My Destiny (Ƙaddarata)

Page 73

by @matarsayyadee3

Aje ai following channel ɗina please 🙏🏼 ***

*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***

Domin shiga comment section kuma ki danna wannan link ɗin👇🏼 *** *_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining link ɗin da ke sama domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜

_*💃🏻💃🏻 _Kuna ina 'yan uwana matar aure da 'yan mata? Shela nake ko wacce ta fito domin kuwa yau na zo maku da albishiri! Kun san matar Sayyadee ta ku ce ba ta samun abun ƙaruwa ta yi shuru domin ta ƙaru ita kaɗai._💃🏻💃🏻

💐💐🌼🌼_Magana ake ta ƙamshi. Toohwa! Mai ya hwaru?_ 🤔 🌷🌷🌸💮

*To maza ku marmatso ga sirrin nan. Shahararriyar nan wacce ke inganta soyayya tsakanin ma'aura wato Fatima Zaransalaty inkiya Queen Zarah ce ta taho mana da wani ƙamshim domin cika hancinar mazajemu da ƙamshi*. _INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_ _TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA KUJI 💃🏻

_Zaran Salaaty ta yi tafiya miƙaƙƙa har Sudan domin farnata ranmu da na mazajenmu ta kawo mana Sudanese perfume👌🏻 wanda idan har kika shafa shi a jikinki ko kin yi wanka ƙamshin bai barin jikinki. Tested and Trusted ƴaruwa. Zaransalaty ba iya sudanese perfume ta kawo maku ba, akwai kayayyaki masu matuƙar inganci na gyaran HQ (kun san dai ba a wasa da headquarter) akwai kayan gyararrakin jiki kala-kala na ƴan mata da matan aure. Sannan Zaransalaty tana sai da Decoration na kayan ɗaki iri-iri wanda baki taɓa ganinsu._

_KAR IN CIKA KI DA SURUTU, KE DAI NEMI ZARANSALATY A NUMBERS ƊINTA KAMAR HAKAA_: *** Or ****

*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_nfection_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_

_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ ***** *****

Ko da isar su filin jirgin bai saura mintuna huɗu zuwa biyar jirgin ya tashi ba. Sauri-sauri suka ƙarisa aka duba kayansu sannan suka nufi inda mutane su kai layi suna shiga jirgi. Wayarsa ya fiddo ya yi dialing number ɗin mahaifinsa ya shaida masa gasu nan zuwa Abuja in lessthan one hour. Sosai mahaifin ya yi farinciki da jin haka.

Da shigarsu cikin ba jimawa aka umarce su da kowa ya saka wayarsa a flight mode tare da saka seatbelt sannan jirgi ya sau sharara gudu a ƙasa kamun nan ya tashi sama ya daidaita ya cigaba sharara gudu.

Cikin mintuna sittin suka iso Nnamdi Azikiwe International Airport. Kusan sune na ƙarshen fitowa daga jirgin. Meemah sai kalle-kalle ta ke yi ba wai na ƙauyenci ba don ita ƙasashe da ziyarta ma ba su ƙirguwa. Ta je Korea, Turkey, Dubai, Maleyshia, Sweden, Cyprus, Equatorial Guinea, Greece, Hungary, Italy, Jamaica, Moroco, Nepal, Paskistan, India da sauransu.

"Let get going. Kallon mai kike yi haka kamar baƙauya?" ya faɗi yana mai riƙe da both akwatunsa da nata.

Ba ta ce masa komai ba ta jira suka jera suna tafiya. Duk wanda ya kalle su ɗauka ya ke ma'aurata ne.

"Wai ke ba ki da tausayi ne? Shin baza ki taimaka min da box guda ɗaya ba?" ya faɗi cikin harshen spanish.

Ɗan taɓe baki ta yi tare da faɗin, "Es lo suficientemente grande para que puedas llevar las 2 cajas. Eres un hombre tan vago, no eres un hombre fuerte (Ha sun yi girman da zai hana ka iya ɗaukar duka biyun? Kai ka cika kasala, kai mutun ne mara ƙarfi.)"

"Dole ki ce haka tun da har kika yi haɗa ƙashi da ni kuma ki ka shammace ni ki ka sumar da ni," ya ƙarisa maganar yana harararta.

Dariya ta fashe da shi don sosai image ɗin ya dawo mata a idanu. Take kuma ta ɗaure fuska tare da zabga masa harara ta furta, "Me golpeaste brutalmente y también me ataste. (Ka dake ni cike da rashin imani kuma ka ɗaure ni a wulaƙance)" ta faɗi tana mai nunawa a idanunta abun ya mata ciwo ainun.

"Then I'm very sorry!" ya faɗi yana murmushi don shi dai bai ga mummunar dukan da ya mata ba da ta haƙiƙance tana faɗi. Idan laifi ne ma to shi akai wa. Ko shi da ke namiji don ya san raga mata kawai ya yi kasancewarta mace amma ba ƙaramin horo ta samu ba wajen jibgar ƙarti da kuma ƙwarewa a harbi. Sosai ta ke da saiti sai dai idan bata so harbi ba. Aizaad bai yi mamaki ko kaɗan ba da ya ga mahaifinsa da kansa ya zo tarbansa fuskan nasa a matuƙar washe. Daga shi sai drivensa kawai suka zo airport ba. Sanye ya ke da shadda ɗan ubansu ya sha ɗinki mai kyau na zamani tamkar ba dattijo ba. Ba wai shigar ta yara bace, ɗinkin ne na zamani da ya ɓoye tsufansa. Kansa sanye da hula, kana ganinsa ka ga Aizaad. Furfura kawai da ɗan duhun fata zai gwadawa Aizaad ɗin, don shi Aizaad ɗin fari ya ke tass.

Da matsanaicin farinciki Alhaji Haruna ya nufe su, yayin da driver ya nufi Aizaad da sauri ya amshi boxes ɗi hannunsa tare da faɗin, "Barka da zuwa yallaɓai!"

"Barka Minka'il! Mun same ku lafiya?" ya faɗi hakane yana mai rungumar mahaifinsa da ya ƙariso da sassarfa yanaa mai jin daɗin ganinsa da kuma matashiyar yarinyar da kallo ɗaya ya mata ya tabbatar wa kansa jinin His Excellency Abdul-Hameed Abdul-Azeez ce ita.

"Welcome home my daughter!" Faɗin alhaji Haruna bayan ya saki ɗan nasa tare da zuwa kusa da Meemah.

"Good afternoon, Sir!" Meema ta faɗi respectfully don akwai ta akwai girmama manyanta ko acan Colombia.

"No, no, no! Don't call Sir, call me Father. You're my daughter, my beautiful daughter." alhji Haruna ya faɗi fuskan nan tamkar gonar auduga.

Murmushi Meema ta yi tare da faɗin, "Yes Father!" tana jin haka nan mutumin ya mata saboda yanda ya ke faram-faram da ita. Kuma shine mutum na farko da ya bata sunan uba a duniya. Shi ya fara ce mata 'yata tunda aka haife ta. Sai ta ji wani ƙimarsa ta shigeta.

"Let go children!" alhj Haruna ya faɗi yana mai nufa wajen mota da sauri.

Aizaad kuma murmshi ya yi yana kallon yadda mahaifin nasa ke rawar jiki da Meema. Driver ya buɗe masu gidan baya, Meemah da alhaji Haruna suka shiga, yayin da Aizaad ya shiga gidan gaba driver ya ja suna nufi hanyar Maitama _Paraguay Close_ inda a can ɗin ne katafare gidan Alhaji Harunan ya ke.

Suna isa ƙofar makeken farin gate ɗin gidan driver ya danna horn, da sauri mai gadi ya wangale gate ɗin shi kuma ya cilla hancin motar ciki tare da yin parking.

Momcy da ke ɗaki tanaa jin shigowar motarsu ta yi wuf ta fito fuskan nata washe da fara'a. Bakinta ya ƙi rufuwa sai fararan haƙoranta ne a waje tare haƙorin makanta da ke ta walwali.

Aizaad ne ya soma fitowa daga gaban mota ya zagayo ya buɗewa mahaifinsa ya fito sannan Meema that looks very tired and sick don sai wani yamutsa fuska take yi. Ka tsaye Momcy ta nufe ta tare da rungumeta ta furta, "Welcome daughter, you're highly welcome my dear." ta ƙarisa maganar tare da kamo hannunta tana kallon fuskan mijinta da murmushi ta furta, "Like father like daughter!"

"Indeed!" alhaji Haruna ya faɗi yana murmushi.

"Momcyyyyy! Kamar ba ki ganni ba. Almost 3-4years ban Nigeria amma ko marmarina ban gani ba a fuskanki. You didn't even hug to welcome me." yaƙarisa maganar kamar yaro cike da shagwaɓa.

Meema sai ta samu kanta da kallonsa ta zabga masa gwalo tana ƙara damƙe hannun Momcy ɗin fuskanta cike da annuri.

Shagala ya yi da kallonta don ba ƙaramin kyau murmushi ke wa kyakkyawar fuskanta ba.

"Ayyaaa! Ai ganin ƴata ya rufe min idanu ya saka ban ganin kowa sai ita. You're welcome too. I cooked your favourite." ta faɗi hakane tana mai murɗa handle ɗin ƙofa suka shige ciki.

"A'aa! Kai tsaye mu wuce dinning don na san kun kwaso yunwa." momcy ta kuma faɗa ta nufi dinning ɗin bayan ta saki hannun Meema.

Alhaji Haruna kuwa kai tsaye bedroom ɗinsa ya wuce jikinsa har tsuma ya ke ya danna layin Baffa Ɓaleri ya kira. Ringing biyu baffa ya ɗauka. Bayan gama gaisuwa da ɗan taɓo harkan kasuwanci sai alh Haruna ya ce, "Ina da babban albishir a wajen ɗanka kuma shugaban ƙasarmu mai adalci. Kai hatta kai ɗinnan ma har da kai cikin albishir ɗin, sai dai ina mai neman alfarmar a bar ni da kaina na sanarwa Mr President albishir ɗin nan da kaina."

Baffa Belɗo gyara zama ya yi a kan kujeran office ɗinsa sannan ya ce, "Wani albishir ne wannan kuwa da na ji muryanka yana bayyanar da tsantsan farinciki a kansa?"

"Babban albishir ne da na san kun daɗe kuna jiran zuwansa." faɗin alhaji Haruna.

"Zan yi farincikin jin wannan albishir ɗin duk da ban san menene ba kuma iya hasashena na kasa hasasowa." Baffa ya faɗi.

"Idan a tsaye ka naimi waje ka zauna, idan kuma a zaune ka ke to gyara zama da kyau."

Ƙara gyara zama Baffan ya yi gabansa na faɗuwa don ya ƙosa ya ji wannan albishir ɗin.

"Jikarka da kuka jima kuna bege da mararin ganinta, wato 'ya ga Abdul-Hameed da 'yarka Zeenah tana wajena a cikin gidana yanzu haka."

Wani irin miƙewa baffa ya yi har gwiwarsa na buguwa da teburin gabansa ya furta bakinsa na rawa, "Mm....mmmai ka ce alhaji Haruna?"

Sake maitawa masa Alhaji Haruna ya yi yana murmushin jin daɗi.

"Gani nan zuwa gidan yanzun nan!" ya faɗi jikinsa har wani tsuma yake yi amma sai alhaji Haruna ya katse shi.

"Calm down Alhaji Abubakar, calm down! Ni da kaina zan kawo maka ita bar Arɗo Barkinɗo nan da awa guda kacal. Abunda na ke da buƙata kawai a haɗa min zama da Mr President ko kuma a gayyace ya zo Arɗo kamun mu ƙariso."

Baffa Ɓaleri bai iya bashi amsa ba sai ƙit ya kashe wayar ya shiga lalubar number ɗin ɗan uwansa Belɗo, wato mahaifin Mr President. Bugu biyu ya ɗaga wayar. Baffa Ɓaleri ko sallama bai masa ba ya furta, "Kazo office ɗina yanzu ka same ni." ƙit ya kashe wayar tare da soma sawa da marwa, ya kuma rasa farinciki zai yi ko kuma kuka.

Hujajan Baffa Belɗo ya shigo Office ɗin nasa ya nufo inda ɗan uwan nasa yake tsaye hankali tashe tare da faɗin, "Lafiya hamma?"

"Kwantar da hankalinka Belɗo. Lafiya ƙalau. Wani labarin farinciki nake son sanar da kai yanzu."

Gyara tsayuwa ya yi fuskansa ta faɗaɗa da farinciki tun kan wan nasa ya faɗa masa abun farincikin da ya ke ƙumshe da ita.

"Yarinyar da ta ɓace 'yar wajen Zinatu ta bayyana yau, tana can gidan Alhaji Haruna a yanzu haka."

Da sauri Baffa Ɓeleri ya kalli ƙasa ganin daga kammala magana baffa Belɗo ya kalli gabasa ya yi sujada, kawai sai shima ya bi sa su ka yi a tare. Bayan ɗagowa sai Baffa Belɗo ya faɗa jikin ɗan uwansa ya fashe da kukan farinciki. Shima baffan sai ya soma sharar hawaye.

"Ta so mu je gida mu sanar da Babiyo wannan abun farincikin. Ai zama bata gammu ba. Bari ka gani na kira Giɗaɗo, Bobbo, Lawal da Modibbo." baffa Belɗo ya faɗi tare da lalubar number ɗinsu ya shiga danna masu kira. Duk wanda ya kira kai tsaye ya ke zuwa office ɗin cike da farinciki. Baffa Lawal ɗin ne kawai bai zo sabida yana Lagos don Babiyo ya yi replacing ɗinsa da baffa Modibbo kamar yadda shi baffa Lawal ɗin ya buƙata don gani ya ke gaba ɗaya Arɗo Barkinɗo suna masa kallon laifin da mahaifiyarsa da 'yan uwansa su ka aikata.

Gaba ɗaya sun ƙi amincewa da su jira har sai nan da awa guda kamun Alhaji Haruna ya kawo Meema, sai duk suka fice daga company suka nufi gidan Alhaji Haruna.

Shi kuwa Alhaji Haruna bayan kammala wayaa da Baffa Ɓaleri sai ya fito falon, lokaci Momcy ta cika masu gabansu da kayan abinci ita da Aizaad. Ita dai Meema sai kallon tuwon shinfakar da miyan egusi ta ji namomi da ke plate ɗin Aizaad ta ke yi don ji ta ke ba za ta iya kai shi bakinta ba sabida rabonta da shi kusan 13 years kenan har ta mance da ɗanɗanonsa.

"deja de mirarme con esos ojos tuyos. ¿No vas a comer tu comida? (Ki bar kallona da waɗannan idanuwan naki. Shin ke baza ki ci abincin bane?)"

"¡Dios no lo quiera! No te estoy mirando a ti, estoy mirando tu asquerosa comida. (God forbid! I'm not looking at you, I'm looking at your disgusting food.)" ta faɗi tana mai maka masa harara.

Taɓe baki ya yi ya kalle tare da faɗin, "You should better understand that you're in Nigeria not Colombia."

"Then I want to go back to my country!" ta faɗi a ɗan hasale.

Ɗage gira ya yi tare da faɗin, "Really! Your country?" ya ƙarisa maganar yana wani shu'umin murmushi tare da cigaba da cin tuwonsa.

Marairaicewa ta yi tare da faɗin, "Please I need Sancocho or Ajiaco. Can you please find it for me?"

"No!" ya faɗi a taƙaice tare da cigaba da cin abincin.

Turo baki ta yi tare da kai hannu ta ɗan tsakuro tuwon ta haɗa da miya kamar yadda ta ga yana yi ta kai baki. Wani irin yamutsa fuska ta yi tare da haɗiyewa daƙyar tana kallonsa. Shi kuma yi ya yi tamkar bai ga abunda ta ke yi ba. To his surprise sai yaga ta janyo bowl ɗin da miyan ya ke ciki ta saka spoon tana tsince naman ciki. Sai da ta cinye tass sannan ta shanye miyan da ke ciki tare da matsar da bowl ɗin tana siɗe baki don miyar ba ƙaramin daɗi ta mata ba. A kuma wannan lokacin alhaji Haruna ya fito yana kallon dinning ɗin.

"Idan sun gama cin abincin ki kai ta ta ɗaki ta kintsa zan kaita gida saboda iyayanta na can sun zaƙu da su ganta.

Da hausa ya yi maganar shiyasa Meema bata fahimta ba duk da dai ta tsinci wasu kalmomi kamar, abinci, gida da kuma ɗaki.

Shi kuma Aizaad sam ba haka ya so ba, ya so ta ɗan yi ko da kwana uku ne a gidan kamun su kaita can gidansu.

Ita ta fara tashi daga dinning ɗin. Da sauri Momcy ta ce, "Har ta gama? Naga kamar bata ci komai ba."

Aizaad da har ya ci leda biyu ya kalli Momcy tare da faɗin, "Baza ta iya cin tuwon ba, ta dai shanye miyan da namomin tamkar wata kura. Wai sai dai na nemo mata Sancocho ko Ajiaco?"

"Kayan ƙwalama ne hakan?" momcy tatambaya

"Sancocho is soup combination of beef and pork or seafood and root vegetables usually eaten with white write or alone, while Ajiaco is three different kinds of potatoes (criolla, sabanera and pastusa), chicken, guasca leaves, with a half an ear of corn. Gashi nan dai cinsa sai su da suka saba." (for those want to see Sancocho and Ajiaco, will show you the picture in comment section.)

"To ina za a same su a nan Nigeria sai a sayo mata?" wannan karan alhaji Haruna ne ya yi maganar.

"Akwai GOPRO ko kuma Cilantro restaurant duk za a iya samu a wajen. Amma kuma ita da ta dawo ƙasarta din-din-din kamata ya yi ta saba da abincin ƙasar." Aizaad ya faɗi.

"Eh hakane! Amma kamun ta saba ɗin sai ta ci wanda ta iya ci gudun zama da yunwa." Momcy ta faɗi.

"Momcy ai ta iya cin shinkafa, taliya, maccoroni, couscous da duk wani miyan ganye. Sai ta riƙa cin waɗannan a hankali kamun ta sabaa da su ɗan wake, fate, gurasa, kunu, alala, tuwo da sauransu. Idan aka ce za a nuna mata duk abunda take son ci na can ƙasar shi za,ta,ci to fa ita da abincin ƙasarta sun yi bue-bye." Aizaad.

"Na ji! Amma for now dai a sayo mata abunda ta ke so." momcy ta faɗi.

Ita dai Meema sai kallon au ta ke yi ta kasa gane abunda suke fada sai dai ta san tabbas magana su ke yi a kanta.

"To lemme take a shower sai mu fita tare na kaita ta zaɓi abunda take so ta ci." Aizaad ya faɗi.

Harara uban ya maka masa tare da faɗin, "Ina faɗa maka iyayanta sun ƙosa shine za ka wani ce sai ka yi wanka kai gaka agwagwa ko? To duk tare za mu fita sai ka kai mu restaurant ɗin a mata takeaway daga can mu wuce gidan iyayanta."

"To shikenan Father. Bari na wanke hannu na fito!" ya faɗi tare da nufa kitchen ya wanke hannunsa sannan ya dawo ya wuce ɗakinsa ya canza kaya sharp-sharp zuwa wata jallabiya ƙalar ruwan zuma wacce ta masa kyau sosai. Ko da ya dawo falo gaba ɗaya a tsaye ya same su har momcy suna jiransu. Meema sai fama ta ke da gyalen abayarta da ya kwance tana ƙoƙarin naɗawa amma ta kasa.

Yana son taimaka mata amma yana jin kunyar idanun iyayansa. Sai kawai ya fice daga ɗakin suka rufa masa bayaa. Meema ce a baya tana kiciniya sa gyale. Ganin ta kasa sai ta ja tsaki tare da warwaresa gaba ɗaya sannan ta kai hannu ta ja zip ɗin ya buɗe gaba ɗaya ta cire ta saƙala a hannunta tamkar jaka ta cigabaa da tafiya a haka babu kuma wanda ya lura da ita. Kuma a daidai nan aka danna horn a gate mai gadi ya wangale gate sai ka motocin su baffa sun danno ciki.

(Ku yi haƙuri wallahi I'm very busy ne all this week. Gobe bikin ƙanwata.)

#Meema #Aizaad #Alhaji Haruna #Baffa Ɓaleri #Baffa Bobbo #Reunion #My Destiny #Matar Sayyadee [9/3, 5:58 AM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)

*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee

☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`