Page 66
Aje ai following channel ɗina please 🙏🏼 ***
*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***
Domin shiga comment section kuma ki danna wannan link ɗin👇🏼 *** *_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining link ɗin da ke sama domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜
_*💃🏻💃🏻 _Kuna ina 'yan uwana matar aure da 'yan mata? Shela nake ko wacce ta fito domin kuwa yau na zo maku da albishiri! Kun san matar Sayyadee ta ku ce ba ta samun abun ƙaruwa ta yi shuru domin ta ƙaru ita kaɗai._💃🏻💃🏻
💐💐🌼🌼_Magana ake ta ƙamshi. Toohwa! Mai ya hwaru?_ 🤔 🌷🌷🌸💮
*To maza ku marmatso ga sirrin nan. Shahararriyar nan wacce ke inganta soyayya tsakanin ma'aura wato Fatima Zaransalaty inkiya Queen Zarah ce ta taho mana da wani ƙamshim domin cika hancinar mazajemu da ƙamshi*. _INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_ _TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA KUJI 💃🏻
_Zaran Salaaty ta yi tafiya miƙaƙƙa har Sudan domin farnata ranmu da na mazajenmu ta kawo mana Sudanese perfume👌🏻 wanda idan har kika shafa shi a jikinki ko kin yi wanka ƙamshin bai barin jikinki. Tested and Trusted ƴaruwa. Zaransalaty ba iya sudanese perfume ta kawo maku ba, akwai kayayyaki masu matuƙar inganci na gyaran HQ (kun san dai ba a wasa da headquarter) akwai kayan gyararrakin jiki kala-kala na ƴan mata da matan aure. Sannan Zaransalaty tana sai da Decoration na kayan ɗaki iri-iri wanda baki taɓa ganinsu._
_KAR IN CIKA KI DA SURUTU, KE DAI NEMI ZARANSALATY A NUMBERS ƊINTA KAMAR HAKAA_: *** Or ****
*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_nfection_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_
_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ ***** *****
"Ni ka riƙewa hannu akan karuwa? Ni ko Hameed?" ta faɗi tana nuna kanta ranta a matuƙar ɓace.
"Nenne ban yi hakan don raini ba, don Allah ki haƙuri ki saurare ni zan miki bayanin komai." Abdul-Hameed ya faɗi da sigar lallashi.
"Wallahi tallahi Nenne kar ki yarda! Shi ma ta tsaface shi tamkar yadda ta tsaface Hamma Jawaad da Hamma Habib. Karuwar banza katuwar hofi, annamimiya makira!" Marwa ta ƙarisa maganar tana nuna Zeenah da ke mata wani kallon banza.
"Kina hauka ne? Idan kika ƙara magana a nan wajen sai na ƙariso na karya miki ƙafa, wawuya sha-sha-sha kawai!" Abdul-Hameed ya faɗi yana nuna Marwa.
Gyaran murya Jawaad ya yi yana jin wani abu na yunƙuro masa na tsantsan kishi, duk sai suka juya suna kallonsa har da Zeenah.
"Kai menene alaƙarka da Zee da har kake tada jijiyoyin wuya? That person you're protecting a ƙarƙashina take. Idan akwai wanda zai buɗe baki sannan ya bugi ƙirji ya furta cewar zai tsaya mata a kowani irin hali to ni ne nan! Don ita ɗin zuciyata kuma bugun numfashina. Na barka ne ka gama irin naka hauka inga iya gudun ruwanka. Shin mai ka sani a kan Zee? Kasan irin wahalar da na yi da ita kuwa? Ka san yadda ta ke cikin zuciyata kuwa? Raba ni da ita wani abu ne da ba zai taɓa yuwuwa ba. And let me give you a concrete warning, kar ka kuskura ka kuma riƙe matata!" yana gama faɗin haka ya kai hannu zai kamo hannun Zeenah sai ta yi saurin matsawa baya ta koma gefen daman Abdul-Hameed.
"Ni kuwa in har ina da rai ba zan taɓa bari ɗaya daga cikin ku ya auri maman Meema. Maman Meema bata san kowa a cikin ku ba sai ni. Munafukin banza da hofi maciyi amana! Ka ban kunya wallahi." Habib ya ƙarisa maganar yana hararar Jawaad.
"Dan iyayanku mata mu kuka raina da za ku riƙa sa'insa a gaban idanun mu a kan mace! Duk ku bar nan wajen kamun rayukanku su ɓaci." Baffa Ciroma ya faɗi yana nuna su da hannu.
Baffa Ɓaleri kuwa vibrating kawai ta ke yi tamkar wanda aka jonawa shocking, ya yin da Nenne ta saki hanci da baki tana kallon su Jawaad tamkar wata kwantacciya.
Inna ƙarama kuwa zabga tagumi ta yi yana kallonsu cike da mamaki.
Hannun Zeenah Abdul-Hameed ya riƙe tare da soma janta, sai dai ko taku biyu bai yi ba ya tsaya cak tare da sakin hannunta sakamakon abunda mahaifinsa ya furta.
"Sakar mata hannu marakunyar banza da wofi. Kuma kar in sake ganin ƙafafuwanku a cikin asibitin nan. Ke kuma Saudatu ki kama hannun yarinyar nan ku wuce can gid........"
Da sauri ta katse mijin nata wajen faɗin, "Kai haƙuri Baffan Hameed ba zan iya kai karuwa gidana ta zauna ba bayan bamu da haɗi da ita a cikin gidannan." tana gama faɗin haka ta ja hannun Marwa suka domin ficewa, saboda tsabar ɓacin ran da take ciki bai bata damar ƙarewa Zeenah kallo ba har ta fahimci tsantsan kamannin da suke da baffa Ɓalerin ba.
"Ina bayanki ɗari bisa ɗari!" baffa Ɓaleri ya faɗi yana mai zabgawa Zeenah mugun kallon ban gama da ke ba.
Sai dai cak ta tsaya sakamakon furucin da Jawaad ya yi ta juyo jikinta na rawa.
A mugun fusace Jawaad ya furta, "Zeenah na ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki, na san hakane saboda gwajin da aka mata lokacin da take fama da wata cuta, kuma na yi mu'amala da ita a lokacin da bataa cikin hayyacinta. Ma'aba ni ma ina ɗauke da cutar!"
Wani irin daskarewa jama'ar sa ke ɗakin gaba ɗaya suka yi amma banda Abdul-Hameed da baffa Ɓaleri don da ma shi ya riga ya san karshen alewa ƙasa kuma a rina wai an saci zanin mahaukaciya.
Wani mugun murmushi Abdul-Hameed ɗin ya yi tare da juyawa ya nufi ɗakin da Babiyo ke kwance da sauri, ko minti ɗaya bai yi ba sai ga shi da syringe. Gadan-gadan ya nufi inda Zeenah take, bai yi wata-wata ya kama hannunta ya daidaici jijiya ya zuƙo jininta. Ganin abunda ya ke shirin yi Nenne ta buga wani irin ihuu, sai dai ko kamun ta kariso wajen har Abdul-Hameed ya caka syringe ɗin a kan na shi jijiyar ba tare da second taught ba.
Ba Nenne ba, hatta Jawaad da ya fadi maganar sai da ya zaro idanu yana kallonsa cike da tashin hankali.
Baffa Belɗo haɗiye wani abu ya yi mai ɗaci don har ga Allah bai ji daɗin abunda matarsa ta faɗi game da ƴar ɗan uwansa ba, duk da itama tana da nata alaƙar da ita ta fanni uwa. Sai dai sun fi alaƙa da Mardiyya matar baffa Giɗaɗo kasancewar da ita Mardiyyan da mama Hafsat (mahaifiyar Zeenah wato matar Baffa Ɓalerin) don uwa ɗaya uba ɗaya suke. Ƙanin Babiyo ne ya haife su wanda suke uba ɗaya. Kuma shine wanda aka haifesa mahaifiyarsa ta mutu sai Babiyo ya cigaba da rainon sa. Jikinsa ba ƙaramin mugun sanyi ya yi ba da jin abunda ya Jawaad ya ce da kuma abunda Abdul-Hameed ɗin ya aikata yanzu. Sai dai ba zai taɓa iya yin wani reaction sabida tsan-tsan so da kawaicin da ya ke wa ɗan uwansa, duk da kuwa zuciyarsa ta yi mugun rawa lokacin da Hameed ɗin ya ke dannawa kansa allurar jinin Zeenah ɗin.
"Wayyooo Allahna na shiga uku na lalace ni Saudatu. Shikenan ta kashee min ɗana!
Marwanatu da ke tsaye ita kanta jikinta kerma ya ke yi tana mamakin wannan wani irin makauniyar soyayya Hamma Hameed ya ke wa Karuwar nan da har zai iya kashe rayuwarsa sabida kasancewa da ita.
Da sauri Baffa Belɗo ya nufi matarsa ganin ta na shirin faɗi mummunar kalma ga Hameed. Tafin hannu ya saka ya rufe mata baki sannan ya kalli Mardiyya tare da faɗin,
"Mardiyya kama ɗiyar 'yar uwarki ku tafi gida tare. kai Abdul-Hameedu kai su gida cikin motarka." Baffa Belɗo ya faɗi hakan wanda ya saka baffa Ɓaleri ya ji tamkar ya rufe sa da duka.
Mardiyya da tun fara faɗan ta ke tsaye jikin bango tana hawaye. Don ta ɗan fahimci abunda ke faruwa duk da ba duka ba. Ta dai fahimci Zeenah ta yi karuwanci kuma ita ɗin ɗiyar yayanta Ɓaleri ne kuma ɗiyar yarta uwa ɗaya uba ɗaya. Shi kuwa Abdul-Hameed daɗi ya ji har cikin ransa da mahaifin nasa ya bashi wannan damar.
Jawaad kuwa haushin Baffa Belɗon ne ya kama shi don zuciyarsa raya masa ta yi ɗansa ya ke wa campaign. Fuuu sai ya juya ya wuce ɗakin da aka kwantar da matarsa tamkar zai ta shi sama. Habib kuma ya fice ya bar asibitin domin komawa gidan makoki.
Mardiyya ita ta ƙariso tare da kamawa Zeenah hannu suka fice daga asibitin zuwa harabar motoci. Bata saki hannunta ba har sai da za ta shiga mota lokacin da Abdul-Hameed ɗin ya buɗe mata gaban mota. Sai bayan ta zauna ya rufe motar sannan ya zagaya ya shiga mazaunin driver lokacin har Mardiyya ta shiga gidan bayan.
A hankali ya ke toƙi yana ɗan juyowa bini-bini yana kallon Zeenah da ke gefensa riƙe da hannunta ɗaya kuma idanunta a rufe
"Zee-meed!" ya kira sunanta cikin wani irin muryar soyayya mai cike da shauƙi.
A hankali ta buɗe idanunta da su kai jazur ta sauke a kansa tana masa kallon ido cikin ido.
Mardiyya da ke baya ji kawai ta yi mota ta tsaya sabida itama idanun nata a rufe suke sai dai ba bacci take ba, tunani take akaan abunda ya faru cikin asibiti. Da idanu ta ke bin Abdul-Hameed da Zeenah da ke gaban mota cike da mamaki don sun manta ma tana cikin motar.
" _Lovey-Dovey_" ta kira sunan a kan laɓɓanta bayan ta lumshe idanu tare da buɗe su.
Hannun ya kai ya kamo hannunta ya shiga murzawa a hankali kusan tsayin mintuna biyar kamun ya buɗe baki ya furta, "Ina kallon wani baƙin ciki da tashin hankali a ƙwayar idanunki Zee. Ki faɗamin damuwarki domin ba zan taɓa sukuni ba idan ina ganinki a haka."
"Meema!" ta faɗi kai tsaye tare da fashewa da kuka mai ciwo tana ƙara damtse hannunsa.
"Meema za ta dawo gare mu In sha Allah nan ba da jimawa ba. Ba zan taɓa hutawa ba har sai na ga 'yarmu na kawo miki."
Lumshe idanu ta yi don ta san duk abunda ya faɗa zai yi ɗin. Can kuma ta buɗe idanun a zabure tare da janye hannunta daga riƙon da ya yi mata sannan ta furta, "Mai yasa ka cutar dkanka saboda ni? Mai yasa kai wa kanka allura bayan ka soka ta a jikin da ke ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki? Mai yasa kake son Meema ta zama cikakkiyar marainiya ta kowacce ɓangare ya kamata a ce idan babu ni akwai ka. Idan har kana raye zan mutu cikin salama domin na tabbatar akwai wanda ba zai taɓa barinta cikin maraicin uwa ba. Why, why _Lovey-Dovey_? Mai ya sa kake sona duk na kasance cikakkiyar karuwa, na yi tarayya da maza kala-kala, na kasace 'yar shaye-shaye wacce ba ta jin maganar mahaifinta. Na cakawa mahaifina wuƙa a ciki da wannan hannun mawa. Shin menene abun so da sha'awa a jikin karuwa ragowar titi. Ka faɗa min shin ina da wani quality ne da ya rage min ne a rayuwata?" Ta faɗi tana kuka sosai tamkar za ta shiɗe.
"Come here!" ya faɗi yana mai jawo ta jikinsa ya rungume tare da bubbuga bayanta sannan ya shiga faɗi cikin kunnanta, "Ni ban yarda kina ɗauke da cutar HIV, na san wannan haɗin na Jawaad ne kawai domin ganin ya raba tsakaninmu da ke. Ke ko da dagaske kina ɗauke da cutar wallahi, tallahi billahil azim ba zan taɓa jin ɗigon sonki ya ragu daga zuciyata ba balle har na,ji marmarin rabuwa da ke. You are my life partner, Zee-meed. _sannan I want you to know that True love is neither physical nor romantic. It is rather the acceptance of all that is, all that has been, all that will be and all that is not. Ina nufin Kauna ta hakika na gaskiya ba a kyawun jiki ya ke ba, kuma ba ba sha'awar da mutum ya ke ji a zuciya ba. So na gaskiya, shine rungumar duk abunda ke akwai, duk abunda ya gabata, duk abunda zai zo, da kuma duk abunda babu shi. Abunda na ke nufi shine, kauna ta hakika ita ce kaunar da ka ke wa mutum ba dom kyawun surarsa ba, ba don sha'war da ka ke masa ba. Shi so na gaskiya shine ka rungumi duk wani abu da ke tattare da ita yanzu, abunda ya taba kasancewa da ita a da, abunda zai faru da ita nan gaba, da kuma abunda ka ke so a gare ta wanda ba ta da shi._ Zee-Meed I love you unconditionally!"
(Jawaad zo, muna da meeting. Don Allah ka,zo ka warware abunda ka ƙulla. Ka,san dai kai ɗan gidana ne. Shin dagaske Zee-meed na ɗauke da HIV ko kuma zafin kishi ya sakaa ka fadi haka? 🥵🥶🤔 )
#Zee-Meed #Jawaad #Habib #Nenne #Ɓaleri #Belɗo #Mardiyya #Marwanat #Family Saga #Eternal love #Romeo and Juliet #My Destiny #Matar Sayyadee *** [9/3, 5:58 AM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)
*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee
☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`