My Destiny (Ƙaddarata)

Page 70

by @matarsayyadee3

Aje ai following channel ɗina please 🙏🏼 ***

*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***

Domin shiga comment section kuma ki danna wannan link ɗin👇🏼 *** *_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining link ɗin da ke sama domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜

_*💃🏻💃🏻 _Kuna ina 'yan uwana matar aure da 'yan mata? Shela nake ko wacce ta fito domin kuwa yau na zo maku da albishiri! Kun san matar Sayyadee ta ku ce ba ta samun abun ƙaruwa ta yi shuru domin ta ƙaru ita kaɗai._💃🏻💃🏻

💐💐🌼🌼_Magana ake ta ƙamshi. Toohwa! Mai ya hwaru?_ 🤔 🌷🌷🌸💮

*To maza ku marmatso ga sirrin nan. Shahararriyar nan wacce ke inganta soyayya tsakanin ma'aura wato Fatima Zaransalaty inkiya Queen Zarah ce ta taho mana da wani ƙamshim domin cika hancinar mazajemu da ƙamshi*. _INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_ _TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA KUJI 💃🏻

_Zaran Salaaty ta yi tafiya miƙaƙƙa har Sudan domin farnata ranmu da na mazajenmu ta kawo mana Sudanese perfume👌🏻 wanda idan har kika shafa shi a jikinki ko kin yi wanka ƙamshin bai barin jikinki. Tested and Trusted ƴaruwa. Zaransalaty ba iya sudanese perfume ta kawo maku ba, akwai kayayyaki masu matuƙar inganci na gyaran HQ (kun san dai ba a wasa da headquarter) akwai kayan gyararrakin jiki kala-kala na ƴan mata da matan aure. Sannan Zaransalaty tana sai da Decoration na kayan ɗaki iri-iri wanda baki taɓa ganinsu._

_KAR IN CIKA KI DA SURUTU, KE DAI NEMI ZARANSALATY A NUMBERS ƊINTA KAMAR HAKAA_: *** Or ****

*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_nfection_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_

_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ ***** *****

Ƙamewa su Maryama su kai ganin mahaifinsu mai ƙarfin zuciya da ko hawayensa ba su taɓa gani ba wai yau shine da kuka a gabansu mai sauti. Babu wani shaƙuwa tsakaninsu sosai, bai hira da su, bai sake masu fuska, bai ba su fuskan da za su nuna masa irin wannan ƙaunar da ke tsakanin uba da 'ya'yansa shi yasa yanzu suke kallonsa kawai suna kuka amma sun kasa ƙarisa inda ya ke duk da yadda suke jin tamkar su nufe sa su rungumesa.

Tamkar ya san menene a zuciyarsu sai ya nufe su da kansa ya tattaro su ya rungumo yana ƙara sautin kukansa.

Mama Hafsat wani irin rintse idanu ta yi tana mai sulalewa ta zauna a ƙasa tana wani irin kukan farincikin abunda ta daɗe tana jiran gani yau Allah ya nuna mata, wato mijinta ya ƙaunaci 'ya'yanta. Take kuma wani miki ya motsa a zuciyarta na tashin 'yarta Zeenatu. Ta yi fatan ina ma tana cikin nan ɗakin a yanzu haka.

Ɗagowa ya yi ya kalle ta tare da faɗin, "I'm very sorry Hafsat! I'm morethan sorry. Ban san da wani irin baki zan roƙi gafarki ba, abunda kawai zan iya furtawa a gare ki shine you're the best wife I've ever seen in my life. Kin yi min biyayya tamkar za ki min sujada, ba ki taɓa saɓa min ba duk da ba wani cikakken farinciki kike samu daga gareni ba. Na ƙuntata miki ke da 'ya'yanki. Don ku yafe min matata ke da 'ya'yanki!" ya ƙarisa maganar tare da zubewa kan gwiwowinsa ya haɗe hannunsa biyu hawaye na masa kwaranya.

Mama Hafsat she was like am I dreaming! Sai ta lumshe idanunta ta kuma buɗewa, still image ɗin da ta gani ta sake gani. Bata san lokacin da rarrafa kusa uban 'ya'yan nata ba ta rungumesa tana kuka sosai.

Shi ma rumgumetan ya yi yana cigaba da faɗin, "I'm sorry Hafsat, I'm very sorry." sai kuma ya miƙawa sauran 'ya'yan nasa hannu, kamar jira suke suka ƙariso suka rungumesa.

"I wish Zeenatu is here with us!" Mama Hafsat ta faɗi duk da zuciyarta na bugawa bata san yadda mijin nata zai yi ba da jin sunan da ta ambata don tuni ya haramta kiran sunanta a gidansa.

Ɗagota ya yi daga jikinsa tare da faɗin, "You wish will come true, Hafsatuna."

Dam gaban Mama Hafsat ya buga, nan da nan jikinta ya hau rawa tana kallon mijin nata. Ba ita kaɗai ba hatta su Maryama mamaki ne ya ke neman sumar da su. Murmushi ya yi da yaga yadda gaba ɗaya sai wulga idanu suke yi. Wayarsa ya zaro cikin aljihu tare da danna number ɗin Ramadan. Ringing biyu Ramadan ɗin ya ɗauka tare da saurin gaida baffan nasa, bayan baffa ya amsa sai ya shaida masa ya kawo masa Zeenatu a gidansa yanzu.

Ramadan kallon wayar ya yi kamun ya kalli Nenne da ke riƙe da remote ɗin da ta ke ƙoƙarin jifan Abdul-Hameed da shi don tun ɗazu ta ke korarsa daga gidan amma ya ƙi fita. Sai iya shege ya ke mata a falo. Bai kunyar idanunta yake rattabowa Zeenah kalaman soyayya da yadda yake jinta a ransa.

"Ni dai ba haka nake da wannan rashin kunyar ba wallahi!" Baffa Belɗo ne ya faɗi hakan lokacin da Abdul-Hameed ya kalli Zeenah ya furta mata cewar ya ƙosa su yi aure ya killace ta a ɗakinsa ya yi ta kallonta.

"Balle kuma ni mace!" Nenne ta faɗi tana harararsu daga Abdul-Hameed ɗin har uban nasa.

"Ni baffa Giɗaɗo da Baffa Modibbo na yo da alama. Don su babu ruwansu da sakaa min idanu. Au! Na manta da sarkin gidan nan, tabbas shi na yo. Don duk zan zauna mu yi hira dashi sai ya kawo zancen matarsa Maimunatu. Wai ko kun ji yadda ya ke kwararo mata zantukan soyayya masu daɗi wanda ban taɓa jin su ba, hmm ita da bata a raye ma kenan."

Wannan maganar da Abdul-Hameed ya yi ne ya saka Baffa Belɗo kai masa mari a ƙeya, Nenne kuma ta ɗaga remote za ta jifa masa sai ga kira a wayar Ramadan.

"Baffa Ɓaleri ke kirana!" wannan maganar da Ramadan ya yi ne ya hana Nenne jifan Abdul-Hameed ɗin tana kallon Ramadan da ya ɗaga wayar.

Bayan yanke wayar sai Ramadan ya kalli iyayan nasa tare da faɗin, "Wai na kai masa Zeenah gida, kuma na ji muryansa tamkar kuka ma yake yi.

Zumbur Baffa Belɗo ya miƙe jin ance ɗan uwansa na kuka. Nenne kuma riƙo hannun Zeenah ta yi tare da faɗin, "Wato a kaita can gidan ya ƙarisa min ita ko? To babu inda za ta!"

Ɗaga mata hannu ya yi kamun ya juya ya kalli Zeenah da har ta soma hawaye jin ance babanta na kuka. "Je ɗauko mayafinki ki same ni a wajen mota."

"Baffa ni ma zan je don Allah!" Abdul-Hameed ya faɗi a marairaice.

"Babu inda za ka je Abdul-Hameed. She's going to reunite with her family. Babu wani abunda zai faru sai alkhairi."

Gyaɗa kai Abdul-Hameed ya yi don basu san wani abu wai shi musu da iyayansu ba.

"Zan iya bin ku ni?" Nenne ta faɗi nan ma kuma ya girgiza mata kai alamar a'a. Sai ta koma ta zauna a kan kujera tana addu'ar Allah ya sa kar Ɓaleri ya cutar da Zeenah sabida irin zafin zuciyarsa.

Jiki a sanyaye Zeenah ta sauko sanye da hijjab har wajen idon sawunta da Nenne ta ɗinka mata su kala goma. Da ido Abdul-Hameed ya bita don nevy blue hijjab ɗin ba ƙaramin kyau ya yi mata. Sai ya kuma fito da baby face ɗinta. Gaba ɗaya a yanzu shekarunta ashirin da tara. Har wajen mota ya rakota yana faɗa mata ta yi ta maimaita Inna lillahi wa inna ilaihir raju'um har su isa gidan. Shi da kansa ya buɗe mata gidan gaba, bayan ta shiga ta zauna kuma ya rufo ƙofar. Bai koma ciki ba har sai motar ta su ta bar gidan. Ji ya ke tamkar ya zama tsuntsu ya bisu. Sam bai son abunda zai taɓa ta ko kuma ya ɓata ranta.

Mintuna kaɗan ta kawo su Ɓeleri street don babu nisa tsakanin gidajansu.

Ɓaleri na jin shigowar mota gidan ya yi sauri miƙewa ya fita, sai su Maryama su ka rufa masa baya.

Buɗe murfin motar ta yi da saurin ganin gizon da idanunta suke mata. Da gudu ta nufe su, su mai sai suka saka gudu. A tsakiyar gidan suka haɗe, sai kawai ta zube a kan gwiwowinta tare da soma taɓa su ɗaya bayan ɗaya tana kiran sunansu, "Adda Maryam, Adda Sa'a, Sajida, Salma, Maimoon, Zubair, Aliyu! Dagaske ku na ke gani?"

"Mu ne Adda Zinatu!" Su Sajida suka faɗi suna kuka.

Jawo su ta yi ta rungume tana kuka sosai. Duk suna ƙanana ta bar su. Gwara ma Sajida ta kai shekaru goma lokacin da ta bar gida. Aliyu ko bai wuce 3years ba, Zubair five and half, Salma 8, Maimoon kuma 6. Amma yanzu Sajida za tai 23, Salma 21, Maimoon 18, Zubair 16/17 don babu nisa tsakaninsu, Aliyu kuma 14. Duk sun girma, matan ma sun isa aure.

"Ina mama, mama tana ina?" Zeenah ta faɗi gabanta na faɗuwa.

Da hannu Adda Maryam ta nuna mata ɗaki da hannu. Da gudu Zeenah ta kwasa ta yi ɗakin da mama Hafsat ke ciki. Tsaye ta same ta jikinta na rawa tana kuka. Wani irin kuka Zeenah ta ɓarke da shi tare da furta, "Maamaaaa!" sai ta faɗa jikinta ta rungume daidai lokacin da Baffa Ɓaleri ya shigo ɗakin shi da ɗan uwansa da su Adda Maryam.

Kuka sosai suke yi ita da mama Halima. Su Adda Maryam ma suna ganinsu suma suka saki na su kukan suka ƙarisa suka rungume su. Baffa Ɓalerin ma hawaye kawai ya ke yi, hata baffa Belɗo don ba ƙaramin tausayi suka ba shi ba.

Duƙawa ƙasa Zeenah ta yi bayan sakin mahaifiyarta ta kama ƙafafunta tare da faɗin, "Ki yafe min baƙin cikin da na ƙunsa miki na tsayin wannan shekarun don girman Allah. Mama ashe haka kika ji lokacin da na bar gida na shiga duniya? Ashe haka haka uwa ke jin ƙuna a zuciyarta idan 'yarta ba ta a kusa da ita kuma bata san halin da take ciki ba. Na cutar da zuciyarku iyayena, ku yafe min ko zan samu salama a cikin zuciyata!" tana maganar tana wani irin tamkar numfashinta zai bar jikinta.

Hannu Mama Hafsat ta kai ta dafa ɗiyarta da lalube don kukan da take yi ya saka idanunta sun rufe kuma dama ta ɗauki shekaru tana jinyar ɓarin jikinta da ya nemi shanyewa sabida damuwa da hawan jini, ga kuma ciwon zuciya da ke addabarta. Har yanzu idan ta yi tari jini ke zuba mata ko kuma idan amai ya yunƙuro mata.

"Na yafe miki Zeenah tun kamun ma ki duƙa ki nemi yafiya ta. Tun lokacin da kika saka ƙafa kika bar gina na riga ya yafe miki. Sai dai kin tafi kin bar ni da kewarki, kin bar ni da tunanin a wani hali kike ciki, mai kike aikatawa kuma a wani hannu kika ɓata. Kullum na kai goshina ƙasa sai na roƙi Allah ya sassauto da zuciyar mahaifinki ke kuma ya kuyo da hankalinki zuwa gida. Tun bayan tafiyarki ba bu wanda ya kuma samun farinciki a gidan. Maryama da Sa'adatu duk sun rasa igiyoyin aurensu sabida ke. Sa'adatu da tsohon ciki aka koro ta gida bayan duka a hannun miji da kuma tsangwamat uwar miji. Ita kuma Maryamu kishiyoyi da gorin miji da na danginsa ya kore ta daga gidan miji. Har yanzu an ƙi bata ɗanta tilo da ta haifa a can. Sa'adatu cikin da ta zo dashi sabida damuwa da rashin abinci da take fama dashi ya sa ɗan bai fito da rai ba. Ga ƙannanki nan su Sajida duk sun isa aure amma ba mai zuwa neman su da aure. Mahaifinki kullum cikin damuwa ya ke amma ƙimarsa da yake taƙama da,shi da kuma zafin zuciya game da kafiya,sun hana shi saduda ya amshi Ƙaddararsa da hannu biyu. Kin yi mummunar kuskure Zeenatu, amma mahaifinki ya fiki kuskure domin hannunka bai ruɓewa ka yanke ka rai. Sannan kuma ɓarna bata taɓa gyara ɓarna. Yanzu gashi sai nadama yake wacce ya riga ya yi ta a ƙurarren lokaci domin komai ya riga da ya lalace!" gaba ɗaya cikin kuka ta yi maganar.

Juyawa Zeenah ta yi ta kalli mahaifinta da ya sunkuyar da kai yana kuka. Sai ta rarrafa ta kama ƙafafunsa tare da fashewa da kuka ta shiga faɗin, "Ni na sani ka yi iyakaci bakin ƙoƙarinka wajen bamu tarbiya ni da su Adda Maryam. Kana ƙoƙari wajen sauke duk wasu nauye-nauyenmu da ke kanka, amma sai Allah ya jarabceka da fanɗararriyar 'ya wacce bata gudun ɓacin ranka. Na ɓata maka suna a duniya. Na shafawa, zuri'arka baƙin fentin da har abadan ba zai gogu ba sai dai idan har abunda ya wuce zai dawo in gyara kuskuren da na yi wadda hakan ba zai taɓa yuwuwa ba. Yau na gasgata maganar da kake yawan faɗa mana cewar mutunci madara ne idan ya zuba ba zai taɓa kwasuwa ba. Abbanmu ka yafe min abubuwan da na aikata maka. Ba kai ba, ni kaina ina dana sanin haihuwataa da kuka yi, domin da ba a haifeni ba da ban zame maku wannan bala'in ba. I'm shameful to this noble family!" wannan karar tsabar kuka har kyarma jikinta ke yi.

Ɗagowa Baffa Ɓaleri ya yi tare da zaunar da ita a kan kujera sannan ya ɗuka a gabanta ya furta, "Zeenatu ba laifinki bane ke ɗaya. Kamar yadda mahaifiyarki ta faɗi ina da kaso mafi rinjaye wajen lalacewarki. Domin da ban kore ki na tozartaki ba a titi da hakan bata kasance ba, kamata ya yi na zaunar da ke na miki faɗa tare da nuna miki haramcin abunda kika aikata ta hanyar nasiha sa ayoyin da hadisan ubangiji. Amma sai zuciya ta kwashe ni na aikata aikin dana sani. Abun ya min ciwo ainun. Gani nake kamar ni bai kamata ace a cikin 'ya'yana a samu fasiƙa ba mai kaucewa hanyar Allah, na mance ko a cikin Annabawan ubangiji masu darajaa akwai waɗanɗa aka jarabce su da 'ya'yansu. Na mance ni ɗin ba kowan kowa bane. Na ɗauki girman kai da zafin rai na ɗaurawa kaina. Ke ma kanki Zeenatu idan baki yafe min ba Allah sai ya mana hisabi domin ba ta hakan ya ce in tarbiyantar da amanar da ya bani ba. Gaba ɗayanku baku san mai ake kira da daɗin mahaifi ba, na kasance tamkar wani boss a cikin gidana babu wani nishaɗi bare shaƙuwa a, tsakaninmu balle har na ja ku a jiki mu yi jira na fahimci damuwarku. Don Allah 'ya'yana ku yafe min." ya ƙarisa maganar tare da haɗe hannayansa biyu yana neman gafara.

Gaba ɗaya sai suka taso suka rungume shi suna kuka. Da sauri baffa Belɗo ya juya ya bar gidan gaba ɗaya yana hawaye domin bawa mahaifi da 'ya'yansa waje su nuna wa juna ƙaunar da ba a yi ba shekaru da dama.

Daren ranar babu wanda ya rintsa tsakanunsu. Bajewa su kai a falo suna hirar da basu taɓa yi ba. Sun yi kuma har sai da hawayensu ya ƙafe lokacin da Zeenah ke basu labarin irin rayuwar da ta yi a gidan magajiya da kuma Lagos. Mama Hafsat sai da ta faki ido ta shiga bayi ta riƙa kwarara aman jini saboda tashin hankalin da ta shiga jin irin rayuwar wulaƙancin da 'yar tata ta yi a garin Lagos. Ta ci kuka a bayin nan har numfashinta na barazanar ɗaukewa.

Baffa Ɓeleri shima zare jikinsa ya yi ya nufi ɗakin da matarsa ta shiga ya tura bayin. Zaune ya ganta daɓas a ƙasa tana kuka ga jinin da ya gani a bakinta da kuma ƙasa. Sai hankalinsa ya yi mugun tashi ya nufe ta ya ɗagota tare da soma jero mata tambayoyi akan yaushe ta fara aman jini.

Hannunsa ta riƙe ta sakar masa murmushi tare da faɗin, "Ko yanzu na faɗi na mutu Allah ya cika min burina. Abu ɗaya kawai ya rage min wanda bai wuce ganin duka 'ya'yana mata a ɗakin mazajensu ba cikin aminci."

"Muje asibiti Hafsat, babu abunda zai same ki. Ba za ki mutu yanzu ba. Idan kin mutu ni kuma na yi yaya da tawa rayuwar?"

"Ka saurare ni don girman Allah. Ban so 'ya'yana su san halin da nake ciki, ban so su ƙara shiga damuwa a cikin wanda suke kai yanzu. Don Allah ka riƙe min wannan sirrin!"

Kallonta ya riƙa yi babu blinking kamun ya haɗata da jikinsa ya shiga zubar da hawayen tashin hankali kamun ya furta, "Duk da hakan zan kai ki asibiti a duba min ke. Zan kai ki a ɓoye kuma na cikin estate ɗinnan ba."

Jinjina kai Mama Hafsat ta yi alamar gamsuwa. Sai ya ƙara ƙanƙameta cikin jikinsa.

Abdul-Hameed dai ranar hankalinsa ba a kwance ya ke ba tun da Zeenah suka fice tare da mahaifinsa. Gashi lokacin da ya dawo bai ce masa komai ba sai ma korasa gida ya yi bayan ya kankara masa warning akan kar ya kuskura ya je gidan baffa Ɓelerin. A ranar dai ko queen Elizabeth ta kasa gane kansa, ta yi turanci har ta gaji ta haƙura ta koma nata ɗakin ta kwanta. Shi kuwa yadda ya ga rana haka ya ga dare. Da sassafe ko takwas ba tai ba ya shiga mota ya tafi gidan baffa Ɓeleri don a can ma ya karya don ko da ya fito Hajiya Asma'u uwar 'yan boko bata farka daga barci ba don ƙa'idarta ita ba a tashinta daga bacci har sai idan ita ta tashi da kanta.

Sosai farinciki ya dabaibaye shi ganin Zeenah ɗinsa cikin farinciki. Don ko da ya isa duk da ba su yi bacci ba jiyan dukkansu a falo ya gansu bisa dinning suna karyawa. Sai da ya duƙa ya gaida Baffan da Mama Hafsat sannan ya ja kujeran dinning ɗaya ya zauna. Gaɓa suka haɗa baki suka gaida shi. Amsawa ya yi yana kallon Zeenarsa da gaba ɗaya ta canza ta koma wata silent.

Gyaran murya baffa Ɓaleri ya yi tare da faɗin, "Ina ka baro matar da kake ƙoƙarin karyawa a nan? Ni fa ban son rashin adalci!"

Ɗan susa ƙeya ya yi tare da faɗin, "Tana gida bata tashi ba, ba a tashinta idan tana bacci ni kuma yunwa nake ji kuma ina son ganin Zee-meed don jiya ko runtsawa ba yi ba ina ta tunanin kar ka dakar min ita." hankalinsa kwance ya yi maganaa kuma har wannan lokacin bai bar kallon Zeenah ba.

Su Adda Maryam kuwa baki sake suke kallonsa jin abunda ya furta da ya basu kunya shi kuwa ko a jikinsa don bai ga wani abun damuwa ba cikin maganarsa.

Mama Hafsat kuwa ko ɗagowa bata yi ba sai yi ma ta yi tamkar bata ji abunda Abdul-Hameed ɗin ya ce ba. Baffa Ɓaleri bai kuma ko tari ba ya cigaba da karyawarsa.

"Zee ki yi serving ɗina ma, wallahi jiya saboda tunanin ki ko abincin dare ban ci ba. Ga baffa ya ce kar in kuskura in zo nan ɗin a jiyan. Ni kaɗai na san halin da na shiga wallahi. Har mafarki sai da na yi wai baffa ya dukan min ke!"

Tsam Mama Hafsat ta tashi hannunta ɗauke da plate ɗin abincinta, kuma dama daga kujeranta sai na Zeenah, sai Abdul-Hameed ya yi saurin tashi ya koma inda Mama Hafsat ta tashi tare da furta, "Thank you mamana."

Baffa Ɓaleri ma sai ya ɗauki nasa plate ɗin ya bi bayan matarsa. Ganin haka su Adda Maryam duk sai suma suka tashi suka bar su daga Zeenah ɗin sai Abdul-Hameed ɗin.

Ƙafa Zeenah ta kai ta take ƙafarsa da ƙarfi har sai da ya furta "Auuch!Mai na yi?"

Dan zaro masa idanu ta yi tare da faɗin, "Can't you see what you've done! Wallahi sam babu ɓurɓushin kunya a tattare da kai Lovey-Dovey. Kai ne fa ka kori baffa da mama har da su Adda Maryam."

"Babu ruwana, sun ga damar tashi ne kawai. Ba ki yi kewa ta ba jiya? Ni fa kasa bacci na yi."

Taɓe baki ta yi tare da harararsa sannan ta ce, "Yaushe zan yarda bayan kana cen tare da amaryarka!" ta faɗi sounding a little bit jealous.

Kafa ta ya yi da idanu, can kuma ya saki wani sanyayyiyar murmushi yana mai jin daɗin kishinsa da ya gani a cikin idamunsa.

"Shiyasa na ƙosa in ɗauke ki in killace a gidana kema ina baki farincikin fiye da yadda ake baiwa amaryar tunda kishi kike da ita."

Wannan karan bayyanar kishinta sai ya ninku fiye da na da har ta mike fuuu za ta nar wajen ya yi saurin riƙo hannunta tare da faɗin, "Calm down, haba Zee-meed. Tsokalarki kawai nake don in ga kishina a idanunki kuma na gani na ji daɗi."

Robar butter ta ɗauko ta buga masa a kai tare da faɗin, "Allah kar ka sake."

"Allah ba zan sake ba!" ya faɗi da irin muryanta duk sai suka fashe da dariya.

Yau ma dai Babiyo bai samu ganawa da family din nasa ba sai bayan isha'i saboda baƙin da ya ke ta samu manya-manyan mutane suna masa barka da dawowa da kuma ya jiki.

Bayan isha'i gaba ɗaya aka haɗu a makeken fadar Babiyo kamar yadda aka saba idan za a gudanar da meeting. Sai dai wannan gujeru biyu ne a gefe da gefen kujeran Babiyo, shi yana zaune a na tsakiya, Inna Ƙarama a gefe dama, Inna Jume a na hagunsa. Mamiyo kuwa tana daga gefe zaune tamkar wata zararriya sai wulga idanu take yi. Ta yi baƙi ta rame ga wani bushewa da laɓɓanta suka yi tamkar wacce ta shekara ba ta sha ruwa ba. Daga gefenta kuma malan mai huluna ne hannunsa biyu cikin ankwa sai sharar hawaye ya ke yi. Hafiz informer da su Baffa Tukur suma a gefe guda don Babiyo shi da kansa ya saka aka kawo su nisa jagoranci hukuma sai dai su suna waje suna jira. Baffa Ɓeleri zuciyarsa ce ta motsa, jikinsa sai kyarma yake yi sai da ɗan uwansa baffa Giɗaɗo da ke kusa dashi ya damƙi hannunsa yana shafawa tare da maimaita masa inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un har shima ya yi nasarar cafkewa ya shiga maimaitawa.

"A buɗe taro da addu'a kamar yadda aka saba!" Babiyo ya faɗi a dake. Don yau a ainahin tsohon Babiyonsa ya fito.

Baffa Ciroma ne ya soma jero addu'o'i mai tsayi, don sai da ya kwashi mintuna goma yana yi. Kowa a wajen sai da jikinsa ya yi mugun sanyi. Bayan kammala addu'a Babiyo ya yi gyaran murya tare da soma faɗin,

"Kamar yadda kowa ya sani, wasu abubuwa da dama sun faru a cikin wannan gida wanda da yawanku suke neman ƙarin bayani. Musamman ma kamun Tukur da Mahmud da DSS suka yi a cikin gidannan bayan tafiyata jinya ƙasar India. Kuma na samu labarin irin tarzomar da iyalansa suka tada saboda ba su san abunda suka aikata ba, ko kuma sun sani san zuciya ya saka su ka aikata abunda suka ga dama don bana ƙasar. To ina so duk wanda bai sani ba ya sani ni Adam inkiya Arɗo Barkinɗo ni da kaina na umarci DSS da so zo gidana su kama 'ya'yana saboda ta'addancin da suka aikata sabida son zuciya da kuma keken ɓeran da mahaifiyarsu ta ɗaura su akai. Haƙiƙa Lauratu ta cutar dani kuma ta cutar da zuri'ata ainun. Ni dai ba zan taɓa yafe mata ba, kuma a yau a yanzu za ku ji abunda Lauratu ta aikata ita da 'ya'yanta da bakunansu.

Yana kawowa nan sai ya kalli Hafiz tare da faɗin, "Na riƙe ka tamkar ɗana dana haifa, amma saboda son zuciya ka haɗa kai da matata kuka ci amanata tare da yi min illa mafi muni saboda abun duniyar da lokacin da na tara ko auranta ban yi ba. Shin mai na aikata maka a duniyar nan da kai min haka? Na baka muhalli a cikin gidana. Na baka aiki kuma na yanka maka albashi mai tsoka, na ɗauke duk wata ɗawaimiyarka da na iyalanka, shin abunda za ka saka min dashi kenan?"

Kan Hafiz a ƙasa babu abunda ya ke yi sai zubda hawayen nadama. Bakinsa na rawa ya furta, "Kai min aikin gafara Babiyo. Wallahi tsautsayi, kwaɗayi da rabon shan wahala ne ya jani na aikata komai. Idanuna sun rufe babu abunda suke gani sai abun duniyar da Mamiyo ta haska min zan samu matsayin kasona idan haƙarta ta cimma ruwa. Ka gafarce ni yallaɓai!" ya ƙarisa maganar yana mai fashewa da kuka.

Kau da idanu daka kallonsa Babiyo ya yi ya mayar kan malam mai huluna tare da faɗin, "Kai kuma kafirin bawa, kuna shiga rigar maluntuka kuna shirka tare da taɓar da jama'ar da suka yarda da ku. Mecece ribarka akan abunda kake aikatawa na cutar da bayin Allah? Shin baka tsoran ranar mutuwarka ce, ko kuma ka ɗauka baza ka mutu bane? Kai ne ka yi min sihiri na tsani 'ya'yan Maimunatu har na kore su a cikin gidana ina mai jin zafinsu, sannan kai wa jikana da jikata sihiri suka aikata zina har suka haihu. Hakan bai isheka ba sai da ka kuma mata sihirin da ta shiga duniya ta cigaba da aikata saɓon Allah. Bayan haka ka kashe min mutane biyu da nake matuƙar so a rayuwata, ka kashe min ƙanina da na raine sa da hannu ta hanyar aika aljanu suka katse masa birkin mota ya yi hatsari, ka kuma bata gubar da Lauratu ta yi amfani da shi ta shaƙawa matata har sai da ta bar gidan duniya. Mai suka tsare maka!" Babiyo ya faɗi da ƙarfi yana hawayen baƙin cikin tuno da mutuwar matarsa da ɗan uwansa.

Mama Hafsat da Marwanatu curewa su kai waje guda suna kuka sosai jin Mamiyo ce sanadin mutuwar mahaifinsu.

"Yallaɓai ni ban sanka ba, ban kuma san komai a kanka ba kuma haka kazalika babu abunda kai min. Matarka ita ce ta zo wajena domin biyan buƙatarta. Tun tana budurwa muke hulɗa da ita. Sai dai ba mu shaƙu da ita sosai ba sai lokacin da ta kasance cikin gidan. Ta zo da ƙoƙan bararta a kan na taimaka na buɗe mahaifarta ta yadda duk lolacin da tai tarayya da mijinta ya kasance ƙwan namiji zai saka mata saboda tana so ta zama ita ce da gida ganin uwargidanta 'ya'ya maza take haifa........."

Wani wawan tsawa Mamiyo ta daka masa da ƙarfi wajen kiran sunanta, "Malam! Ka iya bakinka."

"Cigaba da magana" Babiyo ya faɗi yana gyara zama. Mamiyo kuwa wasu zufa ce ke kwaranyo mata na tashin hankali da tsoron abunda ta jima tana burnewa zai bayyana a yau. Har wani zawo-zawo ta ji yana neman zubo mata.

Malam mai huluna ya cigaba da magana, "Ni kuma da jin haka sai zuciyata ta kwaɗaita min ita, sai na yi amfani da burinta na isar mata da buƙatata amma sai na nuna mata aljanu ne ke buƙatar hakan ba ni ba. Da farko ƙi ta yi ta zage ni kaf, amma asirin da na mata na cusa mata sha'awata ita ta dawo da ita gare ni muka aikata saɓon Allah. Ikon Allah kuma sai ta samu ciki. Ni da kaina na yi duba na gano cikin nawa ne. Amma bai faɗa mata ba har sai da ta haihu ta haifi Tukur."

Gaba ɗaya ɗakin aka ɗauki sallalami, Mamiyo kuwa ta fashe da kuka yayin da Baffa Tukur ya nufi kan malam mai huluna yana faɗin, "Ƙarya kake wallahi! Kai ba mahaifina bane."

"Ka koma ka tambayi mahaifiyarka gata can idan ƙarya nake yi." Malam mai hulana ya faɗi yana yiwa Tukur ɗin kallon ƙauna.

Jikin Baffa Tukur ya hau rawa yana kallon mahaifiyar tasa da kunya ya saka ta sunkuyar da kai ƙasa tana kuka.

Babiyo kuwa wani irin tsit ya yi idanunsa sun kaɗa sun yi jazur, sai kallon sashin da Mamiyo take ya ke yi without blinking.

Malam mai hulana ya cigaba, "Haihuwar Tukur ta saka Mamiyo farinciki matuƙa ganin itama ta fara ajiye magajin dukiyar Babiyo. Sai dai tun daga wannan lokacin ta shiga yi min tamkar boss. Umarni ne kawai tsakanina da ita. Hakan ne ya saka na fito ɓaro-ɓaro na faɗa mata abunda ta haifa ba kai ne ubansa ba ni ne. Sai taƙi amincewa ta zazzageni amma ni kuma sai na yi ta mata barazana tare da faɗin zan tona asiri. Hakane ya saka mu kai DNA test domin tabbatar da ɗan nawa ne ko naka. Da result ya fito sai ya tabbata ɗa nawa ne. Mamiyo ta shiga mugum tashin hankali domin kullum cikin kuka take. Hakanan ba don ta so ba muka ƙulle kamar da amma kuma ban kuma mu'amala da ita ba har ta samu cikin Lawal wanda shi kaɗai ne jininka a cikin 'ya'yanta. Daga nan kuma Mamiyo ta amince min na cigaba da mu'amala da ita don ko haihuwar Lawal da ta yi ta amince a kan ni ne na yi sanadin hakan wanda har ga Allah ba ni da wannan ikon Allah ne kawai ya bata. Mahmud da Jibrila duk 'ya'yana ne. Ko mutuwarsa ni da ita ne sanadi domin asirin da na mata ƙaiƙayine koma kan masheƙiya. Duk a tunani asirin zai faɗa kan ɗanka Lawal ne ba Jibrilana ba." yama kawowa nan ya kuma fashewa da kuka har da fyacen majina.

Wani irin tsit ɗakin ya ɗauka, banda koke-koken 'ya'yansu Baffa Jibrila, Mamiyo, Hafiz da malam mai hulana babu abunda kake ji a ɗakin.

An ɗauki tsayin kaduna lokaci kamun Babiyo ya saki wani murmushin da ya baiwa kowa mamaki a wajen tare da faɗin, "Tabbas jini ya fi ruwa kauri! Ni nasan ɗan da na yi sanadin zuwansa duniya ba za taɓa yarda a haɗa baki da shi domin kashe ni. Tukur, Mahmuda ashe ku ɗin ba jinina bane shiyasa kuka amince da shawarar mahaifiyarku domin ku kashe ni. Haƙiƙa kin cutar dani Lauratu. Allah kaɗai ne zai iya min sakayyyar abunda kika min. Na tsinke igiyoyi ukun da ke tsakanina da ke. Ba zan miki komai ba hukuma za ta hukunta ki akan kashe min mata da kika yi, sauran hisabin kuma ni da 'ya'ya da jikokina munce mu haɗu a ƙiyama don wata shari'ar SAI A LAHIRA! Takardun kamfanin da kike shirin buɗewa kuma gasu nan jinina ya amso min su. Sannan yanzu a gaban idanunki za ki shaida ɗaurin auren jikina Abdul-Hameed da jikata Zeenatu." yana gama faɗin haka ya fiddo dubu ɗari ƴan dubu ɗaiɗai sabbi fil ya ajiye sannan ya nuna Babba Giɗaɗo da Baffa Modibbo ya ce ku zo ku amshi auren 'ya'yanku. Kai Giɗaɗo kai za ka bayar, Modibbo kuma ya amsa."

Cikin abunda bai fi mintuna goma ba akai siga a gaban kowa dake wajen maza da mata, manya da yara aka ɗaura aure. A gaban kowa Abdul-Hameed ya tashi ya fuskanci gabas ya yi sujada.

Kowa da ke wajen sai da aka bishi da goro da sweet har da Mamiyo, Hafiz, Baffa Tukur, baffa Mahmud da kuma malam mai huluna. DSS ne suka shigo suka tafi da su Mamiyo suna kuka suna ihun neman yafiyar Babiyon. Baffa Lawal kuwa dama bai wajen, kamar Babiyo ya san abunda zai faru ya tura shi Yola. Don tabbas da yana wajen zuciyarsa za ta iya bugawa ya faɗi ya mutu.

Babiyo kuwa tsam ya miƙe bayan bubbuga bayan Abdul-Hameed ya shige ɗaki ya kullo ƙofa. Kuka yake son yi amma ya kasa. Ƙirjinsa ne ya masa nauyi don har ga Allah bai taɓa kawowa ko cikin mafarkinsa su Tukur ba jininsa bane.

Babu wanda ya bi bayansa don kowa ya san dole yana bukatar a bar sa shi kaɗai. Ƴaƴan su baffa Tukur da matansu sune cikin matsanaicin tashin hankali jin babu abubda suka haɗa da familyn Arɗo Barkinɗo. Wani can ɗan iskan boka shine siriki kuma kakan 'ya'yansu.

Babiyo da yaga damuwa tana neman yi masa illa, sai ya ɗauro alwala ya shiga raya darensa da salloli tare da miƙawa Allah lamuransa. Cikin hukunci ubangiji wasai ya farka washa gari bayan bacci da ya ɗaukesa wajajen ƙarfe ukun dare. Sai dai duk da hakan bai makara sallar asuba ba. Shiri ma su ka hau yi don tafiya Villa kasancewar a can ne za a rantsar da su Abdul-Hameed.

Asma'u kanta ta shaida mijin nata yana cikin farinciki saboda farincikin da ya sanyata jiya duk da kuwa bai shaida mata ɗaurin aurensa ba.

Hakaa yake ɓangaren Mama Hafsat, ba ƙaramin farinciki ta yi ba da auren Zeenah, baffa Ɓaleri kuwa har da hawayen farinciki.

Wajajen ƙarfe biyu kowa ka gani gidan yana gaban TV yana kallon rantsarwar da ake wa su Abdul-Hameed. Farinciki wajen Hajiya Asma'u tamkar zata zauce. Sai kiran friends da 'yan uwa take. Kanta na wani huruwa yana ƙara girma.

Sai bayan isha'i suka Babiyo suka dawo Arɗo Barkinɗo. Washa garin ranar kuma aka haɗa gaggarumar walima wacce aka gayyaci manya-manyan mutane ciki har da mahaifin Asma'u wato tsohon Gwamnar Kaduna shi da matarsa. Kuma su sun san da zancen auren da Abdul-Hameed ɗin ya yi don Babiyo ya faɗa musu komai amma ban da labarin Zeenah. Ita ce dai Asma'un bata san komai ba.

Sai bayan walima ta tashi lafiya sun dawo gidajansu sannan Abdul-Hameed da mahaifin Asma'u suka nufi gidansa domin shaidawa Asma'un batun aurensa.

Sai da mahaifinta ya mata nasiha sosai shi ma mahaifiyar tata sannan suka shaida mata batun auren. Aikuwa nan take ta shiga ihu tana hauka da faɗin daga aure wata uku kawai har an mata kishiya. Sai da uban ya tsawatar mata tukun ta yi shuru amma bata daina gunjin kuka ba tana tunanin ta yaya za ta tunkari friends ɗinta ta faɗa masu an mata kishiya 3months after her marriage. Uwar dai ta kuma janta ɗaki ta tausasheta don ita macece ta san irin zafin da mace take ji idan aka mata kishiya. Hakan ne ya saka tai ta lallaɓarta tana bata baki da nuna mata dabarun zama da kishiya.

Mahaifin Asma'u ya yiwa Abdul-Hameed nasiha sosai da nuna masa kula da haƙƙin aure da kuma yin adalci tsakanin mata biyu gudun tashi da ɓarin jiki ranar gobe. Kuma sosai ya ji daɗin nasihar kuma ya saka a zuciyarsa zai yi iya yinsa duk da soyayya Zeenah its obvious a idanunsa ga kowa. Amma ya yi alƙawari in sha Allah ba zai shiga haƙƙin Asma'u ba.

Babiyo ya tattaro almajirai da shi kansa da 'ya'ya da jikoki suna ta karatun Alƙur'ani kullum bayan isha'i har sai da suka sauke Alƙur'ani sau goma cikin sati guda tare da roƙon Allah ya haɗe kan zuri'arsa ya warzar da zaman lafiya ƙaunar juna a zuciyarsa ko bayan ransa. Sannan ya kuma taya Abdul-Hameed riƙo akan shugabancin da Allah ya bashi na gida da waje.

Nenne ita da kanta ta zo ta ɗauke Zeenah ta tafi da ita ta shiga yi mata gyara jiki bayan ɗauka wata mai gyaran jiki da ta yi. Cikin sati guda kawai Zeenah ta canza ta koma tamkar balarabiya. Abdul-Hameed kuwa duk nacinsa an hana shi ganinta. Gashi can Asma'u ma ta huro masa wuta don kullum cikin bala'i take da zage-zage da harshen hausa tamkar dai ba queen Elizabeth ba. Don tun ranar da aka faɗa mata ya sake aure ta mance yadda ake magana da turanci. Don bala'in ya fi mata daɗi cikin harshen hausa.

Wata guda sai Zeenah ta kwashe sa gidan Nenne kamun aka miƙa ta gidan mijinta da ke kusa da na Asma'u don tsakaninsu bai fi taku ɗari ba. Gidan ya sha gyara kuma Babiyo ya kashe kuɗi wajen ƙawata mata shi.

Ranar da Abdul-Hameed zai kwana gidan Zeenah kuka Asma'u ta riƙa yi tamkar za ta mutu ganin yadda sai wani rawar jiki yake. Sai kawai ta shige ɗakinta ta kullu.

"Finally you're mine Zee-meed!" Abdul-Hameed ya faɗi yana kallonta zaune tsakiyar gadon sanye cikin kayan fulani ruwan nevy blue. Ba ƙaramin kyau ya yi mata ba. Sai ta fito asalin fulaninta. Hawa kan gadon ya yi ya ɗage lulluɓin da ta rufe fuskanta. Hawaye ya gani suna zubowa daga idanunta, sai ya saka harshe ya yi ta lashe su yana faɗin, "Na faɗa miki ba zan ƙara bari ruwan hawayanki su zuba ma, Zee-meed."

A hankali ta furta, "Kukan farincikin kasancewa matarka nake yi, Abban Meema!"

Yau ce ranar farko da ta kira shi da sunan, sai ya ji wani abu ya tsaya masa a maƙoshi, kewar 'yarsa da ko fuskanta bai taɓa gani ba sai a hota ya shiga dabaibaye shi. Sai kawai ya janyota ya haɗa da ƙirjinsa ya rungume. Ta jima a jikinsa kamun ya ɗagota suka sauko daga kan gadon ya ce, "Mu je mu yi Alwala mu yi sallah domin godiya ga ubangiji da ya nuna mana wannan ranar."

Bayan sun yi sallah sun godewa ubangiji sai ya shiga ciyar da matarsa da gasasshiyar kazar da Nenne da kanta ta gasa masa a oven. Sai da ya ta ƙoshi sannan ya ƙyaleta tare da kawas da kayan sannan ya dawo ya zauna kusa da ita yana kallonta tamkar zai cinye ta. "Ina matuƙar ƙaunarki Zeenah!" ya faɗi yana mai janyota jikinsa. (Ni dai na yi waje daga nan ba ruwana da ganin sirrin ma'aurata 😷🤐)

Abdul-Hameed bai yadda ya zauna a gidan gwamnati ba, a nan cikin Arɗo Barkinɗo ya ke zaune sai akai masa lafiyayyan office ɗinsa a wajen tare da zuba uban jami'an tsaro.

Hajiya Asma'u kuwa ta sauko ta fara kula mijinta sai dai akwai wannan mummunar kishin danƙare da ƙirjinta, amma ganin mijin nata bai banzatar da ita ba sai hankalinta ya ɗan kwanta. Sai dai magana bai taɓa shiga tsakaninta da Zeenah ba idan ka cire sallama da gaisuwa, duk da wasu lokutan suna yawan haɗuwa a gidan Nenne ko kuma idan Babiyo ya kira Meeting.

Su Baffa Tukur, Hafiz, malam da Mamiyo duk an yanke masu hukunci. Su huɗun duk aka yanke masu hukuncin rai da rai a gidan yari. Mamiyo kuwa tana asibiti ƙarƙashin kulawar likitoci domin ƙwaƙwalwarta ta samu matsala sannan ashe tana ɗauke da cervical cancer wanda ita kanta bata sani ba. Ta fita daga hayyacinta gaba ɗaya kuma ga tsufa. Halin da take ciki ma addua take mutuwa ta zo ta ɗauke ta ta huta.

Maryama da Sa'adatu duk sun koma makaranta bisa umarnin Babiyo har da ita kanta Zeenah don kowa ya san gidan Babiyo gidan karatu ne. Dama sun kammala sec school admission kawai aka basu a nan university of Abuja suka shiga karatu kowacce da course ɗinta. Sau biyu Asma'u na baiwa Zeenah carry over sabida haushinta da kishinta da take ji har sai da Babiyo da kansa wannan karan ya tsawarar mata. Hakan ya saka ta barta ta wuce da C level 1 second semester.

Abunda ya fara ɗagawa Asma'u hankali shine cikin da Zeenah ta samu wanda ita ko ɓatan wata bata taɓa yi ba. Sai hankalinta ya mugun tashi ta shiga rerawa Abdul-Hameed kuka duk dare. Ya ji tausayinta hakan ya saka suka je asibiti domin duba lafiyarta, sai dai duk inda suka je sai likitoci su ce matsalar daga ita ne ba za ta iya conceiving ba. Sun zaga asibitoci sun fi talatin a Nigeria amma kowa abunda yake cewa kenan. Daga ƙarshe har ƙasar suka bari can ma sai thesame. Sosai ta shiga mugun tashin hankali don har gida ta koma sai uwar ta yi ta bata bakin tukun ta dawo.

Tare da Abdul-Hameed akai ta rainon ciki har ya isa haihuwa ta haifi 'yarta mace. Gagarumar suna akai, yarinya ta ci sunan Nenne Saudatu ana mata inkiya da Muslimat. Muslimat na da shekara ɗaya da rabi Zeenah ta kuma samun ciki mai shegen laulayi, hakan ya saka Nenne ta ɗauke surukar tata ta koma wajenta da zama. Makaranta ma da ƙyar take iya zuwa don lokacin suna a level 300 ne kuma second semester. Sai da cikin ya yi watanni bakwai tukun ta rage azabebben laulayi kuma alokacin ta shiga level 4 har sun yi jarabawar first semester.

Yau da ya kasance ranar asabar, Abdul-Hameed da gaba ɗaya iyalansa suka shirya domin shopping. Suna zaune su uku a baya sai driver da ke jansu. Muslimat kuma a hannunsa yana mata wasa don yana son 'yar sosai saboda Zeenah tamkar ta yi kaki. Gaba ɗaya ita ta ɗauko bata ɗauko komai na Hameed ba.

Shiga wajen suka yi suka soma siyayya. Har sun gama Zeenah ta tuna akwai wami lesa da take son saya, sai ta koma domin dubawa. Wata kyakkyawar yarinya da baza ta wuce sa'ar Muslimat ba ta gani tana kuka tana jan gyalen mamanta da ke ƙoƙarin ɗauko mata wami tedybear a sama. Da sauri Zeenah ta isa wajen tare da juyo da mata gaba ɗaya kasancewar ko cikin duhu idan taga bayan aminiyarta Ladi katifa za ta gane ta. Wani irin waro idanu Ladi Katifa ta yi tana tare ida ihun kiran sunanta sannan ta rungumeta. Da gudu Abdul-Hameed ya iso wajen hankali tashe, amma sai ya taras da matar tasa da ƙawarta da kusan kullum sai sun yi hirarta shi da ita.

Kuka suke yi sosai na yaushe gamo. Kamun Ladi katifa ta shiga kallon Abdul-Hameed maɗaukakin mamaki ɗauke a fuskanta.

Murmushi Zeenah ta mata tare da faɗin, "It's a long story aminiyata. Ina Salma nice?"

Daidai nan mijin Ladi katifa ya ƙariso wajen shima, sai Ladi ta nuna masa Zeenah tare da faɗin, "Aminiyata da nake baka labari. Ga mijinta."

Da sauri mijin Ladi ya miƙawa Abdul-Hameed hannu cike da girmamawa don ya sansa kuma ya san ko shi ɗin wanene. Securities ɗin da ke zagaye da shi kaɗai ya isa ya shaidawa mutum babban mutun ne shi. A nan dai su kai exchanging number bayan alƙawarin kawota hat gidan Zeenah gobe da mijin Ladin ya yi.

Washa gari kuwa sai ga ta a gidan, bayan cika mata gabanta da kayan ciye-ciye sai suka shiga hirar yaushe gamo. Zeenah ita ta fara labarta mata labarin duk abunda ya faru da ita har izuwa aurenta. Daga nan Ladi Katifa ma ta bata nata labarin tun daga saceta da Yasaar ya saka aka yi, komawarta gida da sakata makaranta da mijin mahaifiyarta ya yi har zuwa aurenta da wani lecturer da suka ƙulla soyayya wanda bata ɓoye masa komai ba a past ɗinta. Bai taɓa aure ba sai dai ba yaro bane don ya girmi Abdul-Hameed ɗin ba sosai. Aikinsa ne ya dawo da shi Abuja shiyasa zaman su ya dawo nan Abujan, ashe rabon ganawa ce. Kuka su kai sosai suka yi har da majina. Zeenah ta rungume 'yar Lafi wacce ke kama da uwarta sosai, kyakkyawa da ita. Kusan lokaci ɗaya ma suka haihu ita da Ladin.

"Oh! ko ina Salmanu jikan Iyan mai danko ya nufa oho. Zan so in ƙara ganinsa wallahi. Shine uwar riƙon Meema tun tana jinjira." faɗin Zeenah hawaye na zubo mata.

Nan Ladi ta shiga lallashinta don ta fahimci kewar ɗiyarce ta dawo mata sabuwa fil.

Haka rayuwa ta cigaba, amintarsu ta dawo sabuwa fil, gashi makarantarsu ɗaya course ne kowa da na shi. Zeenah ta haifi Awwab da sati guda ta zana jarabawar ƙarshe na kammala degree ɗinta. Ladi ma ta kuma haihuwa 'yarta mace Sadiya, sunan surukarta ne sai suke mata inkiya da Meema.

Ɓangaren Asma'u kuwa kishin nan na nan daram sai abunda ya yi gaba. Musammam da ita ba ta haihuwa. Gashi dai bata rasa komai ba, kullum cikin neman hanyar ƙuntawawa Zeenah take yi.

Marwanatu ma ta kuma aure a nan Abuja, tana auren ɗan wani mutum da shima yana da hannun jari a kamfanin Babiyo wato Arɗo Barkinɗo global company limited. Wani irin ƙullewa su kai da Asma'u. Sun zama ƙawaye saboda tarayya da su kai akan abu ɗaya wato ƙiyayyar Zeenah. Sai dai ko da wasa bata taɓa faɗa mata Zeenah ta yi karuwanci ba sabida gargaɗin da Baffanta ya mata.

Zeenah ta kuma haihuwar ɗanta na miji Muhaysim wanda daga shi haihuwar ta kulle mata. Soyayya wajen Abdul-Hameed kuwa kullum ƙara sabunta ya ke yi. Sai duk da hakaan babu ranar da bata ɓoyewa ta yi kukan rashin 'yata Meema da har yanzu ba a san inda take ba.

Abdul-Hameed sun kusa gama tenuwar su akan mulki saboda shugaban ƙasa zai sauka kuma tare za su sauka. Sai dai shi aka tsayar ɗan takarar shugaban ƙasa kasancewarsa mai matuƙar masoya kuma mai gaskiya da rashin tsoro.

Kamfen kawai ake babu kama hannu yaro, su hajiya Asma'u sune 'yan gaba wajen kamfen. Zeenah kuwa ko sau ɗayaa bata taɓa tara mata ba ko fita waje da sunan hakan don Babiyo ya gargaɗe ta ya ce ta zauna a ɗakin aurenta. Dama kuma ita ko bai faɗi hakan bata da ra'ayin yin haka. Kullum dai tana tashi tsayuwar dare tana roƙa masa Allah idan alkhairi ne Allah ya bashi, idan kuma ba alkhairi bane Allah ya hana shi.

Cikin hukuncin ubangiji Abdul-Hameed shi ya ci zaɓe da ƙuru'u mafi rinjaye. Lokacin da ake rantsar da shi ji ya yi gaba ɗaya kamar an ɗauki dutsen uhudu an ɗaura masa.

Asma'u kuwa sai shisshigewa take yi ta ci uban ado cikin rantsattsen lace sai washe baki take yi. Ƙawaye kuwa gasu nan rututu. Matan tsoffin gwamnoni da kuma sabbin da aka rantsar. Burinta bai gama cika ba sai da aka bata kujeran first lady. Kanta wani irin huruwa ya riƙa yi sai take ganin ai tafi Zeenah matsayi wajen His Excellency Abdul-Hameed ɗin ne.

Bai fi shekaru biyu ba a kan mulki, wani faɗa ya haɗa su da Zeenah ta gaggaya mata maganar da ya hana ta barci har ta kira Marwanatu ta shaida mata, shine Marwanatu ta fayyace mata sirrin Zeenah kaf din itama ta samu abun goranta mata.

Hakane ya saka ta tura PA ɗinta ta je gidan Jarida ta faɗi cewar Abdul-Hameed na da ɗiyar shegiya da ya haifa da karuwa, sannan kuma daga bayaa ta zo ta ƙaryata hakan a gaban ƴan jarida.

(Wannan shine kaɗan daga labarin baya)

_Wallahi na rubutu yau, duk wacce ta karanta na yau ba tai min zazzafan comment ba sai na roƙa mijinta ya mata kishiya aradun Allah 😎_

_Gobe ✈✈✈✈ zai sauka_

#His Excellency Abdul-Hameed #Her Excellency Zeenah #Asma'u first lady #Ladi katifa #Babiyo #My Destiny #Matar Sayyadee *** [9/3, 5:58 AM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)

*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee

☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`