My Destiny (Ƙaddarata)

Page 72

by @matarsayyadee3

Aje ai following channel ɗina please 🙏🏼 ***

*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***

Domin shiga comment section kuma ki danna wannan link ɗin👇🏼 *** *_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining link ɗin da ke sama domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜

_*💃🏻💃🏻 _Kuna ina 'yan uwana matar aure da 'yan mata? Shela nake ko wacce ta fito domin kuwa yau na zo maku da albishiri! Kun san matar Sayyadee ta ku ce ba ta samun abun ƙaruwa ta yi shuru domin ta ƙaru ita kaɗai._💃🏻💃🏻

💐💐🌼🌼_Magana ake ta ƙamshi. Toohwa! Mai ya hwaru?_ 🤔 🌷🌷🌸💮

*To maza ku marmatso ga sirrin nan. Shahararriyar nan wacce ke inganta soyayya tsakanin ma'aura wato Fatima Zaransalaty inkiya Queen Zarah ce ta taho mana da wani ƙamshim domin cika hancinar mazajemu da ƙamshi*. _INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_ _TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA KUJI 💃🏻

_Zaran Salaaty ta yi tafiya miƙaƙƙa har Sudan domin farnata ranmu da na mazajenmu ta kawo mana Sudanese perfume👌🏻 wanda idan har kika shafa shi a jikinki ko kin yi wanka ƙamshin bai barin jikinki. Tested and Trusted ƴaruwa. Zaransalaty ba iya sudanese perfume ta kawo maku ba, akwai kayayyaki masu matuƙar inganci na gyaran HQ (kun san dai ba a wasa da headquarter) akwai kayan gyararrakin jiki kala-kala na ƴan mata da matan aure. Sannan Zaransalaty tana sai da Decoration na kayan ɗaki iri-iri wanda baki taɓa ganinsu._

_KAR IN CIKA KI DA SURUTU, KE DAI NEMI ZARANSALATY A NUMBERS ƊINTA KAMAR HAKAA_: *** Or ****

*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_nfection_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_

_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ ***** *****

Tunda ya fita ya bar ɗakin take wani irin kuka da jin shauƙin ganin fuskan mahaifiyarta. Soyayyata ce da ta jima tana dannewa ya yunƙuro mata ta shiga amayar da shi da ruwan hawayenta, ji ta ke tamkar ta yi tsuntsuwa ta ganta a gabanta ta rungumete. Ta jima tana kuka kamun ta miƙe ta shiga bayi ta yi wanka ta sauya kaya zuwa yellow rigar da ta fiddo wacce iya cinyarta kawai ya tsaya. Zama ta yi a tsakiyar gadon tare da faɗawa kogin tunani.

Ɓangaren Aizaad kuwa, yana shiga na shi masaukin ya zauna a kan gado yana mai jin tausayin Meema sosai a zuciyarsa. Ya san cewar ita kanta ta sha gwagwarmayar rayuwa, kuma uwa uba mahaifiyar bata gwada mata soyayya tun fil-azal ba sai gab da za ta bar hannunta, dole ya zama abu wai wahala a wajenta kamun zuciyarta ta sassauto. Amma kuma yana da hope ganin irin da take yi lokacin da ya koma ɗakin da kuma bayan gama yi mata nasiha.

Links ɗin hannun rigar jikinsa ya cire sannan ya zare rigar ya ajiye, sai ya kasance daga shi sai farar singlet. Wayarsa ce ta yi ƙara alamar kira ya shigo, kallon screen ɗin wayar ya yi yaga sunan FATHER da manyan haruffa ya yi appearing, sai ya kai hannu ya ɗauki wayar tare da amsa kirar ya saka a speaker sannan reapectfully ya furta, "Good morning father!"

"Morning Aizaad, hou are you?" mahaifinsa ya faɗi daga ɗayan ɓangaren.

"I'm fine dad. Yanzu haka ina masauki a Lagos, gobe zan taho Abujan da safe?"

"Why? I need to see you today Aizaad. I'm eager to see the daughter of our humble President. Don Allah ka duba ko akwai flight ɗin zai tashi zuwa Abuja yau ɗin nan."

Murmushi Aizaad ya yi don ya fi kowa sanin mahaifinsa bai ƙaunar jira ko kuma jan rai. "Alright dad, zan duba yanzu."

"Allah ya yi maka albarka!" mahaifin nasa ya faɗi tare da kashe wayar yana mai jin matsanaicin daɗi kasancewarsa mutumin da zai miƙa ɗiyar shugaban ƙasa gida. Don jiya shugaban ƙasa ya yi hira da BBC kuma ya yi maganganun da ya girgiza zuciyar jama'a, yayin da ya tsuke bakunan wasu mutanan, wasu kuma ya buɗe masu hanyar sukarsa a manhajar sada zumunta irin su Facebook, whatsapp, IG, Tiktok, Twitter da sauransu. Don ya amsawa duniya Meemah dagaske ƴarsa ce sannan kuma ya ƙaryata zancen da Nigeria ta ɗauka na cewar matarsa na safararan hodar iblis da sauran nau'ikan kayan maye.

_Ba ko wani magana ake fito da shi duniya ta sani ba, wani abun binne sa ake yi har sai ranar tonon silili. Ba kan Mr president kawai aka fara haihuwa ba tare da aure ba. Kowa na da nashi Ƙaddarar a rayuwa! Idan ma abunda duniya ta ke yawo da shi gaskiya ne, to Mr President ba jama'a ya yi wa laifi ba, kuma ba a shiga tsakanin bawa da mahalicccinsa. Haihuwar Meema ita ce tawa ƙaddarar! Walau ku yarda ko kar ku yarda, Allah ya san cewa ni ba mazinaci ba. Bai kuma zama lallai sai kun yarda da ni ba. Ni Abdul-Hameed yarda ubangiji kawai ta ishe ni. Waɗanda suka sanni kuma na san za su iya bada shaida a kaina. Jama'a ba rayuwa Mr President ba ne ya kama ku saka a gaba kuna yaɗawa a social media ba, rayuwarku za ku duba. Shin yaya tsakaninku da ubangijinku ya ke! Ku gyara alaƙarku da Allah ba ku tsaya kuna bincikar halin wasu kuna yaɗawa a duniya ba. Kai mai maganganu a social media, mai rubuta labarin ƙarya don tada hankalin al'umma ko kuma don ka yi suna a duniya ko jin daɗi idan an soki ɗan uwanka musulmi, ka sani wannan hannun da ka yi rubutu da shi, shi zai bada shaida a kanka ranar tonon silili! Ba zan ɓoye ko inji kunyar duniya ba wajen bayyanar da Farida matsayin ɗiyar da na samar bisa Ƙaddaraba. Tabbas Farida jinina ce, ni Abdul-Hameed ni nayi silar zuwanta duniya! Sannan ina gargaɗi da jan kunne a gare ku masu kiran matata da suna na rashin ɗa'a da su goge duk wani writeup ko video sa suka ɗaura don tabbas zan ɗauki mataki. Kuma zan fara bada misali akan wannan mara kunyar yaron ɗan tiktok ɗinnan da ke sake videos ɗin ƙarya da editing hotuna yana haɗawa da fuskar matata. Yanzu haka yana hannun hukuma. Kuma ba zan taɓa gajiya ba wajen saka a hukunta min duk wanda ke ƙoƙarin ɓatawa matata suna!_

Wannan video shi ya yi ta trending a kafafan sada zumunta kowa na faɗin albarkaci bakinsa. Wasu malaman sun fito sun yi sharhi mai ma'ana akan maganganun Mr President ɗin, wasu kuma sun fito sai sukarsa suke musamman ma irin malaman nan ma su shiga rigar malunta suna haifar da tashin hankali da wasuwasi a zukatan al'umma. Don akwai wani malami da an sanshi sosai, mintuna hamsin ya ɗauka ya na zuba sharhi a kan maganganun Mr President ɗin yana sukarsa. Wasu sun ce malamin siyasa ne 'yan adawa ne suka biya shi domin yin wannan maganganun. Sai dai kuma maganganun da Mr president ɗin ya yi ya tsorata matasa da dama don tabbas wannan gayen _Saashi Dking_ yana shiga hannu aka tura shi prison bayan kaisa kotu wanda shima hotunasa yana ta yawo a media ɗin. Hakan ya sakaa wasu da dama da suka dunga yaɗa hotunan Zeenah su kai gaggawan saukewa don sai kulle masu account ake yi. Mahaifin Aizaad na yankewa wayar ya shiga duba ko akwai jirgin da zai tashi zuwa Abuja a yau ɗin, cikin sa'a kuwa ya samu kuma jirgin nan da mintuna arba'in zai tashi. Booking ya yi masu sannan ya tashi ya shirya a gaggauce ya fita domin zuwa ɗakin Meema ya sanar da ita.

Knocking ya yi sannan ya ɗan tsaya kaɗan yana yana jira ta zo ta buɗe masa. Mintuna biyu ta iso wajen ta buɗe ƙofar. Sai da gabansa ya faɗi lokacin da ya yi arba da idanunta sun yi jazur kuma sun kumbura. Sai tausayinta ya lulluɓesa.

Ita kuwa tana buɗe masa ƙofar ta kuya ta koma kan gadon ta zauna tare da saka kanta tsakankanin cinyoyinta.

A hankali ya tako ya ƙariso inda ta ke ya zauna a gefenta tare da faɗin, "I'm sorry, Meema!"

"You don't have to," ta faɗi da dasasshiyar muryanta still kanta na tsakankanin cinyoyinta.

Jin ya yi shuru bai ƙara cewa komai ba sai kallonta da ya ke yi, sai ta ɗago ta kallesa tare da sakar masa murmushin gefen baki sannan ta ce, "Thanks!"

"For?" ya faɗi yana kallonta duk da zuciyarsa ta riga ta ayyana masa abunda ta ke godiya akai ɗin.

"No puedo agradecerles lo suficiente por volverme al buen camino y recordarme lo que realmente importa en la vida, (I cannot thank you enough for putting me back on the right track and reminding me what actually matters in life,)"

Wani murmushin jin daɗi ya saki yana mai godewa Allah da ta yi saurin amsar tunatarwarsa, duk da dama zuciyarsa ba ta amince masa za ta iya aikata abunda ta ce ɗin ba.

"vamos a Abuja ahora mismo. empieza a empacar tus cosas nuestro vuelo es en 40 minutos, y el aeropuerto está un poco lejos de aquí. (Za mu wuce Abuja yanzu. Ki fara haɗa kayanki jirginmu nan da mintuna arba'in zai tashi, kuma daga nan zuwa airport ɗin akwai ɗan nisa.)" ya faɗi yana mai miƙewa sabida bata dama ta shirya.

Jiki a sanyaye ta miƙe bayan fitarsa, don haka nan ta soma jin gabanta na faɗuwa tamkar zai faso ƙirjinta ya fito. Box ɗinta ta buɗe ta fiddo straight skirt mai tsagu ta baya kalar fari ƙal tare da bodyhuge mint green kuma high neck mai dogon hannu. Cikin sauri-sauri ta shirya sabida kar ta barshi yana jira. Gashin kanta ta ɗan ƙara gyarawa duk da babu abunda ya yi sannan ta fesa turare mai uban ƙamshi sannan ta haɗa duk abunda ta yi amfani da shi ta mayar cikin box ɗin sannan ta kulle. Kallon kanta ta yo a jikin madubi, sai ta samu kanta da sakin murmushi sabida mugun kyawun da taga ta yi duk da kuwa ba kwalliya ta yi ba irin can ba. Powder kawai ta shafa da lipstick.

Boc ɗin ta riƙe ta soma ja bayan ta saka takalminta mai tsini kalaar mint green. Kallon babu ko ɗan kwali sabida bataa saba sakawa ba kuma bata ɗauki hakan laifi ba. Gashin nan sai shinning ya ke kuma dama gashi tubarkalla har baya tum tana yarinyarta.

Tana buɗe ƙofa suka ci ƙaro, shi ma ƙananun kayan ne a jikinsa wanda ya masa kyau aihun sai ƙamshin turare ya ke mai sanyi.

"Subhanallah! Indeed black is very beautiful." ya faɗi a cikin zuciyarsa. A fili kuwa amsar jakar hannunta ya yi tare da faɗin, "You can't go home in that dress. You need to change."

Kallonsa ta yi sannan ta kalli shigarta, ita kanta ta san daga skirt ɗin har rigar ba ƙaramin fidda shape ɗinta suka yi ba, amma duk da hakan bata ga abun damuwa da shigar tata ba.

"What wrong with my dress? I can't change anything." ta faɗi tana ɓata rai.

Bai ce mata komai ba sai gaba ma da ya yi zuwa reception domin kai masu keys ɗin su ya saki ɗakin. Duk inda Meemah ta gitta sai maza sun kalleta, haka kawai ya ji ransa na mugun ɓaci da hakan. Ko da suka shiga mota kai tsaye ba airport ya nufa ba, a wani rantsattsan boutique ya yi parking sannan ya umarce ta da ta fito. Kamar baza ta fito ba, sai kuma dai ta daure ta fito ta bi bayansa zuwa ciki.

Kai tsaye wajen abayas ya nufa Meemaa biye da shi a baya tana jin mamaki ganin abunda ya ke shirin yi. Wani haɗaɗɗan Turrkish abayaa kalar mint green ya ɗauko. Ko shi da ya ke matsayin namiji abayar ba ƙaramin tafiya da shi ta yi ba. Sai ka ƙura idanu sosai daga wuyan abayar za ka hangi siririn zip tun daga sama har ƙasa wanda ke ba abayar damar buɗewa gaba ɗaya. Hannu ya kai ya buɗe zip ɗin gaba ɗaya sannan ya juyo ya fuskanci Meema fuskansa a murtuke ya nufe ta. Da sauri ta ja da baya alamar bata so.

"Ke, a Nigeria muke ban san hauka! A haka za ki shiga arewar? Come on zo ki saka kamun na ɓata miki rai." ya faɗi tare ƙarisawa inda take ya saka mata sannan ya ja mata zip ɗin.

Ita kanta da ta kalli kanta a makeken mirror ɗin da ke wajen sai ta shiga admiring kanta tana jujjuyawa. Gyalen abayar ya warware sannan ya mata rollig tare da zagayo dashi ta baya ya matse da office pin ɗin da ya gani a shop ɗin. Meema sai ta zama tamkar baƙar balaraba.

"Kai! I look soo beutiful in this dress. Thank you soo much."

Taɓe baki ya yo tare da barin wajen ya tafi wajen cashier ya sallame ta sannan ya fita Meemah ta biyo shi ta shiga motar ya tada ya nufi hanyar airport da speed ganim they're running out of time.

(Babiyo, ga tattaba kunnanka nan, kai ma Ɓaleri ga jikarku nan zuwa)

#Aizaad #Meemah #Mr President #Zeenah #First lady #Babiyo #Baffa Ɓaleri #My destiny #Matar Sayyadee *** [9/3, 5:58 AM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)

*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee

☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`