Page 64
Aje ai following channel ɗina please 🙏🏼 ***
*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***
Domin shiga comment section kuma ki danna wannan link ɗin👇🏼 *** *_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining link ɗin da ke sama domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜
_*💃🏻💃🏻 _Kuna ina 'yan uwana matar aure da 'yan mata? Shela nake ko wacce ta fito domin kuwa yau na zo maku da albishiri! Kun san matar Sayyadee ta ku ce ba ta samun abun ƙaruwa ta yi shuru domin ta ƙaru ita kaɗai._💃🏻💃🏻
💐💐🌼🌼_Magana ake ta ƙamshi. Toohwa! Mai ya hwaru?_ 🤔 🌷🌷🌸💮
*To maza ku marmatso ga sirrin nan. Shahararriyar nan wacce ke inganta soyayya tsakanin ma'aura wato Fatima Zaransalaty inkiya Queen Zarah ce ta taho mana da wani ƙamshim domin cika hancinar mazajemu da ƙamshi*. _INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_ _TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA KUJI 💃🏻
_Zaran Salaaty ta yi tafiya miƙaƙƙa har Sudan domin farnata ranmu da na mazajenmu ta kawo mana Sudanese perfume👌🏻 wanda idan har kika shafa shi a jikinki ko kin yi wanka ƙamshin bai barin jikinki. Tested and Trusted ƴaruwa. Zaransalaty ba iya sudanese perfume ta kawo maku ba, akwai kayayyaki masu matuƙar inganci na gyaran HQ (kun san dai ba a wasa da headquarter) akwai kayan gyararrakin jiki kala-kala na ƴan mata da matan aure. Sannan Zaransalaty tana sai da Decoration na kayan ɗaki iri-iri wanda baki taɓa ganinsu._
_KAR IN CIKA KI DA SURUTU, KE DAI NEMI ZARANSALATY A NUMBERS ƊINTA KAMAR HAKAA_: *** Or ****
*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_nfection_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_
_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ ***** *****
Ihu Mamiyo ta ke yi tana musu magiya akan su buɗe mata ƙofa ta fitar da ɗanta ta kai shi asibiti amma sun ƙi ko motsi bare su tanka mata.
Baffa Mahmud ne ya yi tunanin ɗaga waya ya kira wasu daga waje. Number ɗin Baffansu Ciroma ƙanin Babiyo da ke gidan tun ana jibi bikin Abdul-Hameed ya kira, bugu uku kuwa ya ɗauki kiran tare da faɗin, "Duk kuna ina tun jiya da daddare Baffanku ke kwance a asibiti amma ban ga ƙafarku ko ta mahaifiyarku ba? Mai ke faruwa ne?" ya ƙarisa maganar a tsawace don shi bai san abunda suka aikata ba.
"Baffa Ciroma gamu nan gidan Babiyo tun jiya wasu 'yan sandan da suka zagaye gidan har cikin falonsa sun hana mu fitowa. Kuma ga Jibrila nan rai a hannun Allah sai aman jini ya ke yi." Baffa Mahmud ya faɗi gabansa na bugawa don ya san idan kowa ya gama sanin abunda suka aikata tofin Allah tsine za ai masu.
"Ƴan sanda! A gidan Hamma Barkinɗon? Gani nan zuwa." ya faɗi mamaki shimfiɗe a fuskansa sosai tare da miƙewa daga kusa da Babiyon.
Caraf Babiyo ya riƙo hannun baffa Ciroma yana son yi masa magana amma muryansa ba ta fita sosai. Duk abunda ya ke ƙoƙarin faɗi ko ɗaya ƙanin nasa bai gane ba. Ganin haka sai Babiyo ya mayar da idanunsa a kan Ɓaleri yana masa nuni da hannu. Jinjina kai Ɓalerin ya yi tare da faɗin, "Zan masa bayani baffa. Babu wanda zai fita scot free a cikin su."
Hawaye ne suka ziraro daga idanun Babiyon yana mai lumshe idanu. Waro manyan idanunsa Baffa Giɗaɗo ya yi don shi sai ya ga abun tamkar gizo wai Babiyo ne da hawaye kasancewar duk babu wanda ya san komai idan ka cire Ɓaleri, mamiyo da 'ya'yanta. Gwara ma Belɗo ya san wasu daga cikin abubuwan da ke faruwa, sai dai bai san yunƙurin kisan da ƴaƴan Mamiyo su kai ba.
Abdul-Hameed da ke zaune a kusa shi ma sai kallon iyayan nasa ya ke yi yana fatan jin ƙarin bayani don ga gukkan alamun something is fishing a tsakaninsu. Sai dai duk abunda ya ke yi ƙasa-ƙasa ya ke yi don ba tarbiyarsu ba ne manya na magana yara su kafe su da idanu, talkless of tambayansu abunda ke faruwa idan ba ai involving ɗin mutun a ciki ba.
Gaba ɗaya iyayan suka fice a ɗakin bayan sun ɗan yi ƙus-ƙus a tsakaninsu. Abdul-Hameed kawai suka bari a ciki. Ganin fitowarsu duka sai Habib shi ma ya shigo ɗakin ya ja kujera ya zauna yana kallon Babiyon da shima kallonsa ya ke yi yana ƙoƙarin yi masa murmushi, amm sabida yanayin bakin nasa a kan laɓɓansa kawai suka tsaya.
_JAWAAD_ Fitowa ya yi daga office domin zuwa pharmacy saboda abubuwan da doctor ya rubuta masa ya je ya sayo don sun bata gado. Da sauri Nenne da Mama Halima da wasu daga cikin 'yan uwa suka tare sa tare da faɗin, "Ya jikin nata? Mai ya same ta."
Takardar hannunsa ya nuna musu tare da faɗin, "Ya rubuta min magani da allurai da kuma ruwa in je in sayo wai sun bata gado." ya faɗi don da matuƙar kunya ya kalli iyayan nasa ya labarta musu abun farincikin da Doctor ya faɗa masa.
Jinjina kai suka yi. Mama Halima kuma nufa office ɗin ta yi don haka kawai zuciyarta ta darsa mata wani abu. Jim kaɗan sai ga ta fito fuska a washe tamkar gonar auduga ta labartawa su Nenne abun farincikin da ta jiyo daga bakin likita. Duk sai suka hau murna don dama fatansu kenan don sun riga sun san Amatum Habeeb ita ma tana ɗauke da nata ɗan tayin.
In few minutes asibitin ya ɗauka da maganar cikin matar Jawaad (kun san mu mata dai ba mu ɓoye irin wannan abun farinciki idan 'ya'yanmu sun sa mu).
Mama Juwairiyyah mahaifiyar Jawaad da jin abunda ke faruwa sai ta yi wuff ta gudu ta bar asibitin saboda kunyar matan ɗanta na fari na ɗauke da ciki kuma an yaɗa (kun san fulani akwai kunya da kara daga mazan har mata{Amma hwa, ina nuhin fulanin mu na da ba haihuwar bariki ba😜 lol,saura inji saukar dutse a kaina}).
Tafiya suke gaba gabaɗayansu cike da tashin hankali, Baffasu Ciroma, baffa Ɓaleri, Baffa Belɗo, Baffa Giɗaɗo, Baffa Modibbo da bai daɗe da isowa ba daga Lagos, da kuma baffa Bobbo (Mahaifin Jawaad). Gaba ɗaya sai sharar hawaye suke yi kasancewar suna tafiyan ne Baffa Ɓeleri na labarta musu komai.
Su kansu sun yi mamakin ganin Ɓaleri cikin Arɗo Barkinɗo kuma kusa da Babiyon don kowa ya san irin korar karen da ya yi masa. Sai dai ba lokacin tambayansa komai bane a jiyan saboda tashin hankalin da suke ci. Amma yanzu labarin da ya basu sai suka gane Babiyon da kansa ya fita ya nemo sa.
Gidan Babiyo suka nufa kowa da abunda ya ke saƙawa a zuciyarsa, musammam ma Ɓaleri sabida baƙar zuciyarsa. Don ba ƙaramin danneta ya ke ba sabida ji yake tamkar ya cinnawa Mamiyo da 'ya'yanta wuta. Mota biyu su ka shiga saboda suna da yawa.
Knocking su kai a ƙofar falon Babiyon. Ba a buɗe ba sai da wani ɗan sanda daga ciki ya leƙa ya ga Ɓaleri tukun ya ja ƙofar ta buɗe suka shiga su duka. Yadda suka ga Jibrilan sai da hankalinsu ya tashi don gaba ɗaya ya yi wani irin kumburi tamkar wanda aka hura da iska. Kuma har wannan lokacin bai daina aman jini ba.
"Ku kama shi mu kai shi asibiti," Baffa Ciroma ya faɗiyana nufa inda Jibrilan ya ke.
Ɓaleri ko motsi bai yi ba don bai jin zai iya taimakawa waɗanda suka kashe masa mahaifiya tare da yunƙurin kashe mahaifinsu. Baffa Modibbo da baffa Bobbo ne su ka yi kama-kama suka dakyar sabida wani nauyi da Jibrilan ya ƙara tamkar gawa.
Suna isa bakin ƙofa ƴan sandan nan suka hana baffa Mahmud da baffa Tukur fita har ma da Mamiyon. Wani irin kuka Mamiyo ta fashe da shi tare da faɗin, "A gaban ku kuna kallo har da kai Ciroma! Shi baza ku faɗa masa mahimmaci na ba a cikin Arɗo Barki...."
Da wani mugun tsawa tare saukar lafiyayyan mari bisa kuncinta mai ɗauke haske na wucin gadi Ɓaleri ya sauke mata dama tuntuni namar jikinsa ke wani irin tafasa jikinsa na mugun rawa.
Duk da kowa ya san abunda Mamiyon ta aikata amma wani irin 2minutes silet wajen ya ɗauka har da su Baffa da ke riƙe da nannauyan jikin Baffa Jibrila don babu wanda bai shiga shock ba. Ba su taɓa kawowa zafin zuciyar Ɓaleri zai iya kaisa ga marin Mamiyo ba.
Harshensa ya soma tattaunawa yana ƙoƙarin yin magana ga idanunsa da suka soma juyewa alamar idan aka barsa a wajen za ai ɗanyen aiki don tabbas zai iya ɗaukan ran Mamiyo. Wani irin baƙin zuciya Ɓaleri ke ɗauke da shi.
Hamma Tukur kuwa kukan kura ya yi tare da cacumar kwalar rigar Ɓalerin ya kai masa naushi a baki tare da furta, "Uwata za ka mara! Mahaifiyata ka mara ɗan karya?"
Ɓaleri wani irin zuciya ce ta yunƙuro masa ya kai masa wani wawan naushi a kan hanci, cikina sakan ɗaya hanci ya cika da jini ya soma tsiyaya. Naushi ya ke kai masa ta ko ina a jikinsa, ciki, ido, baki da hanci. Da ya ga hakan ma bai masa ba, sai ya riƙe kansa ya dunga bugawa da jikin bango ɗakin da iyakacin ƙarfinsa.
Baffa Bobbo da Baffa Modibbo ba su san sun watsar da Jibrila da ke hannunsu ba sun yo kan Ɓelerin da Baffa Ciroma da Mamiyo da ke ihu suka kasa ƙwatar Jibrilan a hannunsa ba.
Da kyar suka iya janye Ɓalerin shi ma kuma ya saki Jibrilan ne ganin babu numfashi a jikinsa (wayyoo Allan mu! Zeenah kin shiga uku idan kika yadda ku kai 2eyes da mahaifinki a cikin Arɗo Barkinɗo! Wayyo ni matar Sayyadee har na soma jin zazzaɓi😬🤒. Hamma Tukur ka daku iya, dakuwa aradun Allah)
Baffa Mahmud kuwa ya kasa motsi sai kallon kowa yake kamar idanunsa za su zazzago, don ji ya ke tamkar idan Ɓalerin ya gama da Tukur kansa zai dawo. 'Yan sandan nan kuwa sunan amma ba su motsa ba balle su kawo ɗauki.
Baffa Ciroma ya cafki hannun Ɓaleri da sai wani huci ya ke yi tamkar kububuwa ya tura shi waje.
"Allah ya isa tsakani na da kai ɗan iska haihuwar asara wanda uwarsa ta haifa tsiya idanunta biyu. Mutuwar ƙwanƙwalati za ka yi, kuma kowa zai ce na faɗa."
Wani zaburowa Baffa Ɓaleri ya yi tari nufa kan Mamiyo, da sauri Baffa Giɗaɗo ya riƙe sa gam ita kuwa Mamiyo duk tsufanta wani tsalle ta yi tare da sakin hannun Baffan Tukur ta yi bayan wani ɗan sanda dake gabas da ita.
"Ka sake ni Giɗaɗo! Sa sake ni na kashe matar nan a cikin gidan nan." Baffa Ɓaleri ya faɗi yana fuzge-fuzge.
"Ba zan taɓa sakin ka ba ka ɗebe zunubin da ta tarawa kanta. Ka barta da abunda take ji yanzu!" Baffa Giɗaɗo ya faɗi yana dannansa.
Wannan karan baffa Ciroma har da shi wajen cicciɓar Baffa Jibrila da ya ƙara hawa him tamkar farashi suka saka shi cikin mota. Amma sam ba a bar Mamiyo da sauran 'ya'yanta sun taka kafarsu zuwa ƙofar falon ba balle su fita.
Bayan wucewar su Mamiyo ta shiga ihu tana kuka tare da jijjiga Baffa Tukur da ya suma tun haɗashi da ginin farko da Ɓalerin ya yi. Ga jinim da ke fitowa a hancinsa har wannan lokacin bai bar zuba ba.
Da sauri ta nufi kitchen ta ɗebo ruwa a cup sannan ta dawo ta buɗe fridge ta ɗauko ƙanƙara ta dawo inda Jibrila ke kwance sannan ta yayyafa masa ruwa. Sai bayan ya farfaɗo sannan ta ɗaura masa ƙanƙarar a kai domin daskarar da jinin da ke zubowa.
A can asibiti emergency a kai da Baffa Jibrila wanda jikinsa ya yi worse sosai. Duk iya iyawarsu sun kasa fahimtar ainahinabunda ke damunsa, sai kawai akaa yanke hukunci haɗa shi da Babiyo domin zuwa ƙasar India a duba su a can. Sai dai kuma duk abunda ya tsara hakan ce ke faruwa. Ko cikakken awa uku ba ai ba baffa Jibrila cikinsa ya yi wani irin mugun kumburi har walƙiya yake yi. Lkitoci suka rufa akansa, sai buga kan ya ke yi a jikin ƙarfen gadon da yake kai, jikinsa ya ɗauki wani mahaukacin zafi tamkar garwashi. Cikin abunda bai wuce mintuna uku ba Allah ya ɗauki rayuwarsa yana ihun da ya cika asibitin domin hatta Laushi da ke nata ɗakin tana bori sai fa ta firgita ta ɗan natsu na wucin gadi.
Gawarsa aka ɗauka aka nufi gida da shi domin masa wanka da jana'iza sannan a kai shi maƙwancinsa. 'Ya'yansa da matarsa sai kuka suke yi tamkar rayuwarsa za ta bar jikinsu. Wai a hakan ma banda iyaye maza babu wanda ya san abunda suka aikata.
Baffa Ɓaleri cewa ya yi babu inda za shi, zai zauna da mahaifinsa ya yi jinyarsa a asibiti kasancewar ba a faɗawa Babiyon mutuwar ɗan nasa ba. Sai dai lokacin da aka isa gida da shi, baffa Ahmadu ya ba da shawarar a faɗawa Babiyon ko Allah zai saka ya yafe masa kura-kuran da ya masa. Duk akai na'am da hakan.
Baffa Ciroma da Baffa Ahmadu sune suka tafi asibitin suka shaidawa ɗan uwan nasu bayan kwantar masa hankali da kuma bashi baki akan ya yafe masa ko ya ɗan samu rahamar ubangiji.
Hawaye kawai Babiyo ya ke ta yi yana son yin magana amma maganar ba ta fita sosai.
A wheelchair aka ɗaura Babiyo sannan aka tura shi har mota sannan Abdul-Hameed ya cicciɓasa a ciki suka nufi gida.
Kan kace kwabo Arɗo Barkinɗo ya cika maƙil da jama'a ta ko ina kasancewar Babiyo da iyalansa sanannu ne ko don sunan kamfaninsu.
Duk mutanan arzikin Babiyo mamaki suke da ganinsa a kan wheelchair don wasu ma sun yi waya da shi da daddare.
Mamiyo kuwa kulleta a ka yi a cikin ɗaki saboda ihu da koke-koke da ta yi ta yi tana tsinewa Babiyo da 'ya'yansa wanda hakan ya jefa mutanan gidan da basu san komai ba mamaki.
Bayan yi masa wanka akaa shiryasa cikin likkafinsa aka shimfidar da shi a ƙasa, sai Baffa Modibbo ya turo keken babiyo zuwa gaban gawa.
Babu abunda Babiyo ke yi sai hawaye. Cikin zuciyarsa kuwa cewa ya ke, "Ka ga duniya ko Jibrila! A jiya ku ka gama haɗa ɗin kashe ni domin dukiyar da ni na tara da gumi na, ashe haukar banza kake yi ba za ka wuve yau ba kana numfashi ko da ace kun yi nasarar kashe nin jiya. Da su kaɗai za su yi wadaƙa kai kuma kana rami kana girbe abunda ka shuka. Kaicona! Kaicona da ban zaɓar maku uwa ta,gari ba dul kaffa-kaffa na. Kaico, da tsauri da zafina tunda gashi bai saka 'ya'yana sun zamo nagari ba, kaico da rashin jan 'ya'ya a jiki don gudun raini da gudun saɓawa umarnin. Da na ja ku a jikina sosai ta yanda muka zama tamkar abokan juna da hakan bata kasance ba, da duk wata matsalarku kun sanar min. Kaico da girman kai da jiƙima! Kaicona ni ɗan Iliyas. Da na san wannan ranar za ta zo da ban bar baya da ƙura ba, da ban riƙa tauye ku 'ya'yana ba. Don na san da yawanku na shiga haƙƙinsu matuƙa amma tsorona da irin ɗanyen hukuncin da na ke yankewa a kanku ya saka bakwa iya min musu da saɓa umarnina! Anya na cancanci a kira Arɗo kuma uba kuwa? Tir! Da halina tabbas. Na yafe maka nawa haƙƙin, Allah ya maka gafara Jibril!"
Kuka yake yi sosai, hawaye ya gama jiƙa gaban rigarsa don har idanunsa ba sa oya buɗewa da kyau da ma kuma ga tsufa don shekarun ba na yau bane. Ganin jikinsa na rawa kamar zai kifo da sauri Baffa Ciroma da baffa Belɗo su kai kansa tare da jan wheelchair ɗin baya suna bashi baki. Baffa Ɓaleri ƙin shigowa ɗakin ya yi sabida taurin kai, kafiya, zafin zuciya da rashin yafiyar da ke cunkushe a ransa. Tsanar da ya yi wa Mamiyo da 'ya'yanta ya munana matuƙa ta yadda gaba ɗaya zuri'arta suka fice masa a rai daga ciki kuma harda 'ya'yan baffa Jibrila ɗin da ba su ji ba kuma basu gani ba.
Daƙyar da lallashi baffa Ahmadu ya tasa baffa Ɓaleri a gaba suka tafi su ka kai gawan baffa Jibrila. Suna dawowa jikin Babiyo ya kuma rikicewa wanda ya saka dole aka mayar da shi asibiti tare da ƙoƙarin fitar da shi zuwa India.
Ɓangaren Khairat kuma, amaryar Baffan Giɗaɗo ne ke zaune da it wacce ita ma ke ɗauke da nata ɗan tayin na sati biyu, sai dai ba mai tona asiri bane don ko ita bata san dashi ba. Amma kuwa shi uban cikin yana sane ko kuma muce yana zargi. Don yanaa dagaa cikin mazan da Allah ya masu baiwar fahimtar ciki a jikin matansu kamun su su gane hakan.
Zeenah kuma, tun kamun rasuwar Jibrila Habib ya zagaya ya koma wajenta. Ƙin sauraransa ta yi sai bori ta ke akan a kai ta wajen 'yarta kawai. Daƙyar da suɗin goshi ya ɗan shawo kanta a kan ta yi hakuri rasuwa akai a gidan amma ya mata alƙawarin tafiya Lagos ya dubo mata ita a duk inda take ko da kuwa zai bada rayuwarsa ne, zai yi hakan domin ita. Sai ta ji ta ɗan gamsu duk da dai hankalinta ba akwance ya ke ba.
*_Bari mu leƙa Queen Elizabeth Amarya_* 😂🤣
Tun bayan da aka kawo ango gidan bata samu lokacinsa na mintuna biyar ba. Don ko da aka kawo sa bai shigo ɗakin ba sai after ten. Shima kazan amarci ya kawo mata ya yi excusing ƙansa ya fita domin bata dama ta shirya shi ma ka ya yi waya da wanda ya bawa kongilar nemo masa Yasaar a can Lagos. Sai dai ko kamun ya koma ɗakin amarya a kai kiransa a waya aka shaida masa Babiyo na can rai a hannun Allah wanfa hakan ya saka ya fice ba tare da yafadawa amaryar tasa fitar ba don a gigice ya fita. Kuma ba shi ya dawo ba sai to three AM da dare lokacin Asma'u bata san inda kanta yake ba. Sai da asuba da ya tashe ta bacci ta gansa, sai ta hau kumbure-kumbure tana fushi. Murmushi ya yi ya hau lallashinta da faɗa mata abunda ya faru (kun san fa ance amarya ko ta buzuzu ce akwai farin jini. Idan baku amince ba ku je ku tambayi Baffa Giɗaɗo 😂).
Sai dai yadda ba ta ɗauki abun serious ba ya ƙona masa rai. Don ko ya mai jikin bata ce ba sai wani turanci banza da wofi da ta ishe sa da shi.
Gaba ɗaya shi bai ma cikin hankalinsa da tunaninsa gashi ya samu kira daga senate akan screening ɗin da za ai masu domin tantance ministers ɗin da kowacce jaha ta kawo za a zaɓa. Babiyo ya riga ya shaida nasa kujeran da za a bashi kasancewar sune manyan ƙasa, amma shi sam hakan bai ɗaɗa shi da ƙasa ba. Ga kuma rasuwar da a ka yi a yau ɗin da rashin lafiyar shi kasan Babiyon.
Da taimakon Asma'u ya shirya domin mutanan Babiyon sai zabga masa kira suke a waya a kan he is delaying. Maza-maza ya kammala sannan ya fito ya shiga mota tare escourt suka nufi senate House.
Asma'u daɗi tamkar zai kasheta, tuni har ta kira ƙawayenta ta gama fesa musu abunda ke faruwa duk da gargaɗin da Abdul-Hameed ɗin ya mata.
Sai da ya kwashi awanni shida a Senate House bayan amsa tambayoyin da bakinsa sai ya nemi ya matsa tsami sannan suka bashi damar tafiya. Ko da motarsu ta shigo Arɗo Barkinɗo kai tsaye ya ce su wuce asibiti domin ganin jikin Babiyo. Asibitin babu mutane sosai sabida tsaron da aka saka da kuma samun nutsuwa da rashin hayaniya.
Baffa Ahmadu, Baffa Belɗo, Baffa Ɓaleri da Baffa Giɗaɗo ne kawai ke asibitin don an kora kowa. Sauran iyayan irin su baffa Bobbo, baffa Modibbo, da baffa Macciɗo suna can wajen zaman makoki. A yara kuma Hamma Jawaad da Hamma Habib sai babban ɗan Baffa Modibbo wato wan Marwantu ne ke asibitin. Iyaye mata kuma Mahaifiyar Modibbo ce kawai wato Inna Ƙarama, Inna Jume tana can wajen zaman makoki.
Dukkansu a waje suke don suma an ce su fito su bar Babiyon shi kaɗai domin ya huta don jininsa ƙara sama ya yi kuma hakan zai iya jawo bugawar zuciyarsa ya mutu.
Shigowar Abdul-Hameed ɗin ne duk ya saka suka juya suna kallonsa don sun san inda ya je.
Duƙawa ya yi ya gaishe su tare da tamayan jikin Babiyo. Duk suka amsa masa da sauƙi sannan suma suka tambayesa abunda ya wakana a can. Faɗa musu duk abunda aka tambaye sa a can ya yi su kuma suka amsa da fatan alheri.
Komawa kusa abokan nasa da su kai kicin-kicin ya yi tare da zama yana fuskantar wards da ke cikin wani korido. Ba tare da ya ce masu uffan ba don duk a tunaninsa abubuwan da suka faru a gidan ne ya canza mood ɗin nasu.
"Ki ban hanya na ce miki!" Laushi ta faɗi da ƙarfi cus she's tired of sitting while her daughter is missing.
Da sauri Jawaad da Habib suka miƙe jin muryan Zeenah. Shi kuwa Abdul-Hameed wani irin bugawa zuciyarsa ya yi jin muryan da ko cikin mafarki ba zai taɓa mancewa da ita ba. Ɓangaren Baffa Ɓaleri kuwa, ji ya yi kunnuwansa na masa gizo da muryan da kwata-kwata bai ƙaunar sake sauraransa a duniya. Amma yadda yaga 'ya'yan nasa sun miƙe su ukun lokaci guda ya saka shi mayar da idanunsa inda suke zuciyarsa na harbawa ba kuma tare ya yi ko yunƙurin miƙewa ba.
"Zeenah! Ina kuma za ki je? Ba mun riga mun gama magana ba." Habib ya faɗi wanda shine ya fara isa kusa da ita tare da tsayawa a gabanta ya yi bake-bake don kada Jawaad ya samu damar haɗa idanu da ita balle ya yi mata magana.
Ji ya yi an janyesa ƙiiiii tare da matsar da shi gefe, a zuciye ya juyo domin duk a tunaninsa Jawaad ne ya masa wannan iskancin mai tafe da rainin hankali. Sai dai ƙyam ya ƙame ganin Abdul-Hameed gaban Laushi tamkar zai haɗe da jikinta yana kallonta ido cikin ido kuma ko uffan bai furta ba. A daidai wannan lokacin Baffa Ɓaleri ya iso wajen don tun lokacin da Abdul-Hameed ya janye Jawaad daga gabanta ya bashi damar ganin fuskan Zeenah ɓaro-ɓaro.
Hannu kawai suka ga ya ziro tare da shaƙar wuyan Zeenah da ƙarfi wanda ya firgita su huɗun duka musamman Zeenah da ko cikin tunaninta bata taɓa kawo ƙara haɗa fuska da idanun babanta ba.........
#Babiyo #Mamiyo #Baffa Ɓaleri #Baffa Jibrila #Abdul-Hameed #Jawaad #Habib #Zeenah #The war #The regret #The Destiny #Matar Sayyadee *** [9/3, 5:58 AM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)
*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee
☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`