Page 62
Aje ai following channel ɗina please 🙏🏼 ***
*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***
Domin shiga comment section kuma ki danna wannan link ɗin👇🏼 *** *_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining link ɗin da ke sama domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜
_*💃🏻💃🏻 _Kuna ina 'yan uwana matar aure da 'yan mata? Shela nake ko wacce ta fito domin kuwa yau na zo maku da albishiri! Kun san matar Sayyadee ta ku ce ba ta samun abun ƙaruwa ta yi shuru domin ta ƙaru ita kaɗai._💃🏻💃🏻
💐💐🌼🌼_Magana ake ta ƙamshi. Toohwa! Mai ya hwaru?_ 🤔 🌷🌷🌸💮
*To maza ku marmatso ga sirrin nan. Shahararriyar nan wacce ke inganta soyayya tsakanin ma'aura wato Fatima Zaransalaty inkiya Queen Zarah ce ta taho mana da wani ƙamshim domin cika hancinar mazajemu da ƙamshi*. _INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_ _TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA KUJI 💃🏻
_Zaran Salaaty ta yi tafiya miƙaƙƙa har Sudan domin farnata ranmu da na mazajenmu ta kawo mana Sudanese perfume👌🏻 wanda idan har kika shafa shi a jikinki ko kin yi wanka ƙamshin bai barin jikinki. Tested and Trusted ƴaruwa. Zaransalaty ba iya sudanese perfume ta kawo maku ba, akwai kayayyaki masu matuƙar inganci na gyaran HQ (kun san dai ba a wasa da headquarter) akwai kayan gyararrakin jiki kala-kala na ƴan mata da matan aure. Sannan Zaransalaty tana sai da Decoration na kayan ɗaki iri-iri wanda baki taɓa ganinsu._
_KAR IN CIKA KI DA SURUTU, KE DAI NEMI ZARANSALATY A NUMBERS ƊINTA KAMAR HAKAA_: *** Or ****
*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_nfection_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_
_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ ***** *****
Gugu ta yi ta shararawa akan titi tamkar za ta tashi sama, su ma kuwa ba su daina bin bayanta a guje ba.
Fuuuu motar Habib da Marwanatu ke ciki ta wuce da gudun tsiya. Babu wanda ya damu da itan a cikin su Jawaad ɗin don hankalinsu kwata-kwata ba a wajen ya ke ba.
Caraf ya Jawaad ya yi nasarar cafkar hannun Zeenah. Fizge-fizge kawai ta ke yi tana ƙwalla kiran sunan Meema.
Habib na isowa wajen ya fizgi Laushi tare da faɗin, "You're very stupid Jawaad! Ka kuwa taɓa ganim tsantsan fusata da ɓacin raina kuwa? Kai wani irin wawa kuma maciyi amana ne?"
"Shut up!" Jawaad ya faɗi a tsawace tare da mayar da dubansa ga Zeenah da jikinta ya saki alamar somewa. Wani irin cicciɓarta ya yi tare saɓawa a kafaɗa ya shiga tafiya kasancewar ba bu nisa sosai daga inda suke zuwa Arɗo Barkinɗo specialist Hospital.
Ganin halin da Zeenah ke ciki shi ya hana Habib cigaba da tada jijiyoyin wuya. Don yana ganin jikin maman Meema a sake jikinsa ya hau rawa ya shiga bin bayan Jawaad ɗin da ke ɗauke da ita a kafaɗa.
Khairat ta fi ƙarfin mintuna talatin zaune a kan titi ga shi dare ya yi sosai. Kuka take yi sosai ganin yanda mijinta Jawaad ya banzatar da ita saboda karuwa ba tare da ya waiwayeta ba bare ya tuna ya barta kan titi a banza. Miƙewa ta yi a hankali tare da soma tafiya har ta isa gida, don ma Allah ya sa ba su yi mugun nisa da gidan ba. Tana shiga ta faɗa kan gado ta shiga rizgar wani irin kuka mai taɓa ƙona zuciya. Sai ta ji gaba ɗaya auren Jawaad ɗin ya fice a ranta. Ƙima da mutuncinsa duk sun bi kwalta.
_BABIYO_ "Ni kake kallo kana faɗawa duk haka, Auwalu? Ni!?" Mamiyo ta faɗi tana nuna kanta.
"Ke, Lauratu! Kar ki kuskura ki kuma faɗin mummunar kalma a kan ɗana ɗaya da ya fita zakka. Tabbas nononki dafi ne kuma mai tsatsa, shiyasa ƴaƴana uku da kika shayar suka gurɓace, ɗayan ne kawai Allah ya kuɓutar min da shi. Domin mahaliccinmu shi da ƙansa ya ce yana fitar da rayayye a cikin matacce, sannan ya fidda matacce a cikin rayayye. Allah ya cire min zakka daga cikin tsatsonki Lauratu, wallahi ba zan iya yafe miki wannan abun da kika aikata min ba. Kin cutar dani kin cutar min da ahalina, ki faɗamin mai ya sa kika kashe mini Maimunatuna!" ya ƙarisa maganar tare da isa gabanta ya shaƙi wuyarta.
Kowa na ɗaki ya girgiza tare da shiga mamakin yadda Babiyo ya yi wuf lokaci guda duk da jikin tsufa ya isa gaban Mamiyo cikin sakanni tamkar iska.
Wani irin kakari Mamiyo ta soma yi tana neman ƙwace hannun Babiyon da ke bisa wuyanta.
Ɓeleri ne ya yi ƙarfin halin isa wajen da suke ya shiga ƙoƙarin cire hannun Babiyon daga wuyar Mamiyon. Da ƙyar ya yi nasarar hakan don ba ƙaramin ƙarfi Babiyo ya saka wajen shaƙe wuyanta ba. Hannunsa ya kama ya fitar da shi daga falon.
Kuka Babiyo ya ke yi sosai don hatta jikinsa rawa ya ke yi sosai tamkar mazari. Zaunar da shi ya yi bisa cuisine sannan ya duƙa a gabansa tare da faɗin, "Baffa!" sai kuma ya yi shuru yana ƙoƙarin tattaro jarumtarsa domin kwantarwa tsohon nasa hankali. Don shi kansa a tafashe ya ke da Mamiyon. Ji ya ke tamkar ya samu bindiga ya saita kanta ya ɗirma mata har sai kanta ya tarwatse.
Buum! aka bugo ƙofar da wani irin ƙarfi wanda ya saka daga Ɓaleri har Babiyo suka ɗago da sauri tare da zubawa ƙofar idanu. Shi Ɓaleri sam bai gane ta ba, don ita haihuwar Lagos ce shi kuma bai ma taɓa zuw Lagos ɗin ba. Kuma idan sun shigo Abuja ita da mahaifiyarsa bai fiye ganinta ba, kuma bugi da ƙari ta girma yanzu. Babiyo ne a kallo na farko da ya yi mata ya ɗan ja dogon tsaki don shi abunda ke gabansa ya saka shi mancewa da sha'aninta don so ya ke ya gyara mata zama akan abubuwan da ta aikata idan ya natsa.
"Wannan kamar 'yar wajen Modibbo ko?" ya faɗi hakan saboda ganin kamanni. "Mai ya faru cikin daren nan? Ɓaleri ya kuma faɗi yana kallonta ganinta tamkar an hankaɗota.
Ita kuwa Marwa bin ɗakin ta ke yi da kallo ganin baƙin fuskan da ba ta san su ba. Can kuma sai ta yi saurin dawowa cikin hayyacinta tuno abunda ya kawo ta cikin gidan. Kai tsaye ta nufi Babiyo tare da zubewa a gabansa ta saki wani tsumamman kuka sannan ta shiga faɗin, "Ga Hamma Jawaad da Habib can za su kashe kawunansu akan Karuwa! Kuma karuwar ba kowa bace face yarinyar da ta raba min aurena da uban 'ya'yana. Yanzu haka suna can bisa titi za su kashe kansu a kanta don kowannen su,na ikirarin kashe ɗan uwansa."
Da sauri Babiyo ya ɗago idanu ya zuba mata, can kuma ya kai hannu saitin zuciyarsa ya dafe ga wani tari da ya sarƙe shi ya shiga jerawa tamkar zai bar duniyar.
Tarin nasa ne ya jawo hankalin Mamiyo da 'ya'yansa suka fito daga ɗakin. Cikin sauri Baffa Lawal ya ƙariso wajen ya tallabosa ta gefen hagu kasancewar Ɓaleri na gefen damansa.
Ganinfa Babiyo tabbas zai iya mutuwa donhar jini ya soma biyowa ta hancinsa, Ɓaleri bai san lokacin da ya kinkimesa ya fice da sauri ba, Baffa Lawal biye da shi a baya.
Mamiyo kuwa wani murmushin daɗi ne ya suɓuce mata tare da furta, "A sauka lafiya" a kan leɓenta.
Sai dai abunda ya matuƙar shocking ɗinta shine lokacin da ta leƙa waje ta window sai ta hango jami'ai zageye da gidan kowanne hannunsa riƙe da bindiga kuma fuskan nan ba annuri ko kaɗan. Wani ja da baya ta yi tana mai dafe ƙirji tare da kallon su Jibrila da su ma hankulan na su a tashe ya ke musammam ma Jibrilan.
Hanyan da zai sadata da ɗakinta ta yi bayan yi masu alama da hannu akan su kwantar da hankalinsu duk da ita ɗin ta ma fi su shiga tashin hankali.
Kan ka ce kwabo asibiti ya shiga da 'ya'ya da manyan jikokin Babiyon don Baffa Ɓeleri kiran Baffa Belɗo ya yi ya shaida masa, shi kuma Baffa Belɗo ya kira Baffa Gidaɗo. Su uku kawai suka san da Babiyo na asibiti, amma abunda ya matuƙar ba su mamaki shine ganin kusan kwatan Arɗo Barkinɗo a cikin asibitin suna koke-koke. Mamaki Baffa Ɓaleri ya shiga yi a kan wanene ya sanar da su. Don hatta Inna Jume da Inna Ƙarama sai da suka zo a wannan daren suna koke-koke.
Ba kowa bane ya yi wannan shelar sai Marwantu, domin ita ta riƙa kiran yara da manya da kuma iyaye mata. Abdul-Hameed shine ƙarshen zuwa don shi ta kira na ƙarshe a waya don cewa ta yi wallahi yau gidan babu wanda zai kwana lafiya har ango.
Jawaad da Habib su ma suna asibitin sai dai ba su san wainar da ake toyawa ba don ba waje ɗaya suke da inda aka kai babiyon ba. Sai kaiwa da komawa suke kamar ma su fareti.
"Alhamdulillah! Ta farfaɗo sai dai mun mata allurar bacci domin ta samu ta huta. Ba komai bane ya same ta face shock wanda ya jawo sanadiyar sumewanta. Amma in sha Allah za ta farka lafiya zuwa safiya.
A tare Habib da Jawaad suka riƙa gyaɗa kai tamkar ƙadangaru.
"Fatima! Fatima!! Fatima!!! Ki sauri ki zo an kawo mai estate ɗin nan asibitin yana emergency. Na ji kamar Nurse Jalila na cewa kamar ya samu paralyzed (shanyewar ɓarin jiki) kuma wai zuciyarsa na barazanar bugawa!"
A firgice Jawaad da Habib suka kalli inda nurse ɗin da take magana a gigice ta ke tare da faɗin, "Ke! Wani mai estate ɗin ne aka kawo shi asibiti ya samu paralyzed?" Habib har ya ƙarisa inda ta ke tsabar kiɗima.
Bakinta na rawa don babu wanda bata sani ba a cikin su ta furta, "Bab...ba.. Babiyo, grandpa ɗinku."
Da wani mahaukacin gudu suka kwasa su biyun tare da nufa unit ɗin da suke kyautata zaton yana can. Zuwan na su ya yi daidai da shigowar Abdul-Hameed daga shi sai wandon shadda da singlet a jiki. Ganin dandazon mutanen da ke wajen ya kuma tabbatar ma su da abunda nurse ta faɗi.
"Mai ya same shi? Yana ina? Ku bar ni in ganshi don girman Allah. Babiyo! Babiyona!!" Abdul-Hameed ya faɗi da ƙarfi yana ƙoƙarin nufa ɗakin da ya ke ciki.
Cikin sauri Baffa Giɗaɗo ya cafko hannunsa tare d riƙesa gam ya shiga faɗin, "Ina za ka je? Likitoci na kansa ne. Ka kwantar da hankalinka In sha Allah zai sa mu lafiya."
Baffa Ɓaleri ne ya kalli agogon hannunsa da ke nuna ƙarfe ɗaya da mintuna hamsin daidai sannan ya kalli jama'ar wajen tare da faɗin, "Don Allah ku kwantar da hankulanku ku koma gida. Zamanku anan da koke-kokenku ba shi zai bawa Babiyo lafiya ba. Addu'a ya ke buƙata daga gareku ku duka. Mu huɗu za mu kasance a nan har zuwa safiya. Ni, Belɗo, Giɗaɗo da kuma Baffa (yana nufin ƙanin Babiyo kumamahaifin matarsa). Ku koma gida ku raya wannann dare da roƙon Allah a kan Babiyo ya samu lafiya. Likitocin asibitin nan kunya ce ta hana su korarku domin a dokar asibiti ba a yarda mutane masu yawa haka su zo asibiti ba kuma suna koke-koke don za su damu sauran patient. Don Allah ku koma gida. Kai ma Abdul-Hameed maza gida ka bar 'yar mutane a gida ita ɗaya. Kuma ku wuce wajen na ku iyalan!" ya ƙarisa maganar yana nuna su Jawaad da su kai curko-curko.
#Babiyo