Page 69
Aje ai following channel ɗina please 🙏🏼 ***
*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***
Domin shiga comment section kuma ki danna wannan link ɗin👇🏼 *** *_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining link ɗin da ke sama domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜
_*💃🏻💃🏻 _Kuna ina 'yan uwana matar aure da 'yan mata? Shela nake ko wacce ta fito domin kuwa yau na zo maku da albishiri! Kun san matar Sayyadee ta ku ce ba ta samun abun ƙaruwa ta yi shuru domin ta ƙaru ita kaɗai._💃🏻💃🏻
💐💐🌼🌼_Magana ake ta ƙamshi. Toohwa! Mai ya hwaru?_ 🤔 🌷🌷🌸💮
*To maza ku marmatso ga sirrin nan. Shahararriyar nan wacce ke inganta soyayya tsakanin ma'aura wato Fatima Zaransalaty inkiya Queen Zarah ce ta taho mana da wani ƙamshim domin cika hancinar mazajemu da ƙamshi*. _INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_ _TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA KUJI 💃🏻
_Zaran Salaaty ta yi tafiya miƙaƙƙa har Sudan domin farnata ranmu da na mazajenmu ta kawo mana Sudanese perfume👌🏻 wanda idan har kika shafa shi a jikinki ko kin yi wanka ƙamshin bai barin jikinki. Tested and Trusted ƴaruwa. Zaransalaty ba iya sudanese perfume ta kawo maku ba, akwai kayayyaki masu matuƙar inganci na gyaran HQ (kun san dai ba a wasa da headquarter) akwai kayan gyararrakin jiki kala-kala na ƴan mata da matan aure. Sannan Zaransalaty tana sai da Decoration na kayan ɗaki iri-iri wanda baki taɓa ganinsu._
_KAR IN CIKA KI DA SURUTU, KE DAI NEMI ZARANSALATY A NUMBERS ƊINTA KAMAR HAKAA_: *** Or ****
*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_nfection_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_
_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ ***** *****
Duk ɗakin su kai na'am da abunda Baffa Modibbo ya faɗi. Zeenah ko ji ta yi tamkar ta ce baffa zan bika amma babu daman haka. Amma duk da hakan wani natsuwa ne ya lulluɓeta ganin irin yadda ta karɓu a hannun Nenne da kuma irin soyayyarta da ta gani a cikin idanunta.
"How I wish a was raised in this family, da duk abunda ya faru bai faru ba. Inna lillahi wa inna ilaihir raju'un!" Zeenah ta faɗi cikin zuciya amma a zahiri sai da hawaye suka kwaranyo mata.
Kallon Abdul-Hameed ya yi fuska a ɓace tare ɗaga mata gira da kai irin why are you crying ɗinnan. Ita kuma sai ta kawas da kai tana kallon gefe.
Murmushi Baffa Modibbo ya yi don a idanunsa komai ya faru har ma da Nennen da ke zaune ƙasa har a wannan lokacin kuma hannun riƙe da na Zeenar amma duk da hakan tana kallon Hameed ɗin da gefen idanu.
"Bari muje Adda Sauda, duk yadda ake ciki za mu riƙa yin waya. Ke kuma ki kwantar da hankalinki ki daina wannan koke-koken don ba zai biya maki buƙatar komai ba sai da ya saka miki ciwo kum...."
Tun kamun ya ƙarisa maganar caraf Abdul-Hameed ya furta, "Yauwa Baffa gwara dai ka faɗa mata. Ni ban son wannan koke-koken da take yi sai kace wacce bata san Ƙaddara ba, haba! Wannan kukan na sukar zuciyata." ya karisa maganar da iyakacin gaskiyarsa.
Daƙuwa Nenne ta yi masa tare da faɗin, "To rasa kunya tashi ka fice min daga ɗaga ɗaki ka wuce gidanka, mu dai fulani da kunya aka sanmu, kar in ƙara ganin ƙafarka a cikin gidannan."
Zaro idanu ya yi tare da faɗin, "Don Allah Nenne ki min rai kar ki hana ni shigo gidannan bayan rayuwata tana ciki. Wai kin san yadda na ke ji kuwa a kanta, hmm! Nenne you won't understand ina ganin lokacinku ke da Baffa aure kawai kuka yi baku san mai ake cewa Love ba."
Waro idanu ta yi gaba kamun ta kai masa duka a cinya da ƙarfi har dai da ya furta Auuch! Sannan ta ce, "Lokacin ne kuwa ake zallar soyayya mai cike da kunya ba irin taku ta 'yan zamani ba. Fice min daga gidan miji!" ta ƙarisa maganar tana nuna masa ƙofa.
Ramadan, Ikilima da Isma'il dariya suka kwashe da ita. Hatta Baffa Modibbo da ita kanta Nenne sai da suka dara, Zeenah murmushi sai da ya suɓuce mata.
"Au baza ka fitan ba!" Nenne ta kuma faɗi with serious face tana nuna masa ƙofa deep down cikin zuciyarta murmushi take yi tare da furta, "The power of blood relation!"
Miƙewa ya yi yana ɗan susa kai sannan ya kalli Zeenah da taƙi bari su haɗa idanu sai kallon wajen dinning ta ke yi. Da sauri ya koma wajen gefen da take kallo tare da faɗin, "Zee-meed look at me once sai in wuce don Allah."
"Wani sunan shaiɗanancin kuma Zee-deem?" Nenne ta faɗin.
Wannan lokacin Ramadan ne ya bata amsa don shi Hameed ɗin dariya ta ci ƙarfinsa sabida yadda Nenne ta kira sunan da furta ba daidai ba.
"Nenne Zee-Meed ya ce fa ba Zee-Deem ba!" Ramadan ya faɗi shima yana dariya.
"To menene shi hakan? Na san dai ba kalmar turanci ba balle ace ban iya ba. Kun fi kowa sanin degree ce da ni Alhamdulillah."
Dariya su kai dukkan su sannan Ramadan ya ce, "Dama yaushe za a samu wanda bai ci karatu ba a Arɗo Barkinɗo daga matan har mazan. A nan ai na jinjinawa Babiyo wallahi. Zee-meed na nufin Zeenah da Abdul-Hameed. Zee ɗin shine Zeenah, Meed ɗin kuma Abdul-Hameed. Farkon sunanta da ƙarshen sunansa ana haɗa ya bada sunan."
"Hmm, ƴaƴan zamani. Allah ya shirya ku. Zo ka fice ban mance ba." Nenne ta faɗi tana kuma nuna masa ƙofa.
"Alright, zan tafi amma zan dawo anjima." ya faɗi yana nufar ƙofa. Sai da ya murɗa ƙofar ta buɗe, har ya saka rabin jikinsa a waje sannan ya juyo tare da kallon Zeenah, karaf kuwa suka haɗa idanu sai ya furta, "I love you!" da ƙarfi sannan ya fice da gudu yana dariya.
Nenne da mamaki ɗanta ke neman kasheta sabida bata taɓa tunanin haka yake ba sai ta kalli ƙofar sannan ta kalli Baffa Modibbo da ke zaune yana murmushi tare da girgiza kai.
"A'a wallahi, dole ne ma azo ai wannan auren da wuri don na ga kan yaron nan rawa ya ke yi wallahi.
"Gaskiya kam! Mu za mu wuce sai yadda ta yiwu" baffa Modibbo ya faɗi yana mai miƙewa tsaye, sai Isma'il shima ya miƙe.
"To, ubangiji Allah ya tsare ya sa kuma a ganta cikin gaggawa tare da amincin Allah." Nenne ta faɗi tana miƙewa.
Har wajen mota suka rasu ita da Ramadan da Ikilima. Isma'il sai kallon Ikilima ya ke da ke ta sunkuyar da kai saboda Baffa Modibbo da ke wajen don ita ba irin Hammanta Hameed bace. Ita tana da kunya sosai. (ko da yake mata ai mun fi maza kunya aradun Allah!)
Bayan tafiyar Babiyo India da kwana biyu Arɗo Barkinɗo ya hargitse saboda tashin hankalin da iyalan Baffa Mahmud da Baffa Tukur suka tashi da ita na zuwan DSS tafiya da su bisa umarnin gwamnati da kuma shi kansa Babiyo. Ga takardan kamu nan kuma sun taho da shi. Sai dai Mamiyo ita ko kallon inda take ma ba ai ba don Babiyo ya ce su ƙyaleta ita har sai ya samu lafiya tukun.
Kuka 'ya'yansu da matansu kawai suke yi tamkar rayukansu zai bar jikinsu gashi ba su san mai ke faruwa ba. Wani tsanar baffaninsu ne ya dirar masu a zuciya ganin babu wani yunƙuri da su kai na hana su tafiya da iyayan na su. Nan da nan sai aka canza magana wai ai sun haɗa baki ne 'yan ɗaki ɗaya (wato su baffa Ɓeldo) domin su cinye dukiyar Babiyo ganin yana can rai a hannun Allah. Bala'i sosai aka yi a wannan ranar har sai baffa Ahmadu wanda shine auta a ɗakinsu Babiyo ya kira meeting ɗin gaggawan a ɗakin Babiyo ya tsawatar sosai tare shimfiɗa layi akan duk wanda ya sake furta makamacin maganar da ke yawo sai ya ɗau mummunar mataki. Kuma daga yanzu bai son a sake ɗauko kowacce magana har sai Babiyo ya dawo anji daga gare sa. Ya kuma yi ƙari bayani da faɗin in sha Allah Babiyo da ƙafafuwansa zai dawo cike da ƙoshin lafiya.
Da wannan maganar aka samu tarzomar ta ɗan kwanta amma dangin su baffa Mahmud da Tukur ta ciki na ciki.
Can state CID akai da su Baffa Tukur kuma a can suka taras da Hafiz driver wanda ya kusa sati a can ɗin. Gaba ɗayaa ya lalace fuskansa ta mokaɗe sabida dukan da yake amsa. Idonsa ɗaya yafi ɗaya girma kuma sunyi baƙiƙƙirin a zagaye tamkar mai bleaching. Ko da ya ga su Baffa Tukur murmushin jin daɗi ya yi don ya san suma za su amshi nasu kiɗin a sama.
_JAWAAD_ Zuciyarsa tamkar za ta soye haka yake ji saboda baƙin cikin abunda ya faru a asibiti. Ga Khairat da yanzu kwata-kwata bai gane kanta, ya yi lallashin ya yi faɗan har ya gaji. Babu wani magana mai daɗi a tsakaninsu, balle su haɗa wajen kwanciya. Abinci dai tana daurewa ta dafa masa ta aje a dinning daga nan ta shige ɗakinta ta kulle. Don haushinsa sosai take ji. Ga laulayin da ta ke yi mai zafi amma taurin kai da haushinsa da ta ke ji ta gwammaci ta mutu da ta bari ya taimaka mata. Har durƙusawa ya yi ya bata haƙuri amma taƙi saukowa. (wannan gadon banzan naku dai bai yi ba sam, haba! Kamar wanda kafurai suka dafa abinci da gashinsu suka ba ku kuka ci😡😏)
_HABIB_ Shikam ɓangarensa da sauƙi kasancewar matarsa ita bataa san komai ba. Allah ya taƙaita Marwa ba ta nufi gidanta ta gumtsa mata ba, kuma su da ma can suna san junansu don Habib ɗin shi ya,ganta ya ce yana so.
Duk ya ji kishi sosai da ganin Abdul-Hameed na son abunda ya ke so, sai ya ji ya samu relief a kan abunda Jawaad ya yi mata. Ko ba komai za su yi 0-0 shi da Jawaad ɗin, shi da ya ci amanarsa bai samu ba, shi ma kuma bai samun ba. Ya ji ya haƙura da Zeenah ne kawai ganin abunda ya faru a asibiti da ya tabbatar masa da daga shi har Jawaad ɗin ba son su take ba, Abdul-Hameed ta ke so. Kuma ya san idan akwai wanda ya cancanci auranta a cikinsu to Abdul-Hameed ɗin ne. Don haka shi zuciyarsa wasai take. Dama kuma abunda ya fi so shine Zeenah ta shiryu ta bar aikata katuwanci ta natsu waje ɗaya ta kula da 'yarta kuma ta zauna ƙarƙashin kulawar namiji, bima'ana ta yi aure. Kuma yanzu Alhamdulillah burinsa zai cika.
_BAFFA MODIBBO_ Sun samu nasarar samun jirgin da zai tashi zuwa Lagos. A ranar suka tafi har da Marwanat don baffa ya ce zaman ta a Arɗo Barkinɗo matsala ne sabida bata da hankali. Gwara ta zauna a wajensa har sai ana gobe su Babiyo za su dawo sai suma su dawo tare. Kuma kamar yadda ya alƙarwata washa gari ga shiga bincike akan lamarin Meema. Tashin farko wajen Division ɗin 'yan sanda da suka ƙwamushe Sabo da Kaza ya nufa, sai dai bai yi mamakin jin an saki shi Sabo da kazan ma saboda a Nigeria ne nan ɗin. Sai dai ya samu nasarar zuwa Prison ya gana da Yasaar. Sai dai ganawar bata amfana masa komai domin dai Yasaar ya samu taɓin ƙwaƙwalwa hakan ya saka babu wani bayani da ya samu daga gare shi.
Kai tsaye ya tafi cibiyar bincike ta nan Lagos ya sanar masu abunda ke tafe da shi. Sabida matsayinsa da sanin shi ko ɗan wanene cikin gaggawa aka shiga bincike babu kama hannun yaro. A cikin sati biyu kacal aka nasarar cafke Sabo da Kaza da kuma abokin Yasaar wato Layos da ya gudu ƙasar Uganda. Har Uganda aka je aka dawo dashi. Kama Sabo da Kaza ya saka aka gano manyan mutane da ke harkar safarar ƙananan yara da miyagun ƙwayoyi kuma duk akai ram dasu bayan bayyana hujjoji.
Da aka gama haɗa duka hujjoji kuma akai kotu da su wanda ana ne Layos ya shaidawa alƙali a kotu cewar Yasaar sayar da Meema ya yi a wajen wani mai suna Adelbarto wanda shi sam bai san sa ba, ya san dai ɗan ƙasar Colombia ne amma wallahi bai san komai a kansa ba.
Ba ƙaramin tashin hankali Abdul-Hameed ya shiga da jin hakan ba don yana cikin kotun kasancewar tun lokacin da baffa ya kira sa awaya yavshida masa jibi za a shiga kotu ya biyo jirgi ya taho Lagos ɗin.
A take aka yankewa Sabo da kaza da muƙarrabansa da hukuncin kisa ta hanyar rataya. Layos kuma zaman gidan kaso na din-din-din.
Bayan sati guda aka maido da yara ƙanana da aka tura su ƙasa daban-daban domin karuwanci. Wasu dai ba a same su ba sabida an riga da an gididdiba su an saida part-part ɗin jikinsu.
Abdul-Hameed kuwa zuciyarsa har wani fat-fat-fat yake lokacin da ya je duban yaran shi da Habib ko akwai Meema a ciki. Sai dai har suka gama duba 'ya'yan ba su ga Meema a ciki ba. Haka suka dawo gidan baffa Modibbo da sakakkiyar gwiwa. Duƙar da kai kawai Abdul-Hameed ya yi hawaye na kwaranyo masa.
Hannu Habib ya kai ya daddaki kafaɗunsa tare da faɗin, "Kai haƙuri abokina, mu cigaba da roƙon Allah in sha Allah za ta bayyana."
Hawaye sosai Abdul-Hameed ya ke yi kamun ya ɗan ɗago kai ya kalli Habib sannan ya mayar da ƙansa ƙasa yana murza hannunsa kamun ya furta, "Wallahi Zeenah nake tausayi. Ban san wani hali za ta shiga idan ta samu wannan labarin. Ni zan tafi har can Colombia domin nemo 'yarmu. Hankalina ba zai kwanta ba sai na cikawa Zee muradinsa. Ba zan iya jure ganinta cikin tashin hankali da kuka a kullum ba."
Wannan karan Baffa Modibbo ne ya yi magana, "Abdul-Hameed yanzu idan ka tafi Colombia ta ina za ka fara nemo Meema? Zuwa za kayi ka fara nemo Adelbarto? Ka sansa ne, ko kuma ka san a inda yake? Ka san state nawa ne a Colombia? Idan na fahimce ka kenan za ka zagaye kaf state ɗin da ke Colombia domin neman su ko? Hmm ka fa abunda hankali zai ɗauka don Allah! Babu inda za ka je daga nan sai Abuja. Ba za ka yanke komai ba sai Babiyo ya diro ƙasarnan. In sha Allah sun kusa dawowa saboda jikin Babiyo sun ce da sauki sosai don har yana takawa da ƙafafunsa yanzu. Ƙarfin jikinne kawai bai dawo sosai ba. Zeenah kuma ka bar komai a hannuna. Ni da kai na zan mata magana. Tare za mu koma idan za ku tafi"
Jinjina kai Abdul-Hameed ya yi sabida gamsuwa da maganar da Baffa Modibbon ya yi.
Kwaba ɗaya suka kara a Lagos suka tattaro suka dawo amma banda Marwa. Ƙarar shigowar motarsu Zeenah da ke zaune a ƙasa Nenne na mata tsifa ta yi saurin fizge kai ta miƙe tsaye gabanta na wani irin bugawa, jikinta babu abunda ya ke yi sai rawa har dai da Nenne ta riƙota ta zaunar da ita a kan kujera.
Shigowar baffa Modibbo, Isma'il, Habib da Abdul-Hameed sai ya ƙara gudun kyarmar da jikin Zeenah ke yi sai wulga idanu take yi ko Allah zai sa ta yi arba da 'yar. Ganin har sun zauna akan kujera Meema bata shigo ba sai ta saka tafukan hannunta ta rufe idanu tare da fashewa da kuka mai sauti.
Da sauri Abdul-Hameed ya koma kujeran da ke kusa da ita ya soma lallashinta da maganganu masu sanyaya zuciya. Sai hakan ya ƙara ɗaga mata hankali saboda tabbacin da ta samu akan ba a ga Meemanta ba.
Baffa Modibbo ne ya yi gyaran murya ya soma janyowa Zeenah ayoyi da hadisai da ke magana akan yarda da ƙaddara. Sai da ya yaga zuciyarta ta yi taushi sannan ya faɗa masu abunda ya faru a Lagos ɗin. Kaɗan ya rage zuciyar Zeenah bai buga ba, don gwara ace taga gawan Meeman za ta fi samun kwanciyar hankali ko da kuwa za tai kuka ta san dai Allah ne ya ɗauki abunsa. Yanzu kuma da ganin ta ne ba ayi ba kuma ba a san inda ta ke ba, wani hali take ciki ba hakan kawai ya isa ya kashe ta da ranta don ta san ita da farinciki da kwanciyar hankali sun yi bankwana.
Wannan ranar dai Zeenah ko ruwa ya kasa wucewa a maƙogwaranta, cikin dare ta yanke jiki ta suma. Nenne, Baffa Belɗo da Ramadan suka kwashe ta su kai asibiti da ita. Gwajin farko ya nuna masu jininta ya mugun hawa, kuma idan bata kwantar da hankalinta ba irin abunda ya samu Babiyo zai iya samunta (wato stroke). Nenne ta gargaɗi Ramadan kar ya kuskura ya kira Hameed ya faɗa masa a cikin daren nan, ya bari sai gobe.
Washa gari da safe hankali tashe ya zo asibitin yana ta faɗa akan don me aka ƙi sanar da shi tun jiyan. Da ya shiga ɗakin da Zennah ke ciki kawai sai ya fashe mata da kuka bayan ya ɗaura kansa a kan gadon da take kwance hannunsa riƙe da nata. Da ɗayan hannunta ta kai kansa ta shiga shafawa hawaye na zubo mata. Ɗagowa ya yi ya kalleta tare da faɗin, "Yanzu ke ma so kike na rasa ki tamkar yadda muka rasa Meema? Kin fi kowa sanin ba zan iya rayuwa idan ba ke ba. Don be strong Zeenah. Za mu yi aure kuma na miki alƙawari a daren farko zan baki wata Meeman da izinin Allah. Allah ya fi ki ƙaunarta, idan har kika dangana ki ka fauwala masa komai shi kuma zai jiɓanci lamuranki. Shin kin manta da nasihar baffa Modibbo ne a gare ki? Meema need only your prayers not your tears. Don girman Allah ki min alƙawarin ba za ki ƙara kukan rashinta ba daga yau."
Lumshe idanu ta yi tana jinjina kai sannan ta furta, "I will try my best to be strong. In sha Allah zan ƙoƙarta. Daga yau zan miƙa lamurana ga Allah. Zan yi ta yin istigfari ina raya darena da bacci, kai ma matsayin mahaifi ina son kai haka. Mu taru mu yi ya mata addu'a."
Abdul-Hameed bai san lokacin da ya miƙe ya ɗagota tare da rungumota yana kuka sosai ba. Babu abunda ya ke faɗi sai, "Ubangiji Allah ya sauƙaƙa miki Zeenah, Allah ya yafe miki kurakuranki da mu baki ɗaya."
Kwananta biyu a asibiti aka sallame ta ta koma gida ƙarƙarshin kulawar Nenne. Kamar yadda ta faɗa, bata kuma sakin jiki ta raya daranta da bacci ba. Ƙarfe uku na bugawa take tashi, kuma bata ƙara komawa har sai rana ta fito tukun.
_Mrs Abdul-Hameed (Asma'u Queen Elizabeth of England 😂)_
Wani irin taƙama da jijjida kai take yi wa ƙawaye da mutanan da take alaƙa dasu kasancewarta sutukar mai kuɗi kuma matar Abdul-Hameed minister mai jiran gado. Watan ɗaya a cikin Arɗo Barkinɗo amma bata taɓa jin yakamata ta wanko ƙafa ta zo ta gaida surukanta ba. Ko rasuwar da akai a gidan bata taɓa shiryawa ta ce wa Abdul-Hameed ya kaita tai masu gaisuwa ba. Duk kuma yana kallonta da abun sai dai bai taɓa mata magana ba ko sau ɗaya kawai yana auna irin nata hankalin ne.
Watan guda da sati ɗaya ta soma fita zuwa University of Abuja ta cigaba da lecturing a can kasancewar tuni ta samu transfer ba tare da ɓata lokaci sabida matsayin da babanta ya taka a da da kuma gidan da take aure a yanzu.
Sau ɗaya ta je gidan Nenne shi ma kuma bata jima ba. Kuma ba su hadu da Zeenah don har ta,tafi Zeenaj ko falo bata fito ba. Don idan ta ce bata jin kishinta ta yi ƙarya. Don ta sn dul macen da ta samu miji kamar Hameed ta gama morewa rayuwar aure don he's such a caring husband.
Watan su Babiyu uku cur a India kamun suka diro ƙasar Nigeria. Ya warke sumul dashi. Ya ƙara kyau tare da haiba. Sai dai tsufansa ya ƙara fitowa sosai kuma ya ƙara haske. Shi ya matsa sai sun dawo a yau don jibi ne za a rantsar da Abdul-Hameed matsayin ministern Abuja.
Gaba ɗaya 'ya'yansa da manya-manyan jikokinsa maza suka kwashi mota tare da securities domin zuwa ɗauko kakan nasu (can na gano maman Musa ana ta ƙoƙarin shiga boat ɗin baffa Giɗaɗo don zuwa airport ɗauko Arɗo Barkinɗo 🤣😜)
Motocin da suka jeru a kan titi suna tafiya za ka ɗauka shugaban ƙasa za aje ɗaukowa a airport ɗinnan. Kowa ka ga fuskansa yana cikin matsanaicin farinciki dawowar Babiyo.
Sanye ya ke cikin riga da wando ta shadda kalar ruwan toka, sai zulla zanna bukar kalar baƙi da ke kansa. Haka takalminsa ma baƙi ne half cover. A hankali ya ke saukowa daga jirgin ga uban securies da ke gefen hagu da daman jirgin suna jiran saukowarsa, gabansa kaɗan mota ce ƙirar BMW fara fat, Abdul-Hameed jingine da motar yana wani murmushin farinciki tare da kallon kakan nasa da ke saukowa daga jirgi.
Saura taku ɗaya ya gama saukowa Abdul-Hameed ya ƙarisa da sauri cike da wani irin shauƙi ya rungume kakan nasa tare da ɗaga shi cak ya ƙariso da shi wajen mota. Lokacin da ya ɗaga shi camera ce ta shiga haska su da hotuna. Iyayan nasa kuwa da sauri suka ƙarisa wajen da suke suna masa daƙuwa. Baffa Ɓaleri har da kai masa ranƙwashi a kai ya yi saurin dafe wajen yana dariya.
Dukkansu kowa ya shiga mota suka bar airport suka ɗau hanyar _Arɗo Barkinɗo_
Gidan cike ya ke danƙam da mutane har da jama'ar Yola Adamawa, wasu ma a bakin farkon gate suka tsaya suna jiran isowarsu.
Sauke glass Babiyo ya yi ƙasa ganin mutana da suka zo tarbansu yana ɗaga masu hannu fuskansa cike da annashuwa. Mutane tafiya suke suna bin motar har cikin Arɗo Barkinɗo. Ganin haka sai motocin suka koma tafiya a slow daidai da tafiyar mutane.
Sun kwashi tsayin mintuna kamun suka ƙariso gate ɗin gidan Arɗo Barkinɗo (Babiyo) wanda anan ɗinne aka dakatar da mutane. Familyns kawai aka bari suka shiga. (Ban da maman Musa don ita sai da ta faki ido ta shige da gudu saboda son sanin abunda zai faru a ciki 😜).
Duk girman falon Babiyo sai da ya yi wa jama'ar gidan kaɗan. Don wasu a tsattsaye suka tsaya, wasu jikokin kuma a kan jikin iyayansu. Wasu a ƙasa, wasu har ta ƙofar ɗaki duk sabida murnar dawowar Babiyon cikin ƙoshin lafiya ba kamar yadda ya tafi ba. Daƙyar aka samu 'yan uwa suka tafi gidajansu sabida Babiyon ya samu ya yi wanka ya kwanta ya huta sabida gajiyar zaman jirgi.
Ana gobe su Babiyo za su dawo baffa Belɗo, baffa Modibbo tare da Baffa Giɗaɗo suka tafi Bauchi suka tattaro iyalan Baffa Ɓaleri da basu san abunda ke faruwa a cikin Arɗo Barkinɗo ba. Don Baffa Ɓaleri bai faɗa masu komai. Cewa matar tasa kawai ya yi zai yi tafi kuma zai ɗan ɗau lokaci kamun ya dawo. Ya dai bar masu duk abunda ya san za su nema.
Ba ƙaramin kuka Mama Hafsat ta yi ba lokacin da ta yi arba da ƴan uwan nata. Sai dai sun yi sun yi ta biyo taƙi acewarta baza ta karyar dokar mijinta ba. Bata amince ba har sai da baffa Belɗo ya kira baffa Ɓaleri a waya tukun sannan ta amince.
Baffa Ɓaleri kai tsaye gidansa ya nufa da ke Ɓaleri street yana hawaye saboda tuna rayuwar da ya yi a cikin gidan kamun mahaifinsa ya yi masa korar kare. Gaba ɗaya kai ya shiga dawo masa cikin kai tiryan-tiryan. Sai labarin da Babiyon ya bashi a India ya dawo masa raɗan a cikin kansa. Bai san lokacin da ya kashe motar ba ya kifa kansa jikin steri ya shiga rera kuka.
Sai da ya yi mai isarsa sannan ya ɗago tare da share hawaye kamun ya furta, "Ƙarshenki ba zai taɓa kyau ba Mamiyo! In sha Allah sai lin yi mutuwar ƙwanƙwalati. Kin cuce ni matuƙa. Kin raba ni da mahaifina na tsayin shekaru, hakan bai maki ba sai da kika rusa min tarbiyyar 'yata. Allah ya isa ban yafe miki ba!" ya faɗi da ƙarfi yana kai wa steri duka tamkar Mamiyon ce a gabaansa.
A ƙasar India Babiyo ya shaida masa duk abunda Zeenah ta aikata ba yinta bane aikin Mamiyo saboda tsafi ta mata don ta lalace. Ya kuma nuna masa evidence a waya lokacin da Mamiyo ta ke magana da malam mai Huluna a waya duk da akwai inda Babiyo ya saka aka masa editing domin nuna cewar tun farkon iskancin da Zeenah ta fara da saka hannun Mamiyo don Ɓaleri ya sauko daga dokin zuciya ya ƙaunaci 'yarsa. Don ya fahimci ɗan nasa shine ya yo gadon ainahin zuciyar kakansa na mugun zafin rai da rashin yafiya. Don ya tabbata ko da ya nuna wa baffa Ɓalerin vidoen lokacin da Mamiyo take cewa a warware farra'un da ta yi wa Zeenah da Abdul-Hameed da kuma sanadin da ya sa ya kusanceta har suka haihu ita kuma ta cigaba da karuwanci saboda asirin da Mamiyo ta matan, Ɓaleri ba zai taɓa yafewa Zeenah ba don zai ce tun farko halinta ne saboda kuskuren nan da ta aikata na bin saurayi har ya yaudareta ya mata ciki wanda shine ya saka ya kore ta daga gidansa.
Tada motar ya yi yana mai jin tsantsan tausayin ƴar tasa saboda tuno abunda ya mata da irin korar karen da ya mata. Duk ita aka fi cuta a cikin zuri'ar domin ita ce aka yi wa asirin da ta riƙa aikata fasiƙanci da maza kala-kala tare da zama a gidan karuwai tana sayar da ƙwayoyi da tabar wiwi.
Parking ya yi sannan ya shiga cikin gidan, a tsaye ya samu matarsa da 'ya'yan shida suna jiran shigowarsa jikinsu duk a sanyaye. Da idanu ya kalli Maryama babbar 'yarsa da duk ta rame, sai ya mayar da kallonsa izuwa wajen Sa'adatu da jikinta ke rawa, sai kawai ya fashe da kuka.......
#Babiyo #Baffa Ɓaleri #Zeenah #Abdul-Hameed #Queen Elizabeth 🤣 #Nenne #Jawaad #Khairat #Meema #My Destiny #Matar Sayyadee *** [9/3, 5:58 AM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)
*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee
☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`