Page 76
Aje ai following channel ɗina please 🙏🏼 ***
*For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* ***
Domin shiga comment section kuma ki danna wannan link ɗin👇🏼 *** *_Don girman Allah zan sake faɗi, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining link ɗin da ke sama domin samun labarin ƙaddarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* 🥰👌🦜
_*💃🏻💃🏻 _Kuna ina 'yan uwana matar aure da 'yan mata? Shela nake ko wacce ta fito domin kuwa yau na zo maku da albishiri! Kun san matar Sayyadee ta ku ce ba ta samun abun ƙaruwa ta yi shuru domin ta ƙaru ita kaɗai._💃🏻💃🏻
💐💐🌼🌼_Magana ake ta ƙamshi. Toohwa! Mai ya hwaru?_ 🤔 🌷🌷🌸💮
*To maza ku marmatso ga sirrin nan. Shahararriyar nan wacce ke inganta soyayya tsakanin ma'aura wato Fatima Zaransalaty inkiya Queen Zarah ce ta taho mana da wani ƙamshim domin cika hancinar mazajemu da ƙamshi*. _INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_ _TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA KUJI 💃🏻
_Zaran Salaaty ta yi tafiya miƙaƙƙa har Sudan domin farnata ranmu da na mazajenmu ta kawo mana Sudanese perfume👌🏻 wanda idan har kika shafa shi a jikinki ko kin yi wanka ƙamshin bai barin jikinki. Tested and Trusted ƴaruwa. Zaransalaty ba iya sudanese perfume ta kawo maku ba, akwai kayayyaki masu matuƙar inganci na gyaran HQ (kun san dai ba a wasa da headquarter) akwai kayan gyararrakin jiki kala-kala na ƴan mata da matan aure. Sannan Zaransalaty tana sai da Decoration na kayan ɗaki iri-iri wanda baki taɓa ganinsu._
_KAR IN CIKA KI DA SURUTU, KE DAI NEMI ZARANSALATY A NUMBERS ƊINTA KAMAR HAKAA_: *** Or ****
*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_nfection_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_
_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ ***** *****
Gaban Marwanatu sai da ya buga da ƙarfi jin furucin Babiyo da ya yi tana fatan Allah yasa ba ya gane ita ce ke kai wa Asma'u rahoto ba.
Babiyo kuwa yana sane da komai ya bar Marwan ne domin ya ga iya gudun ruwanta. Don ya fahimci daƙiƙiya kuma shashasha ce ita. Sai dai bai son ɗaukar wani mummunar mataki a kanta don ya san hakan ba komai zai ƙara ba sai tsanar Zeenatu da zuri'arta a zuciyar Marwanatun wanda hakan ba shine buri da fatansa ba. Babban burinsa shine duka zuri'arsa su zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya.
"Ke Marwa!" Babiyo ya yi kiran sunanta da ya saka cikinta mugun murɗawa tamkar mai ciwon naƙuda. Da ƙyar ta iya amsawa da da na'am tana zazzaro idanu.
"Ke da Zeenatu ku tsaya ban gama da ku ba. Ina son a bar mu ni da ku kawai a cikin ɗakin nan." ya faɗi yana kallon cikin idanun Marwanatun da gaba ɗaya ta gigice don duk iskanci mai iskanci a cikin Arɗo Barkinɗo yana shakka da tsoran Babiyo.
Gaba ɗaya kowa ya fice banda Zeenah da Marwa kamar yadda Babiyo ya sanar. Sai da aka kwashi mintuna biyar bayan kowa ya fice sannan Babiyo ya ɗaga kai ya kalli kowacce a cikinsu sannan ya ja doguwar ajiyar zuciya tare da farawa ta kan Zeenah.
"Zeenatu, tun da kika dawo gidan na fahimci babu jituwa da soyayyar jini tsakanin ki da 'yar uwarki Marwanatu, menene dalili?"
Sunkuyar da kai Zeenah ta yi hawaye na taruwa a idanunta sannan ta soma magana bakinta na rawa-rawa, "Ban san me zan yi na goge tsanar da 'yar uwata ke min ba. Na san ban kyauta mata ba a baya, so da dama na yi ƙoƙarin jawota jikina amma sam ban samu fuska daga gare ta domin duk muka haɗu habaici, zagi da gori kawai ta ke jifana da su."
Wani mugun harara Marwa ta jefa mata a faƙaice wanda sarai Babiyo ya gani, Zeenar ce ma da kanta ke a ƙasa bata gani ba. Sai ya kalli Marwa tare da faɗin, "Ke Marwa menene tsakaninki da Zeenatu?"
Ai kamar Marwanatu na jira ta fashe da kuka mai ciwo don duk ta tuna sakin da Nura ya mata kuma ya sake aure ya mance da ita abun matuƙar ciwo ya ke mata. Ita da 'ya'yanta sai dai su zo su yi mata hutu su koma. Kwanannan ma aka saka ranar 'yar ta Fa'iza wacce bata wuce sa'ar Meema ba. Ta yi kuka har ta ƙoshi don har gobe da ta ke auren wani daban tana ƙaunar mijinta Nura don babu namijin da ya yi haƙuri da ita kuma ya sota iya so kamar Nura kamun shigowar Zeenah rayuwarsa a cewarta.
"Ba kuka za ki yi ba Marwanatuna! Baya ni za ki min domin sanin bakin zare." Babiyo ya faɗi a tausashe don so ya ke da izinin Allah ya shirya tsakaninsu a yau ɗinnan komai ya wuce.
A hankali ta buɗe baki kuma cike da jin daɗin yadda Babiyon ya kwantar da murya yana mata magana ba kamar yadda ta yi tsammani ba, "Sanadinta na rasa duk wani jin daɗi na rayuwata. Mijina, soyayyata, aurena da 'ya'yana. Babu wanda ya ke duban girman laifin da tai min sai nawa laifin ake gani. Sanadinta har karya min hannu Baffanmu ya yi, sanadinta mahaifiyata har gaba ta sha yi da ni, sanadinta wasu su ke min gani-gani a cikin zuri'armu, sanadinta har yau Ramadan bai min magana idan ya wuce amsa gaisuwata, sanadinta Hamma Abdul-Hameed ya hana ni shiga Villa har da kankara min warning wai ni ba alkhairi bace duk na zo gidansa sai wani mummunar abu ya samu matarsa. Kowa ya juya min baya sanadinta wanda kowa ya san ita ce tai min laifi amma sai ake juye abun kaina tamkar ni ce mai laifin." ta ƙarisa maganar tare da jan shassheƙar kuka.
Ajiyar zuciya mai ƙarfi Babiyo ya sauke kamun ya furta, "Wannan shine duk abubuwan da ke ci miki zuciya Marwanatuna?"
Gyaɗa kai ta yi tana sharar hawaye tare da faɗin, "Sune Babiyo. Ita da ta yi ƙazantacciyar rayuwa tana cikin farinciki amma ni kullum cikin ɓakin ciki na ke kwana. Na gaji na neman hanyar ƙuntatawa rayuwarta domin abun daga baya ni ya ke damu saboda zubar da ƙima da darajar wannan family ɗin da na ke ƙoƙarin yi. Wallahi ban yi bacci ba lokacin da naga hotunan Hamma da ita yana yawo a social media ana cin mutuncinsa wanda da ban fitar da sirrin nan wa Asma'u ba da hakan bai faru ba. Ban taɓa tunanin za ta saka a yaɗa labarin ba a gidan redio da social media. Na ɗauka a cikin gida kawai za ta yi amfani da shi wajen ƙuntatawa Zeenatu."
Murmushi Babiyo ya yi domin anzo daidai inda ya ke son a zo ɗin, sai ya gyara zama a akn wheel chair ɗin tare da danna madannin forward ya iso gab da Marwanatun sannan ya furta, "Marwantu ko kin ƙi ko kin so Zeenatu jininki ce. Kuma duk inda za a je a dawo idan aka tsaga jikinki aka tsaga nata sai an ga jini iri ɗaya ke tafiya a jijiyoyin jikinku. Shin na taɓa yi maki magana ko nuna ɓacin rai ko kuma in kore ki kamaar yadda na saba yi wa 'ya'yana idan su ka aikata laifi duk da masaniyar da na samu na abunda kika aikata na taka ƙafafunki mai daraja ki ka je gidan karuwai ki ka yi faɗa da budurwan miji har titi wanda ya jawo kika burmawa mijinki wuƙa a ciki Allah ne kawai ya tsare kuma lokacinsa bai yi ba?"
Girgiza kai ta yi tare da faɗin, "Ko magana sau ɗaya baka min ba. Baffana ne kawai ya dake ni."
Jinjina kai ya yi sannan ya cigaba da magana, "Kamun na cigaba da maganata ina so yanzu ki tattaro duk ɓacin ranki na tsayin shekaru sha uku da kika ɗauka a zuciyarki a kan Zeenatu ki kalleta yanzu ki faɗa mata maganganu masu zafi wanda hakan zai saka zuciyarki ta yi sanyi. Babu wanda zai ce maki dan me, kuma babu wanda zan bari ya ji ko kuma ya nuna zai ɗau mataki. So na ke yau baƙin cikin shekatu goma sha uku ya wanke a zuciyarki ki dawo daidai da 'yar uwarki."
Ɗagowa Zeenatu ta yi ta kalli 'yar uwarta Marwanatu tare da kamo hannunta ta furta, "Ki zage ni, ki min gori, idan ya kama ki dage ni idan har ƙuncinki zai yaye a kaina 'yar uwata. Wallahi ban ƙaunar yanayin da muke ciki. Idan abun ya cigabaa a haka gabar baza ta tsaya ba har jikokinmu ni kuma ba na fata da ƙaunar haka. Don girman Allah ki zage ni kuma ki dake ni ki huce." ta ƙarisa maganar tare da ɗago hannun Marwantu ta riƙa kaiwa kanta zafafan maruka akan kunci.
Marwantu kasa yin ɗaga daga cikin abubuwan da Zeenatun ta lissafo ta yi sai ma kukan da ta shiga rerawa tana kallon Zeenatun da ke ta kaiwa kuncita maruka da hannunta.
Babiyo kuwa bai furta komai ba har tsayin mintuna biyar yana kallon ƙwayar idanunwansu. Babu abunda ya ke hangowa sai wannan ƙaunar ta jini wanda da can ma ƙiyayya ce ta danne na zuciyar Marwanatu.
A hankali ta riƙo hannun Zeenah ta riƙe gam domin ta daina marin kanta, amma har wannan lokacin ta kasa cewa komai sai kallonta da take ta yi kawai tana hawaye.
Gyaran Murya Babiyo ya yi tare da kallon Marwanatu ya ce, "A yau zan baki labarin da na san kin san wani ɓangare amma ba ki san wani ba. Kawai ki saurareni idan kuma kina da tambaya ki min."
Labari ya soma bata dalla-dalla tun daga korar da ya yiwa 'ya'yansa da, rayuwar Zeenatu bayan koran da ya baffa Ɓaleri ya mata har dai zuwa shigowarta Arɗo Barkinɗo sabadin Jawaad. Kuma ya mata da labarin Mamiyo kaf da abunda ta aikata. Sai dai itama kamar yadda ya faɗa baffa Ɓaleri wancan lokaci haka ya faɗa mata. Ya mata nuni da tun fara barikin Zeenah na farko duk Mamiyo ce sila.
Kuka sosai Marwanatu ke yi har jikinta na rawa. Babiyo ya furta, "Shin yanzu za ki cigaba da gaba da ƙullatar 'yar uwarki bisa Ƙaddarar da ita kanta da ana canzawa da ta canza tata Ƙandarar? Ina so ki sani, ko kin haɗa kai da Asma'u domin muzanta Zeenatu da 'yarta ko baki haɗa ba, akwai mummunar tabon da Mamiyo ta yi mata wanda har tabar duniya ba zai taɓa goguwa ba. Shin baza ki barta ta ji da ɗaya ba kawai! Kina tunanin da ba ɗan uwanta ta ke aure ba a yanzu, za ta samu farinciki ne a cikin familyn mijin. Duba ki gani, ke da kike jininta kin kasa dannewa a kullum kuka haɗu sai kin mata zagin ƙare dangi da gori mai tafasa zuciya, to ina ga mutane kuma 'yan waje. Yau gani a gabanki ina taya Zeenatu roƙon gafararki da ki yafe ki bar komai ya wuce ki riƙe 'yar uwarki hannu biyu. Ke ma fa kina da na ki laifi Marwa. Shin kin mance irin ganawar azabar da kika yiwa shi Nura tsoron mijin nakin ne don kawai Allah ya ɗaura masa ƙaunarki? Kin hana sa kwanciyar hankali, kin ƙi ba shi farinciki kuma kin hana shi auro wacce za ta ba shi, kin ga kuwa kin ba shi lasisin bin matan banza. Kuma bugu da ƙari Zeenatu ba ita ta bi Nura ba, Nura ne ya bita har inda ta ke zama. Naka fa naka Zeenatu. Zeenatun dai ce naki ba Asma'u. Kuma ba wai ina rabaa alaƙarku bane don ita Asma'un ba cikin zuri'a ta bace. Itama ta riga ta shigo cikin zuri'a ta tun ranar da shaidu suka shaida aurenta da jikana. Kuma kar ki manta ni da kaina na zaɓo masa ita matsayin mata saboda sanin wanene mahaifinta. Mutun ne na gari sosai."
"Ki yafe min duk abunda na miki 'yar uwataaaa!" Marwanatu ta faɗi bayan ta faɗa jikin Zeenah ta rungume tare da fashewa da kuka.
Itama Zeenatun kuka ta ke yi tare da faɗin, "Ni ma ki yafe min 'yar uwata!"
Ƙarfaffiyar ajiyar zuciya Babiyo ya sauke yana mai jin kamar ya sauke wani babban nauyi da ke kansa. Burinsa kamun ya bar duniya shine haɗuwar kan zuri'arsa kaf.
"Allah ya maku albarka tare da zuri'arku. Nagode sosai da ku ka ban haɗin kai na gyara tsakaninku. Ke kuma Marwanatu zan kiya duk waɗanɗa kika lissafo min da suke ƙin yi miki magana na yi magana da su. Shi kuma His Excellency zai zo ya same ni sai na ji dalilinsa na hana ki shiga Villa. Idan ya kama na mammaka masa sanda ma zan yi."
Dukkansu sai da suka dara sannan suka miƙe hannunsu riƙe dana juna sannan suka fice daga ɗakin. A ranar dai Mama Hafsat mahaifiyar Zeenah ƙin bari ta yi su tafi da Meema a gidanta ta kwana. A cewarta gobe idan Abdul-Hameed ya zo shi da matarsa kamar yadda Babiyo ya ce sa tafi amma yau dai tare za ta kwana da jikarta. Shi ma baffa Ɓalerin hakan ya ce. Su Muhaysim ma sai suka buga tsalle suka ce suma can gidan za su kwana domin ba su gaji da ganin Addarsu ba.
Daren ranar Zeenah bacci ta yi ita da Abdul-Hameed mai cike da farinciki da annashuwa. Sun raba dare suna hira da soyayya kamun su kai bacci. Washa gari da daddare kuma ya tasa Asma'u da ya ke matuƙar jin haushinta a gaba su ka tafi Arɗo Barkinɗo.
Gaba ɗayansu suka natsu gaban Babiyo barin ma Asma'u da jikinta ke rawa da kuma ɓacin ran abunda Babiyo ke faɗi a kanta.
"Ban sa mijinki ya kawo nan don komai ba son don in miki nasiha tare da jan kunnanki don kema tamkar jikata haka na ke kallonki ba sirikar gidan nan ba. Ina sane da duk abunda ki ke aikatawa. Sai dai ina so ki sani, idan ki ka yi abunda zai zubar da ƙima da mutuncin mijinki ba shi kaɗai kika tozarta ba har da ke ɗin nann domin duk inda kika shiga za a ce ga matarsa can. Ki daina bari shaiɗan da tsokar da ke cikin ƙirjinki suna cin galaba a kanki saboda kishi. Na san kece kika sa aka fitar da zancen nan a gidan radio sannan kuma kika kuma fitowa gaban ƴan jarida ki ka ƙaryata. To na baki uzuri a wancan, amma idan kika kuskura kika kuma yin wani abu da zai ɓatawa zuri'ata da gidana suna, to a wannan karon zan ɗauki mummunar mataki a kanki kuma baza ki ji daɗi ba. Sam albasa ba tai halin ruwa ba domin iyayanki mutanan kirki ne ainun. Saboda haka ki kiyaye. Kai kuma (ya mayar da maganar a kan Abdul-Hameed) ka ji tsoron Allah ka kwatanta adalci a gidanka. Kar ka yarda ka kasance cikin mazan da Allah zai tashe su ranar gobe ɓarin jikinsa ɗaya a shanye. Ka bawa kowacce haƙƙinta, kar ka kuskura ka fifita soyayyar wata a gaban wata. Wannan shine iya maganar da na kira na yi muku. Allah ya sa ya shiga kunnunwanku."
"In sha Allah!" Abdul-Hameed ya faɗi yana zunguran Asma'u da ƙafa domin ita ma ta furta wani abun. Da ƙyar ta iya buɗe baki ta ce, "Mun gode Babiyo."
Gyaɗa kansa ya yi tare da faɗin, "Allah ya muku albarka, ku tashi ku tafi dare na yi."
Tare su ka miƙe suka fita zuwa tsakar gidan, da sauri bodyguard suka buɗe musu mota suka shiga. Gidan Mama Hafsat suka fara isa su ka ɗauki su Meema sannan suka wuce gida.
Asma'u tamkar za tai bindiga tsabar yadda maganganun Babiyo ya soki zuciyarta. Sai dai ta san ko giyar wake ta sha bata isa ta ƙara yunƙurin yin wani shirme a media ba don ta san tabbas Babiyo zai iya sakawa ai mata checking out.
Yau ba a ɗakin Zeenatu yake ba, sosai ya ciji yatsa don ya san za a sha hira babu shi, amma gudun shiga hakkin Asma'u kamar yadda Babiyo ya tunasar da shi, karfe goma saura ya yi masu sallama ya haura ɗakin Asma'u.
Washa garin ranar tun sha ɗaya aunty Ladi Katifa ta iso gidan jikinta har rawa ya ke. Tana arba da Meema ta fashe da kuka tare da rungume.
"Meemata ke ce kika girma hakaa? Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un… Allah ka tsinewa Yasaar da Sabo da kaza!" ta kuma fashewa da kuka.
Meeman ma kukan ta ke yi sosai har da shassheƙa kamun ta ce, "Aunty Ladi......"
Rufe mata baki ta yi tare da faɗin, "Aunty Ruƙayya, no more aunty Ladi har abada kin ji Daughterna."
Gyaɗa kai ta yi tare da faɗin, "Aunty Ruƙayya ina aunty Salma nice?"
"Ban san inda Salmanu ya ke ba. Tun ranar da aka raba mu da ke shi ma bamu ƙara ganinsa ba. Amma ina fatan yana cikin ƙoshin lafiya da kwanciyar hankali."
"Ameen" Meemah ta amsa. Daga nan kuma hira ya ɓalle tsakaninsu a can falon Zeenatu. Sun yi kuka tamkar idanunsu zai tsiyaye. Musamman da ta ji wai Meema ta yi auren coci don har hotonta da Leo ranar ɗaurin auren sai da ta nuna masu.
Nan su kai mata nasiha tare da nuna mata illar abunda ta aikata da kuma ƙoƙarin cire mata Leo ɗin a ranta. Ita Zeena ma tun a daren jiya ta fakaici Meema ta ɗauke wayar tda ta dawo dashi daga colombia ta cire sim ɗin ta kakkarya don kar ta kwashi numbers ɗin da ke ciki ta kira Leo ta ɓallo masu aiki. Don a yadda Meeman ta ba su labarin Leonardo ɗin zai iya aikata komai a kanta. Sannan kuma ta cire zoben da ya saka mata ta yi flushing ɗinsa.
_3 months later_ Meema hausa ya ɗan fara zama a bakinta duk da dai ba iyawa ta yi ba. Don namiji mace ta ke mayar dashi, mace kuma namiji. Haka ma ɓangaren koyarwar karatun addini, Aizaad ne ya kawo masu wani malamin da ke koya mata har gida kuma Alhamdulillah tana fahimtar komai. Akwai shaƙuwa sosai tsakanin su da Aizaad sosai duk da bai fito fili ya faɗa mata ba saboda soyayyar da ya fahimci ta faɗa da wani ma'aikaci a wani babban super market. Wani rakiya da ya taɓa mata domin sayo mayukanta ne suka haɗu, shikuma ya gwada yana son ta har su kai musayar number. Wata biyu kenan da haɗuwarsu da Hamza, sai dai bataa taɓa yadda ta faɗa masa ita ɗiyar shugaban ƙasa bace don acewarta tana son ta auri wanda zai ƙaunace ta a yadda ta ke ba don matsayin mahaifin ta ba. Duk lokacin da za su haɗu a gidan aunty Marwanatu su ke haɗuwa. Yayin da shi kuma ta ke jira wani lokaci domin bayyana masa ko ita wacece.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, ranaku suna ta wucewa haka satuttuka da watanni. A yanzu watannin Meema takwas da dawowa cikin zuri'arta. Komai yana tafiya mata daidai a rayuwa. Ɓangaren Aizaad kuma yana nan maƙale da soyayyarta a cikin zuciyarsa sai dai ya yi alƙawarin burne halan a zuciyarsa domin farincikin Meema shine farincikinsa. Kwatsam wata rana Meema na zaune a kan kujera tana yankan farce wayar ya yi ringing. Dubawa ta yi sai taga masoyinta Hamza ke mata waya, cike da farinciki ta ɗauki wayar ta kara a kunne tare da rera sallama. Sai dai abunda ta ji Hamza na faɗi ne ya saka ta miƙe tsaye dafe da ƙirji sannann ta zazzaro idanu.
"Kana ina? Don Allah ka zo mu haɗu a gidan auntyna. Zan maka bayanin ta yadda za ka fahimta. Wallahi ba da niyyar yaudara na yi hakan ba sam!"
Ƙit ya kashe wayarsa ba tare da ƙarisa sauraranta ba. Da sauri ta nufi hanyar ɗakinta ta canza kaya sharp-sharp cikin doguwar rigar abaya tare da naɗe kanta da gyalen don dama sune shiganta don yawanci kayan nata abaya ce. Ɗakin Zeenah ta tafi ta shaida mata za ta je gidan aunty Marwanatu amma baza ta jima ba. Sai Zeenah tai mata Allah ya kiyaye ita kuma ta fito ta shiga mota driver da ja kariyarta suka mata rakiya har gidan aunty Marwanatun da bama ta gida ta je aikin amma ta kusa dawowa. Har aunty Marwanatun ta dawo amma Hamza ya ƙi zuwa gidan. Daƙyar da suɗin goshi ya zo bayan la'asar yana cika yana batsewa.
Da kuka ta isa gabansa inda ya kr tsaye harɗe da hannun wayarsa a gaban aljihu camera na saita tahowarta. Kuma dama ya yi hakane domin ya ɗauki duk wani abu da za su tattauna tsakaninsu.
"Ka saurare ni Hamza in maka bayani. Wallahi ba niyyata in yaudare ka ba. Na yi hakane domin ka soni a matsayin yar kowa ba 'yar shugaban ƙasa ba."
Wani kallon banza ya watsa mata tare da faɗin, "...Tir! In haɗa iri da ke. Ni salihin bawa ne da bai taɓa kusantar zina ba. Don haka ba zai taɓa yiwuwa ba in auri ɗiyar da ta kwanta a mahaifar tantiriyar karuwa wacce ta kashe mahaifinta kuma ƴar ta'adda mai safarar miyagun makamai da kwayoyi. Fice min da gani a idona! Kuma ki sani daga yau ba ni ba ke!"
Tun Meema na kankanuwarta ta tsani a zagi mahaifiyarta balle kuma yanzu da ta girma ta mallaki hankalin kanta. Wani irin zafi zuciyarta ta shiga yi bata san lokacin da ta ɗaga hannu ta riƙa wanke fuskan Hamza da maruka ba har hakan ya jawo hankalin Marwanatu da ke kitchen tana hangensu ta window. Da sauri ta fito daga ɗakin domin zuwa inda suke ganin Meema ta cakumi wuyar Hamza.
"Mahaifiyata ka ke zagi? Wallahi sai in kashe ka babu abunda za faru. Kasan wacece mahaifiyata a zuciyata kuwa? Zan iya ƙarar da kaf danginku a kanta. Waye kai waye ubanka?" tana maganar ne tana haɗa kansa da fense ɗin gidan har kansa ya fara fidda jini kuma ya kasa ƙwatar kansa sabo riƙon da Meema ta masa kuma ƙarfin ba ɗaya ba kasancewar ta samu horo a wannann fannin.
"Kina haukane Meema! Ki sake ki yanzun nan" Marwa ta daga mata tsawa amma Meema ta ki sakin wuyar Hamza. Sai da bodyguard ɗinta dacmasu gadin gidan da kuma mai bawa fulawa ruwa suka haɗu dakyar suka ɓamɓare Hamza a hannun Meema daidai lokacin da wayarsa ta suɓuce daga aljihu. Nan kowa ya yi arba da video ɗin da ya ke recording domin yaɗawa a duniya idan ya fita waje.
A take Meema ta yanke jiki ta faɗi a sume sabida zuciyarta da tai mata nauyi don bata taɓa kawowa ko da wasa Hamza zai ci amanarta ba. Kai tsaye wani babban asibiti da ke nan abuja su ka tafi da ita shi kuma Hamza ɗaya daga cikin bodyguard ɗinta ya yi ram da shi.
A hanya Marwanatu ta kira Ramadan ta shaida masa abunda ke faruwa bayan ta gargaɗe shi da kar ya sanarwa iyayanta gudun tashin hankalinsu. Cikin mintuna 20 Ramadan ya iso asibitin shi da Nenne don yana kusa da ita Marwa ta kira kuma ta ji komai. Inda hankalinsu ya kwanta jin da su kai doctor ya ce babu abunda ke damunta ɓacin rai ne kawai da shock ya sumar da ita. Ɗakin suka shiga sai suka taras da tana ta kuka tamkar ranta zai bar jikinta, sun yi lallashin har sun gaji kuma ta ƙi faɗin ainahin abunda Hamza ya mata kasancewar babu wanda ya kunna video ɗin domin ya gani.
Nenne ce da kanta ta kira Abdul-Hameed ta sanar da shi, cikin ƙanƙanin lokaci tsaro ya cika a asibiti sai ga Abdul-Hameed da Zeenatu hankali a mugun tashe. Don ita Zeenah har ta soma kuka. Abdul-Hameed ɗin ke kwantar mata da hankali.
Sai da aunty Ruƙayya (Ladi Katifa) ta zo sannan Meema ta iya buɗe baki ta faɗa masu abunda ya faru. Magana Mr President ya yi da wani sai ga bodyguard ɗin Meema ya taho ya miƙawa His Excellency wayar Hamza cike da ladabi. Amsa ta yi ya kunna ya kalli duk abunda ya faru, nan da nan fuskansa ta yi jazir sai ya tura wayar cikin aljihu sannan ya yi magana da wani soldier a kunne. Da sauri soldier ɗin ya furta "Yes sir!" bayan ya ƙame tare da sara masa sannan ya juya ya fice.
Ko mintuna talatin Meema bata ƙara yi ba a asibitin akaa ba su sallama suka koma gida. Ɓangaren Hamza kuwa barikin sojoji aka tafi da shi, ya markaɗu tamkar kayan gwari, haka ya bugu tamkar fulawa sannan suka tambaye shi dalilinsa na yi wa 'yar shugaban ƙasa video kuma wa ya saka ki.
Idanunsa ko buɗuwa ba sa yi saboda azabar dukan da ya sha. Nan ya shiga bayanin filla-filla, "Wallahi saka ni aka yi. Uwargidan His Excellency ce ta ba ni naira miliyan huɗu domin na yi soyayyar ƙarya da Farida sannan in tona asirinta a media ta yadda kowa sai ya san Meema ba halastacciyar 'ya bace ta yanda aure sai ya mata wuya. Tun asali ba da soyayya gaskiya na zo mata ba."
"Za kuwa ka ci ubanka yau! Ku cigabaa da ɗumama min shi ta yadda gobe ba zai ƙara ba." wani babban soldier ya faɗi sannan ya fita domin kai wa Mr president video recording ɗin da ya yi wa Hamza saurayin Meema.
Lokacin da Abdul-Hameed ke kallon mamaki da tsanar Asma'u ne suka cika masa zuciyarsa. Bai taɓa tunanin tsanar da ta yi masa har ya kai hakaa ba. Don shi duk wanda bai san Zeenatu da 'ya'yansa to bai da babban maƙiyi kamar sa a duniya. Har ƙwalla sai da ya yi kamun ya bar office ya taho family house tare sa securities ɗinsa.
Sai da Babiyo ya gama kallon video ɗin sannan Abdul-Hameed da idanunsa suka taru da ƙwalla ya furta, "Ba zan taɓa iya cigabaa da zama da Asma'u ba. Na yi iya ƙoƙarin da zan yi na zamaa da ita. Idan har za ta iya min wannan abu to tabbas maƙiyana za su iya haɗa baki da ita su kashe ni. Zan sauwaƙe ma ta tafi kawai!"
Jinjina kai Babiyo ya yi tare da faɗin, "Ina bayanka. Ka yi abunda ka ga ya dace. Iyalinka ne ba zan shiga haƙƙinka ba. Ni ma na yi iya nawa ƙoƙarin domin Asma'u ta cigaba da zama a gidan auranta. Amma yanzu ta riga ta kai matakin da kowa zai tsorace ta a cikin familyn nan, iƙirarin da ta ke yi na cewar tana sonka ƙarya ce. Domin da tana sonka ba za ta taɓa zutar da da 'yarka ba. Domin hausawa sun ce maso uwa ya so 'ya'yanta."
A taƙaice dai a wannan ranar Abdul-Hameed ya saki Asma'u saki biyu tare da haɗa mata sha tara ta arziki sannan ya haɗa ta da securities har Kaduna gidan iyayanta. Kuma dama kamun tafiyarta Babiyo ya kira mahaifinta ya shaida masa komai. Har kuka sai babanta ya yi yana bada haƙuri akan iskancin da 'yar tasa ta aikata sannan kuma ya ƙara da faɗin zai zo takanas domin ya bada haƙuri kuma ba wai don a dawo da 'yarsa ba, sai don iskancin da ta aikata.
Meemah har sai da depression ya kama ta sanadin abunda Hamza ya mata don ba kaɗan ba ta kamu da ƙaunarsa wanda lokaci guda ya juye zuwa ƙiyayya da tsana. Aizaad har Villa ya zo ya taya ta alhini tare da ƙwarara mata gwiwa akan kar ta sare ta cigaba da miƙa lamuranta ga Allah, In sha Allah mai ƙaunar da gaskiya zai bayyana a gare ta kuma su yi aure ba tare da wani ƙalubale ba. Tun abun bai shiganta har ya soma ta watsar da komai ta fara karatun masters ɗinta gadan-gadan. Shikuma Aizaad bai yi ƙasa a guiwa ba ya riƙa shigar da kansa cikin dabara. Lokaci ƙanƙani zuciyoyinsu ta haɗe da juna suka shiga soyayya mai zafi ba tare da ɗayansu ya furtawa ɗan uwansa sirrin da ke zuciyoyinsu ba. Kuma dukkansu sun san sun kamu da ƙaunar juna har ma da wanda ke tare da su sai dai babu wanda ya ce masu uffan kowa ya zuba masu idanu. Gab Meema za ta haɗa masters ɗinta akai zaɓe wanda dama tuni Abdul-Hameed jam'iyya ta ƙara tsayarwa kuma cikin hukunci ubangiji ya kuma lashe kujeran shugaban ƙasa a karo na biyu. Bayan rantsar da shi da wata guda iyayan Aizaad suka zo tambayar auren Farida Meema, cikin mutunci akai komai aka biya kuɗin komai tare da saka ranar biki wata guda kacal.
Farinciki wajen Zeenah da Abdul-Hameed har ma da aunty Ladi da kafatanin Arɗo Barkinɗo tamkar su zuba ruwa a ƙasa su sha.
Aizaad kuwa wani sabon kulawa da zallar kalaman soyayya ya ke zubabawa Faridarsa.
Gobe ne Meema za ta lunching F.A.A Construction Company (Faridat Abdul-Hameed Abdul-Azeez) matsayin CEO. Ita ce da kanta ta canzawa company ɗin da Babiyo ya bata suna acewarta ta fi so ai amfani da asalin sunnata da Aunty Salma nice ta bata kuma a kullum tana burin ganinsa don baza ta taɓa mancewa da shi ba a rayuwarta. Wannan Company wani kyauta ne da His Excellency ya kuma yi mata shi sabida ta samu rashe a Abujan sabida Bauchi ya yi mata nisa tunda anan cikin abujar za ta zauna bayan aure.
His Excellency, Zeenah, Babiyo, Aunty Ruƙayya (Ladi katifa) da sauran jama'ar gidan su kai mata rakiya zuwa taron buɗe sabon kamfanin wanda har yanzu ba a gamaa ginin wani ɓangare daga ciki ba. Ma'aikata da dama suna nan suna aiki.
Meema ce ta riƙe scisors ɗin da zata yanka zaren, sai His Excellency ya ɗaura nasa hannun, Zeenah ma ta ɗaura sannann ta umarci Ladi Katifa ta ɗaura a kan nata hannun sannan suka yanka zaren. Gaba ɗayaa wajen ya ɗauka da tafi ga camera sai ɗaukarsu hoto ta ke yi.
Bayan taƙaitaccen bayani daga bakin mai girma shugaban ƙasa, sai CEO ta fito ta yi nata jawabin wanda ba komai a cikinsa sai godiya ga jajurtattun iyayanta da kakanta sannann ta miƙawa Babiyo da ke kan wheel chair gaba ɗayaa tsufansa ya fito ɓaro-ɓaro don jikinsa ya ɗan soma rawa. Shima gajeran jawabi tare da godiya ya yi sannan tare da rufewa da addu'a bayan tambayoyi daga 'yan jarida zuwa ga Faridat Abdul-Hameed Abdul-Azeez. Wasu ta amsa wasu kuma bata amsa ba.
Bayan ɗan ƙaramin partyn kowa ya soma kamaa hamyar gida ya rage 'yan familyn Arɗo barkinɗo kawai suna ƙara zagaye cikin company.
Ihun da suka ji daga can wajen ma'aikata ne ya saka gaba ɗaya suka fito daga ciki suka nufin wajen ma'aikata. His Excellency ne ya tambayi mai ke faruwa. Jiki na rawa wani lebura ya masa bayani abokin aikinsu ne ya faɗo daga sama kuma kamar ya mutu. Cikin sauri duk suka nufi inda bawan Allah ke kwance shame-shame a ƙasa duk ya ƙurƙurje har a fuska.
"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un, Salam nice!" a tare Ladi Katifa da Zeenatu Laushi suka faɗi hakan.
Da jin haka Meema ta ƙariso wajen da gudu har ta soma kuka tana faɗin, "Aunty Salma nice! tana ina?"
Da hannu Ladi katifa ta mata nuni hannunta toshe da bakinta tana kuka haka ma Zeenah. Hannu Meema ta ɗaura a kai ta soma salati tana ihun kuka.
Nan da nan His Excellency ya saka aka ɗauke shi aka saka a mota, gaba ɗayaa suka wuce asibitin da Meema ta kwanta lokacin da ta suma. Babiyo kuma tuni akaa mai da shi gida sabida shima bai jin daɗin jikinsa.
Emergency aka nufa da shi aka shiga ƙoƙarin ceto ransa. Alhamdulillah sun yi nasarar shawo kan matsalar, kuma abu mafi farinciki babu abunda ya samu kansa. Sai dai ya samu karaya a ƙafa kuma tuni har an masa ɗori. Sai da suka ga komai ya yi daidai sannan suka tafi gida bayan sun bar security ɗaya da zai kula da shi.
Washa gari ko da za su dawo Salamanu jikan iyan mai danko har ya farfaɗo. Lokacin da ya yi arba da Ladi da Laushi ba ƙaramin razana ya yi ba. Duk jikinsu ya canza hakan bai saka ya kasa gane su ba.
"Shin gizon da idanuna suka saba min ne ko kuma dagaske uwar ɗakina da Ladi na ke gani."
Suna hawaye su duka suka tabbatar masa da su ya ke gani. Wani irin kuka ya fashe da shi ya shiga tambayarsu ina suka shige suka bar shi ya yi nemansu tamkar zai rasa rayuwarsa. Zama su kai sannan suka bashi labarin abunda ya faru. Ya ci kuka har ya godewa Allah jin an sai da Meema a ƙasar Colombia. Don ba su faɗa masa ta dawo ba sai da ya ci kuka sannan suka ce suna da suprise ɗin da za su nuna masa. Daidai nan Meema ta turo ƙofar ta shigo ɗakin.
Yunƙurawa Salmanu ya yi amma babu damar tashi, sai ya fashe da kuka tare da faɗin, "Na roƙe ku da Allah ku tura ni ta baya in faɗa kan Katifa in........."
Kamun ya ƙarisa Zeenatu ta ce, "Ashe dai iskancin naka na na jikan Iyan mai danko!"
Dariya mai tafe da kukan farinciki ya fashe da shi ganin Meema ta zama budurwa ta yi kyau ma sha Allah.
Ƙarisowa ta yi tana hawaye tare da faɗin, "Aunty Salma!"
Girgiza kai ya yi tare da faɗin, "Uncle Salmanu jikan iyan mai danko."
"Uncle Salmanu....." ta maimaita tare da rushewa da kukan jin daɗin waɗanɗan ta jima tana masu addu'a akan Allah ya shirya su ga su a gabanta gaba ɗaya cikin shiriyar ubangiji.
Kuka su kai sosai su duka kamun fira ta ɓarke a tsakaninsu. Labari ya basu akan irin wahalhalun da ya sha a Lagos kamun ya koma Birnin gwari wanda dama a can aka haifi iyayansa, bayan rasuwarsu tun yana yaro kuma ya dawo hannun kakarsa Iyan mai danko. A nan ya lalace sakamakon goyon sangarta da rashin kwaɓa da ya samu har dai ya soma daudu, tafiya ta yi tafiya kuma ya koma garin Lagos da zama sanadin wata uwar ɗakinsa karuwa. Bayan ya nemi su Laushi ya rasa kuma ya tattara ya koma Birnin gwari wajen kakarsa da ta tsufa sosai ga kuma cututtuka sun mata yawa da kuma azabar talauci. Ya sha baƙar azaba kamun ya iya aikin leburanci, duk da ya fuskanci ƙalubale don har gobe ya kasa iya saisaita tafiyarsa da maganar mata da yake yi don ya riga ya zama jinin jikinsa. Hakan yasa wani lokaci ko ya samu aiki ake koransa tare da kiransa ɗan daudu ana masa zunɗe tare da furta masa ya tafi ya je ya yi sanaa'ar shayi da buredi ko doya da ƙwai. Haka dai ya daure don ya yi alƙawarin babu shi ba daudu da kawalci har abada. A hakaa har Allah ya haɗa shi da wani mai gidan da ya ke kiransa aiki wanda shine silar zuwansa F.A.A Construction Company.
Sosai suka tausaya masa, Zeenatu kuma ta ɗauki alwashin taimakonsa da jari mai tsoka da shima zai gina kansa don ya mata halasci.
Bayan sati biyu da kwanciyar Salma nice a asibiti aka soma hidimar bikin Meema. Ta kowani ɓangare gyara take sha. Ta ɓangaren Amatul kareem matar Habib, Khairat matan Jawaad, Marwantu da kuma uwa uba Aunty Ruƙayya Ladi Katifa. Kamun sati guda gaba ɗaya Faridat Meema ta sauya ta fito fess sai glowing ta ke yi.
Salmanu jikan iya ya ciki yatsa babu adadi da ya ke kwance a asibiti babu ƙafar takawa ana bikin 'yarsa guda wanda ya gama cin alwashin cin uwar sabada sai ga shi babu shi za ayi.
Ranar juma'a dubban mutane suka shaida ɗaurin auren Faridat Abdul-Hameed Abdul-Azeez 'ya ga shugaban ƙasar Nigeria a babban masallacin Abuja (Central Mosque).
Zeenatu ta yi kukan farinciki har idanunta sun kumbura. Duk wani social media da ka shiga za ka ci karo da hotunan amarya da ango. Sai fatan alkhairi ake yi musamman da babu wani bidi'a sa aka yi ko nuna fariya da ɓarin kuɗi, yayin da wasu a gefe suke suka tare da dawo da zancen da ya wuce (Kun san dai halin jama'a ba sa rasa abun magana).
A ranar aka kai amarya gidan wanda sai da akai da gasken-gasken. Don irin kukan da ta yi tana riƙe iyayan nata biyu abun sai da ya taɓa zuciyar kowa musamman lokacin da ta rungume His Excellency tana kuka shima yana hawaye. A daren video ɗin ya fita media wanda babu wanda ya san waya fitar dashi. Wasu abun ya burge su har da ƙwallarsu yayin da wasu ke zagi suna sukar video ɗin.
Lafiyayyiyar soyayya mai tafiyar da zuciyar wanda ake wa Aizaad ke gwadawa Faridat ɗin sa. Sosai ya ke lallaɓata tamkar kwai ko ƙuda bai ƙaunar ya ga ya taɓata. Bai taɓa tunanin zai samu budurci a jikin yarinyar da ta yi shekaru sha biyu zuwa sha uku a ƙasar waje ba, sai gashi ya samu abunsa intact wanda hakan ba ƙaramin ƙara mata daraja ya yi a idanunsa ba.
Bayan auranta da sati biyu familyn Arɗo Barkinɗo suka tashi da matsanaicin tashin hankalin babban rashi da suka yi na Babiyo sakamakon zazzaɓi mai zafi da ya yi fama dashi da daddare. Kuka da alhinin da familyn na suka yi faɗi ɓata baki ne. Sun yi kuka har sun godewa Allah. Babu abunda ya tsaya masu a rai sai Meeting da ya kira su na ƙarshe ya yi masu wa'azi tare da ƙara tunatar da su akan zumunci da ƙaunar juna sannan ya nemi yafiyar kowa daga cikinsu.
Ba familynsa kaɗai ba, jama'ar gari da ma'aikatansa sun yi kuka sosai da rashinsa. Haka matar Hafiz informer har suma sai da ta yi domin Babiyo bai yada su ba, ya cigaba da kulawa da cinsu ita da 'ya'yanta. Babu abunda bai ɗauke ba na 'ya'yanta duk da irin butulcin da Hafiz ɗin ya masa. Hakaa ma yaran 'ya'yan da Mamiyo ta haifa da malam mai huluna duk sun zo suna kukan tashin hankali don su ma bai yada su ba ya cigabaa da kula da su tamkar dai jikokinsa.
Abdul-Hameed kuwa jininsa sai da ya hau don sai da aka fitar da shi ƙasar bayan rasuwar da mako guda. Sai dai da ƙyar ya amince ya yi sati guda ya juya ya dawo ƙasarsa.
Salmanu sai da ya kwashi wata uku a asibiti sannan aka sallamesa bayan an kwance ɗauri tare da bashi walking stick don ba zai iya tafiya hakanan ba. Kuma kamar yadda Zeenah ta yi alƙawarin inganta rayuwarsa haka ta yi, jari ta bashi na miliyan biyu, Meema ma ta ƙara masa wataa miliyan biyun domin ya soma sana'a. His Excellency da Ladi katifa ma ba a bar su a baya ba. Suma sun bada na su gudunmawar.
Bayan ya warke rass ya soma sana'ar saro takalma a lagos da less yana siyarwa a wani ƙaton shago da ke nan Abuja. Kuma duk bayan sati biyu yana zuwa Birnin Gwari domin duba kakarsa da ke can kasancewar akwai wata bazawarar 'yarta da ke jinyarta.
_After 11 months_ Daga aunty Ruƙayya har Aizaad an rasa mai zama waje ɗaya sai kaiwa da komowa su ke yi tsakanin Labour room suna addu'a. Zeenah kuwa duk bayan wasu mintuna sai ta kira waya ta ji shin Farida ta sauka. Ƙaran kukan jaririn da ya karaɗe ilahirin wajen ne ya saka Aizaad da Aunty Ladi sakin bahagon numfashi suna fatan Allah ya sa uwar lafiya ta ke.
Bayan mintuna biyar sai ga wata nurse ɗauke da jariri cikin farin showel tana dariya tare da nufar Aizaaf ta furta, "Congratulation! It's a bouncing baby boy."
Da mugun zumuɗi ya amshi yaron da har ya kai yatsa baki yana tsosa. Wallahi kamar mu ɗaya!" ya fadi yana nunawa Aunty Ruƙayya da ta miƙo hannu cike da zumuɗi.
"How is my wife?" Aizaad ya faɗi yanaa kallon nurse.
"Ana gyara ta yanzu za mu tura ta ɗakin hutu, amma tana cikin ƙoshin lafiya."
Ajiyar zuciyar farinciki ya sauke sannan ya fiddo waya ya shiga kiraye-kiraye yana shaidawa mutane matarsa ta haihu namiji mai kama da shi.
Kan ka ce kwabo asibitin ya cika sai dai an hana kowa shiga inda take sabida ana son ta samu baccin atleast awanni huɗu.
Da yamma aka sallame su kuma kai tsaye Villa aka yi da ita wajen mahaifiyarta wanda ita ba haka taso ba ta so yiwa Ƙawarta Ruƙayya kara sai dai His EXcellency ya buga tsalle ya ce 'yarsa gidansa za ta dawo. Sai dai bai sani ba Nenne ta gama nata shiri, ana zuwa da Meema ta saka aka juya da su zuwa gidanta. Babu yadda yaso haka ya haƙura.
Faɗin irin sunan da aka yi ɓata baki ne, wannan haihuwar ba ƙaramin ɓarin kuɗi akai ba daga duka ɓangarorin, wato ɓangaran Aizaad da Meeman. Sai dai a cikin Arɗo Barkinɗo akaa yi sannan His Excellency ya yi kyakkyawar gargaɗi akan kar a saki a yaɗa komai a media. Yaro ya ci sunan His Excellency Abdul-Hameed anamasa inkiya da Aryaan.
Sai da Meema ta yi kwanaki sittin a wajen Nenne sannan ta miƙa ta gidan mijinta bayan Ɓulɓul din da ta yi ita sa ɗanta wanda idan ka ganshi za ka ɗauka ya fi watanni biyu a duniyaa.
Bayan gyaran da Meema ta sha, har gida aunty Ruƙayya ta kai mata wasu zafafan magungunar da Binta Umar Abbale ke siyarwa masu inganci da dawowa da mace martabarta a idanun mai house.
Tammat bi hamdullilah! Nan na kawo ƙarshen littafin My Destiny Ƙaddarata. Kuskeran da na aikata Allah ka yafe min, kuma Allah ya sa a anfana da darussan da ke ci. Ku yi haƙuri na san baza ku so ƙarewarsa a haka ba. Ni kuma iya abunda na tsara kenan don wallahi idan na ce zan ja shi ya yi tsayi ku kanku labarin guddurar ku zai yi.
Nagode sosai fans ɗina masu min comment. Asiya (Mummy) tana godiya bisa addu'o'in fatan alheri na aurenta da kula mata.
Sai mun haɗu a next book ɗina mai Suna👇🏼
_DlNAAYAH SAFRAAZ_ *BETWEEN TWO LOVERS*
Labarine da ban taɓa rubuta irinsa ba, akwai cakwakiya, sadaukarwa, ƙiyayya da zazzafan soyayya a cikinsa game tausayi mai narka zuciya. Ku dai kar ku yarda ayi wannan tafiyar babu ku. Ba zan ba ku kunya ba in sha Allah.
Matar Sayyadin ku ce. Allah ya sada mu da alkhairi. Love you all fans 😍😍