Page 71
Aje ai following channel ɗina please 🙏🏼 ***
*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***
Domin shiga comment section kuma ki danna wannan link ɗin👇🏼 *** *_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining link ɗin da ke sama domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜
_*💃🏻💃🏻 _Kuna ina 'yan uwana matar aure da 'yan mata? Shela nake ko wacce ta fito domin kuwa yau na zo maku da albishiri! Kun san matar Sayyadee ta ku ce ba ta samun abun ƙaruwa ta yi shuru domin ta ƙaru ita kaɗai._💃🏻💃🏻
💐💐🌼🌼_Magana ake ta ƙamshi. Toohwa! Mai ya hwaru?_ 🤔 🌷🌷🌸💮
*To maza ku marmatso ga sirrin nan. Shahararriyar nan wacce ke inganta soyayya tsakanin ma'aura wato Fatima Zaransalaty inkiya Queen Zarah ce ta taho mana da wani ƙamshim domin cika hancinar mazajemu da ƙamshi*. _INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_ _TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA KUJI 💃🏻
_Zaran Salaaty ta yi tafiya miƙaƙƙa har Sudan domin farnata ranmu da na mazajenmu ta kawo mana Sudanese perfume👌🏻 wanda idan har kika shafa shi a jikinki ko kin yi wanka ƙamshin bai barin jikinki. Tested and Trusted ƴaruwa. Zaransalaty ba iya sudanese perfume ta kawo maku ba, akwai kayayyaki masu matuƙar inganci na gyaran HQ (kun san dai ba a wasa da headquarter) akwai kayan gyararrakin jiki kala-kala na ƴan mata da matan aure. Sannan Zaransalaty tana sai da Decoration na kayan ɗaki iri-iri wanda baki taɓa ganinsu._
_KAR IN CIKA KI DA SURUTU, KE DAI NEMI ZARANSALATY A NUMBERS ƊINTA KAMAR HAKAA_: *** Or ****
*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_nfection_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_
_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ ***** *****
_Meemah_ Jirgin na saisaita a sama Meemah ta saki ajiyar zuciya tare da kwantar da kanta a jikin kujera ta lumshe idanu tana tunanin halin da Leo zai shiga idan ya farka babu ita. Da sauri ta buɗe idanu tare da kallon sama inda ta ajiye ɗan ƙaramin akwatin kayanta. Sai ta miƙe dama kuma tana kusa da window ne ta ja zip ta ciro hoton da su kai a bakin church bayan an gama ɗaura masu aure.
"I'm prominse you Leo, I will come back just for you. I pray you won't do anything stupid." ta faɗi tana ta kallon fuskanta a hoton tare da kai hannu ta shafa kamun ta saka a ƙaramin jakar da ke hannunta.
Wata ma'aikaciyar jirgi ce ta nufo inda ta ke tare da faɗin, "Madam, what do you like to eat please?"
Ɗan juyowa ta yi ta kalleta tare da faɗin, "Just water!" don bata jin za ta iya cewa wani abu a halin da take ci. Kawai she's eager to see in Nigeria.
Tafiyar awanni ashirin da biyu ya kawo su Murtala Muhammed International Airport, wanda ya yi daidai da takwas da mintuna arba'in na safiyar washa garin ranar da ta taso daga Colombia. Ita ce ta goma sha biyu na fitowa na fitowa daga cikin jirgi hannunta janye da akwatinta. Wani iskan farinciki ta ji ta zuƙa lokacin da ta gama fitowa daga jirgi tana kalle-kalle har ta shigo reception, turus ta tsaya lokacin da ta ga ƙaton bana a hannun wani da bata ga fuskansa ba saboda ya rufe da abunda ke hannunsa. A jikin banar an rubuta _you're highly welcome to Nigeria Meemah!_ A ƙasa kuma aka kuma rubuta _Welcome Home sweet Lulu_
Da maɗaukakin mamaki ta nufi wajen kai tsaye tare da kawas da banar don ganin fuskan wanda ya zo tarbanta bayan ta san babu wanda ya san za ta taho Nigeria. A waya ta yanki ticket tai komai, ta dai je airpor ɗin sau ɗaya lokacin da Leo ya yi dropping ɗinta a inda za ai mata kwalliyar biki. Sai ta yi amfani da wannan damar tai saurin zuwa ta dawo.
Wani murmushin takaici mai ɗauke da tsantsan mamaki ta saki tana kallon fuskansa tare da furta, "You must be joking! How do you know I will be here?"
"Mu je za mu yi magana a cikin mota!" Aizaad ya faɗi yana murmushi sam ya manta ma ba ta jin hausa yanzu. Sai kuma ya tuna ai tana fahimtar abunda mutum ya faɗi mayarwar ce kawai take mata wahala.
"I you serious, quien diablos eres tu? mantente alejado de mi! (Dagaske kake? Kai ɗin waye? Ina faɗa maka kai nesa dani!)
Tana gama faɗin haka ta gitta sa ta wuce ta soma tafiya da saurin domin ta ɓacewa ganinsa. Sai dai duk inda ta saka ƙafa shima yana biye da ita.
"I know where your parents are!" Aizaad ya faɗi yana daidai lokacin da ya cimmata.
Cak ta tsaya tare da juyowa ta kallesa murmushi a fuskansa sannan ta furta, "Is this also a trick? Abu mai mahimmanci na zo yi a Nigeria kuma ina kammala zan koma inda na fito, so ina roƙonka ka fita a rayuwata ka kyaleni. Na bar wannan harkar da ka sanni da shi tun a can Colombia. Ba harkar cocaine ta kawo ni nan ba, abu mai mahimmanci ne da ya shafi rayuwata!" da yaren spanish tai masa magana.
Tsayuwa ya gyara bayan ya cusa hannu cikin aljihunsa sannan ya ce, "Duk magiyarki ba zan kyaleki ba. Na san mahaifiyarki ki ka zo nema. Kar ki manta wayarki ta zo hannuna lokacin da na kama ki a Mexico, kuma dama zuciyata ta ba ni za ki gudu shiyasa na yi abu a wayarki ta yarda duk wani motsinki ina sane da shi. Duk wayar da kika yi tana shigowa wayata, haka suk saƙon da kika tura ni ma ina gani da kuma wanda zai shigo miki. Na san komai Meema, na san plan ɗinki na son kashe mahaifiyarki. Ina wajen kika yi auren hauka ke da abokin nan na ki Leo, na kuma bi bayanku lokacin da ya ɗauke ki a mota ya kai ki wani gida. Kuma a idanuna kika fito jiya da safe kika shiga mota domin gudu ki zo airport ki taho Nigeria gudun kar ya farfaɗo daga suman wucin gadin da kika saka ya yi. I know everything Meema. Jirgi ɗaya muka hau dake. Ni ma yau na diro ƙasar. Ina gefenki ta hannun hagu amma na ƙi bari ki ganni. Jirgi na gama landing na yi saurin riga ki fita. Kin san wani abu you're very lucky Meema da kika samu Aizaad na bibiyar lamuranki. Da badan ni ba, da tuni ba a batunki a Colombia. Kar ki tunanin kariyar da Leo ya baki ce ta saka ki ka sha a lokacin da 'yan sanda su ke kai maku hari, sau da dama ina kare ki daga hana alburushi fasa kwanyanki. Harbin da akai wa Leo a kafaɗa wancen ranar, da ba dan bige hannun jami'in da na yi ba azuwan rashin sani, da ba kafaɗar Leo bullet zai shiga, kanki zai fasa." ya ƙarisa maganar yana nuna kanta da yatsa.
Meema was shocked da jin abunda ya ke faɗi. "So all this days you were following me?"
Girgiza kai ya yi tare da bata amsa cikin yaren Spanish, "Shekaru huɗu na yi ina bibiyarki! Mu je a have alot to tell you."
Wannan karan kasa yi masa musu ta yi sai ta samu kanta da bin bayansa tana wani tunani a ranta.
Wajen wata black _Porsche 911_ suka nufa. Da idanu Meema ta bi motar don sosai ya mata kyau. Key ya danna matar ta yi ƙara sannan ya buɗe mata gidan gaba ta shiga sannan ya ɗauki box ɗinta ya zaga ya saka a boat kamun nan ya zagayo ya buɗe side ɗin driver ya shiga ya kullo motar sannan ya tada ya hau hanya.
Babu wanda ya ƙara cewa uffan a cikinsu har suka iso wani haɗaɗɗan eatry sannan ya juyo ya kalleta tare da faɗin, "You must be hungry, and also I. Mu je mu ci abinci." ya ƙarisa maganar da yaren spanish ganin ta fi ƙwarewa da son yin shi kasancewar shine yaren da ake yi a inda take. Ko turanci sai jefi-jefi suke yin sa a can.
Shi ya far fita sannan ta fito ta bi bayansa har cikin wajen. Waje ya nuna mata ta zauna sannan ya zauna yana kallon tun daga kanta har zuwa rabin jikinta kasancewar teburin da ke gabansu ya hana shi ganinta fully. Jeana ne a jikinta sai rigar chantly mai kamar lace kuma shara-shara dom hatta red bra ɗin jikinta ana iya hangowa. Ta wajen cikinta ne kawai rigar ke da kauri don ba a iya hango cikinta. Siririn hannu rigar ke da shi. Gashin kanta a buɗe ta yi masa watarfall braid style, gashin shi ba ja ba kuma ba maroon ba sabida rina shi da ta yi.
"You're such a beautiful lady I've ever seen." ya faɗi amma cikin zuciya sai dai fuskansa na bayyanar da murmushi.
Waiter ne ya zo wajen tare da ba miƙa menu. Shi ya amsa ya yi ticking abunda ya ke so sannan ya miƙawa Meema domin itama ta zaɓa. Chips and egg with liver source ta yi ticking. Cikin abunda bai fi mintuna biyar ba aka kawo masu.
A hankali take cako irish ɗin tana kaiwa baki tana tauna. Shima chips ɗin ya ke ciki da plantain yana kallonta ta ƙasan idanu yana nazartanta. Yana da hanyoyi masu sauƙi da zai tura ga iyayanta, sai dai yana tsoron ta aikata wani mummunar abun da za ta zo tana dana sani. Musamman da yanzu Nigeria ta ɗauka da batunta na yadda aka samar da ita don ya gani a social media. Kuma tun washa garin ranar da ta mamayeshi ta sumar da shi ya saka aka masa bincike akanta da labarin da ya bata. Cikin ƙanƙanin lokaci sakamakon bincikena ya riskesa da na abunda First Lady ta saka aka yaɗa har da hoton Meeman tana jaririya, har da rahoton hukuncin da aka yankewa su saboda da kaza.
"In tambayeki?" ya faɗi cikin harshen turanci bayan ya goge bakinsa da tissue.
Ba tare da ta kalle shi ba ta ce, "Ina jin ka."
"Yanzu sai ki samu tabbacin akan mahaifiyarki bata aikata abunda kike zarginta da shi ba, za ki iya samun waje a zuciyarki ki yafe mata."
Banza da shi ta yi tamkar bata ji abunda ya ce ba. Sai ma ture plate ɗin abinci ta yi tare da goge bakinta da tissue ta miƙe. Shima miƙewar ya yi tare da miƙawa waiter kuɗinsa sannan ya nufo hanyar fita tana biye da shi a baya.
Shi da kansa ya kuma buɗe mata ƙofa ta shiga sannan ya rufe ya zaga ya shiga ɗayan ɓangaren ya tada mota. Kai tsaye wani rantsattsan hotel ya nufa ya kama ɗakuna biyu. Boxes ɗinsu kawai suka ajiye sannan suka kuma fita. Wannan karan Prison direct ya wuce da ita domin nuna mata wani abu.
Har inda Yasaar ya ke a kulle babu ƙafa da hannu ya kaita tare da rakiyar jama'an. Abunda ya bata mamaki shine irin girmamawar da aka riƙa bashi tun daga bakim gate har ciki.
"Ko kin gane wannan?" ya faɗi yana mai nuna mata Yasaar da ya koma tamkar tsumma sai jan ciki ya ke. Ashe akwai cutar sida a jikinsa wacce sai da ta gama cinye jikin ta bayyana. Ya rame ya lalace ya koma tamkar ƙwarangwal. Ga kuma uwa uba cutar haukar da ke damun ƙwaƙwalwarsa.
Girgiza kai Meemah ta yi tare da faɗin, "Ban taɓa ganinsa ba!"
"Wannan shine Yasaar ɗin da ya sayar da ke a wajen Adelberto, sai dai bai ci ko ƙwandala daga kuɗin ba ya samu wannan lalurar. Kamar yadda ya ci amanar ubangidansa haka abokinsa ya ci amanarsa. Ƙarya Esmeralda take maki da ta nuna maki hoton mamanki. Shi ya basu hoton mamanki ya ce su yi maki barazana dashi idan kin yi ƙoƙarin yi masu taurin kai. Mamanki na can cikin tashin hankali da ciwo a zuciya tun ranar da kika bar ƙasar nan har zuwa yanzu. Ta jima tana bege da mararin ganinki!"
Wani kallon banza Meema ta masa tare da juyawa ta fice daga ɗakin ta nufi hanyar fita. Ajiyar zuciya Aizaad ya sauke kamun ya bi bayanta don ya fahimci akwai taurin kai a tare da. Kamun fahimtar da ita zai sha wuya sosai.
"Ka kai ni wajen ita wacce kake kiranta da mamana idan har da gaske taimakona za ka yi!" Meema ta faɗi daidai lokacin da suka ƙarisa wajen mota.
Bai ce mata komai ba sai buɗe mata mota da ya yi ta shiga, sai shima ya buɗe mazauninsa ya zauna tare da tada motar ya koma hotel ɗin da ya kama. Sai da ya rakata har ɗakinta sannan ya tsaya a bakin ƙofa tare da faɗin, "Gobe da safe za mu bar Lagos zuwa Abuja inda iyayanki suke."
Kallonsa ta yi bayan ta shiga ɗakin tare sa faɗin, "Abunda na sani shine a nan Lagos na bar mamana, kuma bata da kowa a garin Abuja. Idan baza ka taimaka min ba ni zan iya da kaina."
Shigowa ya yi tare da jawo ƙofar ya rufe sannan ya harɗe hannunsa a ƙirji ya furta, "Idan kika haɗu da mamanki mai za ki mata?"
"Kashe ta zan yi!" ta bashi amsa kai tsaye ba tare da tsoro ko shakka ba.
Murmushi ya yi mai sauti sannan ya ce, "Baza ki iya ba! Kuma ina da tabbacin haka."
"We shall see!" ta faɗi tana mai kwantar da box ɗinta a kan gado tare da buɗe ta fiddo wata doguwar riga ƙalar yellow ta aje sannan ta mayar da murfin box ɗin ta rufe.
"Can I?" ya faɗi yana mai nuna mata gefen gado.
"Sure!" ta faɗi bayan ta kallesa sau ɗaya ta kawas da kai.
Zama ya yi sannan ya mai da hankalinsa gaba ɗaya a kanta tare da furta, "Mahaifiya ta wuce duk inda kike tunani Meemah. Tashin hankalin da a yanzu iyayanki suke ciki kawai ya ishe su ba sai kin ƙara masu da ƙiyayyarki ba. Look, ba zan yi forcing ɗinki ki fasa ƙudurinki ba, amma ina so ki sani duk wani abu da za ki aikata saboda idanunki sun rufe, wallahi tallahi ƙololuwar nadama zai saka ki ko da kuwa a iya maganar banza ya tsaya. Na san kin san hanyoyin kisa da dama sabida da irin rainon aka girmar dake. Kuma na san ko a cikin Villa za ki iya aiwatar da nufinki, sai dai ina gargaɗinki sa kakkausar murya akan ki janye ƙudurinki!"
"Shawara ce ko uwani?" ta faɗi tana kallonsa a tsiwace.
"Duka biyun!" ya faɗi tare da miƙewa. Sosai ya ke da damar daƙileta akan duk wani burinta, sai dai bai son haka ya fi son ta fahimci illar abunda ta ke ƙoƙarin yi tun kamun ta isa ga iyayanta. Tun lokacin da ya fara ganinta a Colombia haka kawai ya ji sam bata cancanci abunda ta ke aikatawa ba. Hakanne ya saka ya yi ta bibiyarta har ya yi nasarar cafketa a Mexico ta faɗa masa ko ita wacece.
Shi senior officer a hukumar DSS, wani muhimmin aiki ne ya kai shi Colombia na tsayin shekaru huɗu. Kuma daɗin daɗawa mahaifinsa sanannan mutum ne a Arɗo Barkinɗo don yana da hannun jari a companynsu. Sannan suna da kyakkyawar alaƙa da Baffa Ɓaleri don makaranta ɗaya suka yi kuma class mate ɗinsa ne shi.
Har ya kai ƙofar ɗakin sai kuma ya dawo kusa da ita tare da ajiye mata wayarsa sannan ya fice daga ɗakin ya jawo ƙofa.
Kamar baza ta taɓa wayar ba, sai kuma ta kai hannu tare jawo wayar ta shiga kallon screen ɗin babu kyafta idanu. Kallon fuskan wanda a ƙasa hotonsa ta ga an rubuta da manyan baƙi _HIS EXCELLENCY ABDUL-HAMEED ABDUL-AZEEZ_. Zoomin hotonsa ta,yi sosai tana ganin photo copynta a jiki. Don tabbas ko makaho ya shafa hoton ya kuma shafa nata fuskar zai tabbatar akwai alaƙa na jini tsakaninsu. Ba ta fahimci rubutun hausar da aka yi ba don ya mata tsauri sosai. Tana kaiwa kan hoton Zeenah ta tsayar da idanunta cak a kai. Wani irin abu ta riƙa ji mai kama da kewa na yunƙuroma har bata san hawaye na zubo mata ba. Sai kawai ta samu kanta da kai hannu tana shafa screen ɗin wayar. Ta kasa gaba ta kasa baya, sai kallon fuskan uwar take yi. Da kyar da ita yin gaba, nan ta shiga arba da hotunan kala-kalaa tun tana ƙarama. Wasu ita kaɗai, wasu kuma ita da aunty Ladi katifa da aunty Salma nice. Can kuma ta ƙara ganin hoton mamanta da wanda jikinta ya gama bata shine mahaifinta, sun yi matuƙar kowannen su ɗauke da murmushi a fuska, can gefe daga sama sai aka kawo hotonta tana karama, ƙasan hoton kuma hoton Zeenah ce taba riƙe a hannunta tana busawa. A ƙasan hoton kuma aka yi rubutu kamar haka; _Ɓoyeyyen sirrin shugaban ƙasar Nigeria ya bayyana! Shugaban Ƙasan Nigeria mai ci a yanzu wanda aka fi sani da *DODONSU* ko kuma *Baban matasa* yana da ɗiyar da ya haifa da amaryarsa kamun auren su. Amaryar tasa dai shahararriyar karuwa ce da ta yi ƙaurin suna a garin Lagos tun daga shekarar dubu biyu. Amaryar dai ba ta tsaya iya karuwanci ba, kamar yadda kuka ga hotonta na baya, ita ɗin 'yar ƙwaya ce kuma mai shafarar miyagun ƙwayoyi. A wani majiya mai ƙarfi ma ance bata tuba dagaa harkan shaye-shaye ba, kuma tana da hannu a duk wani shugawar da ake da kayan maye a ƙasar musamman hodar iblis. Shin jama'a wani raddi za ku yi wa shugabar ƙasar namu na sabon hukuncin da ya fitar cewar duk wa da aka kama da miyagun kwayoyi a harbesa? Ni dai na ce hukunci daga gida ake farawa!_
Duk da Meema ba ta fahimci hausar ba, amma ta tabbata ba magana mai daɗi akai a wajen ba. Kashe hasken wayar ta yi ta aje a kan gadon jikinta a mugun sanyaye.
Haɗa kai ta yi da gwiwa sai ta samu kanta da fashe da kuka daidai lokacin da Aizaad ya turo ƙofar ya shigo. Har inda ta ke ya ƙariso, bai hana ta kukan ba don tabbas tana buƙatarsa. Sai da ta yi mai isarta sannan ta yi shuru tana shassheƙa, shi kuma a wannan lokacin ne ya soma magama cikin kwantar da murya.
"Muhimmancin Hakkokin Iyaye Tun ranar farko da Allah madaukaki ya halicci mutum ya sanya jagorancin 'ya'ya a hannun iyaye wanda yake shi ne uba na farko Annabi Adam (a.s). Wadannan hakkokin an yi bayaninsu a wasu ayoyin na Kur'ani mai girma, aka kuma hada tauhidi da biyayya ga iyaye domin nuni zuwa ga girman wadannan hakkoki a fadinsa madaukaki; "Kuma yayin da muka riki alkawarin Banu Isra'ila da cewa; kada ku bauta wa kowa sai Allah kuma ku kyautata wa iyaye" . Sannan har ilayau aka sake nuna matsayi babba da Annabi Yahaya ya kai saboda biyayya ga iyaye ana yabonsa da cewa: "Ya kasance mai biyayya ga iyayensa bai kasance shakiyyi ba ". Kamar yadda Annabi Isa (a.s) yake fada da dukkan alfahari cewa: "Kuma mai biyayya ga mahaifiyata kuma bai sanya ni shakiyyi ba" . Musulunci ya himmantu da nuni zuwa ga wannan matsayi na hakkin iyaye yayin da manzon rahama (s.a.w) yake shelanta cewa: "Aljanna tana karkashin tafin iyaye mata ne" . a wata ruwayar ya zo cewa; "Karkashin tafin iyaye mata, dausayi ne daga dausayin aljanna" . Imam Ali Sajjad (a.s) yana siffanta irin wannan hakkokin da fadinsa: Ka sani hakkin babarka cewa; ta dauki cikinka wasu watanni tana ba ka abinci daga 'ya'yan itaciya da nononta, kuma ta bayar da gaba dayan rayuwarta domin kare ka, kuma ba ta yi sanyi ba tana mai yarda da kwana da yunwa amma kai ka koshi, ta zama da kishirwa kai ka koshi, ta kasance babu kyakkyawan tufafi kai kuma kana da tufafi, ta shiga rana kai kana inuwa, saboda ba ka nono tana rasa bacci ta jure wa rashin bacci, ta kare ka daga zafin lokacin zafi da kuma tsananin lokacin sanyi. Kuma ta jurewa dukkan wata wahala domin kai, ka sani ba zaka iya gode wa ni'imar uwa ba, ba zaka iya sauke hakkinta ba, sai dai Allah ya yi maka taimako ya kuma ba ka dacewa . Imam Sajjad haka ya kasance mai kiyaye hakkin uwa, an taba tambayarsa me ya sa ba ka cin abinci tare da baabarka? sai ya ce: Ina jin tsoron kada in riga baabata daukar wata loma da ita take so, sai ya kasance na saba wa abin da take so da wannan! Imam Sadik (a.s) yana cewa; "Wani mutum ya zo wajen manzon Allah (s.a.w) sai ya tambaye shi ya ma'aikin Allah! Wane makusancina ne zan yi wa alheri? Sai ya ce: Baabarka. Ya sake tambaya: bayan nan? Sai ma'aikin Allah ya ce: Baabarka. Sai ya sake tambayaka a karo na uku. Sai ma'aikin Allah ya ce: Babarka. A karo na hudu Sai ma'aikin Allah ya ce masa: Babanka . Amma kada mu manta irin wannan girmamawa ba mai cancantar ta sai uwa da ta dauki nauyin shiryar da 'ya'yanta ta sha wahala wajen nuna musu hanyar daidai ba wacce ta wulakanta su ba ta watsar da su babu wani tausayi ko damuwa da abin da zasu iya kasancewa nan gaba. Yaron da bai samu soyayya da kauna daga uwa ba, zai taso tabbas cikin matsalolin rayuwa iri-iri na tunani, kuma a nan gaba zai iya kasancewa daga cikin wadanda ba zasu iya fahimtar ma'anar tausayi ga iyaye ko al'ummarsu ba, don haka iyayen da suka yi masa irin wannan tarbiyya suna kawo wa al'ummarsu wani bala'i ne. Game da girmama uba kuwa Imam Sajjad yana cewa: "Amma hakkin babanka ka sani shi ne asalinka kuma ba don shi ba, da babu kai, kuma duk wani abu da kake gani gareka da yake kayatar da kai, to ka sani babanka ne mafarin wannan ni'imar gareka, sai ka gode wa Allah, ka gode masa gwargwadon wannan. Babu karfi sai da Allah" . Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: "Addu'ar mutane uku tabbas abin amsawa ce; 1- Addu'ar wanda aka zalunta; 2- Addu'ar matafiyi; 3- Addu'ar Uba ga dansa ; Sannan akwai fadin Ubangiji game da iyaye da cewa: Ya hukunta kada a bauta kowa sai shi kuma a kyautata wa iyaye, suna manya ne ko kuma dayansu, Ubangiji ya hana a ce musu tir ko kaico, sannan ya yi umarni da a gaya musu magana mai girma da girmamawa. Kuma akwai bayanai da suke nuni ga cewa; wadanda suke cutar da iyayensu suna nesa da rahamar Allah kuma suna cikin azaba a lahira. Abu Walad Hannad ya tambayi Imam Sadik (a.s) game da ma'anar fadin Allah (s.w.t): "Ku kyautata wa iyaye"? sai Imam Sadik (a.s) ya amsa masa da cewa: "Kyautatawa a nan tana nufin ku yi musu kyakkyawar mu'amala, kada ku tilasta su su biya muku bukatunku koda kuwa masu kudi ne. Kuma ku kula da halayensu da matsalolinsu, shin Ubangiji madaukaki ba ya cewa ba zaku iya samun kyakkyawa ba har sai kun ciyar daga abin da kuke so? Sannan sai Imam Sadik (a.s) ya ce: "Koda kuwa sun tsufa kada ka sake ka yi musu mafi kankantar wulakantawa, sannan kada ka daga murya a kansu, wato koda sun bata maka rai kada ka wulakanta su, idan suka dake ka to kada ka yi kara a kansu, kada ka fadi magana mai zafi, ka gaya musu magana ta girmamawa; wato ka yi musu magana mai taushi da nuna kauna kamar ka ce musu Allah ya ba ku hakuri, wannan shi ne fadin alheri. Amma da Allah madaukaki yake cewa: Ka shimfida musu fukafukin rusunawa don tausayi da kauna, wato ka tausasa zukatansu da kallon tausasawa da tausayawa, kuma kada ka taba daga murya a kan tasu, kada ka sanya hannunka a kan nasu, kada ka shiga gabansu yayin tafiya" . A wata ruwayar Imam Sadik (a.s) yana cewa: "Me zai hana wani mutum musulmi ya kyautata wa iyayensa suna raye ne ko suna mace! Ya yi musu salla, ya bayar da sadaka don su, ya yi musu hajji da azumi, kuma ladan nan kamar yadda za a ba wa iyayensa shi ma fa haka nan za a ba shi, haka nan saboda wannan al'amari da yake ji na alheri ga iyaye Allah zai ba shi lada mai yawa. Kaunar batattun iyaye Mu'ammar dan Khallad ya tambayi Imam Ridha (a.s) cewa: Shin zai iya yi wa iyayen da ba bisa tafarkin gaskiya suke ba addu'a? Sai Imam ya ce: Ka yi musu addu'a kuma ka yi musu sadaka, kuma idan suna raye ba su san hanyar gaskiya ba to ka kyautata musu! Domin manzon Allah (s.a.w) ya ce: Ubangiji ya aiko ni da rahama ne da tausayawa, ba da tsanantawa da cutarwa da rashin kyautatawa ba . Kyautata wa iyaye yana daga alamomin sanin Allah madaukaki da girmansa, domin babu wata ibada da take gaggauta kusantarwa zuwa ga Allah fiye da kyautatawa iyaye, domin hakkin iyaye reshe ne na hakkin Allah madaukaki. Amma da sharadin kada iyaye su kautar da 'ya'yansu daga tafarkin gaskiya da shiriya, su ba su tarbiyya sahihiya mai amfani da inganci, kuma ba su canja yakinin 'ya'yansu da kokwanto ba, ba su damfara su da duniya ba maimakon Allah (s.w.t) da gudun duniya. Amma idan iyaye suka kauce wa tafarkin Allah madaukaki to saba musu zata kasance ibada ce, domin ba a saba wa Allah domin biyayya ga abin halitta, kamar dai yadda Allah madaukaki ya ce: "Idan suka tilasta maka ka yi shirka da ni da wani abu wanda ba ka san shi ba to kada ka yi biyayya garesu" . Daga nan zamu iya fahimtar cewa girmama uwa da uba dole ne ya kasance ba a cikin abin da ya saba wa Allah ba, domin babu biyayya a kan bata da sabon mahalicci madaukaki, amma kuma duk da haka ba a yarda da yi musu wulakanci da mummunan halaye ba, dole ne kuma a girmama su ko suna da imani ko ba su da shi. Kuma Imam Bakir (a.s) a game da haka ya kawo mana magana mai gaskiya abin gaskatawa da cewa; Ubangiji madaukaki bai toge kowa ba game da abubuwa uku: 1- Kiyaye amana ga kowa koda kuwa kafiri ne; 2- Cika alkawari ga kowa koda kuwa ga mutumin banza; 3- Kyautata wa iyaye koda kuwa na gari ne ko batattu ;
A takaice muna iya fahimtar cewa; musulunci ya karfafa yin alaka da juna tsakanin 'yan'Adam kuma ta wannan hanyar ne zai kiyaye kasantuwar al'ummu a matsayin tsintsiya madauri daya, kuma ya samar da wata nau'in hadin kai tsakanin al'umma gaba daya da kara mata dogaro da juna. Sabanin al'ummar da babu koyarwar addini a cikinta da dan'Adam ba shi da wata kima, a nan ana daukar dan'Adam kamar wani kaya ne da za a yi amfani da shi domin cimma burace-buracen duniya kawai, sannan kuma babu batun maganar kimar dan'Adam balle maganar dogaro da juna. A irin wadannan wuraren babu maganar kimar kyawawan halaye kamar kyautata wa iyaye da sadaukar da kai, da zabar wani a kanmu, da kunya, da kame kai, da sadar da zumunci, da mutuntaka, da daukakar rai.
Sanin Hakkin Iyaye Godiya ga wanda ya yi mana ni'ima wani al'amari ne na dabi'ar halittar mutum, kuma hankali ya karfafe shi, don haka ne ma Allah madaukaki ya umarci 'ya'ya da su yi godiya ga wahalhalun da iyaye suka yi na dawainiyarsu a fagage daban-daban, Allah madaukaki yana cewa: "Mun yi wasiyya ga mutum da iyayensa, babarsa ta dauki cikinsa cikin rauni a kan rauni, kuma yayensa cikin shekaru biyu, (don haka) ka gode mini da iyayenka zuwa gareni zaku koma" . Kuma akwai aya mai tsawo a cikin Kur'ani da ta yi magana kan hakan a surar ahkaf wacce take nuni da wasiyyar da aka yi wa mutum na kyautata wa iyayensa, sakamakon irin wahalhalun da suka sha kansa.
Sanyaya Halaye Ga Iyaye Kallon iyaye da tausayawa yana daya daga cikin abubuwan da shari'a take ganinsu a matsayin ibada, manzon rahama (s.a.w) yana cewa: Kallon fuskar iyaye ibada ne . A wani hadisin mai girma da daukaka yana cewa: Babu wani mutum da zai kalli iyayensa da soyayya da kauna da tausayawa sai Ubangiji ya ba shi ladan hajji karbabbe a kowane kallo da ya yi, sai aka tambayi manzon Allah (s.a.w)! Idan da mutum zai kalli fuskar iyaye sau dari yana da wannan ladan kuwa? Sai ya ce: Haka ne, idan ya yi hakan sau dari a rana yana da ladan hajji dari da zai samu .
Nisantar Tsanantawa Ibrahim dan Mahzam yana cewa: Wata rana na fito daga wajen Imam Sadik (a.s) a madina na tafi gidana, babata tana rayuwa tare da ni, sai ta yi jayayya da ni kan wani al'amari kuma na gaya mata magana maras dadi da ba ta dace ba. Wayewar garin wannan ranar bayan sallar asuba sai na sake zuwa wajensa (a.s). Yayin da nake shigowa ba tare da na ce komai ba sai Imam (a.s) ya ce da ni: Ya kai dan Mahzam! Daren jiya ka yi magana mai zafi mai kaushi ga babarka, shin ba ka sani ba cewa cikinta ne ya zama gidanka tsawon lokaci, da goyonka da ta yi, kirjinta ya zama abincinka, saboda me kake yi mata magana mai zafi, kada ka sake yin hakan !
Godiya Ga Iyaye 'Ya'ya na gari kodayaushe suna kokarin ganin sun gode wa iyayensu, kuma wannan aiki ne mai matukar muhimmanci da amfani. Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: Hutu a kan gado saboda hidima da kyautata wa iyaye wanda yake sanya su farin ciki, da kuma haduwa da su da fuska mai walwala ya fi yaki da takobi a tafarkin Allah… idan wani ya bakanta wa iyayensa to sallarsa ba za a karbe ta ba. Haka nan Imam Sadik (a.s) ya ce: Idan kana son ka samu tsawon rayuwa to ka faranta wa iyayenka.
Kiyaye Mutuncin Iyaye Kiyaye mutuncin iyaye yana daga cikin hakkokin iyaye kan 'ya'yansu, wani lokaci wasu 'ya'yan sukan yi aikin da zai sanya cin mutunci da zagi ga iyayensu a cikin mutane, kuma wannan yana jawo wa iyayen jin bakin ciki da zubar mutunci. Don haka ne 'ya'ya su guji abin da zai kawo wulakanci ga iyayensu, a kan haka ne manzon rahama (s.a.w) yake cewa: Mutum ya zagi iyayensa yana daga manyan zunubai. Sai aka ce ya ma'aikin Allah (s.a.w) yanzu mutum ya zagi iyayensa? Sai ya ce: haka ne mana, idan mutum ya zagi iyayen wani, shi ma wancan sai ya zagi iyayensa .
Ba Wa Iyaye Dukiya 'Ya'ya na gari masu imani su ne wadanda suke sanya komai nasu a hannun iyayensu, kuma ba su taba fasa bayar da dukiyarsu ga iyayensu ba, komai nasu suke bukata sai su ba su. Imam Ridha (a.s) yana fada a wata wasiyya mai hikima da ya yi ga 'ya'ya yana mai cewa: Farin ciki ya same ka idan ka yi biyayya ga babanka, ka kyautata masa, ka kaskan da kai a gabansa da girmama shi da darajanta shi, ka yi kokari kodayaushe muryarka ta yi kasa da tasa, saboda shi ne asalin samuwarka da dalilin zuwanka duniya, kuma kai reshe ne daga gareshi, idan da babanka ba ya nan da ba a same ka ba, don haka sai ka ba wa babanka da babarka dukiyarka. A wata ruwayar an ruwaito daga manzon Allah (s.a.w) cewa; Da kai da dukiyarka duk na babanka ne .
Biyayya A Kan Tafarkin Gaskiya A bisa koyarwar Kur'ani wani abu ne wajibi a yi biyayya ga iyaye, kamar yadda Imam Ali (a.s) yake fada cewa; "Hakkin uba a kan da shi ne ya bi shi a komai banda a sabon Allah madaukaki" . Kuma haka nan wani mutum daga kasar Yaman ya zo wajen manzon Allah (s.a.w) domin ya tafi yaki tare da shi, sai Annabi (s.a.w) ya umarce shi da ya koma ya nemi izini da yardar iyayensa, "…idan sun bayar da izini ka yi yaki, idan ba haka ba to sai ka yi musu kyawawan halaye, ka sani wannan aikin gareka ya fi dukkan biyayya ga dukkan umarnin Allah bayan kadaita Allah" . Kamar yadda dai muka yi nuni ne a baya cewa; kiyaye dukkan wadannan hakkokin yana kasancewa ne idan bai saba da keta hakkin wasu ba, don haka idan wani ya tauye hakkin 'ya'yansa da matarsa da 'yan'uwansa da sauran jama'a da sunan kare hakkin iyaye da biyayya garesu wannan bai dandani imani ba, kuma maimakon ya samu lada zai samu zunubi ne. Don haka ne ma muke karfafa cewa: Biyayya ga iyaye tana kasancewa ne banda inda ta saba wa Allah madaukaki da umarninsa.
Lokacin Tsufa Wani babban bala'in da ya hau kan al'ummun da suke da'awar ci gaba a wanan duniya shi ne rashin kimanta tsofaffi, a wasu al'ummu idan iyaye sun tsufa sai a kai su gidan kula da raunana, sai iyaye su rasa samun mai nuna musu kauna a kusa alhalin suna bukatar haka daga 'ya'yansu kamar yadda 'ya'yansu suke bukata daga garesu yayin yarintarsu. Haka nan zaka ga iyaye tsofaffi suna cikin dandana azabar rashin samun wannan tausasawa da tausayawa, kai akwai wanda na ga yana kuka a gidan irin wadannan raunana a talabijin yana cewa; yau shekara bakwai ke nan sai dai dansa ya aiko masa da kayan abinci amma bai gan shi da idanuwansa ba, har ma yana neman hukuma ta tiamaka masa dansa ya zo ya gan shi da idanuwansa. Irin wannan rayuwa tana da daci matuka ga iyaye tsofaffi: Wannan abin takaici da yake wakana a wasu kasashen har na musulmi yana da zafi da zogi a zukata matuka, iyayen da suka dora dukkan rayuwarsu ga hidimar 'ya'ya da al'umma amma bayan duk wannan wahala sai sakamakonsu ya kasance tsarewa da kullewa kamar 'yan gidan yari, suna masu kirga kwanakin mutuwarsu har zuwa wafatinsu, a irin wannan duniya mai da'awar samun ci gaba da 'yancin dan'Adam. Idan mun yi dubi zuwa ga abubuwan da muka kawo zamu ga yadda addinin musulunci ya yi umarni da girmama iyaye ta yadda ya haramta gaya musu mafi karancin kalmar da take nuni zuwa ga wulakanci . Ibrahim dan Shu'aib ya ce da Imam Sadik (a.s): Ina da uba wanda ya tsufa ya yi rauni matuka da gaske, ina goya shi, kuma ina kai shi waje domin ya biya bukatarsa. Sai Imam (a.s) ya ce masa: Duk yadda zaka iya ka yi wa babanka hidima, kai har ma ka dauki loma da hannunka ka sanya masa a bakinsa, wannan ne aikin da zai kasance sanadiyyar kubutarka daga wuta .
Hakkokin Iyaye Bayan Mutuwa A mahangar musulunci hakkin iyaye kan 'ya'ya baya karewa da mutuwa, kamar yadda iyaye suke da hakki a lokacin da suke raye haka nan ma suna da hakki kan 'ya'ya bayan mutuwarsu. Wasu daga cikin irin wadannan hakkokin sun hada da: 1- Ziyarar kabarinsu; 2-Karanta musu Kur'ani; 3-Ba su ladan ayyukan alheri; 4-Biya musu basussukansu; 5-Yi musu hajji a ba su ladan; 6-Yi musu sadaka a ba su ladan; 7-Yi musu azumi a ba su ladan; 8-Ba su ladan 'yanta bayi; 9-Yi musu salla a ba su ladan; 10- Yi musu addu'a .
Sakamakon Kyautata Wa Iyaye Idan mun koma zuwa ga hadisan imamai (a.s) zamu samu cewa sun yi nuni zuwa ga wani sakamako da za a samu sakamakon kyautata wa iyaye, kuma zamu yi nuni zuwa ga wasu daga cikinsu:
Aljanna Wani mutum ya zo wajen Imam Sadik (a.s) ya ce: Ya kai dan manzon Allah! Babana ya tsufa kuma ni ina goya shi kuma ina kai shi ko'ina domin biyan bukatarsa. Sai Imam ya ce: Ka yi masa hidima iyakacin yadda zaka iya, ka sani wannan aikin shi zai kai ka aljanna ne .
Ladan Shahada Wata rana manzon Allah (s.a.w) ya ga wani saurayi wanda ya shagaltu da neman abin rayuwarsa sai ya ce masa: "Ya kai saurayi! Shin kana kula da wani da wannan kudin da kake samu? Sai ya ce: E. Sai ya ce: Waye? Sai ya ce: Babata. Manzon Allah (s.a.w) ya ce: Kada ka daina yi mata hidima, don ka sani aljanna tana karkashin kafafunta". Kuma Manzon Allah (s.a.w) ya kara da cewa: Da ladan shahada ya kasance ga wanda aka kashe a tafarkin Allah ne kawai da ke nan shahidan al'ummata 'yan kadan ne, sannan sai ya kawo mutane bakwai na musulmi da ake kirga su cikin shahidai kamar haka: 1-Wanda ya kone a wuta; 2-Wanda ya mutu a cikin matsatsin mutane; 3-Matar da mutum yayin haihuwa; 4-Wanda gini ya fado masa ya mutu; 5-Wanda ya nutse a ruwa ya mutu; 6-Musulmin da ata dabba ta cinye shi; 7-Da wanda yake kokarin ganin ya yalwata wa iyalinsa dai iyayensa; Wadannan dukkaninsu suna cikin shahidai ;
Ya Fi Jihadi Lada Manzon rahama (s.a.w) yana cewa: Shugaban masu alheri ranar lahira shi ne wanda yake yi wa iyayensa abubuwan alheri bayan mutuwarsu. Imam Sadik (a.s) ya ce: Wani mutum ya zo wajen ma'aikin Allah (s.a.w) sai ya ce: Ya ma'aikin Allah! Ni zan yi maka bai'a kan yin hijira da yaki. Sai manzon Allah (s.a.w) ya tambaye shi: shin daya daga cikin iyayenka yana raye? Sai ya ce: E, duka biyun suna raye. Manzon Allah (s.a.w) ya sake tamaya: Shin kana son ladan lahira wajen Allah madaukaki? Sai ya ce; E. Sai manzon Allah ya ce: To ka koma wajen iyayenka, kuma ka kyautata musu.
Mafi Kyawun Aiki Cikon annabawa (s.a.w) yana cewa: Duk wanda yake son ya samu tsawon rayuwa da yalwa a rayuwa da arziki, da kuma dukiya mai yawa, to ya kyautata wa iyayensa. Domin kuwa wannan aikin wani bangare ne na biyayya ga Allah madaukaki. Wannan al'amari tabbas yana nuna mana cewa izzar duniya da lahira tana cikin biyayya ga iyaye ne. Kuma ya zo a wata ruwaya cewa: Mansur dan Hazim ya tambayi Imam Sadik (a.s): Wane aiki ne ya fi sauran ayyuka. Sai Imam (a.s) ya ce: Salla a lokacinta, da biyayya ga iyaye, da jihadi a tafarkin Allah" .
Tsawon Rayuwa Da Samun Da Nagari Manzon rahama (s.a.w) yana cewa: "Duk wanda ya yi mini alkawarin kyawawan halaye ga iyayensa to ni ma zan lamunce masa dukiya mai yawa da tsawon rayuwa, da soyayya da kuma daukaka tsakanin iyalai da danginsa . Haka nan a wata ruwayar ya zo cewa; "Ku bi iyayenku sai 'ya'yanku su bi ku" .
Saukin Mutuwa Imam Sadik (a.s) ya ba wa 'ya'yan da suke aikin alheri da kyautata wa iyaye ladan cewa: "Duk wanda yake son ya samu sauki a wajen Ubangijinsa yayin mutuwa to ya sadar da zumuncinsa, kuma ya kyauta wa iyayensa, idan ya yi haka to zai samu sauki yayin fitar ransa kuma ba zai samu talauci da miskinanci a rayuwarsa ta duniya ba. Wani saurayi daga sahabban manzon Allah (s.a.w) da ya yi rashin lafiya aka kwantar da shi. Sai manzon Allah (s.a.w) ya tafi domin ya gai da shi. Ga halinsa ya yi tsanani kuma ga shi karshen rayuwarsa ne. sai manzon rahama ya umarce shi da ya fadi kalmar shahada, amma sai harshensa ya kasa kawo wannan kalma. Sai manon Allah (s.a.w) ya tambayi wata mata da take wurin cewa: Shin wannan saurayi yana da uwa kuwa? Sai ya ta ce: E, ni ce babarsa. Sai ya ce: Shin kina fushi da shi ne? Sai ya ta ce: E, ya ma'aikin Allah. Sai manzon rahama (s.a.w) ya nemi ta yafe masa kurakuransa, sai ta ce: Ya ma'aikin Allah na yafe masa saboda kai. A wannan lokacin sai manzon Allah ya sanar da wannan saurayi wannan addu'a: Ya man yakabalul yasira wa ya'afu anil kasir, ikbil minni alyasir wa'afu annil kasir, innaka antal afuwwul gafur. Sannan sai ya lakkana masa kalmar shahada, a wannan lokacin ne saurayi ya bude bakinsa cikin sauki ya fadi wannan kalma ta shahada" .
Ladan Hajji Manzon Allah (s.a.w) ya ce: babu wani da da zai kalli fuskar iyayensa da tausayawa da rahama sai Ubangiji ya rubuta masa ladan hajji kan kowane kallo da ya yi. Sai sahabban manzon Allah (s.a.w) suka ce: Ya ma'aikin Allah! Idan mutum ya kalli fuskar baban da babarsa a sau dari fa za a ba shi wannan ladan? Sai ya ce: Haka ne, koda kuwa ya kalla sau dari ne to za a ba shi ladan hajji sau dari. Ubangiji madaukaki mai iko ne ya ba shi lada sama da haka .
Shafe Zunubai Samun gafarar zunubai yana daya daga cikin abubuwan da ake samu saboda kyautata wa iyaye. Imami na shida yana cewa; wata rana wani mutum ya zo wajen Annabi (s.a.w) sai ya ce: Ya ma'aikin Allah! Lokacin da na sami 'ya, sai na rene ta har ta balaga, har zuwa wata rana sai na sanya mata tufafi na yi mata ado, sannan sai na kawo ta wajen rijiya na jefa ta ciki. Tana ihu tana neman taimakona, karshen abin da na ji a wurinta shi ne tana cewa da ni: Baba!! Ya ma'aikin Allah mene ne kaffarar wannan sabon? Sai manzon Allah (s.a.w) ya ce masa: Ya kai wannan mutum shin babarka tana raye? Sai ya ce: A'a. sai manzon Allah ya ce: Shin goggonka tana raye? Sai ya ce: E. Sai manzon Allah (s.a.w) ya ce masa: Ka tafi ka kyautata mata ka yi mata hidima domin ita tana matsayin babarka ce, kuma yi mata kyawawan halaye shi ne kaffarar wannan zunubin . Imam Sadik (a.s) ya kara da cewa: A zamanin jahiliyya iyaye maza sun kasance suna kashe 'ya'yansu domin kada su fada a ribace su a wasu kabilun su haihu a can.
Samun Baban Matsayi Annabi Musa (a.s) ya ga wani mutum mai matsayi babba a wajen Allah, mai daraja madaukakiya sai ya yi burin ya samu matsayinsa. Don haka sai ya tambayi Allah madaukaki ya Allah! Mene ne ya sa bawanka ya kai ga wannan matsayin? Sai Allah madaukaki ya ce: Ya kai Musa! Ya kasance mai kyautata wa iyayensa ne… .
Dacewa a Rayuwa Hidima ga iyaye yana daga cikin mafi muhimmancin abubuwan da suke kawo dacewa a rayuwa a dukkan bangarorin rayuwar mutum, kuma da samun nutsuwar rayinsa. Cikon manzanni (s.a.w) ya yi nuni da wannan a fadinsa mai daraja: Ubangiji ya sanya ni'imomi hudu sakamakon ayyuka hudu: 1- Samun ilimi sakamakon girmama malami; 2- Tabbatar imani sakamakon girmama Allah madaukaki; 3- Jin dadin rayuwa sakamakon girmama iyaye; 4- Samun tsira daga jahannama sakamakon barin cutar da mutane.
Biyayya Ga Manzon Allah (s.a.w) Wani mutum ya tambayi manzon Allah (s.a.w) game da wahalar da yake sha da iyaye. Sai manzon raham ya ce: Ka kyautata wa babarka, ka kyautata wa babarka, ka kyautata wa babanka, ka kyautata wa babanka, ka kyautata wa babanka. Daga nan ne zamu ga cewa biyayya ga umarnin manzon Allah (s.a.w) yana cikin biyayya ga Allah ne wanda wannan shi ma yana da nasa ladan, kuma yana cikin gaskiya da cin nasara. Ubangiji yana cewa: "Duk wanda ya bi Allah da manzonsa to hakika ya rabauta rabauta mai girma" . Don haka da nagari wanda yake kyautata wa iyayensa yana cikin biyayya ga manzon Allah (s.a.w) ne kuma zai samu darajar da Allah madaukaki ya yi alkawari.
Mummunan Sakamakon Saba Wa Iyaye Kamar yadda biyayya ga iyaye take da kyakkyawan sakamakon duniya da lahira saboda biyayya ce ga Allah haka nan ma munana halaye ga iyaye yake da nasa munanan sakamako masu cutarwa, kuma zamu yi nuni da wasu daga cikinsu a nan kamar haka: 1- Korewa daga wurin Annabi (s.a.w) 2- Nisanta daga adalci 3- Rasa ni'imomin Ubangiji kamar aljanna 4- Matsaloli a duniya 5- Azabar rai mummuna 6- Fushin Allah 7- Gajarcin rayuwa 8- Hana shi hakkokin zamantakewa 9- Sabo ne babba."
Sai ya ɗago ya kalleta tare da cigaba da faɗin, "Kin san mai yasa na miki duk wannan dogon jawaban? Saboda ki san iyaye ba abun wasa ko wulaƙantawa bane. Na san dai har yanzu duk tsayin zaman da kika kwasa a Colombia bai saka kin canza addininki ba, don ban manta jero salatukan da kika riƙa yi ba lokacin da na kama ki a Mexico. Na san dai akwai ƙarancin sanin addini a tare da ke wanda hakan ne ma ya saka kika yarda ki ka yi aure da kirista wanda a addininmu na musulunci Manzon Allah Saw ya yi hani da wannan auren. Addidin musulunci bai yarda mace ta auri namiji kirista ba, amma an yarjewa namiji musulmi ya auri kirista. So ki sani babu wani aure a kanki don ba a yi komai a kan koyarwa addinin musulunci ba. Da dai shi yaron ya musulunta ne to tabbas aurenku ya halasta! Gobe zan kai ki wajen iyayanki, ya rage gareki ki yanke hukunci akan ƙudurinki, na barki lafiya!" yana gama faɗin haka ya ɗauki wayarsa ya fice daga ɗakin.
#Aizaad #Meemah #His Excellency #Zeenah #Arɗo Barkinɗo #My Destiny #Matar Sayyadee *** [9/3, 5:58 AM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)
*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee
☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`