SIRRIN ZUCIYA

Chapter nineteen

by @aysharano22

🤍SIRRIN ZUCIYA🤍

By Aysha Rano✨

10

Kallonta har yanxu Ayaan keyi and idan yace baiji zafin wayan nan kalaman nata ba shima yasan yayima kanshi karya ne, sunyi mishi ciwo fiyeda tunanin mai karatu. Matsawa yayi jikinta sosai har suna shaqar kamshin perfumes din junansu ya zuba blue eyes dinshi da instantly suka koma ja cikin nata idanun voice dinshi har canzawa yayi sbd bacin ran da yake ciki yace"you want an answer right?"...yana rufe baki itama cikin bacin ran tace"yes i want an answer"...sake matsawa yayi dab da ita yayi gripping shoulders dinta firmly da duka hannayenshi har snn kuma bai dena kallon cikin idanuwanta ba yace"well that is because I LOVE YOU"...ya karasa mgn yana haki kmr wanda yayi tseren mita dubu...idanuwa sosai Juwairiyya ta zuba a kanshi kila so take ta gane gaskiyar mgnr daya fada cikin idanunshi bakinta kuma ya kasa furta komai.

Shiko Ayaan yacigaba da cewa"i love you so much Ju, and I can not stand seeing you with another man, ko bazaki soni ba nidai ki bar kula wasu mazan, wlh duk na ganki da wani ciwo nakeji a cikin zuciyata"...kallonshi kawai Juwairiyya keyi kallo irin na mamaki ba kmr dazu da take mishi kallon bacin rai ba, kuma ta kasa furta ko kalma daya kmr wacce ya rufewa baki.

Goshinta Ayaan ya hade da nashi snn ya zagaya waist dinta da hannayenshi ya rufe ido kafin yacigaba da cewa"tunda nasan kaina ban tabaji inason wani abu kmr yanda nake sonki ba...your presence consumes me"...ya dakata ya sauke numfashin da yakeji yana janyoshi da kyar sbd halinda yake ciki...har snn kuma Juwairiyya bata iya cewa uffan ba to taga abinda yafi karfinta...dauke goshinshi yayi daga kan nata yayi cupping fuskanta da hannahenshi wnn karon muryarshi na nuna yana dab da breaking down yace"i want to spend every fucking day of my life with you, God! how i feel about you scares the fuck out of me...i want to be always around you, i want to always love you, i want to always serve you, i want to always....."bai karasa ba ta dora finger dinta akan bakinshi tana girgixa mishi kai a hankali idonta har ya ciko da hawayen tausayinshi tace"stop saying that Ayaan, it's not going to work"...tun bata rufe baki ba yace"why?"...tace"because i'm older than you, na girmeka da 4 years ko ka manta ne?, so kawai mucigaba da zana frie......" bata karasa ba itama ya katseta da cewa"no kar kice haka plss, I don’t want to be your friend i want to be your boyfriend", kallonshi kawai take tana girgiza mashi kai alamar hakan bazai taba yiwuwa ba, fahimtar hakan yasashi sake riko hannunta yana kallon tsakiyar idanunta yace"look, you don't have to love me as much as i love you, but plsss just love me plsss Juwairiyya plsssssss"...ya karasa mgn hawaye na cika idanunshi don idan tace bazata iya aurenshi ba sbd ta girmeshi mutuwa zaiyi.

Hannu Juwairiyya takai tana share mishi hawayen da the more tana gogesu the more suna sake sauka kan fuskan nashi dukda cewa itama nata idon hawayen ne cike taf a ciki na tsananin tausayinshi tace"its ok stop crying, i'll think about it sai in baka amsa daga baya"...bude idanuwan da sukayi jagab da hawaye yayi yana turo mata bakinshi kmr wani dan yaro yace"promise?"...saida ta saki smile dukda halinda take ciki kafin tace"yeah promise?"...yace"you are not going to say no, are you?"...shiru tayi tana kallonshi kmr baza tayi mgn ba can dai tace"am not"...rungumeta yayi gam a jikinshi yanajin inama yana iya maidata jikinshi su zama abu daya shikam da yayi haka ko don ya gujema duk qaddarar daka iya shiga tsakaninshi da ita...cikin raunin murya ya sake ce mata"main tumse bohot pyaar karta hoon Ju"(i love you so much Ju).

Lumshe ido Juwairiyya ta sakeyi hawaye na gangarowa saga idanunta na tausayinshi amm bata iya ce mashi komai ba, he hugged her for like five mins kafin ya saketa yana karasa share tears dinshi...itama goge nata tayi kafin ta kalleshi da alamun gajiya tattare da ita tace"ka rakani gida pls"...ba musu ya gyada kai tareda kama hannunta suka cigaba da tafiya kowa yana saqe saqe cikin zuciyarshi haka har suka iso gidanta, saida ya rakata har ciki kmr yanda ya saba snn ya saki hannunta ya maidasu kirjinshi ya rungume yana kallonta...har ta juya zata shiga ya kira sunanta a hankali yace"Ju"...dakatawa tayi tareda juyowa tana kallonshi ya shiga takawa a nutse har ya isa kusada ita ya sake hugging nata hade da pecking forehead dinta kafin ya dago yana dubanta da murmushi a fuskanshi yace"i love you, always remember that"...kallonshi kawai Juwairiyya keyi tanajin yanda duk ya sake jefata a cikin rudani...murmushin itama ta daure ta mayar mishi tareda ce mishi"good night"...daga haka ta shige ciki shi kuma ya fita ya kama hanyar tafiya nasu gidan duk jiki da zuciyarshi babu dadi sbd baisan amsar da zai samu daga gareta ba.

Daren ranar ko bacci kasayi yayi haka yaita juyi kan gado yana tunaninta, tun Lee na bashi baki yana karfafa mishi guiwa kan cewar zata soshi har yayi bacci nan kusa dashi amma shi babu ko alamun bacci cikin idanunshi...wajen karfe uku ya sauko daga gado ya shiga bathroom ya dauro alwala snn yazo ya fara nafilah yana rokon shidai Allah ya mallaka mashi Juwairiyya, baisan da yawa daga cikin abubuwan da mutum keso suna iya zamowa akasin alkhairi a tare dashi ba shiyasa a komai akeso mutum ya nemi zabin Allah ba zabinshi ba...haka har saida yaji bacci ya fara zuwa mishi snn ya idar da sallahr yayi addu'a ya kwanta a nan inda yayi sallahn bacci ya kwasheshi wanda da kyar ya iya tashi yayi sallahr asuba itama yana idarwa ya sake komawa wani baccin har saida gari ya danyi haske snn ya tashi yayi shirin tafiya school suka fita tareda Lee da shima ya gama nashi shirin.

Karfe biyu zasu gama lectures dinsu na ranar amma Ayaan kasa hakura yayi karfe biyun tayi ya fito sbd tun sassafe yake kiran wayar Juwairiyya baya shiga, yaje class dinsu kusan sau hudu daga safe zuwa yanzu ana ce mishi bata zoba tun yana daukan abun wasa har ya fara damuwa sbd bata taba yin irin haka ba gashi kuma har yanxu ya kasa samunta a waya duk yabi ya wani gigice sai kace uwarshi ce juwairiyyan.

Yana fitowa kai tsaye class din nasu ya koma amma har snn bata zoba, ya koma gidansu nan ma ba kowa a ciki, ya tambayi Nusy tace itama kanta batasan inda ta tafi ba shiyasa duk hankalinshi ya sake tashi...Lee ne ya biyo bayanshi don yasan ba cikin nutsuwarshi yake ba haka suka hadu sukaita nemanta a tare hadda Nusaiba amma ba ita ba alamarta...har gidan wani friend dinta Eric Nusaiba tace suje ko tana tare dashi nan ma ba kowa a gidan...zuwa yanzu hankalin Ayaan ya gama tashi gaba daya baisan dalilinda zaisa Juwairiyya ta kashe wayarta ba snn tayi disappearing ace tun safe ana nemanta baa ganta ba kuma baa sameta a waya ba...tashin hankali sosai ya sake shiga da yaga da gaske fa ba ganin nata zasuyi ba duk a rikice yake cewa"Lucas to kodai sbd bata sona ne ta tafi?...kilan bazata iya cemin bata sona ba shine ta tafi, dan Allah kuce mata ta dawo wlh bazan sake mata mgnr soyayya ba na hakura indai zan dinga ganinta kullum ya isheni, kuce mata ta dawo plsssss"...ya karasa mgn yanajin wani daci a cikin bakinshi.

Kallonshi kawai Lee keyi cikeda tausayinshi ganin yanda soyayya tayi mashi mummunan kamu tun da qananun shekarunshi...kama hannunshi yayi ya rike shima duk jiki a sanyaye yace"haba Ayaan take it easy mana, har shekaranka nawa ma da zaka daurama kanka wnn bala'in?...you are just 20 for God's sake kayi kankanta da daukan wnn pain din"...rungumeshi kawai Ayaan yayi yana sauke ajiyar zuciya as ko one word ya kasa fitowa daga bakinshi...zafi yakeji sosai a cikin kirjinshi, zuciyarshi gaba daya yakeji kmr zata baro kirjin nashi ta fito...shi kanshi yasan akwai kamshin gsky maganganun da Lucas ya fada yasan he's too young for all these, kila hadda karancin shekarun nashi ma yasa soyayyar ke bashi wahala har haka tunma kafin a fara dating.(shiyasa manya dai suke cewa komai na yaro saika tsinci yarinta a ciki, sorry Ayaan😜)

Ba Lucas ba kadai hatta Nusaiba saida ya bata tausayi ita kanta ta aminta ba karamin so yakema Juwairiyya ba...batasan meyasa tafi zargin Juwairiyya na tareda Eric ba don shine kadai wanda idan tana tareda shi bata zuwa school, fitinannen yaro ne na bugawa a jarida Kuma he's a bad influence a kanta amma Juwairiyya har yanxu ta kasa ganewa...da kyar Lee yaja Ayaan suka tafi gida da nufin idan sukaci abinci saisu sake fita nemanta tunda gashi har dare ya kusa suna abu daya...itama Nusaiba sallama ta musu ta tafi suma sukayi gida har snn kuma bai bar torturing kanshi yana cewa tayi hakuri ta dawo ba abun har ya fara ba Lucas haushi kuma.




***.
Rano✨