

Kuka mai ƙarfi Baffa Lawal ya fashe da shi tare da faɗin, "Na kasa jure abunda kike yi. Na yi ƙolarin nusar da ke amma kin kasa ganewa saboda son duniya ya gama rufe miki idamunki. Kin tura kanki cikin halaka wacce za ki dauwama cikinta kuma na tabbata idan ba ki tuba ba ita ce za ta kai ki ga shiga wuta! Ɗaukar alhakin ya yi yawa shiyasa na fayyacewa Baffanmu komai. Sai dai abunda ba ki sani ba, Baffa rami ya miki ke kuma kika afka, don ko wani takunki a hannunsa ya ke. Jiya Hafizu ya zo ya shaida min duk yadda kuka yi ana saura kwana biyu ɗaurin auren Abdul-Hameed. Ni kuma ban yi ƙasa a guiwa ba na zo na faɗawa Babiyo don ba zan taɓa bari ki kashe Abdul-Hameed da Babiyo ba......" _GIDAN JAWAAD_ Wani irin shaƙo wuyan Zeenat ta yi tare da soma kaiwa hancinta naushi tana faɗin, "Yau sai na kashe ki kamar yadda kika kashe min aurena. Sai na halaki tsinanniyar karuwa. Annoba, baƙar ashana ƙona gari!"

Finciko Zeenah a hannun Marwa Khairat ta yi daidai lokacin da Jawaad ya iso wajen ya riƙa ɗauke fuskan Marwanat ɗin da Mari hagu da dama.

Ko bi ta kan zafin marin ba ta yi ba, ƙoƙarinta kawai ta damƙo Zeenat da gaba ɗaya jikinta ke sakewa a hankali.

"Ke kina hauka ne! Wannan fa matar abokin Hamma Jawaad ce, ba ma anan garin take ba. You must be mistaken." Khairat ɗin ta faɗi tana ƙoƙarin riƙe hannun Marwanat.

Shi kuwa Jawaad da gudu ya taro Zeenat da ke ƙoƙarin faɗuwa ƙasa a jikinsa yana ƙwala kiran sunanta tare da jijjigata.

"Wallahi tallahi ita ce. Ko a cikin jahannama mai cike da mutane zan iya nuna ta! Wannan da kike gani Karuwa ce, bata taɓa aure ba. Ƙarya ne ba matar abokinsa ba ce. Duk faɗin garin Lagos babu namijin da bai santa ba. Shahararriyar karuwa ce. Ita ce ta raba ni da mijina. Na san kin samu labarin yarinyar da na bi gidan karuwai na yi faɗa da ita har ta sanadinta na cakawa Nura wuƙa ciki, to wallahi ba kowa bace sai ita. Kuma yau ɗin nan duk wanda ya nemi hana ni kasheta wallahi shi ma sai na kashe shi."

Da wani irin tsantsan mamaki Khairat ta juya ta kalli inda Jawaad ya ke, sai abunda idanunta ya gane mata ya saka ta kuma waro su akan Jawaad ɗin da ke rungume tsam da Zeenah yana ƙwala kiran sunanta.

Ita kuma Zeenah tun hayaniyar farko a ɗaki lokacin da Khairat ta shigo ta gan su da Jawaad kanta ya shiga juyewa fiye da yadda Jawaad ɗin ya zo ya same ta. Kuma dama farkawarta kenan daga bacci saboda wasu hotuna fuskoki da suka riƙa mata gizo a mafarkinta da kuma lokacin da ta farka. So ta ke ta fahimci komai don tabbas ta san fuskokin nan sai dai kuma ta rasa a ina. Hoton fuska Meemaa ce ta fara zuwa mata, sai na Abdul-Hameed, Ladi Katifa, mahaifiyarta, 'yan uwanta (Su Maryamaa) da kuma hoton Salma nice sai na gidan hajja Lanti.

"Kan kaza-kazan cen kayyasa! Jawaaad!! Mace rungume a jikinsa? Ashe dama kai maƙaryaci ne, azzalami? Ka kawo min karuwa har cikin gidana, ka saka ina ta ɗawainiya da ita tun a wata ƙasar, ashe duk karuwarka na ke wa wannan bautar! Ni ce yi mata girki, kula da magungunar da take sha, duba ta ko wani dare domin tabbatar da lafiyanta, ashe duk karuwa na ke wa! Ka cuce ni Jawaad, zama na da kai ya ƙare." ta ƙarisa maganar tare da rushewa da kukan baƙin ciki.

"Khairiyya, ki nutsu zan miki bayanin komai. Wallahi ba abunda kike tunani bane. Ni ba fasiƙi bane zan iya rantse miki da alkur'ani!" Jawaad ya faɗi a sanyaye don ko kusa bai ji haushin maganganun Khairat ɗin ba. Don shi shaida ne macece mai biyayya da haƙuri.

Wani mugun harara Marwanatu ta jefi Jawaad ɗin da shi tana jin tkar ta shaƙe duk ta kalle shi sabida Laushin da har wannan lokacin tana kwance a kan cinyarsa a some.

"Taimaka ki ban ruwa in yayyafa mata suma ta yi," ya faɗa yana kallon Khairta.

Cikin wani irin mugun sauri Marwantu ta nufi kitchen ɗin Khairat ɗin tare da kandamo ruwa cikin babban jug sannan ta soke wuƙa a cikin jani tare da fitowa. Kai tsaye ta nufi inda Jawaad ya ke ta antayawa Laushi ruwan gaba ɗaya a jikin har shi ma sai da ya samu na shi rabon.

A mugun firgice Zeenah ta farfaɗo tare da miƙewa ta tsaya ƙem a tsaye tana kallon kowa na ɗaki na kusa daƙiƙa biyar kamun ta mayar da kallonta kan Jawaad a firgice ta furta, "Ina 'yata, ina Meemata take?"

Wani irin nannauyen ajiyar zuciya Jawaad ya saki don yanzu ya tabbatar memory ɗin Zeenah ya dawo tass!

Kukan kura Marwantu ta yi bayan zaro wuƙa daga jikinta ta nufi kan Zeenah. Ihu Khairat da ke fuskantar Marwa ta yi, don tun lokacin da ta fiddo wuƙar ta ganta.

A zabure Zeenat ta sheƙa a guje ta nufi ƙofar fita daga falon. Da gudu Jawaad ya rufa musu baya Khairat biye da shi.

Gudun ceton rai kawai Zeenah ke yi ba tare da sanin inda ta nufa ba, Marmawat ma ba ta daina binta da gudun ba, haka Jawaad da Khairat da ke sanye da kayan bacci doguwar riga mai santsi.

Jawaad kasancewarsa namiji kuma duk ya fisu gudu, shi ya yi nasarar cimma Marwa bayan gudu mai tsayi tare da taɗiyeta ta yi mummunar faɗuwa a kan titi sannan ya amshe wuƙar hannunta tare da rufawa Zeenah baya har ya yi nasarar cafko ta jikinta babu inda ba ya ɓari. Daidai nan wata mota ta faka a gabasu.......

(To wanene kuma wannan 🤔)

Ku yi maleji😴

#Babiyo #Mamiyo #Ɓaleri #Baffas 😂 #The CIDs #Jawaad #Zeenah #Khairat #Marwanat #Memories back #My Destiny #Matar Sayyadee *** [8/18, 10:47 PM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)

*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee

☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`