My Destiny (Ƙaddarata)

Page 61

by @matarsayyadee3

*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***

Domin shiga comment section kuma ki danna wannan link ɗin👇🏼 *** *_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining link ɗin da ke sama domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜

_*💃🏻💃🏻 _Kuna ina 'yan uwana matar aure da 'yan mata? Shela nake ko wacce ta fito domin kuwa yau na zo maku da albishiri! Kun san matar Sayyadee ta ku ce ba ta samun abun ƙaruwa ta yi shuru domin ta ƙaru ita kaɗai._💃🏻💃🏻

💐💐🌼🌼_Magana ake ta ƙamshi. Toohwa! Mai ya hwaru?_ 🤔 🌷🌷🌸💮

*To maza ku marmatso ga sirrin nan. Shahararriyar nan wacce ke inganta soyayya tsakanin ma'aura wato Fatima Zaransalaty inkiya Queen Zarah ce ta taho mana da wani ƙamshim domin cika hancinar mazajemu da ƙamshi*. _INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_ _TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA KUJI 💃🏻

_Zaran Salaaty ta yi tafiya miƙaƙƙa har Sudan domin farnata ranmu da na mazajenmu ta kawo mana Sudanese perfume👌🏻 wanda idan har kika shafa shi a jikinki ko kin yi wanka ƙamshin bai barin jikinki. Tested and Trusted ƴaruwa. Zaransalaty ba iya sudanese perfume ta kawo maku ba, akwai kayayyaki masu matuƙar inganci na gyaran HQ (kun san dai ba a wasa da headquarter) akwai kayan gyararrakin jiki kala-kala na ƴan mata da matan aure. Sannan Zaransalaty tana sai da Decoration na kayan ɗaki iri-iri wanda baki taɓa ganinsu._

_KAR IN CIKA KI DA SURUTU, KE DAI NEMI ZARANSALATY A NUMBERS ƊINTA KAMAR HAKAA_: *** Or ****

*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_nfection_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_

_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ ***** *****

Da sauri ya fito daga motor don da da farko har ya yi gaba sai kuma ya dawo baya ganin kamar Jawaad. Shima kuma Amatu ce ta saka shi fita nemo mata tsamiyar biri da ɗanyen kuɓewa wai shi take son cin a wannan daren. Sai dai haka ya gama bulayinsa bai samu ko ɗaya ba sai rake yana fatan ta sha ta kwanta ta barshi ya huta don gobe ya ke son komawa Lagos akan batun Laushinsa.

Daam! Gabansa ya buga da ƙarfi ganin kamar maman Meema ce tsaye kusa da Jawaad ɗin. Wani irin miƙa hannu ya yi tare da juyo ta gaba ɗaya yana kallon cikin idanunta kamun ya furta, "Maman Meema!" a kan laɓɓansa, can kuma ya ƙwala kiran sunan nata da ƙarfi yana shirin rungumeta amma sai Jawaad ya yi saurin shiga tsakaninsu fuskan nan nasa a matuƙar murtuke.

Shi kuwa Habib sam bai fahimci yanayin ɗan uwan nasa ba sai kawai ya rungumesa tare da fashewa da kuka ya furta, "You're really a true friend ɗan uwana! Ban san da bakin da zan yi maka godiya ba akan wannan abun da kai min. Naji daɗi kuma nagode. Wallahi da gobe na ke shirin komawa Lagos domin neman ta. Maman Meemata!" ya ƙarisa maganar bayan sakin Jawaad yana ƙara kallon Laushin daidai zuwan Khairat da Marwanat da ke ɗingisawa.

"Ke! Dama kina gidan Jawaad? Tun wajen ten Mama ta kira ni ta shaida min kin ce za ki zo ki kwana gidana." faɗin Habib don tun fitar Marwan ta kira Habib ta shaida masa, sai shikuma ya faɗa mata bai gida ya ɗan fita.

Maimakon Marwa ta ba shi amsa, sai kawai ta faki idanun Jawaad ta cacumi Zeenah da dambe. Ita kuwa Zeenah dama a wuya take, ɗazun ma don akwai makami a hannunta ne. Wani irin dambe suka hau yi kowacce na ƙoƙarin ganin ta kai 'yar uwarta ƙasa. Da ƙyar dai Jawaad da Habib suka raba faɗa. Habib ya janye Laushi, shi kuma Jawaad ya janye Marwanatu.

"Me ke faruwa haka? Ke kina hauka ne za ki kama ta da dambe?" Habib ya faɗi.

Kuka Marwa ta fashe da shi tare da faɗin, "Wallahi sai na ga bayanta zan haƙura! Ita ce fa ta kashe min aure. Ita ce wannan karuwar da ta shiga tsakanina da Nurana."

Waro idanu Habib ya yi yana tariyo labarin da Marwan ta ba shi lokacin tana kulle a ɗakin da Baffa Modibbo ya yi prison ɗinta a Lagos.

"Maman Meema," Habib ya yi kiran sunanta yana mai riƙe hannunta guda ɗaya.

Saurin fizgewa ta yi tare da faɗin, "Menene dalilin kawo ni nan ɗin? Ku bani 'yata in fita in bar nan. Ku ban 'ya na ce!" ta ƙarisa maganar tana kuka.

Da sauri Habib ya kalli Jawaad tare da faɗin, "Jay ina Meema?"

Watsa hannu Jawaad ya yi tare da faɗin, "Don't really know."

Ihu Laushi ta saki mai ƙarfi tana neman yi musu hauka. Da ƙarfi Jawaad ya furta, "Shut up, my dear! Ke mai yasa duk lokacin da kike cikin tashin hankali ihu ne kawai ya ke zuwa ƙwaƙwalwarki?"

Dafa shi Habib ya yi tare da faɗin, "Ka bita a hankali, Jay. Dole ne hankalinta ya tashi. Ni shaida ne a kan irin ƙaunar da take wa 'yarta."

"Stay out of this malam ka kama hanya ka wuce gidanka tare da wannan mahaukaciyar yarinyar kamun zuciya ta ɗebe ni na kakkaryata." Jawaad ya ƙarisa maganar yana nuna Marwa.

Wani kallon mamaki Habib ya yiwa Jawaad, sai kuma dai ya haɗiye abunda ke ransa tare da kallon Zeenah ya furta, "Get inside the car, Maman Meema." ya faɗi hakane yana nuna mata motarsa.

Da sauri Jawaad ya fizgo hannu Laushi tare da faɗin, "Do not allow me to show you the real other side of me! Na faɗa maka to stay far away from Zeenah, domin auranta zan yi."

Wani dariya Habib ya yi mai tafe da tsantsan mamaki da baƙin ciki kum ya furta, "Are you for real?"

Khairat kuwa wani irin tsayuwa ta yi a gaban Jawaad tare da faɗin, "Matar abokin naka za ka aura? Ba gane ba! Ina ta ƙoƙarin danne zuciyata domin gasgata ƙanzan kuregen da ka faɗamin akan wannan cewar matar abokinka ne sun yi aure ba tare da sanin iyayansu ba bla-bla-bla.... Yanzu kuma kana faɗin wai za kai me? Sake maimaitawa in ji!" ta faɗi a rikice da kuma tashin hankali.

Marwanatu kuma wani dariyar rainin hankali ta yi tare da faɗin, "Wato karuwancin na ki bai tsaya a kan mijina kawai ba har da 'yan uwana ko?"

"Khairat, kar ki shiga maganar nan yanzu. Ki bari idan muka koma gida zan miki bayani." Jawaad ya faɗi bayan ya kalle ta.

"Na gaji! Na gaji da wannan bayanin ƙaryar taka. Wallahi ka ba ni kunya Hamma Jawaad, yanda na ke ganin ƙima da girmanka yanzu ban gani. Da girmanka ka karkace kai ta shimfiɗa min karya tamkar na ƙwarai. Ni wallahi yanzu Allah ɗaya kawai za ka ce min in yarda."

"Zeenah, ki wuce mu tafi na ce!" Habib ya kuma faɗi sounding very angry.

"Ka ga wasa a idanuna ne, Habib? Kar ka bari aminta da zumuncinmu ya lalace, don akan Zeenah zan iya aikata komai wallahi."

"I'm really disappointed on you, Jawaad. Amanar da na baka kenan? Ashe kai ba cikakken ɗan adam bane? Kai maƙaryacine kuma maciyi amana. Kuma ina so ka sani In sha Allah da kai za a shafa fatihar aurena da Zeenah, sai dai ka faɗi ka mutu!"

Murmushin gefen baki Jawaad ya yi sannan ya gyara tsayuwarsa tare da kama hannun Laushi ba tare da ya kuma furta ko kalma ɗaya ba.

Ita kuwa Laushi tamkar wawuya haka ta tsaya tana kallon su tana jinjina hauka da wautarsu a zahiri. Don ita burinta kawai ta ga 'yarta sannan ta tafi biɗar Meed ɗinta da ta ke wa wani irin mahaukacin so da ƙauna. So ta ke ta gansa ta yi kuka a ƙirjinsa tare da nuna masa abunda suka haifa sannan ta tambaye sa dalilin da ya sa ya barta tsayin shekaru ba tare da ya neme ta. Sosai take da abubuwa a zuciyarta wanda ta ke so ta tattauna da wani domin ta samu amsar wasu tambayoyi, kuma Meed ne kawai zai iya amsa mata su a halin yanzu. Kewa sosai take ji na mahaifiyarta da 'yan uwanta.

Ihu ta saki jin alamar ana neman tsinka mata hannu. Kallonsu ta yi ganin kowannen su ya ja hannunta yana neman janye ta zuwa garesa.

''Ku sake ni! Ni ban son ko ɗaya daga cikin ku. Na roƙe ku da Allah ku faɗa mininda 'yata take na kama kaina."

"Babu inda za ki je kina tare da ni!" duk su biyun suka faɗa a tare.

Kauuu! Jawaad ya ɗauke fuskan Habib da zazzafan mari, shi ma Habib bai yi wata-wata ba ya sauke masa nasa sawayen. Cikin daƙiƙu suka cacumi kwalar rigar juna abunda tundaga yarinta ba su taɓa kwatantawa ba sabida an gina masu biyayyan na gaba da su cikin zuciya ko da kuwa daƙiƙa ɗaya ɗan uwanka ya ba ka.

Laushi kuwa wani irin juyawa ta yi tare da soma tafiya don baza ta iya tsayawa ganin wannan haukan ba. 'Yarta kawai ta ke biɗar gani. Tunani ta soma yi ta inda za ta fara neman Ladi Katifa don kwata-kwata ba ta ma san ko a ina take ba. Rass! Gabanta ya faɗi ta tsaya cak tunowa da abunda ya faru da ita last a Lagos kamun ta shiga yanayinta na motsawar raunanniyar jijiyar jinin ƙwaƙwalwa. A hankali kuma zaman da ta yi a Denmark ya dawo ras a kanta. Don dama ko da memory ɗinta ya dawo ba komai bane ya dawo mata lokaci guda.

"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'u! Yasaar, Meemata. Shikenan na shiga uku na lalace." ta faɗi da ƙarfi tare da kwasa a guje tamkar mahaulaciya.

Habib ne ya fara hangota saboda Jawaad ya yi nasarar kaisa jikin motarsa tare da ɗaga hannu zai kai masa naushi amma kuma sai ya fasa.

"Maman Meema!" Habib ya faɗi da ƙarfi tare da nasarar ture Jawaad da dukkanin ƙarfinsa sannnan ya bi bayanta da gudu, Jawaad ɗin ma ya rufa masa baya.

Marwanatu ganin duk sun kwasa a guje, sai kawai ta buɗe motar Habib ɗin ta shiga tare da tadata don ya bar key a jiki ta nufi gidan Babiyo.

Khairat kuwa silalewa ta yi a ƙasa tare da fashewa da kuka ta shiga faɗin, "Menene abun so a jikin karuwa da har amintattun 'yan uwa biyu suke shirin kashe kawunansu a kanta? Anya kuwa ba asiri yarinyar tai masu ba?"

#Jawaad #Habib #Zeenah #Khairat #Marwanatu #My Destiny #Ƙaddarata #Matar Sayyadee *** [8/18, 10:47 PM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)

*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee

☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`