Page 67
Aje ai following channel ɗina please 🙏🏼 ***
*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***
Domin shiga comment section kuma ki danna wannan link ɗin👇🏼 *** *_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining link ɗin da ke sama domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜
_*💃🏻💃🏻 _Kuna ina 'yan uwana matar aure da 'yan mata? Shela nake ko wacce ta fito domin kuwa yau na zo maku da albishiri! Kun san matar Sayyadee ta ku ce ba ta samun abun ƙaruwa ta yi shuru domin ta ƙaru ita kaɗai._💃🏻💃🏻
💐💐🌼🌼_Magana ake ta ƙamshi. Toohwa! Mai ya hwaru?_ 🤔 🌷🌷🌸💮
*To maza ku marmatso ga sirrin nan. Shahararriyar nan wacce ke inganta soyayya tsakanin ma'aura wato Fatima Zaransalaty inkiya Queen Zarah ce ta taho mana da wani ƙamshim domin cika hancinar mazajemu da ƙamshi*. _INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_ _TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA KUJI 💃🏻
_Zaran Salaaty ta yi tafiya miƙaƙƙa har Sudan domin farnata ranmu da na mazajenmu ta kawo mana Sudanese perfume👌🏻 wanda idan har kika shafa shi a jikinki ko kin yi wanka ƙamshin bai barin jikinki. Tested and Trusted ƴaruwa. Zaransalaty ba iya sudanese perfume ta kawo maku ba, akwai kayayyaki masu matuƙar inganci na gyaran HQ (kun san dai ba a wasa da headquarter) akwai kayan gyararrakin jiki kala-kala na ƴan mata da matan aure. Sannan Zaransalaty tana sai da Decoration na kayan ɗaki iri-iri wanda baki taɓa ganinsu._
_KAR IN CIKA KI DA SURUTU, KE DAI NEMI ZARANSALATY A NUMBERS ƊINTA KAMAR HAKAA_: *** Or ****
*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_nfection_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_
_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ ***** *****
Baki sake Mardiyya ke kallon Abdul-Hameed da ya mance sam tana a cikin motar. Sai dai sosai zuciyarta ta narke da ganin irin ƙaunar da Abdul-Hameed ke yiwa ƴar yar nata.
"Oh ya rab! I wish." Mardiyya ta faɗi a zuciyarta tana ƙara zuba masu idanu tamkar ta samu television.
"Da ana mayar da hannun agogo baya, da na koma baya na gyara ɓarnar da na aikata. Ina mugun dana sani a rayuwata. Zafin zuciya da rashin karɓar kaddara Abbana ya kore ni daga gida don na aikata kuskure, ni kuma zafin rai da taurin kai game da bushewar zuciya ta turani ga faɗawa halakar shiga karuwanci don in baƙanta masa. Sai dai gashi hakan bai ƙare ni da komai ba sai shiga halaka da faɗawa tasku kala-kala. Na sha duka a hannu maza lokacin da na ke zaune gidan Hajja Lanti, na faɗa harkar shaye-shaye da sai da ƙwayoyi da tabar wiwi, na ci amanar saurayin da ya ɗauke nauyina da na 'yata, ƙarshe kuma na faɗa hannun mai hatsari wanda tare suke da wanda na ciwa amana har hakan ya jefa 'yata cikin hatsari wanda ita kanta na cusgunawa rayuwarta. Bata san menene daɗin uwa ba sai a gaɓar da za a sace min ita. Kulawata ƙanƙani ta sani, amma ita kuma tana min wani irin soyayyar da ni kaina ban yiwa iyayena kwatankwacinsa ba. Idan ban da lafiya ba ta ƙara samun sukuni har sai na warware. Idan na buge ta hakan ba shi zai hanaa ta zo ta rungumeni ba ko da kuwa zan yanka naman jikinta ne. Tana matuƙar ƙaunata da yi min biyayya, ta sha tambayata ina mahaifinta, t sha yin kuka idan ta ganni da wani namijin, ta sha yin fushi da ni tdaina cin abincinna a duk lokacin da wani ya kwanaa a ɗakina. Duk wanda ya aibata ni kuwa na riƙe fuskansa kenan kuma ta tsane shi. Idan ta ga hawayena ba ta ƙara sukuni, ta riƙa manne min tana hawaye itama tare da tambaya tana faɗin aunty Laushina wa ya ɓata miki rai. Inna lillahi wa inna ilaihir raju'un, wayyoo zuciyata! Meemata kina ina? Ki dawo gare ni don Allah!" ta ƙarisa maganar tana kuka sosai.
Shuru motar ta ɗauka, babu abunda ka ke ji sai shassheƙar muryan Zeenah. Abdul-Hameed bai iya ya ƙara ce mata komai ba. Duk da bai taɓa ganin 'yarsa ba, amma yana jin matsanaicin ƙaunarta da son ganinta. Amma kuwa ya fi ƙaunar uwar 'yar a kan 'yar. Kukan da take yi yanzu ba ƙara kekketa masa zuciya yake ba. Sam bai ƙaunar ganin ɗigon hawayenta idan ba na farinciki ba.
Hannunta ya ƙara damtsewa da hammunsa na hagu sannan ya yi amfani da hannun damarsa ya riƙo ƙeyarta tare da haɗa goshinsu waje ɗaya ya furta, "In sha Allah hawayen nan na ki sai sun zamo na farinciki. Na miki alƙawarin nan Zee. 'Yarki za ta dawo gare ki. Ba zan bari ki cigabaa da kukan rashinta ba, sannan don girman Allah let bygone be gone. Ban so ki ƙara magana akan pass ɗinki. Mu yi fucosing akan future don Allah."
Rimtse idanu ta yi tana jinjina masa kai hawaye na zubo mata. Baki ya kai ya yi kissing idonta sannan ya jinginar da ita a kan kujera sannan ya kuma saka yatsunsa biyar cikin nata yatsun kamun ya tashi motar ya hau tuƙi da hannu ɗaya.
Sai da ya hau titi sannan ya tuna inda zai kai Zeenah ɗin kuma a wannann lokacin ya tuna cewar Mardiyya na cikin motar. Kallonta ya yi ta mirror, karaf suka haɗa idanu da ita. Murmushi ya saki mai ɗan sauti sannan ya kawas da kansa tare da shafa kai sannan ya mayar da hannun steri. Itama murmushin ta yi tare da kawas da idanunta don ta fahimci sam Abdul-Hameed bai da kunya, duk da ya girmeta amma ai sunan ƙanwar mahaifinsa ta ke amsawa tunda da wanda ya haifi mahaifinsa da wanda ya haifi mahaifinta uba ɗaya suke, uwa ce kowa da tasa. Kuma bugu da ƙari ita ɗin kanwar mahaifiyar wacce yake so ne uwa ɗaya uba ɗaya.
A hankali ya riƙa tafiya a kan titi yana kallon motocin jama'a da ke shigowa gidan domin ta'aziyya. Tafiyar da bata wuce ta mintuna takwas zuwa goma ba, sai ga su da kwasar sha biyar. A harabar gidan ya yi parking, babu kowa a gidan har da yaran kasancewar gaba ɗaya suna gidan makoki.
A hankali ya saki hannunta sannan ya buɗe mota ya fita tare da zagayawa inda take ya buɗe mata murfin motar sannan ya riƙo hannunta ya taimaka mata ta fito. Mardiyya kuwa ita da kanta ta buɗe motar ta fito. Ba tare da ta ko kalli inda suke ba ta yi wucewarta sabida bata son ganin abun kunya.
Wani irin jiri ne ya ɗibi Zeenah lokacin da ta tsaya da ƙafafunta, da sauri ya kai hannu ta dafe motar shi kuma ya yi sauri riƙota yana faɗin, "Careful!"
"Jiri na ke gani!" Zeenah ta faɗi tana mai runtse idanunta.
"Let me carry you," yana ida faɗin haka ya mata ɗaukar jarirai ya nufi ɓangaren Mardiyya da ita.
Mardiyya ta cire hijjab ɗinta ta aje a gefe kenan ko kai ga zama ba tai ba Abdu-Hameed ya turo ƙofa ya shigo ɗauke da Zeenah a hannu. Da sauri Mardiyya ta juya ta bar falon tare da shigewa kitchen sabida nan ne ya fi kusa da inda za ta ɓuya cikin saurin gudun ganin abun kunyar da ɗan nata ke yi. Shi kuwa ko kula da ita bai yi sai ma kwantar da Zee ɗin da ya yi a kan three sitter sannan ya zauna a ƙasa yana kallon fuskanta da ke a rufe fuskansa ya nuna alamun tashin hankalin hanayin da take ciki.
Cikin sauri kuma ya miƙe tare da nufar kitchen, Mardiyya da ke leƙensu ganin inda ya nufo sai ta yi saurin fitowa kamun shi ya iso ta shige ɗakin baccinta.
Bayanta ya bi da kallo kamun ya taɓe baki sannan ya shige kitchen ɗin. Kalle-kalle ya fara yi a ƙatoton kitchen ɗin har ya yi arba da kayan tea. Cikin sauri ya kunna standing gas ɗin ya zuba ruwa a tukunya ya ɗauraye sannan ya sake zuba ruwa amma na gora. Kamun ya yi zafi sai ya miƙa hannu cikin cabinet ya ɗauko milk, suger and bounvita ya zuba su a cup. Ruwan ta tafasa sai ya juye rabi a cikin cup ɗin tare da juyawa sannan ya ɗauko wani cup wanda babu komai ya ciki ya fiffita shayin ya rage zafi sannan ya dawo falon ɗauke d cup ɗin shayin. Sai da ya je gabanta sannan ya aje cup ɗin a gefe ya ɗago ta tare da zaunar da ita.
"You must be hungry, that's why you're feeling dizzy. Take this cup of tea you'll fell much better, In sha Allah." ya ƙarisa maganar ya na mai kai mata cup ɗin baki.
Sipping kaɗan ta yi sai ta sautin furzar da shi sabida zafin da ya ratsa bakinta, "Akwai zafi!" duk ta faɗi lokaci ɗaya.
Gaba ɗaya sai ya ruɗe don ji ya yi tamkar shi ya ƙona bakinsa. "I'm sorry! I'm really sorry. Laifina ne da ban fara kaiwa bakina na ɗanɗana yanayin zafinsa ba. Give a minute ina zuwa." ya ƙarisa faɗin hakan tare ajiye cup ɗin da ya karɓa a hannunta a ƙasa sannan ya koma kitchen ɗin da sauri.
Da idanu kawai take binsa, ita kanta ta san she's the luckiest person on the earth da ta samu na mijin da ke mata irin wannan makauniyar soyayyar.
Mintuna kaɗan ya dawo hannunsa riƙe da empty cup ya zauna a inda ya tashi sannan ya shiga fiffita mata. Sai da ya kai baki ya yo sipping ya ji a bakinsa ya masa daidai sannan ya ba ta. Lokacin da ta kai cup ɗin bakin har wani miƙewa ya akan guiwowinsa yana kallon tafiyar maƙogwaranta. Sai da ya tabbatar ta haɗiye ruwan bai ƙona ta ba sannan ya saki ajiyar zuciya tare da zama ya tanƙwase ƙafa yana kallonta.
Sai da ta kusa shanyewa sannan ta ji ta ƙoshi. Miƙa masa cup ɗin ta yi tare da faɗin, "I'm full!"
"Ma sha Allah!" ya faɗi tare da amsar cup ɗin ya miƙe ya mayar kitchen sannan ya dawo ya zauna yana kallonta.
Murmushi ta sakar masa tare da faɗin, "I miss you alot, Lovey-Dovey."
"Miss you more Zee-meed. Na yi kewarki tamkar zan haukace."
"Ka yi aure ko? Na san dole za kai aure." ta faɗi fuskanta babu yabo babu fallasa.
Shikuwa sai da gabansa ya buga da ƙarfi don bai son abunda zai soki zuciyarta ko kuma ya ɗaga hankalinta. Kamar ba zai ce mata komai ba, sai kuma ya daure ya furta, "Shekaranjiya aka ɗaura min aure. Amma kuma kar ki saka komai a ranki, auren da na yi ba zai taɓa canza matsayinki a cikin raina ba. You're a very speacial to my heart, Zee-Meed."
Rufe idanu ta yi sannan ta canza maganar tare da faɗin, "Menene alaƙata da nan gidan? Ya akai ka zama ɗan uwana? Mai yasa mahaifina ya ce nan ɗin gidan ubansa ne? Ina son sanin tarihin komai."
"Ki huta a yanzu. So na ke ki bacci ki samu natsuwa for now. Ni kuma zuwa da daddare zan dawo na baki tarihin gidannan, sai dai ni ma ba kowani tarihi na sani ba. Zan baki labarin iya abunda na sani da kuma sanadin da baffanki da baffana suka bar Arɗo Barkinɗo!"
Jinjina masa kai ta yi don ita kanta for now tana buƙatar space domin tunani, sannan kuma tana buƙatar Ladi Katifa da Salma kusa da ita. Don da su kawai ta yarda har take iya faɗa masu wani abu da ya dangance ta har su bata shawara.
"Ki tabbatar kin yi bacci cikin salama. Zan dawo, sai na dawo!" ya ƙarisa maganar yana yi wa goshinta kiss sannan ya fita daga ɗakin.
_ARƊO BARKINƊO SPECIALIST HOSPITAL_
Ƙarar da suka ji tamkar an jeho wani abu daga ɗakin da babiyo ke kwance ya sakaa gaba ɗaya suka runtuma zuwa ɗakin har da Babiyo har da Nenne da ke kuwa tana riƙe ƙirjinta.
Abunda ya matuƙar ba su mamaki shine ganin ba kowa ba ne ya yi wannan jifar face Babiyo da ya yi amfani da hannunsa mai ɗan lafiya ya riƙa jifa da abunda ke kusa da shi saboda ba zai iya magana ba har 'ya'yan nasa su ji. Don ya gani kuma ya ji duk abunda ya wakana a waje don nurse ɗin da ta shigo dubasa lokacin da aka kori kowa waje ita ce ta taimaka ta ɗaga masa gadon kamar yanda ya mata alama da hannu. Kuma gaton yana fuskan glass window ɗin da ke ɗakin ne.
Ɓacin rai muraran suka gani kwance a fuskan Babiyo. Sai ƙoƙarin maganaa ya ke amma ya kasa sabida bakin nasa da ya karkace. Duk sai suka isa gare sa suna badhi haƙuri duk ba su san ainahin abunda ya ke magana a kai ba.
Hannun mai lafiya ya ɗaga ya zaro biron da ke gaban aljihun Baffa Ciroma, hakanne ya fahimtar da su duka magana ya ke son yi ta hanyat rubutu. Sai Baffa Ɓaleri ya yi saurin ɗaukar wani ƙwalin magani ya ɓarka ya miƙa masa. Duk da rawan da hannun nasa ke yi nai hana shi yin rubutu kusan layi shidda ba sannan ya jefawa baffa Ciroma (wato ƙaninsa) a fuska.
Da sauri baffa Ciroma ya ɗau takarda. Abunda ya fara gani a saman rubutun shine, _Ka karanta a zahiri kowa ya ji kashedi da wasiyyata_. Baffa Ciroma na gaam karanta ya soma karanta gundarin maganar a zahiri.
_Ni Arɗo Barkinɗo na haramtawa kowa a cikin gidan amfani da kalmar tsinuwa ko kara ga 'ya'yansa. Sannan ban yafewa duk wanda ya kuma faɗin mummunar kalma ko son raba min kan ahali ba ko shi wanene. Na ji duk abunda ya faru kuma na gani da idanuna! Kar wanda ya kuma tada maganar da ke tsakanin 'yar wajen Abubakar (Ɓaleri) da su Abdul-Hameed ba. Kuma Ɓaleri ya janye kakkausar maganganun da ya yi a kan ɗiyarsa. Idan Allah ya yi ni mai tsayin rai ne, idan muka dawo daga India zan warware maku abunda duk baku sani ba game da Abdul-Hameed da Zeenah wanda suna daga cikin waɗanda aka cutar saboda ni. Idan kuma na mutu kamun warware komai, wasiyya ita ce a gare ku da ku ɗaura igiyar aure a tsakaninsu, sannan ku haɗe kawunanku ku yafi junanku. Tukur da Mahmuda da uwarsu kuma hukuma za ta ji da su, sannan ban yarda maganar yunƙurin kisan da su kai min ya shiga duniya ba. Ɓaleri kai ne mai kafiya, naci da zafin zuciya! To ka sani bayan babu ni kai ne maƙwafin uba a cikin wannan gida. Ina roƙonka da girman Allah ka sassauta wannan baƙin ɗabi'ar taka da ni da kai mu ka yo gadonta wacce bata haifa mana komai ba sai ɗa mara ido. Idan kun amince kun yi min alƙawarin cika min burina ku duka anan ku saka hannayanu sannan ku kao wa sauran da basu a nan su ma su saka hannayensu. Idan kuma ba ku amince ba ku jefar da takardar ku yi waje!"
Da kuka Baffa Ciroma ya ƙarisa karanta saƙon Babiyon. Shi ya fara saka hannu sannan ya miƙawa Ɓaleri. Ɓaleri jijiyoyin kansa har harbawa suke ya rattaba nasa hannun. Haka sauran da ke ɗakin.
Nenne kuwa hannun ta ɗaura a ka tare da ficewa daga ɗakin jin ɗanyen hukuncin da Babiyon ya yanke na haɗa aure tsakanin karuwa da ɗanta. Don har yanzu nutsuwa bai saka ta fahimci Zeenah 'yar wan mijinta bane.
Da maɗaukakin farinciki Hameed ya isa gidansa. Ko da ya shiga ya taras da amaryarsa a falo, sai kawai ya nufeta ya rungume yana mai jin wani farinciki na taso masa na ganin Zee-meed ɗinsa.
Ita kuwa Asma'u kanta ne ya yi wani irin girma ta ɗauka adon da ta caɓa ne ya zauna angon nata.
A wannan rana dai sosai ya bataa farinciki don sam bai buƙatar abunda zai canza masa mood ɗinsa. Yana relating da ita sai shaiɗan ya yi ta maishe masa fuskan Asma'un yana koma masa na Zeenah. Da a ce Asma'un na cikin hayyacinta da ta fahimci da sunan da ya ke kiranta da shi, don babu abunda bakinsa ke faɗi sai "Zee-meed you make me forget how to breathe. Nobody is perfect, but you're so close it's scary. All I need is you right here. You give me endless butterflies. Just the thought of you right now makes my heart soar. I love you more than I did yesterday but not more than I will tomorrow."
Farinciki tamkar zai kar Asma'u a wannan yini. Suna tare har dare don hatta sallah tare su kai a ɗaki. Ƙarfe takwas ya cancanɗa wanka ya fita Asma'u sai zuba shagwaɓa take. Shi kuwa da ya bar gida kai tsaye gidan Baffa Giɗaɗo ya nufa domin ganin ruhinsa. Kamar yadda ya mata alƙawari duk wani abu da ya sani game da gidan sai da ya faɗa mata, ciki gar da sanafin barin baffanninsu gidan. Sosai ZEENAH tai kuka don har sai da ya ji dama bai faɗa mata ba. Tausayin mahaifinta sai ya lulluɓeta har ya saukar mata da zazzaɓi.
Washa gari kamar yadda Baffa's su kai alkawari babu wanda ya ƙara bi ta kan maganar Zeenah da su Abdul-Hameed, sai hankalinsu ya karkata gaba ɗaya a tafiyar da Babiyo zai yi zuwa ƙasar India jinya wanda daga shi sai baffa Ciroma da baffa Ɓaleri..........
#Zeenah #Abdul-Hameed #Babiyo #Ɓaleri #Nenne #Asma'u #Ƙaddarata #My Destiny #Matar Sayyadee *** [9/3, 5:58 AM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)
*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee
☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`