My Destiny (Ƙaddarata)

Page 68

by @matarsayyadee3

Aje ai following channel ɗina please 🙏🏼 ***

*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***

Domin shiga comment section kuma ki danna wannan link ɗin👇🏼 *** *_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining link ɗin da ke sama domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜

_*💃🏻💃🏻 _Kuna ina 'yan uwana matar aure da 'yan mata? Shela nake ko wacce ta fito domin kuwa yau na zo maku da albishiri! Kun san matar Sayyadee ta ku ce ba ta samun abun ƙaruwa ta yi shuru domin ta ƙaru ita kaɗai._💃🏻💃🏻

💐💐🌼🌼_Magana ake ta ƙamshi. Toohwa! Mai ya hwaru?_ 🤔 🌷🌷🌸💮

*To maza ku marmatso ga sirrin nan. Shahararriyar nan wacce ke inganta soyayya tsakanin ma'aura wato Fatima Zaransalaty inkiya Queen Zarah ce ta taho mana da wani ƙamshim domin cika hancinar mazajemu da ƙamshi*. _INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_ _TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA KUJI 💃🏻

_Zaran Salaaty ta yi tafiya miƙaƙƙa har Sudan domin farnata ranmu da na mazajenmu ta kawo mana Sudanese perfume👌🏻 wanda idan har kika shafa shi a jikinki ko kin yi wanka ƙamshin bai barin jikinki. Tested and Trusted ƴaruwa. Zaransalaty ba iya sudanese perfume ta kawo maku ba, akwai kayayyaki masu matuƙar inganci na gyaran HQ (kun san dai ba a wasa da headquarter) akwai kayan gyararrakin jiki kala-kala na ƴan mata da matan aure. Sannan Zaransalaty tana sai da Decoration na kayan ɗaki iri-iri wanda baki taɓa ganinsu._

_KAR IN CIKA KI DA SURUTU, KE DAI NEMI ZARANSALATY A NUMBERS ƊINTA KAMAR HAKAA_: *** Or ****

*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_nfection_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_

_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ ***** *****

Gobe ne ake jirgin su Babiyo zai ɗaga zuwa ƙasar India. Kowa da kowa na gidan sai da suka zo domin yi masa Allah ya tsare ya bada lafiya suna kuka tamkar ance musu zai mutu ne. Mutanan Babiyo ba manyan 'yan siyasa danƙam da gidan.

Social media kuwa tuni ta ɗauka har da hotunansa a manhajar facebook yana yawo. Wasu har da ƙara magi da gishiri bayan posting hotunanasa suka yi rubutu a ƙasa kamar haka; _Shahararren ɗan kasuwan nan wanda kuma yana ɗaya daga cikin manyan shugabannin Siyasa kuma mamallakin `ARƊO BARKINƊO GLOBAL COMPANY LIMITED` ya samu wata lalura ta sanƙarau. Ana dai babu inda jikinsa ke motsawa sai ƙwayar idanunsa._

Daga nan comments suka riƙa shigowa mara daɗi da kuma masu matan alkhairi da roƙon Allah ya bashi lafiya. Ma su roƙon masa lafiya sun fi yawa akan masu faɗin abunda bai kamata ba. Don wasu ma cewa su ke jinin mutane ne ke tambayarsa saboda dukiyarsa ta mafiya ce. (Mutanan dai sai Allah. Allahn ma haƙuri ya ke da su. Idan anyi ruwa su ce anyi ruwa, idan an hana su su yi ƙorafi, idan anyi zafi su koka, haka idan anyi sanyi ma su kowa. Wanda Allah mai duniya gaba ɗaya bai iya masa ba, kun ga kuwa babu mai iya masa. Allah ya sa mu dace.)

Washa gari duk manyan gidan iyaye maza da mata da da kuma manyan jikoki su kai wa Babiyo, baffa Ciroma da baffa Ɓaleri rakiya har airport. Ba su baro Nnamdi Azikiwe International airport ba sai da zirgin ya ɗaga sannan suka dawo gida cike da kewa. Domin Babiyo bai taɓa barin Arɗo Barkinɗo irin haba ba sai dai idan Hajji zai je ko kuma Yola wanda bai wuce ya yi kwana uku ko huɗu. Idan ya jima da yawa shine wata guda.

Ko da suka dawo gida daga airport, kai tsaye Baffa Modibbo ya nufi gidan ɗan uwansa Baffa Belɗo shi da babban ɗansa namiji Isma'il. Isma'il ɗin ne ke driving jikinsa har tsuma ya ke don baffa Modibbon ya riga ya faɗa masa abunda ya ke son ya masa a cikin gidan.

Suna parking Isma'il ya miƙa hannu baya ya ɗauko narkekiyar bulalansa dorina mai bakuna uku sannan ya riƙe tare da mayar da hannunsa baya. Baffa Modibbo ne ya yi knocking ransa a mugun ɓace.

Ikilima da ke zaune a kan kujera tana kallo TV tana kuma jefa cincin a baki da ke cikin wani bowl ta kalli ƙofar. Marwa da ke gefenta ta taɓe baki tare da faɗin, "Wata ƙila Hamma Hameed ne. Don na ji ɗazu na naje kaiwa Nenne abinci a ɗaki tana waya da shi tana faɗa sosai."

Harararta Ikilima ta yi da gefen idanu don haushinta take ji ganin daga zuwanta ta canzawa gidansu mood. Ba ta ce mata uffan ba ta nufi ƙofar tare da buɗewa.

Murmushine ya bayyana a fuskanta ganin waɗanɗa suke ƙofar, sai ta ɗan duƙa kaɗan ta furta, "Baffa Jaɓɓama, Hamma Isma'il Jaɓɓama!"

Dukkansu da kai suka amsa mata, Marwa kuwa jin sunana da ta ji Ikilima ta furta sai gabanta ya buga da mugun ƙarfi har bata san ta miƙe tsaye ba, bowl ɗin cincin ɗin da itama ta ke ci ya watse a ƙasa jikinta na rawa.

Wani tsalle ta yi za ta arta na kare, sai dai kash! Yayan nata ya fita zafin nama domin shima tsalle ɗaya ya yi ya dira gabanta tare da taɗiyo ƙafafunta sai ga ta tim a tsakiyar ɗaki. Bai yi wata-wata ba ya shiga ce mata amshi da dorinarsa don ya samu labarin duk iskancin da ta yi tun daga zuwa gidan Jawaad da ta yi da irin husumar da ta tayar har zuwa kiran Nenne da ta yi suka je asibiti nan ma aka kuma wata husumar da a yanzu haka ya haifar da ɓacin rai mai tsanani tsakanin Baffa Belɗo da Nenne don ta yi rantsuwa ɗanta ba zai auri karuwa ba. Shi kuma baffa Belɗo ganin ya ke ta raina mahaifinsa kuma tana ci masa fuska tunda yarinyar da ta ke kira karuwa 'yar ɗan uwansa ce wanda ita har yanzu Nennen ba ta sani ba.

Dukan Marwanat Isma'il ya ke yi da dukkan ƙarfin da Allah ya ba shi kuma a ko ina ya samu a jikinta. Ramadan da ya riga su Baffa Modibbo shigo gidan, jin ihu da hayaniya a falo sai ya yi saurin fitowa, da mugun sauri ya koma baya ganin babu wanda ya lura da shi sannan ya furta, "Daki shegiya ka farfasa mata jikinta wataƙila yanzu ta dawo cikin hayyacita. Mahaukaciyar banza kawai!" ya ƙarisa maganar tare da jawo ƙofar ɗakinsa a hankali ya rufe ƙofar ya murza key don kar ma ya cigaba da jin ihu har imani ya shige sa ya yi ƙoƙarin zuwa cetonta.

Nenne kuwa tana can sama kuma ɗakinta a rufe, babu yadda za a yi ta ji ƙaran dukan ko kuma iface-iface da koke-koken Marwanatun. Ikilima kuwa tana tsaye jikinta sai rawa ya ke ganin irin mugun dukan da Hamma Isma'il ya ke wa Marwa. Gaba ɗaya sai tsoransa ya gigitata. Don shi ma zafin ran garesa sosai ta fi kowa sanin haka don shine wanda za ta aura duk da su suka haɗa kansu. Yunƙurin farko da ta yi domin kiran Nenne sai Baffa Modibbon ya galla mata mugun hararan da ya saka ta koma ta maƙale jikin ƙofa jikinta na rawa.

Marwanatu ta daku iya dakuwa. Sai da jikinta ya farfashe sannan Baffan ya dakatar da shi tare amsar bulalan hannunsa ya furta, "Ja ta ka watsa min ita a mota domin barin gidan nan yanzu. Ba zai yu yadda ta kashe auranta ta riƙa neman sanadin na wasu ba. Ga shi yanzu tana neman sanadin na yayata da matarsa. Kuma wallahi ba ki isa ba. Daga yau idan na ƙara jin kin faɗi aibun Zeenatu ko kuma kin samu wani da maganar abunda ta aikata a baya ko kika ƙara faɗa da ita, wallahi abunda zan aikata a gare ki sai kin ce ba ni ne mahaifin da ya yi sanadin zuwanki duniya ba! Fitar da ita nace Isma'il!"

Da sauri Isma'il ya nufe ta tare da cicciɓarta ya yi waje da ita ya saka a mota. Baffa Modibbo kuma kallon Ikilima ya yi tare da faɗin, "Shiga ciki ki kira min Adda Saudatun."

Da sauri Ikilima ta yi upstairs domin kiran Nennen. Jim kaɗan sai ga su tafe a tare. Nennen hannunta riƙe da tissue da take goge hawaye. Idanunta sun kaɗa sun yi ja.

Kallonta ya riƙa yi har sai da ta zauna a kan kujera. Idanunta sun yi jazur kuma sun yi luhu-luhu da su alamar an kwana kuma an yini ana kuka. Da dasasshiyar muryanta ta gaida shi shi kuma ya amsa yana mai bata girman na kasancewarta matar babban wansu duk da ya girme mata.

"Adda Saudatu!" ya yi kiran sunanta kuma sai ya yi shuru yanaa kallonta don har ga Allah ya fahimci irin abunda take ji a zuciya.

Ko kamun ya ƙara cewa wani abu, sai ga sallamar Abdul-Hameed bayan ya turo ƙofar. Turus ya tsaya yana kallon mahaifiyar tasa da ta masa kallo ɗaya ta sunkuyar sa kai. Gaba ɗaya sai ya ji jikinsa na masa rawa kuma ƙafafuwansa sun gaza ɗaguwa sabida yadda ya ga kamannin mahaifiyar tasa ta canza.

"Taho Abdul-Hameedu zo nan zauna." Baffa ya faɗi yana nuna masa ƙasa kusa da ƙafafun Nennen.

Daƙyar ya iya ɗaga ƙafafunsa ya tako ya zauna a inda Baffan ya nuna masa. Daidai nan Ramadan shima ya fito daga nasa ɗakin sai shima baffan ya nuna masa wajen zama.

"Adda Saudatu, don girman Allah ina so ki ɗan bani hankalinki domin yi maki wani bayani." Baffa ya faɗi sai ta ɗago ta kallesa.

"Na san kina cikin tsananin baƙin ciki da ɓacin rai bisa abubuwan da suka faru shekaran jiya. Na san kowacce uwa za ta ji zafi sosai ace ɗanta ya aikata abunda ya yi shekaran jiya. Kamun in tsunduma kan batun da nake tafe dashi, ina so ki kwantar da hankalinki ɗanki mai ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki domin Jawaad ƙarya yake yi. Tun a ranar na tafi na same shi kuma ya faɗa min gaskiya har da hujjoji don sai da ya bani rahoton lafiyar Baffa Ɓalerin. Bata ɗauke da HIV kawai ya faɗi hakane domin kishi don shima yana sonta ne. Tare suka tafi can ƙasar da Babiyo ya tura shi, tana tare da shi kusan tsayin watanni huɗu zuwa biyar."

Da mugun maɗaukakin mamaki Nenne ke kallon Baffa Modibbo kamun ta furta, "Ɗiyar Hamma Ɓaleri kuma? Magana fa ake akan karuwar da ke neman raba kawunan 'ya'yan gidannan tare da ƙoƙarin kashe min aurena."

Girgiza kai Baffa ya yi tare da faɗin, "Ba ita ke neman kashe miki aure ba, Marwa ce. Kuma tabbas yarinyar ɗiyar Ɓaleri ce, jaririyar da Hafsatu ta haifa. Lokacin da Babiyo ya kore su daga gidan nan ita ce jarirai do ko arba'in ba su bai a gidan nan aka fitar da ita babu kaya, kin tuna?"

Jinjina kai Nenne kawai ke yi hawaye na kwarara a idanunta. Daƙyar ta iya buɗe baki ta ce, "Hamma Modibbo how comes?"

Gyara zama ya yi tare da warware mata labarin da Baffa Ɓalerin ya bashi wanda ya yi sanadiyar da ya saka ya kori Zeenah daga gidansa har ta faɗa karuwanci. Gaba ɗaya tun dagaa kan Nenne, Ramadan da Abdul-Hameed kuwa suke yi.

"Wannan wani irin banza hali da ɓakar zuciya ce ke bibiyar ahalin gidan nan na korar ɗa idan ya aikata kuskure! Inna lillahi wa'inna ilaihir rajun³" Nenne ta maimaita sau uku tana mai rufe fuska da tafin hannunta bayan fashewa da kuka.

Ɗakin ya yi shuru na wasu lokaci kamun Abdul-Hameed ya buɗe baki tiryan-tiryan ya soma ba su labarin haɗuwarsa da Zeenah har zuwa kusantarta da ya yi wanda daga shi har ita basu san mai ya jasu zuwa ga hakan ba. Ya kuma ƙara masu da bayanin d tunda wannan abun ya faru ya mance da ita a rayuwarsa tamkar an shafe masa ƙwaƙwalwa, sai kwanannan komai ya dawo masa tamkar dai aikin aljanu. Bai rage komai ba har cikin da ya yi mata da haihuwar da ta yi da kuma sace 'yar da aka yi.

Sosai kukan Nenne ya ƙaru har jikinta wani irin rawa yake yi tamkar mazari. Hatta Modibbo ya tsorata da yadda yaga Nennen na kuka. Sai ya shiga bata haƙuri tare da faɗa mata maganganu masu kwantar da hankali da kuma faɗin ubangiji game da tawakkali.

"Don Allah ku je ku kawo min Zeenatu nan gidan na ganta. Ku ɗauko min ita don girman Allah. Ashe 'yata ce! Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Allah ka sassauta mata. Allah ka sa muci wannan jarabawar."

Abdul-Hameed tun da ya ji Nenne ta ce ya ɗauko mata Zeenah ya tashi da sauri ya fice daga ɗakin, gaban rigarsa duk ya jiƙe da hawaye. Ko kallon Isma'il da ke masa magana hankali tashe bai yi na ya shiga mota ya tada ya bar gidan. Ganin haka sai Isma'il ya yi saurin nufa cikin gidan don sanin abunda Abdul-Hameed ɗin ke wa kuka.

Bayan kamar mintuna goma sai ga shi ya dawo shi da Zeenah da idanunta ke a soye alamar ita ma kwana dai ta yi tana kukan. Shi ya murɗa handle ɗin ƙofar ta buɗe sannan ya nuna mata hanya ta shiga. Kanta na ƙasa ta shiga ciki, sai ta samu waje ta raɓe ta zauna jikinta na rawa. Da sauri Nenne ta taso tana mai toshe bakinta sabida kukan da ya ƙara yunƙuro mata.

Ita kuwa Zeenah ganin Nenne ta nufo ta gadan-gadan sai ƙanƙame jikinta tare da rintse idanu tana jiran saukar duka. Zaro idanu ta yi jin an ɗagota an rungume tare da sakin kula, kawai sai ta samu kanta itama da fashewa da matsanaicin kuka.

Hannunta Nennen ta kama ta zaunar a kan kujera tare da zama ƙasa tana kallonta. Sai yanzu ta ke hango tsantsan kamanninta da Ɓaleri da kuma Babiyo. Don idan kaga Ɓeleri ka ga Babiyo, haka idan ka ga Zeenah ka ga Ɓaleri tamkar ya yi kaki.

Ba tare da sun tambayeta ba ta shiga basu labarin komai tun daga farko abunda ya saka baffanta ya koreta da irin wulaƙantata da ya yi a titi, alwashin da ta ɗauka, zuwan gidan magajiya, haɗuwarta da Ladi katifa, zunɗen da akai ta yi wa mahaifin har ya kai an daina binsa salla, haɗuwarta da Abdul-Hameed da yanda ya canza mata rayuwa har ta yi nadamar abunda ta aikata da kuma ƙudurinsu na yin aure bayaan ta gama istibura'i, tsautsayin da ya afka masu na yin Zina har ta samu ciki da kuma shafewar tunaninta, zuwanta gida domin ɗauko sarƙar zinari, rigimar da suka yi da mahaifinta har ta caka masa wuƙa bisa rashin sani, guduwanta Lagos da kuma rayuwarta da ta yi, haɗuwarta da Salma nice da kuma Yasaar,faɗansu da Marwanatu, haɗuwarsu da Habib da Jawaad, komawarta gidan Sabo da kaza da zama da, abubuwan da ake aikatawa a can, ciwon da ya same ta na raunanniyar jijiyar jinin ƙwaƙwalwa da kuma dalilin zamanta a Denmark tare da Jawaad.

Da hannu bibbiyu Nenne ta riƙa kaiwa Zeenah duka tana kuka a lokaci guda tare da faɗin, "Kin yi kuskure babba, kin aikata kuskure Zeenatu. Abunda kika yi bai dace ba sam. Idan bawa ya shiga wani musiba wajen Allah yake komawa ba faɗawa halaka irin wacce kika yi ba. Yanzu menene ribar abunda kika aikata. Kinsan illar da kika yi wa kanki kuwa? Kin cuce mu kuma kin cuci kanki har da zuri'ar da za ki yi nan gaba don wannan tabon da kika yafawa kanki zai ta bibiyarki ne har sai kin ji tamkar ki birne kanki da ki huta da baƙin cikin duniya. Mai yasa? Mai yasa kika aikata hakan? Why Zeenah?" ta ƙarisa da ƙarfi tana mai jawowa jikinta ta rungume.

"Babban mai laifin shine Hamma Ɓaleri. Babu inda addini ya ce ka kori 'yarka mace don ta aikata kuskure. Da a lokacin da tai cikin farko bai kore ta ba, ya jata jikinsa ya nuna mata illar abunda ta aikata tare da azabar da Allah zai yi wa mazinaci da duk hakan bai faru ba. Maimakon hakan sai ya turata tura ta duniyar bayan aikata mata da tsinuwa da bala'i kala-kala da ya ke jifanta da shi. Wallahi idan Zeenah na da laifi hamma shi ke da kaso saba'in bisa ɗari. Haba! Wannan baƙar zuciya da mai ya yi kama? Kuma abunda zai baki mamaki Adda Sauda, wallahi har yanzu babu nadama a idanunsa. Ba ki ga irin dukan da ya yi mata a asibiti ba yana ikirarin kashe ta. Wallahi zafin zuciyar Hamma tsoro ya ke bani. Ya fi Babiyo nesa ba kusa ba!" baffa Modibbo ya faɗi.

"Idan shi bai sonta ni ina so ya bar min. Hannunka na ruɓewa ka yar da shi ne? Ko so ya ke ta kuma faɗawa wani halakar? To ni ma ina bayan Babiyo In sha Allah sai Abdul-Hameed ya aureta. Allah dai ya bashi lafiya ya dawo da su cikin aminci." ta ƙarisa maganar da kuka.

Abdul-Hameed kuwa ji ya yi tamkar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha don daɗin abunda mahaifiyarsa ta furta.

"To yanzu mu dawo batun ita 'yar da Zeenah ɗin ta haifa. Ta yaya za mu samu nasarar cafke shi ɗan iskan har ya fito mana da jikarmu. Ohh! Allah sarki yarinya baki ji ba kuma baki gani ba." Baffa Modibbo ya faɗi yana mai zabga tagumi.

Sai a lokacin Abdul-Hameed ya buɗe baki tare da faɗin, "In sha Allah sai inda ƙarfina ya ƙare wajen dawo da Meema cikin ahalinta. Gobe da kaina zan tafi Lagos ɗin domin soma bincike akan shi Sabo da kazan da kuma tsinannen Yasaar ɗin, In sha Allah za ta bayyana cikin gaggawa."

Girgiza kai Baffa Modibbo ya yi tare da faɗin, "No, babu inda za ka for now sabida abunda ke gabanka yanzu. Ni da kaina zan koma Lagos na yi bincike sosai. Don idan ban mance ba kamar akwai wanda naji ance an kama shi da miyagun ƙwayoyo har da bama-bamai da yake ajewa a gidan budurwansa, kuma babban mutum ne shi."

Da sauri Zeenah ta kalle shi tare da faɗin, "Ina kyautata zaton shi ɗinne. Don ban manta ba lokacin da mu kai magana da Ladi Katifa a waya lokacin ina masaukin da wanda Jawaad ya saka ya ɗauko, ta faɗa min ƴan sanda sun zagaye gidan da na ke ciki."

Jinjina kai Baffa ya yi tare da faɗin, "Zan bibiyi case ɗin In sha Allah. Yanzu haka ma zan duba inga ko akwai jirgin da zai tashi zuwa Lagos sai na tafi ni da Isma'il tun yau."

#Zeenah #Abdul-Hameed #Meemah #Nenne #Baffa Modibbo #Isma'il #Marwanatu #Yasaar #Sabo da kaza #Lagos #My Destiny #Matar Sayyadee *** [9/3, 5:58 AM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)

*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee

☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`