My Destiny (Ƙaddarata)

Page 63

by @matarsayyadee3

Aje ai following channel ɗina please 🙏🏼 ***

*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***

Domin shiga comment section kuma ki danna wannan link ɗin👇🏼 *** *_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining link ɗin da ke sama domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜

_*💃🏻💃🏻 _Kuna ina 'yan uwana matar aure da 'yan mata? Shela nake ko wacce ta fito domin kuwa yau na zo maku da albishiri! Kun san matar Sayyadee ta ku ce ba ta samun abun ƙaruwa ta yi shuru domin ta ƙaru ita kaɗai._💃🏻💃🏻

💐💐🌼🌼_Magana ake ta ƙamshi. Toohwa! Mai ya hwaru?_ 🤔 🌷🌷🌸💮

*To maza ku marmatso ga sirrin nan. Shahararriyar nan wacce ke inganta soyayya tsakanin ma'aura wato Fatima Zaransalaty inkiya Queen Zarah ce ta taho mana da wani ƙamshim domin cika hancinar mazajemu da ƙamshi*. _INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_ _TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA KUJI 💃🏻

_Zaran Salaaty ta yi tafiya miƙaƙƙa har Sudan domin farnata ranmu da na mazajenmu ta kawo mana Sudanese perfume👌🏻 wanda idan har kika shafa shi a jikinki ko kin yi wanka ƙamshin bai barin jikinki. Tested and Trusted ƴaruwa. Zaransalaty ba iya sudanese perfume ta kawo maku ba, akwai kayayyaki masu matuƙar inganci na gyaran HQ (kun san dai ba a wasa da headquarter) akwai kayan gyararrakin jiki kala-kala na ƴan mata da matan aure. Sannan Zaransalaty tana sai da Decoration na kayan ɗaki iri-iri wanda baki taɓa ganinsu._

_KAR IN CIKA KI DA SURUTU, KE DAI NEMI ZARANSALATY A NUMBERS ƊINTA KAMAR HAKAA_: *** Or ****

*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_nfection_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_

_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ ***** *****

Jawaad ɗin ne ya fara juyawa ya nufi inda Zeenah ke kwance, ganin haka sai wuf Habib ya bi shi a baya yana mai ɗaure fuska.

"Ina kuma za ku je ku da na ce maku ku wuce gidanku!" Baffa Ɓeleri ya faɗi ransa na ɓaci.

Cak suka tsaya tare da juyowa. Jawaad ne ya yi ƙarfin halin faɗin, "Abu zan duba a ciki yanzu zan fito in wuce."

Jinjina kai Ɓalerin ya yi ba tare da ya kuma cewa komai ba, don wani irin zafinsu ya ke ji kasancewar su na daga cikin waɗanda suka janyo halin da mahaifinsa ke ciki. Jira ya ke Babiyon ya samu kansa ya koma kansu.

Nurse Fatima ya kira gefe tare da bata amana Laushin akan ta duba masa ita, duk kuma abunda ta ke ciki ta yi gaggawan kiransa ta faɗa masa.

Shima Habib ɗin abunda Jawaad ya yi shi ya yin, sai dai inda suka bambamta kowanne da wanda ya bawa ajiyarta. Shi Jawaad Nurse Fatima ya ba, shi kuma Habib Nurse Jalila.

Babu wanda ya kalli ɗan uwansa a cikinsu har suka fice daga asibitin. A parking space ya Habib ya ga motarsa. Ba tare da ya yi mamakin ganinta a wajen ba ya nufa tare da buɗewa ya shiga ciki. Kallon wayarsa da ke haske ya yi tare da miƙawa hannu ya ɗauka, take ya wato idanu ganin forty-six miss calls daga Amatu. Da sauri ya yi reverse tare da barin asibitin ya nufi hanyar gida.

Shi kuwa Jawaad a ƙafa ya ƙarisa gida kasancewar babu nisa sosai daga asibitin zuwa gidansa. Ƙaramin ƙofar gate ya buɗe tare da kutsa kai cikin gidan sannan ya mayar da ƙofar ya kulle ya nufi cikin gidan gabansa na faɗuwar abunda zai taras a ciki.

Kwance ya same ta flat a kan gadon, hasken ɗakin ya ɗan ƙara domin ya ganta da kyau. A zabure ta miƙe zaune don ba ta ji shigowarsa ba sam saboda nisa da ta yi a tunani. Ganin shine, wani dogon tsaki ta ja tare da maida kanta ta kwanta ta cigaba da kukanta.

Jiki a sanyaye ya ƙarisa kan gadon tare da zama a baki-baki. So ya ke ya fara mata magana amma kuma yana jin tsoron haka, don fisabilillah ya san kwata-kwata bai kyauta ba. Ga ƙaryan da ya dage ya shararo mata tamkar wannan ranar baza ta zo ba.

"Gaskiya ban yi dabara ba sam! Da na san wannan ranar za ta zo da wuri haka da wallahi ban shirga miki wannan ƙaryar ba. Gashi nan dai yanzu duk girma ya faɗi." Duk a cikin zuciya ya yi maganar.

Ya kusan mintuna talatin a haka bai iya ce mata komai ba, ita kuwa Khairat wani irin baƙin ciki ne ya mamaye zuciyarta da kuma mugun haushinsa da ya ninku a zuciyarta ganin kamar bata ma kai ya bata haƙuri ba da yi mata magana masu kwantar da hankali ko da kuwa ƙaryar zai kuma shirga mata. (Fisabilillah mu fa mata muna ƙaunar lallashi da magana mai daɗi. Muna da wani irin raunanniyar zuciyar da duk iya girman ɓacin ranmu da an tarairaiye mu an nuna mana so da ƙauna, musammam ma namiji ya ɗan yi ƙwallar nan sai mu ji duk faɗin duniya babu kamar mu. Nan da nan dai zuciyarmu ta narke tamkar kitse a wuta. Haba maza, ku gane mana!🙄)

Shi kuwa Jawaad miƙewa ya yi ya nufi bayin da ke ɗakin sabida zuciyarsa da ta raya masa cewar ƙyale Khairat ɗin for now saboda a wuya take kuma komai zai iya faruwa idan ya ce zai mata wani bayani. Sai kawai ya shige ba yi ya yo wanka tare da ɗauro alwala ya tada sallah ya yi raka'a biyu ya roƙi ubangiji akan Allah ya sassauta fushin matar tasa ya kuma baiwa Babiyo da Zeenah lafiya.

Ɗan leƙawa ya yi sai ya ga bacci ɓarawo ya kwashe Khairat ɗin. Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi don shi fisabilillah tsoranta ya ji yana yi a yau ɗin. Lallaɓawa ya yi ya gyara mata kwanciya tare da kashe wutar ɗakin sannan ya hau gadon ya kwanta bayan ya yi addu'a ya shafa ma kansa da ita Khairat ɗin.

Rufe idanu ya yi amma sam bacci ya ƙi zuwa masa, abubuwa huɗu ne su kai masa tsaye a rai. Na farko idan Babiyo ya samu labarin Zeenah na cikin estate ɗin nan bayan ya farka, na biyu kuma cikas ɗin da Habib ɗin ya ke son kawo masa, na ukun Khairat ɗinsa da ya ke matuƙar so don kamar yadda ya ke jin ba zai iya haƙura da Zeenah ba, haka ya ke jin ƙasa da sama za su haɗe ba zai iya rabuwa da matarsa da take da wani special waje a zuciyarsa ba, sai na ƙarshen ita kanta Zeenah ɗin. Yadda ya ga rana dai haka ya ga dare.

Kiran sallar farko ya tashi zaune ya riƙe kansa saboda wani nauyi da ya masa. Idanunsa ya ɗan juya ya kalli inda Khairat ke kwance a ƙudundune. Hannu ya kai ya taɓa goshinta da kanta, sai ya ji ya ɗau zafi alamar zazzaɓi ya rufe ta. Bargo ya ja mata da kyau ya lulluɓeta sannan ya sauka ya kunna wuta ya kashe mata AC.

Bayi ya shiga, da ya kalli kansa cikin madubi sai da gabansa ya faɗi saboda wani irin ɓulu-ɓulu da idanunsa suka yi, ga wani ja tamkar gauta da suka koma. Duk wanda ya gansa a haka ya san bacci bai wadace sa ba.

Alwala ya ɗaura ya dawo kan dardumar da ya yi sallah akai jiyan da daddare ya yi raka'atal fajri tare da wuturi. Zama ya ɗan yi shuru a kan dardumar. Sai a wannan lokacin ya soma jin idanunsa na nauyi alamar baccin ya soma zuwa. Sosai ya yi yaƙi da zuciyarsa ya nannaɗe dardumar sannan ya fita daga ɗakin bayan ɗaukar key ɗin mota kasancewar da nisa dagaa gidansa zuwa masallacin Arɗo Barkinɗo.

Yana fita da mintuna goma aka kwaɗa kiran sallar asuba a masallacin wanda ya ɗauki ilahirin Estate ɗin gaba ɗaya tamkar a kunnuwan jama'a ake yinsa.

Khairat ma da ke bacci a wahale sabida zazzaɓi, kiran sallar ne ya farkar da ita. Ji take hatta ƙasusuwanta ciwo suke mata. Da kyar ta iya yaye bargon sannan ta zuro ƙafafunta ta sauko ta shiga bayi. Bata damu da rashin ganinsa a ɗakin ba, don ta tabbata yana masallaci. Sai dai abunda ya kuma ɓata mata rai shine fitan da ya yi ba tare da ya tashe ta. Shaa! Wasu hawaye suka zubo mata tare da jim dana sanin auren sa don ta fahimci shi ba sonta ya ke ba, tun da can ita ke haukanta.

Da ruwan zafi ta yi alwala sannan ta dawo falon ta canza kaya zuwa doguwar riga ta saka safar ƙafa. Da sauri ta ɗago tana ƙara saurara dakyau jin muryan da ke karatun sallah a cikin speaker.

"Tabbas da matsawa! Hamma Abdul-Hameed da jan sallah ba Babiyo ba." ta faɗi a bayyane jikinta na wani irin rawa. Don ta tabbata abu biyu ne zai hana Babiyo jan sallah a duniya, na farko mummunar rashin lafiya da ba zai iya miƙewa ba, ko kuma mutuwa. Don tun da ta tashi tai wayo a Arɗo Barkinɗo ba ta taɓa jin wani murya na jan sallah ba face na Babiyo.

Sallar ta tada gabanta na mugun bugu tana kuma fatan Jawaad ya dawo da wuri duk da tana matsanaicin jin haushinsa tai masa tambayar da ke zuciyanta wanda bata fatan ɗaya daga cikin abunda ta raya ya tabbata. (Sai haƙuri Khairat don tabbas Babiyonku na can kwance a kan gadon asibiti bai san inda kansa ya ke ba.)

_MAMIYO_ Tana shiga ɗakinta ta rarumi waya ta dannawa malam mai hula kira, yana ringing ji take tamkar zuciyarta za ta faso ƙirjinta. Sai da ya kusa katsewa ya ɗauka tare da yin sallama. Ko amsa sallamarsa ba ta yi sai ta soma kora masa jawabai.

"Malam ka faɗa min in kwantar da hankalina ni ce da nasara, amma a yau komai ya kwaɓe min. Yau Ardo ya san ko ni wacece. Sannan kuma ya kama 'ya'yana dumu-dumu da ƙoƙarin kashe mahaifinsu! Ka faɗa min menene mafita!?" ta ƙarisa maganar da ƙarfi.

Ɗan jim malam ya yi kamun ya furta, "Na faɗa miki tuntuni kar ki warware alaƙar da kika raba na wancen yarinyar da Abdul-Hameed amma idanunki sun rufe, na faɗa miki warware farra'un yana nufin warware duk wani shirinki amma ki ka ƙi saurarena balle na miki bayani dalla-dalla. Na faɗa miki hakan zai jawo mace-mace amma kina nuna duk wanda zai mutu ke dai bai dame ki ba in dai akan cikar burunki. Kuma irin aikin da nake maki ƙaiƙayine koma kan masheƙiya!"

"What? Mai kake faɗi haka? Kasan kuwa mai kake faɗa min?" Mamiyo ta faɗi jikinta na rawa tamkar mazari.

"Eh, ranki shi daɗe. Tun farkon aikin nan da na miki sai da na gargaɗe ki kar ku sake da dai da rana ɗaya ku yi kuskuren da shi mai gidan na ki zai gane abunda kike shiri a kansa. Don suna da wani kafi tun kaka da kakanni. Duk wadda ya nufe su da sharri to zai koma masa gwargwadon abunda ya nufe su da shi. Kakan mijinki shahararren malami ne da ke da taurin kai da kafiye kuma bai yafiya sam! Ya riga ya yiwa zuri'arsa wani kafi na kan gidansu akan duk wanda ya cuce su ya koma masa ko shi wanene."

"Mai ya sa baka taɓa faɗa mini haka ba? Kenan kai ma yaudarata kake duk tsayin shekarun da muka ɗauka tare? Menene ban maka shi a duniyar nan? Har hajj sau biyu ina kai ka. Kai da iyalanka duk ni nake ci da ku, irin sakayyar da za kai min kenan?"

Ɗan murmushi ya yi sannan ya ce, "Na miki iya ƙoƙarin da zan miki. Kuma ke ma kin san kin buga na ki irin mulkin a cikin Arɗo Barkinɗo domin Allah ya ara miki lokaci. Kin cutar da mutane da yawa haka kuma kin salwanwar da rayukan da ba su ji ba su gani ba. Kin kashe uwargidanki, kin kashe mahaifin Mardiyya, kin yi sanadiyar da aka kori Ɓaleri da Belɗo. Kin sa Abdul-Hameed ya yi zina ya kuma samar da 'ya. Kin cuci rayuka da dama. Hatta shi kansa Babiyon kin cire masa jin ƙan 'ya'yansa a zuciyarsa kuma kin wawushe dukiyarsa kin gina tafkeken kamfani tare da ƙoƙarin janye masa masu hannin yarinsa, kin....."

"Enough!" Mamiyo ta faɗi a tsawace tare da cigaba da magana, "Ban kira ka a wayaa domin kai min duk wannan lissafe-lissafen ba. Na kira ne domin ka ba ni mafita. Ina son ka kashe min Babiyo a wannan daren! Ka tura aljanunka su tsinke jijiyar maƙogwaransa ni kuma na yi maka alƙawarin miliyan hamsin idan na ji kukan mutuwarsa gobe."

Wani mahaukacin dariyar ya ɓarke da shi tare da faɗin, "Ki saka a ranki aikin ki ya kammala, sai na ji saƙo goben!" ƙit ya kashe wayar yana faɗin, "Wawuya!" a zahiri.

Ajiyar zuciya mai ƙarfi Mamiyo ta saki tana jin zuciyarta wasai yanzu. Kashe wuta ta yi bayan turawa 'ya'yan nata saƙo a waya sannan ta hau gado ta kwanta.

Bayan idar da sallar asubha da kyar Khairat ta shiga kelaye wani irin amai ana kan darduma don ta kasa motsawa daga inda take. Tun tana saka ran ganin Jawaad immediately after the prayer har ta cire rai. Ba ƙaramin galabaita ta yi ba. Sai 7:14 ya shigo gidan don daga masallaci haɗuwa su kai gaba ɗaya suka tafi asibiti wajen Babiyo. Babu wanda bai zubda hawaye ba saboda yadda Babiyo ya koma a dare ɗaya kawai. Ya samu matsalar shanyewar ɓarin jiki saboda mummunar hawa da jininsa ya yi. Maganarsa ma sam ba ta fita sosai. Sai dai yai ta kallon 'ya'yansa nasa hawaye na zubowa daga kurmin idanunsa.

Hannunsa mai lafiyar ya ɗaga a hankali yana nuna Baffa Ɓaleri da Baffa Belɗo. Da sauri suka nufe sa tare da duƙawa suka kamo hannunsa. Wani irin kuka suke yi tamkar zuciyarsu za ta fashe lokacin da yake shafa kawunansu yana ƙoƙarin yin magana amma bakin ya ƙi buɗewa da kyau su ji abunda ya ke cewa.

Abdul-Hameed da ke wajen kansa yana tsiyayar da hawaye tamkar ruwan fanfo ya kama hannun Babiyon ya cusa yatsunsa ya riƙe nasa tare da kwantar da kansa a ƙirjinsa ya shiga faɗin, "In sha Allah Babiyo za ka samu lafiya, za ka warke tamkar yadda kake da. Za ka cigaba da bada umarni muna yi maka biyayya. Ba mu gaji da kai ba, ba mu gaji da ganinka ba, ba mu gaji da tarbiyyar da kake bamu ba!"

Gaba ɗaya mutanan ɗaki suka shiga wani irin kuka tamkar ce masu akai Babiyon ya mutu. Shi kansa Babiyo hawaye ya ke sosai yana murza hannun Abdul-Hameed da ke cikin nasa.

Sai da likita ya roƙi a fita a barshi da mutum biyu kawai sabida bai son hayaniya don hawan jinin har yanzu bai daidaita ba.

Gaba ɗaya sai aka koro su, baffa Giɗaɗo da Baffa Macciɗo kawai aka bari a ciki.

Ko da suka fito waje, waje ɗaya Abdul-Hameed ya samu ya dunga kuka tamkar ƙaramin yaro, haka Habib da Jawaad. Babu wanda a cikinsu ya tuna da wata Zeenah da suka kawo asibitin jiya. Jawaad ɗin ne ma ya miƙe domin komawa gida saboda tuno da da Khairat da ke kwance a gida babu lafiya.

Yana buɗe ɗakin ya ganta kwance a darduma cikin amai. Da sauri ya nufe ta ya ɗaga ta tare da nufar bayi da ita. Suna shiga bayin ta soma wani irin yunƙurin amai gashi babu komai a cikin. Sai da ta yi aman ta gama sannan ya taimaka mata ta yi wanka da ruwa mai ɗumi sannan ya dawo da ita ɗakin ya sauya mata kaya tare da saka mata safa sannan ya shiga gyara inda t ɓata. Bayan ya kammala ya koma kitchen ya haɗa mata tea ya dawo. Da ƙyar ta iya yin surɓa uku ta soma yin yunƙuri wanda hakan ya sa ya kyaleta tare da ciccɓarta ya kai mota ya kulle gidan suka nufo asibiti.

Akwai mutane sosai a asibitin duk da ba a barin kowa shiga inda Babiyon ya ke.

Jawaad ya fito daga gidan gaba da sauri tare da koma gidan baya inda ya kwantar da Khairat ɗin ya ɗagota tare da fito da ita daga motar. Cikin sauri su Mama Halima da Nenne suka nufe sa tare da taimaka masa suka riƙe suka shigar da ita cikin asibitin.

Office ɗin doctor aka nufa da ita tare da kwantar da ita a observation bed a nan office. Jawaad na tsaye a office ɗin doctor ya shiga duba ta. Sai da ya tambayeta abunda take ji sannan ya duba bp ɗinta tare da yi mata scanning.

Zama ya yi a kan kujeransa bayan ya bato inda Khairat ke kwance tare da nunawa Jawaad ɗin wajen zama.

Sai da Jawaad ɗin ya zauna sannan ya miƙa masa hannu fuskansa bayyane da farinciki tare da faɗin, "Congratulation, you're going to be a father in the next coming 8months"

Wani iri miƙewa Jawaad ya yi yana jin wani mahaukacin farinciki na baibaye ilahirin jikinsa ya kuma riƙe hannun doctor ɗin gam yana faɗin, "Thank you doctor, thank you doctor!" tamkar shi ya bashi cikin

Sai kuma ya saki hannunsa tare da nufa inda Khairat ke kwance idanuta a rufe don ita kaɗai ta san abunda take ji a jikinta da kuma irin yanda kanta ke mugun yi mata ciwo. Hannunta biyu ya riƙe ya ɗagota tare da haɗata da ƙirjinsa tare da kai baki kan goshinta ya furta, "I love Khairiyyata, ke alkhairi ce a gare ni. Kin ba ni abunda ba zan taɓa mancewa ba. Thank you very much. Allah nagode maka da wannan kyautar." ya ƙarisa maganar tare da sakin hannunta ya mai goshinsa ƙasa ya yi sujada.

_BABIYO'S HOUSE_ Da sassafe Mamiyo ta fito fuskannan cike da farinciki don a tunaninta za ta iske gawan Babiyo an kawo sa an shimfiɗe, sai dai tana isowa falo ta ci karo da 'ya'yan nata domin 'yan sandan farin kayan nan sun hana su baffa Jibrila barin falon Babiyo. A nan suka kwana a ƙarƙashin kulawar su.

"A nan kuka kwana ne?" Mamiyo ta faɗi tana kallon su kamun ta mayar kan 'yan sandan da ke tsaye tamkar saƙagai a tsaye.

Da sauri baffa Jibrila ya taso domin ƙarasowa kusa da Mamiyo yana shirin soma surfa bala'i sai wani mugun tari ya turnikesa, tun yana yi a tsaye har ya kai kasa yana mai dafe ƙirjinsa. Kan ka ce kwabo wani irin jini ya shiga fesowa daga bakinsa tamkar wanda ya gumtsi ruwa tari ya riƙesa. Gaba daya 'yan uwan su kai kansa har da mamiyi da zaninta ya kwance ya faɗi tsabar tashin hankali.

Wani irin bala'en'en amai mai tafe da guda-gudan jini Baffa Jibrila ya shiga kwararawa sannan kuma lokaci guda ya shiga jijjiga idanunsa na juyewa. Jinin nan kuwa ba ta bakinsa kadai ba hatta ramukan hanci da kunnansa fita yake.

Ihu Mamiyo ta ke yi tana neman taimakon 'yan sandan nan amma ko gezau ba su yi ba kuma suna kallon komai sai,dai ba a basu izinin gusawa daga inda suke ba, sannan kuma ba a yarda Mamiyo ko 'ya'yanta su bar wannan dakin da suke ba ko da kuwa zuwa tsakar gidan ne.....

(Taɓɗijam! Abunda zan iya cewa kenan 😥)

#Mamiyo #Babiyo #Baffa Jibrila #Jawaad #Khairat #My Destiny #Matar Sayyadee *** [8/18, 10:47 PM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)

*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee

☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`