My Destiny (Ƙaddarata)

Page 75

by @matarsayyadee3

Aje ai following channel ɗina please 🙏🏼 ***

*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***

Domin shiga comment section kuma ki danna wannan link ɗin👇🏼 *** *_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining link ɗin da ke sama domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜

_*💃🏻💃🏻 _Kuna ina 'yan uwana matar aure da 'yan mata? Shela nake ko wacce ta fito domin kuwa yau na zo maku da albishiri! Kun san matar Sayyadee ta ku ce ba ta samun abun ƙaruwa ta yi shuru domin ta ƙaru ita kaɗai._💃🏻💃🏻

💐💐🌼🌼_Magana ake ta ƙamshi. Toohwa! Mai ya hwaru?_ 🤔 🌷🌷🌸💮

*To maza ku marmatso ga sirrin nan. Shahararriyar nan wacce ke inganta soyayya tsakanin ma'aura wato Fatima Zaransalaty inkiya Queen Zarah ce ta taho mana da wani ƙamshim domin cika hancinar mazajemu da ƙamshi*. _INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_ _TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA KUJI 💃🏻

_Zaran Salaaty ta yi tafiya miƙaƙƙa har Sudan domin farnata ranmu da na mazajenmu ta kawo mana Sudanese perfume👌🏻 wanda idan har kika shafa shi a jikinki ko kin yi wanka ƙamshin bai barin jikinki. Tested and Trusted ƴaruwa. Zaransalaty ba iya sudanese perfume ta kawo maku ba, akwai kayayyaki masu matuƙar inganci na gyaran HQ (kun san dai ba a wasa da headquarter) akwai kayan gyararrakin jiki kala-kala na ƴan mata da matan aure. Sannan Zaransalaty tana sai da Decoration na kayan ɗaki iri-iri wanda baki taɓa ganinsu._

_KAR IN CIKA KI DA SURUTU, KE DAI NEMI ZARANSALATY A NUMBERS ƊINTA KAMAR HAKAA_: *** Or ****

*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_nfection_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_

_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ ***** *****

Abdul-Hameed da ke can kusa da ƙofa sunkuyar da kai ya yi yana tsiyayar da hawaye, haka ma su baffa, Momcy da alhaji Haruna. Aizaad ma idanunsa ne ja su ka yi sai ya sunkuyar da kai ƙasa. Yayin da Babiyo ya kafe su da idanu feeling guilty don ji ya ke shine sanadin duk wani abu da ya faru da iyalan nasa.

Zeenah da ke rungume da 'yarta ji ta yi numfashinta na neman ɗaukewa sannan ƙafafunta na neman gaza ɗaukarta. Abdul-Hameed shi ya fara lura da hakan ya yi saurin ƙarisawa inda suke a tsaye ya riƙo Zeenah tare da rabata da jikin Meemah da kyar dan riƙe junansu su kai sosai sannan ya zaunar da ita akan ɗaya daga cikin kujerun ɗakin ya hau yi mata fifita da ƙasan rigarsa.

Meemah kuma gefen da mamanta ke zaune ta zauna tare da riƙo hanmunta ƙam don ji ta ke tamkar wani zai ƙwace mata ita. Babu abunda ke fitowa daga idanunsu sai hawaye. Burin Zeenah shine ta keɓe da 'yarta domin tai mata wasu tambayoyi game da rayuwar da ta yi a can ƙasar Colombia.

Baffa Ɓaleri ne ya yi gyaran murya tare da faɗin, "Koke-koken ya isa haka Zeenatu. Ba ta haka ya kamata ki godewa Allah ba da ya sake haɗa ki da ƴarki da ki ka cire rai da sake ganin ta ba. Ba na son wannan koke-koken yana ɗaga min hankali ba ni kaɗai ba har da sauran 'yan uwana gasu nan."

"Bar su, bar su su yi kuka Abubakar! Kukan farinciki suke yi. Ni kai na ji na ke tamkar na fashe da kukan! Ka mance irin kukan da kai min ne lokacin da na kira ka dawo Arɗo Barkinɗo? Ko kuma mancewa ka yi da lokacin da 'ƴan uwanka ga su nan suka rungume ka kuna ta kuka a gabana har da na kewar mahaifiyarku? Ka barsu su yi kuka wani nauyine ke raguwa a zuciyarsu. Sai daga baya na ganr tabbas zubar da hawaye ma ni'ima ce da Allah ya yiwa ɗan Adam. Yi kuka Zeenah, Farida ke ma yi kuka!"

Aikuwa kamar ya zuga su suka cigaba da rusa kuka tamkar an yi mutuwa. Sai da suka gaji don kansu sannan su kai shuru suna shassheƙa. Luran da Babiyo ya yi nauyin ya ragu sosai a zukatansu sai ya danna forward a wheelchair ɗinsa ya ƙariso gaban Zeenah da Meemah ya tsaya tare da kallon Meemah sannan ya furta, "Ba komai na ke so a tattauna a wajen meeting game da lamarinki ba, shiyasa na ke son yanzu a gaban mu ɗinnan kawai ki faɗa mana tarihin rayuwar da kika yi tsayin shekaru goma sha uku a ƙasar Colombia domin na yi tankaɗa da rairayen abunda sauran 'yan uwa ya kamata su ji da wanda bai kamata ba su ji ba." da rayen masu jajayen kunne ya yi maganar kasancewar bai jin spanish.

Meemah ta ɗago ta kalli kakan maman nata tare da share guntun hawaye sannan ta buɗe baki ta soma ba su labari tiryan-tiryan tun lokacin da Adelberto ya miƙa ta a hannun Esmeralda, rayuwar cikin cage ɗin da ta yi da su Leo da Issabella, videon mahaifiyarta da aka nuna mata na mahaifiyarta tana karɓan kuɗin cinikinta da ta yi da kuma sharaɗin da Esmerald ta bata na mata aiki tsayin shekaru goma sha kamun ta samu freedom, training da aka musu na harbin bindiga, faɗar hannu da kuma sarrafa cocoaine da yadda za su iya fitar da suzuwa wata ƙasa a jirgi ko a mota ba tare da an cafke su ba. Kashe Carlos mijin Issabella da Alajendro ya yi bisa umarnin Esmeralda, aikin da Esmeralda ta saka Meemah ta yi saboda ceton Issabella da ɗanta Nicolas, kashe ta da ta yi bayan ta saka ta haɗiye Cocaine da kuma farka cikinta da ta yi har izuwa kamun da Aizaad ya mata da labarin da ta bashi, guduwa da ta yi daga wajensa bayan sumar da shi, haɗawa Esmeralda plan ɗin da aka kamata aka kasheta, yadda ta auri Leonardo a coci da guduwar da ta yi ta barsa domin zuwa ta kashe mahaifiyarta. Haɗuwarsu da Aizaad bayan saukarta a jirgi, kai ta gidan yari wajen Yasaar da ya yi har izuwa nasihar da ya mata har ya karya alkadarinta na fasa kashe mahaifiyarta da ta yi niyyar yi.

Dogon ajiyar zuciya Zeenah ta saki mai ƙarfi tare da danne ƙirjinta da hannu sannan ta silalo daga kan kujeran a sume. Da sauri Meema da His Excellency suka riƙo ta suna. Meema fasa ƙara ta yi don idan mahaifiyarta ta mutu itama zuciyarta bugawa za ta yi ta mutu. Abdul-Hameed kuwa ruɗewa ya yi hawayen na zubar masa na tashin hankalin labarin da Meemah ta gama ba su da kuma halin da matarsa ta ke ciki a yanzu. Kasa yi mata komai ya yi, momcy ce da itama hankalin nata a tashe ya ke ta taho ta riƙo Zeenah a hannun Abdul-Hameed tare da faɗin, "Ku ban ruwa suma ta yi!"

Da sauri Abdul-Hameed ya juya domin ɗauko ruwan har yanaa tuntunɓe ya nufi kitchen ɗin Babiyon ya ɗauko ruwa ya dawo. Su Baffan ma gaba ɗaya miƙewa suka yi hankali a tashe suna kallon Zeenah da bata munfashi.

"Buɗe min murfin ka tsiyayomin ruwan a hannuna!" Momcy mahaifiyar Aizaad ta faɗa tana mai miƙawa Abdul-Hameed hannu shi kuma ya tsiyaya mata ruwan ta shafa sau uku a fuskan Zeenah.

Wani numfashi mai ƙarfi Zeenah ta ja tare da tashi zaune zumbur tana kalle-kalle. Sai da ta gama ƙarewa 'yan ɗakin kallo tsaf sannan ta furta, "Ke nan ba mafarki na ke yi ba? Inna lillahi wa inna ilaihir raju'un! Na shiga uku ni Zeenatu. Yanzu Meema ke ce kika yi wannan ƙazantacciyar rayuwar a ƙasar Colombia? Meemah haɗiyar cocaine, harbi da bindiga da kuma aure kafiri a coci? Na shiga ukuna! Taurin kaina bai jawo min komai ba sai asara da dana sani. Tur! Da rayuwata. Ni da ma mutuwa kawai na yi na huta! Ashe tarihi ya kusa maimaita kansa, na yi yunƙurin kashe mahaifina ni ma 'yata ta taho da zummar kashe ni. Da badan turo Aizaad da Allah ya yi ba da tarihi ya maimaita kansa. Wallahi, tallahi billahil azim ban san wani ɗan iska ba mai suna Adelbarto balle kuma wata Esmeralda da ke can ƙasar da ban taɓa leƙawa ba. Na shiga uku, Baba ka yafe min laifukan da na aikata maka!" ta faɗi bayan ta rarrafa ta kamaa ƙafafun baffa Ɓaleri.

Kowa a ɗakin kuka kawai ya ke yi na tausayin Zeenah da 'yarta. Babiyo ma hawayen kawai ya ke yi ya kasa furta komai don shi kansan he was shocked da labarin rayuwar da Meeman ta yi a Colombia.

"Wannan labarin ya tsaya iya mu anan kawai. Kada labarin safara cocaine da Meemah ta yi ya shiga kunnuwan kowa a cikin gidan nan, haka ma labarin auren cocin da ta yi ban so kowa ya ji. Ke kuma ki sani babu wani aure tsakaninki da shi yaron nan domin addininku ba ɗaya ba kuma ko da ya musulunta ba zan yarda makashi ya auri ɗiyar jikokina ba. Daga yau a wannan rana ki mance da kin taɓa rayuwa a colombia balle kuma wani ɗan iskan yaro can wai shi Leo. Ban so na ƙara jin sunan ko sau ɗaya a bakinki. Za ki samu miji ɗan gidan mutunci mai addini in sha Allah. Gaba ɗayan mu nan ahalinki ne kuma muna matuƙar ƙaunarki. Zan baki labarin da ke baki san shi ba a yanzu, amma kamun nan ina so ki sani ko wannan (ya nuna Abdul-Hameed) da ya ke amsa sunan uba a gare ki ba zai taɓa kwatanta soyayyar da mahaifiyarki ta ke maki ba sai dai ya yi iya nasa. Makirci ita wannan kafirar ta haɗa domin ta raba ki da mahaifiyarki. Amma mahaifiyarki mutuwa ne kawai bata yi ba na rashinki a kusa da ita," tun daga nan ya soma bawa Meemah tarihin rayuwar gidan kaf tun daga lokacin da ya kori 'ya'yansa bisa sharrin da Mamiyo ta masu har izuwa bayan raba su da Yasaar ya yi, zamanta a Denmark da yadda ta zo Arɗo Barkinɗo da abubuwan da suka faru har zuwa auran da Zeenah da Abdul-Hameed ya yi. Komai sai da ya faɗa mata cikin harshen turanci yana sharar hawaye.

Meemah kuka ta shiga rerawa bayan kwanciya flat ɗin da ta yi a ƙasa ta rumtse idanu maganganun suna mata amsa kuwa a kunne. Can kuma ta rarrafa ta kama hannun maman da baban ta riƙe gam tana kuka sannan ta faɗa jikinsu ta rungume.

Abdul-Hameed sai ya haɗasu su biyun ita da Zeenah ya rungume yana kuka tamkar ƙaramin yaro.

Su baffa ma kukan suke yi. Alhaji Haruna idanunsa har ɗan kumbura su kai jin labarin da Babiyo ya bada a kan yadda ahalinsa suka nemi tagayyar sabida dukiyar da anan gidan duniya za a barta da kuma jinjina irin kafiya da taurin kan familyn tun daga kan kakan-kaka.

"Ku tashi ku kai yarinyar wajen kakanninta mata su ganta, kuma ku tabbatar waɗannan kayan jikin nata ta sauya su. So na ke da dawo cikakkiyar ɗiyar fulani." Babiyo ya faɗi don ya gaji da ganin koke-koken. Shi kansa ji ya ke tamkar kansa zai rabe gida biyu. Ya yi tsufan da ƙwaƙwalwarsa bata buƙatar tashin hankali sam.

Zeenah kamar jira dama take sai ta miƙe ta riƙo hannun Meemah suka soma tafiya. Abdul-Hameed ɗin ma miƙewar ya yi ya bi bayansu ganin yadda matar tasa ke tangadi kamar za ta faɗi ƙasa. Shi ya buɗe ƙofar suka fito daga ɗakin. Wani irin ƙamewa tare da sarawa ja kariyar nasa suka masa sannan suka buɗe masa mota cikin saurin bayan wasu daga cikin sun zagaye su gaba da baya gefe da gefe har su ukun suka shiga gidan baya. Magana ya yi da soldier ɗin da ke gaban mota a kan inda za su nufa yanzu, shi kuma ya sanar ta cikin over-over sannan suka tada motar suka nufi gidan Nenne. Har ga Allah Zeenah ta swaje mamanta suka soma zuwa sai dai bata nuna hakan a fuska ba.

Nenne na can bata san mai ke faruwa ba, tana farfajiyar gidan ta ga mai gadi ya wangale gate uban motoci sun fara shigowa. Tsaye tai tana kallon ikon Allah don duk Abdul-Hameed ɗin zai zo sai ya sanar da ita ko da kuma shi kaɗansa zai zo cikin ɓadda kama.

Bayan motoci sun tsaya da sauri aka buɗe masu murfin motar suka fito daga ciki. Jikin Nenne wani irin rawa ya fara yi lokacin da idanunta ya yi arba da Meemah. Kallo ɗaya ta mata ta gane ita ce Meeman da suka jima suna nema da begen ganinta. Amma domin tabbatarwa sai ta juya da sauri ta doshi ƙofar ɗaki tare da murɗa handle ta buɗe tana kallon Muslimat da ke kan kujera remote a hannunta tana kallo. Babu inda ta baro Meema, kamanninsu ɗaya tamkar 'yan biyu. Sai dai ita Muslimat ta fita hasken fata kaɗan. Don ba baƙa bace sosai ɗinnan. Ita chocolate colour ne, don a cikin baƙaƙen mutane ma za a iya kiranta da fara. Jawo ƙofar Nenne ta yi ta kulle sannan cikin sauri-sauri hawaye na zubo mata ta nufi wajen su duk da suma tahowar suke yi. Kai tsaye ta janyo Meemah ta rungume a jikinta ta fashe da matsanaicin kuka tana faɗin, "Wallahi ko makaho ya shafa fuskan yarinyar nan zai tabbatar da jinina ce. Wannan yarinyar 'yarka ce ko Hameed?"

Meemah sai kallon fuskan Nenne take yi ganin anan suka samu kamanni da kalar fata sabida Abdul-Hameed bai ɗauko komai daga mahaifinsa ba idan ka cire yankan idanu. Komai na Nenne ya ɗauko har da kalar fatarta wacce itama ta ɗauko wajen mahaifiyarta.

Gyaɗa kai Abdul-Hameed ya yi tare da faɗin, "Meemah ce Allah ya dawo mana da ita yau."

Kallon gaban ta yi tare da zubewa ta yi sujada tana hawayen godiya ga ubangiji sannan ta miƙe ta kama hannun Meemah suka nufi cikin ɗaki. Muslimat ce ta fara ɗago kai ta sauke a kan Meemah da ke kallonta cike da so da ƙauna don babu tantama ita ce Muslimat ƙanwarta da ta ji Babiyo ya ambata lokacin da ya ke bata labari. Da sauri Muslimat ta miƙe tsaye tare da cilli da remote ɗin hannunta ta nufi Meemah da gudu ta rungume tare da faɗin, "Adda Meemah!"

Hakan da ta ce da ƙarfi ne ya jawo hankalin Muhaysim da Awwab da ke ɗakin da babansa ya yi gwauranci suka fito da gudu don babu wanda ban labarin Meemah addarsu da ta ɓace ba a cikin su.

Nufa su kai inda Muslimat ta ke rungume da Meemah su ma suka rungume ta suna kukan farincikin dawowarta don suma suna mahaukacin kewa da ɗokin ganinta.

Bayan sun natsu sun zauna ne Nenne ta shiga tambayar Abdul-Hameed yadda aka yi suka ga Meeman. Shikuma ya yi mata bayani sai dai bai yarda ya faɗa mata komai daga cikin tarihin rayuwar Meema a colombia ba saboda gargaɗin da Babiyo ya yi. Duk da hakan Nenne ta yi kuka sosai sai nan-nan take da Meema. Kan ka ce kwabo gidan Nenne ya cika da 'yan uwa. Yayun Zeenah su Adda Maryam duk sun zo, haka Ikilima ƙanwar Abdul-Hameed ita da 'ya'yanta da mijinta Isma'il. Ramadan ma sa nasa iyalan duk sun zo. Jawaad da Habib da iyalansu ma sun zo. Habib sai nuna kansa ya ke yi tare da faɗin, "Kin tuna ni Meemah? Kin tuna uncle Habib da ya kai ki yawo a mota?"

Dariya Meemah ta kyalkyale da shi don ta tuna sosai. Yana daga cikin mutanan da baza ta iya mance su ba a rayuwarta.

Meemah wani irin ta riƙa ji a jikinta na matsanaicin farincikin kasancewa cikin 'yan uwa. Musamman yadda ta ga ana yi da ita. Kowa so ya ke ta zauna kusa da shi. Hotuna ko sun yi babu adadi.

Wasu daga cikin sa'anninta abokan wasa sai janta suke wai sai ta koya masu yaren Spanish. Idan ta yi magana sai su fashe da dariya musamman idan suka faɗi abu da hausa ko fulani suka sa ta maimaita, sai ta faɗe shi tamkar tana yaren spanish sabida zamaa da yaren ya yi a bakinta. Hatta English ɗinta irin na can Colombia ne wanda za ka ji sa tamkar yare sai dai babu wanda ke jin turanci da ba zai gane abunda ta ke faɗi ba. Ainahin British English ɗin ma ta iya sabida an koya masu yaruka da dama sabida yanayin harƙallar da suke yi a can. Abunda ya sakaa Spanish English ya kamaa bakinta sosai sabida shi suka fi yi a Colombia. Idan sun yi mai kyau to sun bar ƙasar ne.

A nan gidan Nenne su kai Isha'i kamun gaba ɗaya suka ranƙaya zuwa gidan Babiyo domin meeting kamar yadda ya sanar. Maƙil ɗakin ya ke yara da manya. Babiyo sai ya riƙa bin su da idanu yana godiya ga Allah a zuciyarsa ganin yadda ya azurta shi da zuri'a, kuma yana fatan yadda suka haɗu duka a yau Allah ya haɗa su a gidan Aljanna kamar dai haka.

Bayan doguwar addu'a daga bakin Babiyo da kansa wannan karon wanda haka ya saka jama'a da dama zubar da hawaye, sai ya gabatar da Meema ga kowa har da wanda sai a yanzu suka ganta. Ɗan taɓo labarin baya ya yi kaɗan akan Mamiyo da abunda ta aikata don waɗanɗa basu sani ba su sani saboda wanke Meema da iyayanta tare da guje mata gori duk da yasan bai iya ya hana hakan ba dole ne sai wasu sun goranta mata walau cikin dangi ko waje. Sannan ya ƙara da yi mata kyautar da ya girgiza kowa a wajen saboda sanin da ya yi bata da gadon Abdul-Hameed bayan ya mutu duk da babu wanda ya san gawar fari. A gaban kowa ya damƙa mata takardun kamfanin da Mamiyo ta buɗe ita da 'ya'yanta mai suna Laurat and Sons wanda a rubuce a takardar da Babiyo ya damƙawa Meemah ya koma *_Meemah Construction Company_*.

Babu wanda bai yi farinciki ba da wannan kyauta da Babiyo ya yiwa Meema. Gaba ɗaya su baffa suka shiga yi masa godiya don duk mai hankali ya fahimci dalilin Babiyo na yin wannan kyautar.

Ba anan kawai Babiyo ya tsaya ba, sai da ya yi nasiha mai ratsa jiki game da mahimmancin zumunci da kuma azabar da Allah zai yiwa mai yanke zumunta sannan ya ƙara da jaddawa akan bai so Meemah ta ƙara amfani da makamanciyar kayan da ta zo da su daga can ƙasar da ta baro. Sannan kuma ya ƙara da cewar a nema mata malamin addini da zai riƙa koya mata sanin ubangijinta da sauran takardun musulunci irin su Alqur'ani, hadisi, fiqhu, sira, tajweed da sauransu.

Marwanatu jikinta har ɓari yake tare da ƙosawa Babiyo ya yi sallama ta fita ta je ta kira Asma'u a waya ta shaida mata abunda ya faru tare da kyautar da Babiyon ya danƙarawa Meemar.

Babiyo kallon Abdul-Hameed ya yi tare da faɗin, "Gobe kamar iyanzu ina buƙatar ganinka tare da Asma'u. Ku biyu kawai! Kowa zai iya tafiya Allah ya tashe mu lafiya" ya faɗi yana mai ɗaga hannu.

#Meemah #Zeenah #Abdul-Hameed #Asma'u first lady #Marwanatu #Aizaad #My destiny #Matar Sayyadee #Ƙaddarata *** [9/4, 8:49 PM] Matar Sayyadee: 🦜 *_MY DESTINY_*🦜 ( ~Ƙaddarata~)

*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee

☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.`