50 final book 1
🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾
Mallakar
KHADIJA WRITES
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)
⸻
💖 Dedicated To My Mom 💖
⸻
Nagode sossai da addu'o'inku jikina da sauki Alhamdullilah masu kira masu chat facebook and whatapps wanda nawa reply da wanda ban samu dama ba na karanta koma nagode
wannan paging sadaukar ne gare ku masoya a duk inda kuke khadija Writes na godiya marar adadi
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
🅿️-----50
da kyar Suhail ya shan ruwan da iman ta kawo masa ya jingina da gadon matsalolin zeenah kullum ƙaruwa suke
gaba ɗaya case ɗin da ya dawo da shi ma ya fita daga kansa
wayarsa ya dauko yayi dailing Numbe dinta abu daya ake ta fada masa wayar a kashe take
tashi yayi ya shiga bathroom wanka yayi ya saka jallabiya ya gabatar da Salla la'asar da bai samu yayi ba
ya gama kenan yana tattare bayan daya samu a prison daga Amina Iman ta shigo abincin ta ajiye ta koma bakin gadon ta zauna papper dake gaban sa take bi da kallo
ta fuskanci abinda aka rubuta ga kuma hoton Amina dake cikin files din
a hankali ta buɗe baki ta ce"yaya Suhail wannan ce ta kashe mijin nata"
da mamaki ya dago kai ya kalleta bai taɓa tunanin zata gane miye a gaban saba
"Eh,Iman"
takardun gaba daya ya miƙa mata ya ce"ki karanta sai ki taimake ni wajen warware matsalar my co-barr"
murmushi tayi ta amshi files din tana duba tare da karantawa cikin nutsuwa kusan minti Talatin ta shafe tana dubawa kafin daga bisani ta ajiye
yanayin fuskar ya dan sauya zuwa tausayi Suhail ya kalleta ya ce"uhmm ina sauraren ki"
hawaye daya soma zubo mata ta share Suhail ya ce"Iman a haka zamuyi aikin "
girgiza kai tayi cikin kuka ta ce"yaya Suhail na tausaya mata ne, i'm just imagining idan nice a halin da take ciki ya zanji kuma a bayanin ta ce lokacin da aka kashe sa tana asibiti kaga ba ita tayi kisan ba"
murmushi Suhail ya ce"idan karya take fa"
ajiyar zuciya ta sauke ta ce"mizai hana kaje asibitin ka tambayi likitan da yayi aiki ko babu CCTV Cameras ai akwai record da ko wani asibiti ke dashi lokacin da mutun ya shiga daku malokacin ya fita"
shiru Suhail yayi yana tunanin Shawarar iman tun da ya fara sauraren cases din hankalin bai kawo na yaje asibitin ba mamakin kaifin tunanin yake duk da ƙaranci shekarun ta ya lura da yadda take da tunani basirar da Allah ya bata
Suhail ya ce"zan je amman da sharaɗi ke zaki rakani"
fara'ar dake kan fuskar ta karu ta ce"zan raka ka"
anan suka ajiye maganar cewa gobe zasu je garin tsani Asibitin da Amina da mahaifiyar ta suka je
zeenah ba ita ta dawo gida ba sai bayan magariba Suhail ya zaune a falo yana kallo iman na Kitchen tana girka masu Abincin dare
ta shigo sanye take da riga da wando tayi rolling da mayafi hannun ta riƙe da jaka da makullin mota tana ƙarƙadawa sai taunar cingum take
cike da takun ƙasaita ta shigo falon bata ko lura da suhail dake kan kujera tayi hanyar uptsair
"zeenah daga ina kike"
a yadda yayi Maganar sai taji gabanta ya fadi shiru tayi bata ce komai ba
a fusace ya tashi ya ƙarasa wajen ta launin idanunsa har ya sauya kala cikin daga murya ya ce"Zeenah tambayar ki nake daga ina kike"
zeenah ta ce"daga inda aka san mutunci na da kuma amfani na nake mana, Suhail idan kana da kunya bai kamata ka tsaya kana tambaya ta daga inda nake ba tunda baka dauke ni a matsayin mata ba,baka cin abinci baka kula dani baka hira dani ba Abinda nake samu a wajen ka face kwanciyar aure ita da kana samun yadda kake so a wajen wancan kwailar matar taka nasan da baka zo ba"
Suhail ya kalli kofar Kitchen din a hankali ya sassauta murya sa ya ce"zeenah taya kike tunanin zaki sami farin ciki daga gare ni tunda baki iya kula da miji ba kuma batun kwanciyar aure dan Allah daga yau idan na shigo dakin ki ki rinƙa rufewa sai a ga ni dake waye zai fi cutuwa kinga da ganan sai a gane mai taimakon wani ni dake"
bata kara kulasa ta haye uptsair Suhail ya koma Kitchen dan tabbatar wa kansa Iman taji abinda zeenah tace ko kuwa
tana tsaya a Kitchen tana zuba abincin cikin flask Suhail ya kafta da ido ganin yanayin fuskar ta bata chanza ba amman a zahiri taji duk abinda zeenah tace kuma Suhail bai musanya maganar ta ba kenan ta tabbata gaskiyar Abinda zeenah ta fada akan ta bata biya masa bukatar sa yadda ya kamata
sai ta gama jera komai dinning ta koma dakin ta
washe gari da wuri ta rashi wanka kawai tayi kancewar girkin zeenah ne tea kawai ta hada da omlette taci
tana zaune a falon ƙasa tana jiran Suhail kamar yadda yayi mata alƙawarin zasu je tsauni tare
bata fi mintuna lalatin da zama Suhail ya fito cikin shigar sa ta ƙananun kaya white trouser sai daek blue din T-shirt ta kamfanin polo sai zuba Kamshi yake
ganin zaune a falo ya sa shi tabbatar wa kansa Iman ta damu da cases din nan kuma ba karya tayi ji kwana tayi tana tunanin halin da Amina ke ciki
fuska a sake ta ƙaraso kusa dashi "yaya Suhail ina kwana"
"morning Ammi's Daugther how was You night"
"Alhamdullilah"
tare suka fita har wajen motar key din motar ya miƙa mata ya ce"yau ke za kiyi driving din mu"
murmushi tayi wanda ke fito da zallah kyawun fuskar ta ce"yaya Suhail ni ay ban iya mota ba"
"Eh,na sani yanzu nake son ki koya ai"
"ka barshi next time zan tuƙa idan na koya"
murmushi Suhail yayi ya buɗe mata front seat ta shiga kafin ta dawo nasa seat ya tada motar suka fita
duk abinda ya faru akan idon Zeenah dake tsaye bakin taga komawa tayi kan gado dabas ta zauna wayar ta janyo ta rasa wanda zata kira ta fada masa halin da take ciki ko zata samu sauƙin ciwon da take ji a cikin Zuciyar ta
mahaifiyar ta kira koda ta dauka ta fashe mata da kuka tana faɗin "mommy Suhail baya sona momy ya fitata matarsa a kaina naya kula dani"
hajiya ta ce"hold on zeenah,duk abinda ya faru bana ganin laifin kowa sama dake babu namijin da Ai iya jure halayen ki Suhail mutun kirki ne babu ta yadda za'ayi ya sauya maki haka nan kawai ko ni da nake mahaifiyarki haƙuri nake dake idan zaki chanza ki chanza idan ba jakabkar ki kara kawo min karar mijinki i have nothing to do"
tana Gama fadan haka ta Katse wayar wayar take zeenah ta sake fashewa da wani sabon kukan har sai sa jennifer taji ta shigo dakin
hankalin a tashe ta ce"Ma lafiya ko baki da lafiya ne"
tana ƙoƙarin taɓa ta ce"jennifer leave my room idan ba haka ba zan huce a kanki"
jin haka jennifer tayi ficewar
tafiya suke a mota cike da hirar masoya har suka ƙarasa garin tsauni a kofar asibitin ya faka wanda ke nesa da gari a kofar Asibitin an rubuta
General hospital tsauni security ya buɗe masa kofar ya shiga cike da tarin tambayoyi duk a zatonsa masu kula da Asibitoci ne ba kasaifa manya Mutane irin haka ke kawo bqa asibiti ziyara ba
Ku dan rage da wannan zuwa gobe
share
like
and comment