My Destiny (Ƙaddarata)

Page 74

by @matarsayyadee3

Aje ai following channel ɗina please 🙏🏼 ***

*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***

Domin shiga comment section kuma ki danna wannan link ɗin👇🏼 *** *_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining link ɗin da ke sama domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜

_*💃🏻💃🏻 _Kuna ina 'yan uwana matar aure da 'yan mata? Shela nake ko wacce ta fito domin kuwa yau na zo maku da albishiri! Kun san matar Sayyadee ta ku ce ba ta samun abun ƙaruwa ta yi shuru domin ta ƙaru ita kaɗai._💃🏻💃🏻

💐💐🌼🌼_Magana ake ta ƙamshi. Toohwa! Mai ya hwaru?_ 🤔 🌷🌷🌸💮

*To maza ku marmatso ga sirrin nan. Shahararriyar nan wacce ke inganta soyayya tsakanin ma'aura wato Fatima Zaransalaty inkiya Queen Zarah ce ta taho mana da wani ƙamshim domin cika hancinar mazajemu da ƙamshi*. _INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_ _TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA KUJI 💃🏻

_Zaran Salaaty ta yi tafiya miƙaƙƙa har Sudan domin farnata ranmu da na mazajenmu ta kawo mana Sudanese perfume👌🏻 wanda idan har kika shafa shi a jikinki ko kin yi wanka ƙamshin bai barin jikinki. Tested and Trusted ƴaruwa. Zaransalaty ba iya sudanese perfume ta kawo maku ba, akwai kayayyaki masu matuƙar inganci na gyaran HQ (kun san dai ba a wasa da headquarter) akwai kayan gyararrakin jiki kala-kala na ƴan mata da matan aure. Sannan Zaransalaty tana sai da Decoration na kayan ɗaki iri-iri wanda baki taɓa ganinsu._

_KAR IN CIKA KI DA SURUTU, KE DAI NEMI ZARANSALATY A NUMBERS ƊINTA KAMAR HAKAA_: *** Or ****

*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_nfection_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_

_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ ***** *****

Tsam Alhaji Haruna ya tsaya yana kallon motocin murmushin ɗauke a fuskansa kuma yana jinjina irin zumuɗinsu na son ganin jikarsu sabida kasa tsayawa jiran shi da kansa ya kawo ta. Motocin na gama parking ya nufe su yana dariya.

Baffa Ɓaleri har da tuntuɓe yana wauware idanun yana neman ta inda zai fara hango jikar tasa, haka ma Baffa Belɗo.

Ita kuwa Meema tana ta bayan Aizaad ya ɗan kare ta saboda juyawar da ya yi ya ganta ta cire abayar ta riƙe a hannu. Ransa a ɗan ɓace ya furta, "¿Qué es esta Meemah? ¿Podrías por favor ponerte tu Abaya? (Menene haka Meemah? Don Allah ki mayar da abayar ki saka.)"

Turo baki ta yi ta bashi amsa da turanci, "To ni na kasa ɗaura abun a kaina kuma zafi nake ji shiyasa na cire. Ba zan iya saka irin waɗannan kayan ba akwai zafi!"

Harara ya maka mata tare da faɗin, "Nan ba Colombia bane dole irin waɗannan za ki riƙa sakawa da hijjab har ƙasa."

Itama hararar ta maka masa tare da faɗin, "Ba zan saka ba, I swear to God!" tana gama faɗin haka ta ɗaura masa Abayar a hannunsa sannan ta gitta shi ta dawo ta gabansa kuma a wanna lokacin ne idanun duka Baffa's ɗin nata ya sauka a kanta.

Da idanun ta riƙa binsu musamman Baffa Ɓaleri da Baffa Belɗo. Shi Baffa Ɓaleri kamannin mamanta take gani a fuskansa, shi kuma baffa Belɗo irin yankan idanunsu ɗaya har da girarsu da ya ke a ciccike har yana haɗewa da ɗan uwansa.

Baffa Ɓaleri kuwa wani kuka ne ya ke taho masa bayan ya gama ƙarewa Meema kallo wanda ko makaho ya shafa ya san tabbas jikin Abdul-Hameed ce. Tsinuwa da Allah ya isa ya riƙa jerawa Mamiyo cikin zuciyarsa ganin jikarsa a gabansa tamkar ɗiyar arna. Zuciyasa ya shiga yi masa susa da wani irin ƙuna. Ba tare da ya shiryawa hakan ba sai kawai ya fashe da kuka ya shiga tsiyayar da hawaye.

Sai Baffa Belɗo ya dafa kafaɗansa shima ya shiga hawayen. Baffa Giɗaɗo kuwa idanunsa ne su kai jazur ya yin da Baffa Modibbo ya nufi inda Meemah ta ƙame a tsaye tana kallon kakannin nata. Baffan Modibbo na ƙarisawa kusa da ita sai jikinta ya hau wani irin rawa.

Hannunta ya kama ya taho da ita har gaban sauran kakannin nata, sai dai a gaban Baffa Ɓaleri da kansa ke a ƙasa ya tsayar da ita sannan ya furta, "Dukkan mu nan iyayan iyayanki ne. Wannan shine babban wanmu gaba ɗaya. Sunansa Baffa Ɓaleri, shine ya haifi mahaifiyarki." da turanci ya yi maganar don yanayinta kaɗai ya isa ya tahimtar da kai babu hausa a bakinta.

Baffa Ɓeleri ɗagowa ya yi ya kalli cikin idanun Meemah da jajayen idanunsa yana jin wani irin ƙaunarta da ya mamaye zuciyarsa lokaci guda. Ita kuwa Meemah da sauri ta sunkuyar da kanta ƙasa don ji ta yi idanunsa ya mata wani irin kaifi tare da shakka da tsoronsa da ya shigeta lokaci ɗaya don har ja baya kaɗan sai da ta yi. (Hoo Baffa Ɓalerinmu. Duk iskancin mutum idan ya ganka sai ya risina😜)

Baffa Modibbo ya kuma nuna mata Baffa Belɗo tare da faɗin, "Wannan kuma shine wanda ya haifi mahaifinki, daga wannan (Ya nuna baffa Ɓaleri) sai shi. Shine ɗa na biyu da aka haifa a Arɗo Barkinɗo kuma uba ga shugaban ƙasan Nigeria."

Baffa Belɗo hannu Meema ya kama tare da faɗin, "Jikana a kowani rana muna yini ne da kewa da ƙishirwan ganinki. Ashe Allah zai cika mana burukanmu kamun ya ɗauki ranmu!" yana ƙarisa maganar emotionally tare da fashewa da kukan da ya saka hatta mahaifin Aizaad, mahaifiyarsa da shi kansa sai da suka share ƙwalla.

"Muje, ku muje mu kaita wajen Babiyo ya ganta zuciyarsa ta yi sanyi. Kullum sai ya yi maki addu'a a cikin sallarsa akan Allah ya bayyanar da ke cikin aminci. Muje yau zuciyarsa ta yi fari!" faɗin Baffa Belɗo.

"Yau Arɗo Barkinɗo zai kasance cikin farinciki da aka jima ana jira. Alhamdulillah, Allah kai ne abun godiya." Baffa Bobbo mahaifin Jawaad ya faɗi.

"Ka yi mana abunda ba za mu taɓa mancewa da shi ba Alhaji Haruna. Kai da ɗanka Allah ne kawai zai biya ku abunda kuka mana. Haƙiƙa kai mutun ne nagari. Mun gode da wannan farincikin da ka saka mu yau. Iyayan yarinyar nan kwana za su yi suna maka addu'a. Yanzu zan ɗaga waya na kira His Excellency domin ka faɗa masa albishir da bakinka." wannan karan Baffa Giɗaɗo (Mahaifin Habib) ne ya yi maganar tare da fiddo wayar a cikin aljihunsa ya shiga danna numbobin Abdul-Hameed ɗin.

Meemah kuwa ji ta yi kanta ya mata wani irin gingirim. Sai ta ji kamar ma garin na juya mata kuma ta kasa fahimtar shin ita ɗin Legitimate ko Illegitimate daughter ce, wato ƴar halak ko shegiya.

Cike da biyayya Abdul-Hameed ya ɗaga kiran tare da gaishe da ƙanin mahaifin nasa. Baffa Giɗaɗo ya furta bayan amsa gaisuwarsa, "Ga alhaji Haruna investor na ABGCL (Arɗo Barkinɗo Global Company Limited) zai yi wata muhimmiyar maganaa da kai." yana gama faɗin haka sa sakan huɗu ya miƙawa Alhaji Haruna wayar.

Duk da Alhaji Harunar ya girme masa sosai amma cike da girmamawa har da wani rissinawa yake gaishe da His Excellency kasancewarsa shugaban ƙasar Nigeria. Shima daga can ɓangaren da girmamawa ya ke mayarwa Alhaji Haruna da gaisuwar.

"Ranka ya daɗe idan kana tsaye ne ka nemi waje ka zauna, idan kuma kana zaune ne ka gyara zama da kyau domin wani albishir gareni da zan faɗa maka wanda na san a wajanka babu wani albishir da ya kaisa farinciki daga ciki kuwa har da sanarwa da akai cewar kai ka lashe kujerar takarar shugaban ƙasar Nigeria."

A take jikin Mr President ya hau rawa. Daga shi sai P.A ɗinsa a cikin katafaren office ɗinsa da ke cikin Villa. Bai jima da gama waya da Zee-meed ɗinsa ba baffa Giɗaɗo ya kira sa a wayaa. Ji ya yi miyau ɗin da ke bakinsa yana ƙafewa. Don duk duniya albishir ɗaya za ai masa a yanzu da zai ji babu kamarsa, shine a faɗa masa Meemah ta bayyana a ƙasar Nigeria. Ji ya yi ya kasa furta ko kalma ɗaya sai zuciyarsa da ke wani fat-fat-fat.

Daga can ɓangaren kuwa, alhaji Haruna ya fahimci halin da Mr President ɗin ya ke ciki sai ya cigaba da magana, "Abunda ka jima kai da matarka kuna mararin gani na tare dani a yanzu haka. 'Yarka Meemah tanaa gidana tare da iyayanka. Ka same mu a family House ɗinku yanzu haka can za mu tafi wajen Babiyo."

Wani irin miƙewa tsaye ya yi jikonsa na wani irin karkarwar da ya baiwa PA mahaukacin mamaki don ya san mawuyacin abu ne wani abu ya gigita Mr President haka saboda tsananin juriya da danne kansa, amma yau ɗaya ya ga ƙwalla a idanunsa da kuma wani irin shauƙi. Don ajiye wayar ya yi akan tabur tare da fitowa sarari ya kalli gabas sannan ya yi sujada. Ya jima kansa a ƙasa yana hawayen farinciki kamun ya ɗago. Yana ɗagowa ya ɗaga hannu samaa tare da faɗin, الْحَمْدُ للهِ الَّذِي بِنِعْمَتِهِ تَتِمُّ الصَّالِحَاتِ .

P.A sai murmushi ya ke yi don yasan ba ƙaramin abun farinciki Mr. President ɗin ya ji ba.

"Ka je ka faɗawa securities su shirya mota zan tafi Arɗo Barkinɗo yanzun nan." HiscExcellency ya faɗi bayan ya miƙe tsaye daga sujudul shukur ɗin da ya yi.

Da sauri P.A ya fice daga office ɗin bayan ya furta, "Yes sir!"

Abdul-Hameed jikinsa har wani tsuma ya ke yi wajen lalubo number ɗin da ya yi saving da Queen of my heart ya danna kira. Ringing biyu Zeenah ta amsa kirar tare da karawa a kunne ta yi sallama cikin sanyayyiyar muryan da ta koya tun lokacin da ta tuba da bariki.

"Ameen wa'alaikissalam sarauniyar zuciyata. A kullum muryanki ta daki kunnena ji nake kamar ana mun busar sarewa. Muryanki kawai idan ta daki kunnuwata ɗimautani ta ke yi."

Murmushi mai sanyi Zeenah ta yi tare da faɗin, "Shiyasa sam ban nesa da wayata don na san a rana idan baka min kira goma ba to za ka yi ashirin. Ko mintuna talatin ba mu yi da gama waya da kai ba ka sake kira. Ni ma kuma ban taɓa gajiya da jin daddaɗar muryanka da ta fi na kanari zaƙi. Duk lokacin da raina ya ɓaci ko na shiga tashin hankali, da na tuna ina da kai sai inji zuciya ta wanke tare da jin ƙwarin gwiwar cigaba da numfashi. Duk daƙiƙa ɗaya na bugun numfashina da sunanka ya ke bugawa!"

"Ina da gaggarumar tukuici game da wannan daddaɗar kalaman naki. Tukuicin da zai saka ki faricikin da sai kin zubar da hawaye. Shin kin shirya amsar wannan tukuicin?" Abdul-Hameed ya faɗi fuskansa bayyane da zallar farinciki da annashuwa.

Zeenah a kwance take akan makeken gadonta, bata san lokacin da ta miƙe zaune ba gabanta na bugawa duk da kuwa bata san wani tukuici mijin nata zai mata ba. Sai cewa ta yi, "A shirye nake domin na tabbata tukuici indai daga wajenka zai fito to abu ne mai tsayawa a rai tare da sanya shauƙi da annashuwa."

Murmushi ya kuma yi mai sanyi sannan ya ce, "Tukuicina na daban ne, idan na bada ni ma sai an ba ni wani abu in return."

Cikin taɗa Zeenah ta furta, "Zan dage a daren yau na yi wa su Muhaysim ƙanwa, shin hakan ya yi?" ta ƙarisa maganar tana kashe idanu tamkar dai Laushin da can. (😂🤐 ba ruwana kada Mr president ya saka a nemo ni a garƙame ni)

His Excellency wani siririn dariya ya yi tare da shafo ƙeyarsa sannan ya ce, "Na gamsu da wannan tukuicin. Allah dai ya miki albarka! Ki shirya gani nan zuwa zamu fita zuwa wani waje yanzu."

"In sha Allah!" Zeenah ta faɗi tana ƙoƙarin sauka daga kan gadon.

"I love you, sai na ƙariso." ya faɗi tare da hura mata kiss.

"I love you too!" ita ma ta mayar masa tare da hura masa kiss ɗin sannan ta yanke kiran.

Can gidan alhaji Haruna kuwa, gaba ɗaya su Baffa suka shiga motocinsu domin zuwa family house. Father, Momcy, Meemah a mota ɗaya suka zauna yayin da Aizaad ke driving. Sai da suka soma zuwa Resturant suka sayawa Meemah Sancocho tukun sannan suka nufi Arɗo Barkinɗo Estate.

Sosai Estate ɗin ya ƙara shan gyaran da sabon fentin da ake masa duk shekara. Wannan karan ma farin fenti da ratsin ash colour akai wa kafatanin Estate ɗin. Masallaci da gidan Babiyo ne kawai ya kasance fari ƙal babu ratsin ko wani kala a jiki tun daga wajen gidan har ciki. Furnitures ne kawai suka kasance Emerald green.

A katafaren farfajiyar Babiyo su kai parking, motar da su Aizaad ke ciki ne ƙarshen shigowa saboda sune a baya. Meemah ce ta soma ɓalle murfin mota ta fito tana gyara zaman straight skirt ɗin jikinta saboda karkacewar da ya ɗan yi. Aizaad sai harararta ya ke yi yana addu'ar ta ɗago kai ta kallesa domin ya nuna mata abayarta da ke ajiye a kujeran gaban mota da ta tashi ko Allah zai saka ta gane ta saka, amma inaa Meemah bata ma san mai ya ke yi ba. Hannu ma ta kai wajen high neck bodyhug ɗinta tana gyarawa. Ɗaga hannun da ta yi sama ba ƙaramin ƙara bayyanar da bayyananniyar kyawun dirin jikinta da Allah ya yi mata ba. Kayan sosai ya fidda shape ɗin jikinta. Domin hatta well curve bra ɗinta ana ina, hangosa ɓaro-ɓaro, haka hip ɗinsa da ke cikin straight skirt tamkar ita tai kanta.

"Wai kai baza ka fito bane? Mu fa suke jira gasu can tsattsaye!" Momcy ta faɗi lokacin da ta ɗan duƙa daidai window ɗin da Aizaad ke gefen.

Ɓalle murfin ya yi ya fito yana mai jin matsanaicin kunya idan ya kalli Meemah cikin wannan shiga. Jerawa su kai har inda su Baffa su ke sannan gaba ɗaya suka nufi ainahin part ɗin Babiyo.

Baffa Ɓaleri sai satan kallon Meemah ya ke yi yana ɗan tsoki a zuciyata tare da tsinewa rainon yahudawa.

"Gaskiya yarinyar kin shigo da ƙafar dama. Da ace a da kika shigo Arɗo Barkinɗo lokacin Babiyo na, Babiyon cikin wannan shiga da tabbas sai an yi ƙaramin yaƙi billahil lazi. Don irin guguwar tashin aljanu a filin saharar da zai faru a fadar Babiyo Allah ne kaɗai zai iya tsagaita shi. Don ni na ga kaina matsayin korarre sau dubu billahi!" baffa Ɓaleri ya faɗi ciki-ciki.

"Ko kuma a ɗaura maka aure da 'yar cikinka ba!" baffa Giɗaɗo ya faɗi yana dariya ƙasa-ƙasa don sarai ya ji abunda Baffa Ɓalerin ya faɗi.

Dariya Baffa Ɓaleri ya yi tare da faɗin, "Shiyasa naga kai da aka maka hakan matar ta yi haihuwa huɗu ga cikin na biyar na ya kusa zuwa duniya. Tsabar zari har gwarne ka ke yi! Gaskiya Giɗaɗo a gaishe ka."

Wannan karan sosai sautin dariyar Baffan Giɗaɗon ya fito don sai ya tuna cikin farko da Mardiyya ta yi ba ƙaramin ɓoye-ɓoye suka riƙa yi ba tamkar cikin shege. Gwara shi sau dubu ma a kan uwar gayyar wato Marwanatu. Don har sai da jininta ya hau tsabar fargaba da kunya. Yanzu kuma komai ya wuce kamar ba ai ba. Soyayya a gaban uban kowa gwada masa take yi don wani lokakin ma mugun mamaki yake ji idan ta yi wani abun tamkar ba wacce aka riƙa kai ruwa rana da ita ba. Sai dai abunda ke saka shi farinciki da ita shine tsantsan biyayyarta a gare shi da kuma uwar riƙonta wato matarsa Mama Halima.

Sallama su kai sannan suka murɗa handle ɗin ƙofar suka shiga. Zaune ya ke a kan Wheel chair saboda ƙafarsa da bai iya takawa ya yi tafiya sam, ko a cikin falonsa bare kuma waje. Sallah ma yanzu ya daina ja a masallaci, amma kuma har yau bai daina zuwa masallaci yin salloli biyar ɗinnan ba. Hasken ibada ne ya saka har yanzu jikinsa da ɗan ƙarfi. Idanunsa ras yake gani, haka haƙoransa ko guda ɗaya bai fita ba. Sai dai tsufansa sosai ya fito kuma jikinsa ya ɗan tattare. Remote ne a hannunsa yana kallon labaran da ake nuna wa tashar NTA kuma duk akan cece-kucen da wasu jama'ar suke yi ne akan His Excellency Abdul-Hameed da matarsa da ake ta cewa karuwa ce kuma 'yar safarar miyagun ƙwayoyi sannan bugu da ƙari yana da ɗiya wacce ba da aure shi da matarsa suka haifa ba. Murmushi ya yi mai sauti lokacin da ya ke ji da kallon hirar da Abdul-Hameed ya yi da BBC ɗin.

Su Baffa shuru su kai tun sallamar farko da ya yi suka amsa sai suka samu waje suka zauna suna jiran ya kammala sauraran abunda ya ke kallo a TV ɗin.

Sun kwashi mintuna talatin suna zaune zaman jira kamun Babiyo ya miƙa remote ya kashe TV yana murmushi sosai wanda ke nuni ga ya ji daɗi sosai da amsar da Abdul-Hameed ɗin ya baiwa duniya. Juyowa ya yi ya shiga kallonsu ɗaya bayan ɗaya kamun ya sauke idanunsa a kan Meemah ko ƙyaftawa babu. Meeman ma kallonsa take yi cikin idanu ganin kamannin wanda aka ce mata shine mahaifin mummynta tamkar ya yi kaki. Ita ta fara yin ƙasa da kanta sannan cikin harshen turanci ta furta, "Good afternoon sir!"

Jinjina kai kawai ya yi sannan ya mayar da kallonsa izuwa kan alhaji Haruna suka gaisa don ya sansa farin sani saboda Investor ɗin shi ne na kamfaninsa wanda shine na ɗaya kaf Nigeria don babu abunda kamfanin bai yi.

Aizaad ma gaishe sa ya yi cike da ladabi kamar yadda iyayansa su ka yi da kuma su baffa. Sai dai idan ka cire Alhaji Haruna da matarsa kaf sauran da kai ya amsa masu gaisuwar yana ƙara mayar da idanunsa akan Meemah kamun ya furta, "Ita wannan kuma fa? Duk da na sani kuma ina ji a jikina zuri'ar gidan nan ce amma mai yasa na ganta babu kaya kuma har kuka iya kawota gabana a haka. Shin har lalacewar tawa ta kai haka?" Babiyo ya faɗi yana mai mayar da idanunsa a kan su Baffa.

*_VILLA_* Tana saukowa daga kan gado ta mufi wajen madubi ta gyara fuskanta kasancewar ta yi wanka. Role on mai matuƙar tsada ta shafa sannan ta fesa bodyspray kaɗan saboda fita za su yi. Gaban closet ɗinta ta zaro wata ɗanɗasheshiyar less kalar fari mai ratsin dark green. Ɗinki doguwar riga ce ta ji stone work tun daga ƙasa har sama. Bayan ta gama sakawa sai ta kalli kanta a madubi tare da sakin murmushi don fitowa ta yi tamkar wata yarinyar yar 25 bayan kuma shekarunta na haihuwa 41 ne cif, don ko Meema a yanzu shekarunta 24 da haihuwa. Gyale babba ta ɗauko dark green ta yafa, haka takalminta ma dark green ne mai ma matsakaicin tudu na kamfanin Calvin Klein.

Ƙofa ta nufa ta buɗe tare da soma saukowa zuwa ƙasa daidai lokacin da His Excellency ke haurowa zuwa ɗakinta. Cak ya tsaya yana kallonta don ba ƙaramin kyau ta yi masa ba sosai. Wani murmushi ta sakar masa da ya kusan tsayar da bugun numfashinsa, ji ya yi kamar iska ta ɗauke shi don kawai ganinsa ya yi a gabanta ya riƙo hannunsa yanaa kallon ƙwayar idanunta. "A kullum ƙara kyau da zama very young kamar 'yar sha takwas kike yi a wajena wallahi. You look very very pretty Zee-meed."

Wani juya idanu ta yi (irin na 'yan bariki 🤐😂) tare da furta, "Really?"

"Goodness! Allah kwalliyar nan za ta ɓaci yanzun nan. Kin san fa ni ban sanya wajen kashe arna." ya faɗi yana mai jawo ta jikinsa sosai.

"Don Allah ka yi haƙuri kar ka ɓata min kwalliyata!" ta faɗi da wani salo na shagwaɓa da ya kusan zautar da tunanin His Excellency. "I need water!" ya faɗi yana kama maƙogwaransa har da ɗan tarinsa.

Hannunsa ta kama suka koma bedroom ɗinta. Ɗan ƙaramin fridge ɗin da ke ɗakin ta buɗe ta fiddo bottle wata ta buɗe tare da kaiwa bakinta ta gumtsa sannan ta matsa daf da shi ta karkato da kansa ta juye masa ruwan kaf a bakinsa ya shanye. Kuma dama ta san abunda ya ke so kenan shiyasa ya ce he need water. Sai goran ruwan ya yi rabi sannan ta rufe tare da faɗin, "Na san dai ka ƙoshi!"

Marairaicewa ya yi tare da faɗin, "Ina son ƙari."

Lakuce masa hanci ta yi tare da zame suit ɗin jikinsa ta tayasa unbottuning shirt ɗinsa ta cire.

"Malama ba wanka zan yi ba, kaya kawai zan canza don ni kaina a ƙage nake na son nuna miki wannann tukuicin."

"Ni ma haka Lovey-Dovey, amma ban san mai yasa ƙirjina ke bugawa ba." ta faɗi a marairaice.

Kunnensa ya ɗaura a Ƙirjin tare da faɗin, "Kai! Saurara ka daina ɗagawa matata hankali. Abun alkhairi da farinciki za ta gani a yau ɗinnan." yana gama faɗin haka ya ɗago ya kalleta yana nuna mata closet da idanu.

Wajen ta nufa tare da ɗauko masa shaddarsa fara ƙal sai maiƙo take yi ta ji ɗinki mai ɗaukar idanu. Ita ta taimaka masa ya saka sannan har links sannan ya kallesa tare da janta zuwa wajen mirror ya yi masu hoton nan da ake yi ta gaban mirror da tsadaddiyar iphone ɗinsa. Ba ƙaramin kyau su kai ba. Sai suka fito tamkar wasu yara.

"Ina su Muhaysim?" ya faɗi yana saka takalminsa half cover farare ƙal.

"Suna Barkinɗo Estate wajen mama (tana nufin mahaifiyarta)."

Gyaɗa kai ya yi tare da faɗin, "Mu ma Barkinɗo za mu je yanzu ai!"

Rass! Gabanta ya kuma bugawa da ƙarfi amma kuma bata ce komai ba kuma ta yi ƙoƙarin calming kanta don kar ya fahimci halin da take ciki.

Tare suka jero suka sauko har babban falon da ke ƙasa wanda a nan ɗinne za ka bi hanyar corridor ɗin da zai kai ka sama sashen Queen Elizabeth wato the only first Lady of Mr President.

"Wait for me here, will be back in lessthan 10minutes." ya faɗi yana shafa kumatunta.

Gyaɗa masa kai ta yi tare da masa murmushi shi kuma ya nufi hanyar da za ta sada shi da ɗakin Hajiya Asma'u uwargida a wajen His Excellency.

Knockin ya yi a ƙofar ɗakinta sannan ya harɗe hannu yana jiran ta zo ta buɗe masa ƙofa. Sai da ta kwashi mintuna biyar yana tsaye sannan ta taho ta buɗe a yangance. Ta ci uban kwalliya cikin arniyar shadda ƙalar maroon da ya sha ɗinkin kece raini. Ɗaurin ɗanƙwalin nan ya zauna a kanta ɗas-ɗas kana iya hango gashin dokin da ta saka daga ta ƙeyarta wanda ta yi parking ɗinsa da ribbon.

"You're highly welcome your Excellency!" ta faɗi tana murmushi tare da masa kallon ƙasa-ƙasa don ba ƙaramin kyau ya yi mata ba, take lokaci guda wani irin kishi ya turniƙeta tamkar zuciyarta za tai bindiga.

Danne zuciyarsa ya yi ya shiga ɗakin saboda wani irin haushi da takaicinta da ya ke ji. Mutunci da girman mahaifinta da ya ke gani ne ya hana shi sakinta tuntuni. Amma wannan karan ta yi crossing limit ɗinta shiyasa ya ke son furnishing ɗinta to the extent da sai ta tsuguna tana roƙonsa ya sake ta ta tafi gidan ubanta.

"Na ganki cikin shiri har da gyale, ina zuwa haka da yamman nan?" ya faɗi yana ƙare mata kallo. Ɗinkin skirt da riga ta yiwa shaddar kuma ya kamata sosai duk da siririya ce tamkar za ta ɓalle. Gashi ta saka rigar mama irin push up ɗinnan, fuskan nan tasha uban make-up kamar za ta gasar kyau.

Murmushi ta yi a yangance tare da faɗin, "School zan shiga. Ina da class amma test kawai zan basu in karɓi attendance in dawo gida. Don ina son mu tattauna game da wancen tsinanna gidan redio da suka fitar da zancen ƙaryar nan tare da ambatan sunana don kawai su ga sun ture gwamnatina a wajenka babu kuma ƙaryansu don ni da kai till death apart us."

"Hakan na da kyau! Sai dai ni ban da lokacin jin shashanci magana akan gidan redio. Ki tabbatar magrib a gidana ta miki, zan fita zuwa Family house yanzu!" ya faɗi yana kallon agogon hannunsa.

Wani irin duum tamkar saukar aradu maganarsa ta yi mata. Dom tun da suke bai taɓa bata lokacin da za ta dawo gida ba idan za ta fita ba sai yau. Sai ta ji duk ta muzanta tamkar a idanun duniya ta faɗi haka. Ita fa ko fitar ba faɗa masa take ba sai dai ta fice tare da convoy tana feeling ita matar shugaban ƙasa. Tana daga cikin matantan masu nuna Feminism a cikin gidansu. Ji take da ita da mijin ɗaya suke. Bata taɓa girka masa ko ruwan tea ba bare kuma abinci, gaisuwa idan bai gaisheta ba bai isa ita ta buɗe baki ta gaida shi ba. Wani irin girman kai da tsantsan jahilci ke damunta. Kuma ba dai don bata samun tarbiyya ba, daidai gwargwado iyayanta sun bata, sai dai ita ɗin rayuwar turawa da al'adunsu ta ɗaurawa kanta.

"What did you mean, your Excellency? Yau ni ce ka ke baiwa lokacin da zan dawo gidan nan kamar wata 'yarka? No no no no.. Don even start that bullshit!. Yaushe mu ka fara hakan da kai? Ni na taɓa tambayanka ina za ka je, yaushe za ka dawo ko kuma daga ina ka ke? Babu wanda zai takura min wallahi! Idan ita (tana nufin Zeenah) ta zauna kana juya ta sabida bata san ciwon kanta ba ko kuma tana tsoran saki sabida ta san ba wanda zai auri ragowar ƙazaman Lagos ni ba zan......."

Wani haɗaɗɗan marin da ya ɗauke ta da shi ne ya hana ta ƙarisa sauran maganar da ya maƙale mata sakamakon gigicewar da ta yi.

Da hannu ya nuna ta tare da faɗin, "Sau ɗaya tak idan ƙazamin bakinki ya kuma zagar min uwar 'ya'yana sai na miki shegen duka na kora ki gidan ubanki. Wawuya sakarya!"

Ja da baya ta yi gabanta na faɗuwa saboda yadda idanunsa suka sauya tamkar na zaki ga su sun canza launi zuwa jajur har maiƙo-maiƙon suka yi alamar zallar ɓacin ran da ya ke ciki.

A cikin zuciya ta riƙa ɗurawa Zeenah da shi kansa Abdul-Hameed ɗin zagi tana ayyana irin rashin mutunci da tozarci da za ta yi masu su duka biyun na ɗaukar fansa yatsunsa biyar da ya ɗaura a fuskanta da kuma gorin rashin haihuwar da ya mata a kaikaice.

"Ni ka ke gorantawa akan rashin haihuwa Abdul-Hameed?" ta faɗi tana mai fashewa da matsanaicin kukan makirci.

"An miki gorin ki yadda za ki yi! Kin haihu ɗinne? Ke Allah ne ya rufa miki asiri ma da bai baki haihuwar ba don ba ƙaramin sakaryar uwa za ayi ba. Don baki da tarbiyar da za ki iya ba wani." ya faɗi a hasale.

"Eh! Shiyasa naga ita 'yar gwal ɗin taka da tana tafiya tarbiya na zuwa ta haihu a gidan karuwai, ɗan daudu ya yiwa yarinyar wanka tare d huɗuba ya raɗa mata suna ta kuma tashi a gidan karuwai tanaa kallon yadda maza ke kwanciya da mahaifiyarta a gabanta tare da shaye-shaye da sai da miyagun ƙwayoyi. Duk cikin tarbiyar ce ai!"

"Asma'uuuu!" ya faɗi da ƙarfi tare dashaƙar wuyarta ya haɗa da bango tamkar zai kasheta. Sai zazzare idanu ta ke yi tana ƙoƙarin janye hannunsa amma ta kasa sabida ƙarfin ba ɗaya ba. Sosai ta yi matuƙar tsorata don ta sadakar kasheta Mr President zai yi.

"Zan iya kashe ki a nan ɗakin kuma in binne gawarki babu abunda zai faru! Wallahi tallahi wa billahil azim idan bakinki ya kuma faɗin mummunar kalma a kan matata sai kin yi dana sanin haihuwarki da uwarki ta yi. Banza 'yar iskar mata!" ya ƙarisa maganar tare da cilli da ita ƙasa sannan ya taka ƙafarta ya fito daga ɗakin yana huci.

Kallo ɗaya Zeenah ta masa ta fahimci yana cikin ɓacin rai mai tsanani don yana isowa inda ta ke hamnunta kawai ya kama bayan ya maƙale glasses ɗinsa baƙi da ke ɓoye ƙwayar idanunsa. Motocine kusan guda ashirin a ƙofar part ɗin suna jiran isowarsa. 'Yan sanda ne da sojoji jibge a tsaye kuma a ƙame tamkar babu rai a jikinsa.

Da sauri wani ɗan sanda ya taho ya buɗe masu ƙofa suka shiga bayan sun sara masu daga soldiers ɗin har mopols ɗin sannan suka rufe motar kowa ya shiga nasa motar sannan suka tada motar tare da ƙoƙarin barin Villa.

A cikin motar ma hannun Zeenah na cikin na Abdul-Hameed. Ɗayan hannunta ta yi amfani da shi ta soma shafa hannunsa da ke kamanta nata alamar calming ɗinsa har suka hau titi. Siring ɗin da ke tashi gaba ɗaya ya cika masa kunne yana ƙara tunzura fushinsa. Magana ya yi wa soldier ɗin da ke gaban mota akan a kashe. Cikin second goma komai ya yi tsit.

A hankali cikin tausasshiyar murya kuma cike da hikima da gogewa a barikin da ta taɓa yi (Allah ka raba mu da rayuwar bariki mu da zuri'armu da musulman duniya baki ɗaya. Wanda suke cikinta kuma Allah ya shirya su su dawo kan hanya) ta shiga furta masa daɗaɗan kalaman da ya sanyaya zuciyarsa har ya samu natsuwa fushin ya yaye duk da kuwa bata san ainahin abunda ya ɓata ran nasa ba, amma dai ta san bai rasa tsakaninsa da matarsa ce don daga can ya fito da ɓacin ran.

Baffa Ɓaleri ne ya soma magana kasancewarsa babba a wajen, "Kai mana aikin gafara Babiyo, yau ta dawo Nigeria daga can ƙasar da take zaune. Muna yanzu muka san da dawowarta daga bakin alhaji Haruna shine muka tafi can gidan nasa domin mu je mu ɗaukota mu kawo ta nan wajenka. Ƙaguwa ce ta samu mancewa mu sayo mata hijjab a hanya kamun isowarmu nan ɗin gudun kar mu yi maka laifi."

Jinjina kai Babiyo ya yi tare da faɗin, "Wannan ba 'yar wajen Abdul-Hameed ba ce Musulima? Shine ta ke min turanci maimakon Fulfulde? Kuma ban gane maganar da kuke min ba ku fito dalla-dalla ku yi min bayani."

Baffa Belɗo ya amshe maganar, "Babiyo wannan ba Muslimat ba ce, ɗiyar Hameed ce da muka ɗau shekaru muna bege da fatan ganin ta ta dawo gare mu. Ita ce yarinyar da Zeenatu da Abdul-Hameed suka haifa sakamakon abunda Mamiyo ta aikata masu. Yau suka dawo daga Colombia ita da ɗan wajen alhaji Haruna.

Babiyo da sauri ya mayar da idanunsa a kan Meemah idanunsu sun kaɗa sun yi jazur, hannu ya kai kan idanunsa ya sharce gundun hawaye sannan ya miƙawa Meemah hannu ya furta, "Come here my great grand daughter!"

A hankali Meema ta miƙe jikinta na ɗan rawa-rawa don ji ta yi idanunsa sun fi na wanda aka nuna mata matsayin kakanta kaifi da kwarjini. A gaban wheel chair ɗin da ya ke zaune ta zauna a ƙasa haka kawai wasu zafafan hawaye suka shiga kwaranyo mata suna ɗiga a ƙasa.

Hannu ya kai ya dafa kafaɗunta tare da faɗin, "Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah! Ashe zan ga wannan ranar kamun Allah ya ɗauki rayuwata? Allah nagode maka da ka sada ni da ɗiyar Abdul-Hameed kamun ƙasa ta rufe min idanu. Ni ne nan na haifi wanda ya kawo ubanki duniya tare da Maimunatuna. Ki yi haƙuri da zuwanki ta gurɓatacciyar hanya a gidan duniyar nan. Allah shi yasan dalilin haka, amma ina so saka a ranki ni nan kamun Allah ya ɗauki rayuwata zan tabbatar na inganta rayuwarki ta kowacce fuska. Allah ya miki albarka." yana faɗin haka ya mayar da dubansa ga Baffa Ɓaleri tare da faɗin, "Ka faɗawa kowa na gidan nan akwai meeting zuwa anjima bayan isha'i."

Yana kammala faɗin haka motocin su Abdul-Hameed na parking. Kashe Siring ɗin da ya saka aka yi ne ya hana mutanan ciki gane isowarsu. Da gudu aka buɗe masu mota suka fito tare da jerawa suka nufi hanyar part ɗin Babiyo.

Security ɗaya shi ya zo da gudu ya murɗa handle ɗin kofar daidai lokacin da Abdul-Hameed ɗin ya zabga sallama. Gaba ɗaya mutanan da ke zaune a falo suna ɗago tare da zubawa ƙofar idanun suna mai amsa sallamar. Meema kuwa ƙur ta kafe shi da idanu tana jin wani matsanaicin kuka na son kufce mata don tamkar photocopy ɗinta take kallo. Zeenah ce ta kutso kai ta shigo kanta a ƙasa tare da rage tsayinta gabanta na wani irin bugawa wanda ta rasa ko na menene. Daƙyar ta iya buɗe baki ta gaida mutanan falon.

Da wani irin zumuɗi da shauƙi tare da kewa Meemah ta miƙe tsaye ta furta, "Aunty Laushiiiiiii!"

Wani irin ɗagowa Zeenah ta yi tare da miƙewa tsaye tana kallon Meemah idanunta a waje. Tsikar jikinta wani irin miƙewa ya shiga yi yayin da ta ke kallon ɗiyarta tamkar a mafarki tana tsiyayar da hawaye kuma lokaci guda bakinta da jikinta na wani irin rawa.

Da gudu Meemah ta faɗa jikinta taƙanƙame tare da faɗin, "Mummyyyy!" ta rushe da wani irin matsanaicin kuka mai tada hankalin mai sauraro.

Zeenah ƙanƙame 'yarta ta yi don ji ta ke tamkar mafarki ta ke yi ita ma ta shiga rera kuka mai sauti......

#Meemah #Zeenah #His Excellency #Queen Elizabeth #Babiyo #Baffa Ɓaleri #Aizaad #Reunion #My Destiny #Matar Sayyadee *** [9/4, 8:49 PM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)

*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee

☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`