Page 65
Aje ai following channel ɗina please 🙏🏼 ***
*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***
Domin shiga comment section kuma ki danna wannan link ɗin👇🏼 *** *_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining link ɗin da ke sama domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜
_*💃🏻💃🏻 _Kuna ina 'yan uwana matar aure da 'yan mata? Shela nake ko wacce ta fito domin kuwa yau na zo maku da albishiri! Kun san matar Sayyadee ta ku ce ba ta samun abun ƙaruwa ta yi shuru domin ta ƙaru ita kaɗai._💃🏻💃🏻
💐💐🌼🌼_Magana ake ta ƙamshi. Toohwa! Mai ya hwaru?_ 🤔 🌷🌷🌸💮
*To maza ku marmatso ga sirrin nan. Shahararriyar nan wacce ke inganta soyayya tsakanin ma'aura wato Fatima Zaransalaty inkiya Queen Zarah ce ta taho mana da wani ƙamshim domin cika hancinar mazajemu da ƙamshi*. _INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_ _TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA KUJI 💃🏻
_Zaran Salaaty ta yi tafiya miƙaƙƙa har Sudan domin farnata ranmu da na mazajenmu ta kawo mana Sudanese perfume👌🏻 wanda idan har kika shafa shi a jikinki ko kin yi wanka ƙamshin bai barin jikinki. Tested and Trusted ƴaruwa. Zaransalaty ba iya sudanese perfume ta kawo maku ba, akwai kayayyaki masu matuƙar inganci na gyaran HQ (kun san dai ba a wasa da headquarter) akwai kayan gyararrakin jiki kala-kala na ƴan mata da matan aure. Sannan Zaransalaty tana sai da Decoration na kayan ɗaki iri-iri wanda baki taɓa ganinsu._
_KAR IN CIKA KI DA SURUTU, KE DAI NEMI ZARANSALATY A NUMBERS ƊINTA KAMAR HAKAA_: *** Or ****
*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_nfection_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_
_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ ***** *****
Wani irin shaƙa ya mata da iyakacin ƙarfinsa don har ƙumbunansa suna kartar naman wuyanta. Nan take ta soma wauware idanu tare da ɗaura hannayensa biyu bisa hannun Baffa Ɓeleri tana ƙoƙarin cire hannunsa amma ta ƙasa, ga numfashinta yana alamar ɗauke don daƙyar ta ke kokuwar fuzgosa.
Da hannu ɗaya ya shaƙeta, ɗayan hannun kuma ya yi amfani da shi ya riƙa sauke mata maruka tamkar ya fulawar da aka riga aka kwaɓa.
Abdul-Hameed ne ya soma isa wajen a gigice da kuma matsanaici tashin hankali ganin Baffan nasa zai kashe masa mace da ya fi so duk duniya idan aka cire mahaifiyarsa. Su baffa ma ga gudu suka ƙariso wajen duk da Jawaad da Habib sun riga su don har sun soma taya Abdul-Hameed da ke ƙoƙarin cire hannu baffan a wuyan Laushi.
Wani irin jifa ya yi da ita sannan ya shiga taka ruwan cikinta da iya kacin ƙarfinsa kuma a lokaci ɗaya yana shurinta tamkar ball. Duk yawansu sun kasa dakatar da shi daga irin mugun dukan da ya ke wa Zeenah wanda tun ƙarisowar su Baffa suka fahimci 'yarsa ce saboda tsananin kamannin da suke da juna. To amma tambayar ita ce mai ta masa yake mata irin wannan dukan haka.
Wasu tagwayen maruka Baffa Ciroma ya saukewa Baffa Ɓaleri sai da ya yi taga-taga zai faɗi. Amma tsabar taurin kai da zafin zuciya sai ya ƙara yunƙurawa zai yi kan Zeenah da ke kwance a ƙasa cikin jini amma sai Baffa Ciroma ya damƙo hannunsa tare da faɗin, "Idan har na isa na kai matsayin mahaifi a wajenka kar ka kuskura ka kuma kai hannunka jikin yarinyar nan!"
Cak! Baffa Ɓaleri ya tsaya amma jikinsa wani irin rawa ya shiga yi sosai kamar yadda 'yan tauri suke yi lokacin da ake zabga masu kirari. Kuma ba komai ya jawo haka ba sai tsabar tafasa da zuciyarsa ya ke yi akan ganin Zeenah da ya yi a gabansa. Ji ya ke tamkar ya ga bindiga a hannunsa ya harbeta ko zuciyarsa ta yi sanyi.
Abdul-Hameed da ke duƙe kusa da Zeenah yana kallon jinin da ke zuba daga gefen bakinta da kuma ramukan hancinta, bai san lokacin da ya ɗago ya zabgawa Baffa Ɓalerin da ke kallonsa sama yana tunani wani irin mugun harara ba. Sai ya kai hannu ya taimakawa Zeenah da ke son miƙewa tsaye.
Sai bayan ta tsaya da kyau sannan ta kalli mahaifinta da shima ya ke kallonta suna jifan juna da mugun kallon tsana.
A dake kuma cike da rashin tsoro ta gyara tsayuwarta sannan ta furta, "Ka dake ni iya yanda ranka yake so ku kuma ka kashe ni, hakan ba zai taɓa canza cewar kai ne wanda ya yi silar zuwana duniya ba, kuma wallahi duk inda na shiga sai na faɗa kaine mahaifin da ya tsine min tare da watso ni waje ko zani babu a jikina don kawai na aika kuskure."
Waro idanu waje Jawaad da Habib suka yi tare da ƙara ƙamewa cike da tsantsan mamaki da tashin hankalin furucinta. Musamman ma Habib don tun kallon farko da ya yiwa Baffa Ɓalerin da Zeenah ɗin lokacin da ya shaƙi wuyanta ya ga tsantsan kamanni tamkar an tsaga kara.
"Ashe shiyasa ganin farko kika shiga zuciyata na ji ina matuƙar ƙauna da tausayinki. Ashe ke ɗin jina ce. No wonder tun farkon ganin da na miki na ji kamar na san ki tuntuni." duk cikin zuciya Habib ya yi maganar.
Baffa Ɓaleri kuwa harshensa ya soma taunawa yana jin wani baƙin ciki da kunyar kiransa da mahaifi da Zeenah ta yi. Don har cikin zuciyarsa ya yafe ta wa duniya.
"Mai kike faɗa haka? Abubakar ɗin ne ya kore ki daga gidansa? To saboda me?" baffa Ciroma ya faɗi bayan isa inda Zeenah take tare da kamo kafaɗunta.
A hankali Abdul-Hameed ya furta, "Zee-meed! Zee-meed ɗina dagaske ke ce? Ina abunda kika haifa? Ni ne ubansa?"
Zeenah kallon Abdul-Hameed ta yi ba tare da ta baiwa Baffa Ciroma amsar tambayan da ya yi mata ba ta soma kaiwa Abdul-Hameed duka a ƙirjinsa da hannu bibbiyu amma ba ta yarda zai ji zafi ba ta shiga faɗin, "Ina ka shiga? Ina ka gudu ka barni cikin gararin rayuwa? Ka san wahalar da na sha kuwa? Why? Why?" ta faɗi tare da fashewa da kuka ta faɗa jikinsa.
Idanunsa ne su kai jajir tare da ciccikowa da hawaye. Sai kawai ya sakaa hannu biyu ya rungumota jikinsa tsam tare da soma magana cikin kunnenta, "I don't know what really happened, Zee-meed. But I want you to that you're still in my heart till my last breath. Ke ko mutuwa na yi ba zan daina sonki ba. Ban san ya kai komai nawa ya goge a ƙwaƙwalwata ba, amma ina da tabbacin loosing memory na yi wanda bai jima da dawowa ba. Na yi kewanki, na yi nemanki tamkar zan haukace. Har wajen Magajiya na je ta faɗa min kin koma Lagos. A can Lagos na saka a binciko min ke amma sai akaa faɗa min wai kin gudu ke da ƙawayenki saboda wani abu da kika aikata wanda sam ni ban gasgata ba. Ina matuƙar ƙaunarki Zee-meed. Ban san ta yaya rayuwa za ta tafi min daidai ba idan babu ke!"
Wani irin tsit wajen ya ɗauka tamkar mutuwa ta gitta. Hatta baffa Ɓaleri mai zafin zuciya baki sake ya ke kallonsu rungume da juna. Sai yanzu abunda Hafiz informer ya faɗa masa wancen ranar ya dawo masa raɗam a ƙwaƙwalwa.
Jawaad da Habib kuwa mutuwar tsaye suka yi tare da jin wani matsanaicin kishi na yunƙuro masu amma sun kasa ƙwaƙƙwarar motsi don har wannan lokacin Zeenah na rungume a jikin Abdul-Hameed.
"Zuciyata na min ciwo my _Lovey-dovey_, ina jin zafi sosai. Ina jin tamkar zan mutu. Ba zan iya rayuwa mai tsayi babu Meema ba. Na roƙeƙa ka nemo min 'yata. 'Yarmu ta ɓata an sace ta. Yasaar ya gudu da ita zai cutar min da 'yata."
Ɗagota ya yi daga jikinsa yana kallon idanunta sannan ya furta, "Ƴarmu? Ƴar da kika haifa min?"
Gyaɗa masa kai ta yi hawaye na zubo mata bibbiyu daga idanunta. Kanta ya riƙe sannan ya haɗa da goshinsa tamkar zai sumbaceta sannan ya furta, "I promise you, ba zan ƙara bari hawaye su sake zubowa daga idanunki ba. And ba zan ƙara bari wani ko wanene shi ya kai hannunsa kan jikinki ba. Idan kuwa haka ta faru, definitely people will see the other side of me!" ya ƙarisa maganar da ƙarfi duk da ba kallon iyayan nasa yake ba don ya juya masu baya ne yana kallon Zeenah.
A zuciye Baffa Ɓaleri da sai a lokacin ya dawo daga suman wucin gadin da ya yi tun fara iskancin da Zeenah da Abdul-Hameed ɗin suke na rungume-rungumen juna tare da faɗin, "Za ka rama mata ne? Na ce zaka rama mata ne lalataccen yaro! Dama ai lalatacce sai lalatacciya. Ashe duk jirgi ɗaya ya kwaso ku. To ba a gidan ubana ba billahil lazi! Sai dai ku tafi can ku ƙarata da iskancinku."
Kai a ƙasa Abdul-Hameed ya furta, "Ka yi haƙuri Baffa, ba zan iya ɗaga hannuna a jikinka ba don ba irin tarbiyar da ku ka amsa daga iyayanku sannan ku ka bamu bane. Sai dai na rantse da girman Allah zan iya barin kowa da komai a kanta!" ya ƙarisa maganar yana mai ɗago hannun Zeenah kuma wannan karan yana kallon cikin idanum baffan Ɓalerin.
Wani irin lumshe idanu Zeenah ta yi jin abunda _Lovey-dovey_, ɗinta ya faɗi. Sai ta ji ta ƙara jin mugun ƙaunarsa a zuciyarta. Kuma ko ba kowai ta san a yanzu akwai wanda ya tsaya mata. Sai dai kuma gaba ɗaya kanta ya ƙulle ganin mahaifinta a nan inda take. Mai yake yi a nan ɗin, ta dai ji kamar jiya Habib ya faɗa mata a Abuja take. To mai ya kawo mahaifinta Abuja a wannan katafaren wajen kuma har yake iƙirarin gidan ubansa bayan ta san cewar mahaifin nasu ɗan jihar Sokoto ne.
"Ni kake faɗawa haka?" Baffa Ɓaleri ya faɗi yana nuna kansa cike da mamaki don ko cikin mafarki aka faɗa masa ɗan kaninsa zai yi masa wannan rashin kunyar zai ƙaryata.
Tagwayen maruka Baffa Belɗo ya riƙa saukewa Abdul-Hameed a fuska tare da nuna shi da yatsa sannan ya ce, "Ban haifi ɗan da zai raina min ɗan uwa ba dan ubanka! Tsuguna har ƙasa ka dafa ƙafafunsa ka nai mi gafara ko in yafe ka cikin 'ya'yana!"
Daidai wannan lokacin Marwanatu ta shigo cikin asibitin hannunta riƙe da hannun Nenne tana ja domin kawo ta wajen karuwa kamar yadda take faɗi.
"Yauwa Nenne ga 'yar iskan can mai haɗa duniya faɗa. Ta kashe aure yanzu kuma tana son kashe rayuka!" Marwa ta faɗi kasancewar ta labarta mata faɗan da Jawaad da Habib su ka yi.
A zafafe Nenne ta isa wajen tare da ware hannunta za ta zabgawa Zeenah mari, caraf Abdul-Hameed ya riƙe hannun tare da mayar da Zennah bayansa.
Gaba ɗaya daga Habib har Jawaad sai suka zama 'yan kallo suna kallom ikon Allah da al'ajabi....
#Ɓaleri #Abdul-Hameed #Jawaad #Habib #Zeenah #Belɗo #Nenne #Marwa #My Destiny #Matar Sayyadee *** [9/3, 5:58 AM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)
*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee
☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`