ALIYU HAYDAR

Chapter 14

by @nieemartullah

Bayan sunyi sallar maghrib suna cin abinci aunty Naja tazo tace ma mom ta gama gyara dakin da ta saka ta,sannu tayi mata tace zata iya komawa bakin aikinta mom ta kalli ummi tace Hajjaju muje kiyi wanka ki huta nasan jikin naki babu qwari sosai,toh Ummi tace tare da miqewa ta bi bayan mom,bayan duk sun gama cin abincin JAY tace Munarh zo muje kema kiyi wanka sai ki kwanta kiyi bacci,toh tace mata ta miqe tabi bayanta tana riqe da hannun Ayaanah..................
Raj!Raj! kazo kana da baqi, tohm sweetheart ina zuwa, mintuna kadan sai gashi ya fito sanye da Moroccan jallabiya, yana ganin wanda suke zaune a parlour murmushin fuskar sa ya fadada Saleemarh kune yau a gidan namu ba sanarwa? Kai Sooraj kaji tsoron Allah yanxu don zamu xo gidan ka har sai mun fada maka,toh ko mu koma inda muka fito ne since we are not welcome here? Dariya yayi yace ke matsala ta dake ba'a yi maki wasa toh sannun ku da zuwa Shaheedarh ce tace yawwa yaya, ina yini,lafiya qlau yasu aunty duk lafiyan su qlau, sweetheart baki kawo ma su Saleemarh ko ruwa ba? Dagowa tayi daga kallon da take yi tace amma Raj kana gani kallo nake yi and besides ai naga ba baqi bane a gidan nan sun san ko wani lungu da saqo na gidan nan They can get anything they want by themselves ta fada ba tare da ta kalli inda suke ba, tunda ta fara magana Saleemarh ke tsaye tana jiran jin wani kalan hukunci Sooraj  zai dauka ga mamakinta sai kawai taga yayi dariya yace yeah you are right,Saleemarh you can go to the kitchen and get something for you and Shaheedarh  zuciyar ta kamar zata faso qirjinta ta fito haka take ji amma ta wayen ce tace kar ka damu we are full daga gida muke, ba tare da tunanin komai ba yace tohm shikenan, Shaheedarh yaushe kika zo Abuja ne babu sanarwa murmushi tayi tace yaya gidan aunty Saleemarh naxo kuma tun last week nake cema aunty Saleemarh mu zo gidan ka tace wai sai yau,toh ya ban ganki da akwatin ki ba?don gaskiya anan zaki har ki gama hutun ki tabbb wallahi aunty baza ta yadda ba Saleemarh da take jin kaman ta kama Sooraj ta rufe shi da duka bata ce masu uffan ba a cikin maganar da suke yi tana zaune tana girgiza qafa,bayan ta gama kallon series din da take kallo a zeeworld ta miqe tace Raj idan ka gama dasu ina jiran ka ina so muyi magana,bari na zo muyi magana ai su Saleemarh ba baqi bane zasu iya jira har ya juya a fusace Saleemarh tace kaga mallam muna da wurin zuwa sai anjima ta miqe taja hannun Shaheedarh suka yi hanyar qofar parlour ganin kaman ran su ya baci yasa yabi bayan su lokacin har ta shiga mota tana qoqarin yin reverse,knocking yayi ta bangaren driver inda Saleemarh ke zaune,da kaman baza ta bude ba sai kawai ta bude tace mallam lafiya duk irin walaqancin da kuka yi mana kai da matar ka bai ishe ka ba ka manta wani abu ne da baka fada mana ba ka biyo mu ka fada mana ?ta fada a zafafe kaman zata kai masa bugu,Subhanallah kar kice man laifi muka yi maki?wani banzan kallo ta watsa mashi tace ai sai ka qara ganin qafar mu a gidan ka sannan kai da figaggiyar matarka me kama da mariqar lema zaku samu damar yi mana rashin kirki bata jira me zai ce ba tayi ma motar ta reverse har ta kusa bige shi, baiga wani laifin da suka mata ba gashi ya santa da exaggerating abubuwa don haka be saka komai a ranshi ba ya wuce cikin gida kiran da Layla take masa .................................................
Don Allah ka fada man meke faruwa tun bayan zuwan uncle HAYDAR naga kamar kana cikin damuwa,don Allah ka fada man abinda ke faruwa ko wani abu ya faru ne? Babu abinda ya faru kawai dai matsalolin HAYDAR ne, gaskiya dai bana jin dadi kawai duk lokacin da uncle yake cikin matsala shikenan zaka hana kanka sukuni?nima ka hana ni,kasan dai duk lokacin da baka cikin walwala nima raina baya yi man dadi, ya kamata ace matsalar mu ita ce zaka saka a ranka, amma fah uncle is just a friend to you and nothing more, mune family dinka,mu ya kamata ace kana damuwa da abinda yake faruwa damu,tunda ta fara magana yake kallonta yama rasa abinda zai ce mata,girgiza kai kawai yayi ya kuma yi murmushi yace baxa ki taba fahimtar waye ko kuma ya HAYDAR yake a wuri na ba idan har na cika dan halak toh ya kamata na dauki matsalar HAYDAR fiye da yadda zan dauki tawa matsalar baki san yaya muke da HAYDAR ba?kawai na aure kine kin ganshi a matsayin aboki kuma amini na amma duk da haka zan baki wani dan taqaitaccen labarin alaqar mu da shi maybe daga nan zaki iya fahimtar meyasa a kullum nake daukar damuwar HAYDAR na saka a raina sama da tawa,Shekaru talatin da biyar da suka wuce,a wata unguwa Lagos street a garin Maiduguri knocking aka yi a jikin gate din wani gida mai gadi ya fito ya bude ganin mace a tsaye yace shigo mana hajiya shigowa tayi tace sannu baba ina yini, lafiya qlau hajiya sannu da zuwa ki shiga tana ciki,toh tace masa sannan ta nufi hanyar da take tunanin ita ce entrance din parlour,tayi knocking sannan ta murda ta shiga da  sallama daga can cikin daki a amsa mata sannan aka ce ina zuwa, bayan dan mintuna sai ga wata matashiyar mata ta fito daga daki sanye da baqar jallabiya baqa mai hula irin ta mata,tana ganin baquwa zaune tace sannu da zuwa,yi haquri na barki kina jira, murmushi tayi tace babu komai ai,kitchen ta shiga ta dakko mata ruwa da snacks ta aje mata sannan ta zauna,ruwa ta dauka ta sha sannan tace nasan baki gane ni ba ko? Murmushi tayi tace tace lallai akwai ki da qi fadi,toh gaskiya bama ki sanni ba na dai shigo ne musan juna, suna na Asma'u amma duk mutane da Husnarh suke kira na gida na yana kallon naki,tunda ke baki shigo ba nace ni bari na riga ki samun ladan, murmushin fuskar ta ne ya fadada tace amma har naji kunya ina ta zan shiga mu gaisa Allah bai yiba sai gashi ke kin riga ni,nima bana dan jin dadi ne shiyasa amma ayi man afuwa ni kuma suna na Saudart, laaa babu damuwa wallahi keda kike fama da kanki Allah dai ya raba lafiya tace Ameen,toh na gaishe ki ni zan koma sai mun qara gaisawa ta fadi hakan tana miqewa, kai Husnarh ba dai har tafiya ina ta murna na samu me dauke man kewa zaki ce zaki tafi? Don Allah ki bari sai zuwa anjima sai ki tafi gashi ko abinci ban kawo maki ba kar ki damu next time idan naxo sai naci abinci,da haka ta samu tayi convincing dinta ta barta zata tafi,har bakin gate ta rakota ta kuma yi mata alqawarin ita zata zo in shaa Allah,bayan kwana biyu itama taje gidanta daga haka alaqar su tayi qarfi suna zumunci sosai a tsakanin su har ta kai ga mijin kowacce a cikin su yasan dayar har ma suna gaisawa a tsakanin su wata rana da yamma Husnarh ta kira wayar Saudart amma bata dauka gashi zasu yi dare don sun shirya ne akan zasu je kasuwa yin siyayya gashi yamma nayi Saudart bata dauki waya ba hakan yasa ta yanke shawarar shiga ta duba taga ko lafiya,tayi sallama amma ba'a amsa mata ba hakan yasa ta wuce bedroom din Saudart tayi knocking amma shiru da har ta juya zata koma wata zuciyar tace ki shiga ki gani ko ba lafiya ba,handle din qofar ta kama ta murda sai dai abinda ta gani ya kusa sa numfashi barin qirjin ta Saudart ce a kwance babu alamar rai a tattare da ita da farko rasa abinda zata yi ma tayi sai daga baya ta aro jarumta ta shiga toilet ta debo ruwa a hannunta ta shafa mata amma a banxa hakan yasa ta qwalawa mai aikin Saudart kira bayan tazo tace ta taimaka mata su kama ta su fita da ita su kaita asibiti,da taimakon me aikin Saudart suka sakata a mota driver ya jasu zuwa asibiti, suna zuwa aka kar beta akayi emergency da ita, tun bayan da suka shiga da ita emergency ta ma rasa wani kalan tunani zata yi,bayan kusan mintuna arba'in likitoci suka fito,tambayar yaya jikinta ta fara yi masu wani likita yace ta biyo shi office,bayan ta zauna ta qara tambayar shi yaya jikin nata?ta farfado? Yaya abinda ke cikin ta?Ka fada man gaskiya menene ya sameta?calm down hajiya jikinta da sauqi babu abinda ya sameta and Alhamdulillah kin kawota a lokacin da ya kamata so bata cikin ko wani irin hadari shima abinda yake cikin ta lafiyan sa qlau,sai a lokacin hankalinta ya kwanta,munyi mata scanning and kuma komai normal da ita da babyn ta duk suna lafiya munyi mata allura ne don ta samu ta dan yi bacci ta samu nutsuwa,godiya tayi ma doctor din sannan ta fito daga office din sai a lokacin ta tuna bata fadama kowa abinda ya faru ba gashi ta bar wayanta a gidan Saudart,reception taje ta ari wayan wata Nurse tayi dialling number mijinta bayan ya dauka tayi masa bayanin abinda ya faru tace ya fada ma mijin Saudart don yasan abinda ke faruwa, bayan mintuna goma sha biyar sai ga mijin Saudart yazo tare da mijin Asma'u, wurin likita suka je yace masu wata matsala yace da ta tashi daga baccin da take yi idan bata jin komai za'a bata sallama,sosai hankalin su ya kwanta da suka ji haka,sai bayan sallar isha'i ta farka don lokacin har Asma'u taje gida ta dafa mata abinci, bayan ta tashi babu ciwon komai tayi sallah amma kuma ta kasa cin abincin da aka dafa mata likita yazo ya duba ta ya basu sallama,lokacin da suka koma gida Asma'u tace Saudart me kike son ci na dafa maki,girgiza kai tayi tace bana jin cin komai amma da zan samu shi zan iya ci miqewa Asma'u tayi tace toh shikenan dama ina da zogale a fridge sai nayi maki kwadon shi,mijin Saudart yace muna ta saka ki dawainiya murmushi tayi tace babu komai ai Saudart kaman yar uwa na dauketa,anan ta bar Saudart da mijinta ta wuce gidan ta babu bata lokaci ta hada ma Saudart kwadon zogalen,bayan ta gama ta zuba shi a food flask dinta ta dawo,tunda taga kwadon take ji kaman yawun bakinta zai zubu,Asma'u ta tafi dakko plate a kitchen tana dawowa ta tarar har ta fara ci a cikin flask din,dariya tayi tace kai Saudart kaman zai gudu tana kai wani bakinta tace baza ki gane bane rabo na da wani abu ya shiga cikin ciki na tun shekaran jiya gashi kuma yau na samu abinda naji inaso,a haka lokaci ya wuce sakanni suka koma mintuna,mintuna suka koma awanni,awanni suka koma ranaku,ranaku suka koma satittika,satittika suka koma watanni yau cikin Saudart ya shiga wata na shida dama a cikin watannin nan yau lafiya gobe babu yau suna gida gobe suna asibiti kullum Husnarh ita ke tare da ita tana bata kulawa,yau ma ta tashi bata jin dadi amma haka ta daure take nuna jarumta don bata son daga ma makusantanta hankali lokacin da dare yayi matsanancin ciwon ciki ya kamata da qyar ta janyo wayarta ta kira mijinta amma bai dauka kasancewar yana cikin meeting babu yadda ta iya ta kira number Husnarh,Husnarh na ganin kiran Saudart a irin wannan lokacin gabanta ya fadi bata iya daukar wayar ba kawai ta saka doguwar riga ta fito ta wuce gidan Saudart tana shiga ta ganta a kwance a parlour tana murqususu,da sauri ta kamata ta fito da ita tayi ma driver magana ya zo ya tafi dasu asibiti,a lokacin da suka isa asibiti ita ma Husnarh ta gama galaibaita itama ana fara attending Saudart Husnarh itama ta fadi a qofar dakin da aka shiga da Saudart itama ta suma, gadon dake gefen na Saudart aka kwantar da Husnarh,lokacin da Saudart ta farka taga Husnarh kwance a gadon asibiti itama ta shiga damuwa sosai ta rinqa blaming kanta tana ganin kaman itace tayi sanadin kwanciyar Husnarh a gadon asibiti,wayar Husnarh dake ajiye a gefen drawer din da aka kwantar da ita ta dauka ta kira number mijin Husnarh ta sanar masa suna asibiti,hankalin shi a matuqar tashe yace mata yana zuwa,bai dauki lokaci ba ya qaraso yana zuwa lokacin likitan ya dawo da result din gwajin da aka yi masu su duka biyun,results din Saudart ya fara budewa yace madam ya jikin da sauqi doctor toh masha Allah haka dama nake son ji amma ya kamata ace kina yin exercise ko da a cikin gida ne ki rinqa zagayawa toh shikenan doctor  amma ya jikin yar uwata yake,kar ki damu babu komai ita ma stress ne yayi mata yawa ita da abinda ke cikinta shiyasa tayi collapsing tana da ciki ne na tsawon watanni biyu amma babu wata matsala,wannan ahalin sunyi matuqar murnar da alqalamina bazai iya rubutawa ba,a haka suka ci gaba da tattalin junan su,Allah yasa Husnarh bata da laulayi mai wahala hakan yasa bata wani shan wahala ta cigaba da kula da Saudart har zuwa watan haihuwar Saudart ya shiga,amma bata haihu ba sai da cikinta ya shiga wata na goma wata ranar talata cikin dare Saudart ta fara naquda tun tana iya jurewa har dai ta kasa ta fada ma mijinta abinda ke faruwa,tunanin kiran mijin Husnarh yayi amma sai yayi tunanin itama tana fama da kanta, ganin babu yadda ya iya yasa yayi dialling number mijin Saudart,bayan ya dauka suka gaisa yace don Allah a fada ma Husnarh Saudart ce ke labour tana jin haka ta saka hijab tace masa su tafi,dama a asibitin suke awo,saboda haka suna zuwa aka karbeta tun cikin dare suke asibiti har gari ya waye ana abu daya,kowa sai da ya tausayawa Saudart saboda irin wahalar da take sha, har zuwa maghriba ta ranar laraba bata haihu ba har likitoci ma sun fidda ran zata iya haihuwa da kanta,ana ta shirye shiryen yi mata CS Allah ya bata iko ta haihu da kanta ta haifi dan ta namiji qato da shi, tana haihuwa ta buqaci ganin Husnarh, bayan an shiga da ita dakin da take ta kama hannunta ta riqe cikin nata sannan ta bude baki a galabaice tace Husnarh ga amana nan na baki ina ji a jiki na mutuwa zanyi saurin toshe mata baki Husnarh tayi tana girgiza mata kai tace don Allah ki dena fadin haka kina karya min zuciya don Allah ki bari ta fada tana goge hawayen dake idonta,mutuwa ta zama dole Husnarh ko yau ko gobe ko mun shirya ko bamu shirya mata ba,nasan mahaifin shi ba mai kula da abubuwan dake faruwa bane,ina son ki kula min da kyautar da Allah ya bani,ki zama bango abin jingina a rayuwar sa,ki cike masa gurbin uwa da ya rasa,da ace mahaifiyata na dai rai nasan zata kula min dashi amma yanxu ke kadai nake da yaqinin zaki kula dashi kaman yadda zaki kula da naki da zaki haifa,don Allah ki dena wannan maganar kina sawa ina losing duk wani hope da nake dashi don Allah ki bari ta fada tana hade hannayenta alamar roqo,ashe duk maganar da suke yi jini ne ya balle mata don kar ta daga ma Husnarh hankali yasa tayi shiru zata qara wata magana jikin ta ya fara jijjiga,Husnarh bata san lokacin da ta kwala kiran doctors ba,suna zuwa suka ce ta fita su duba ta tace a'a babu inda zata je don gani take tana fita za'a ce mata Saudart ta mutu da qyar suka fitar da ita daga dakin suna qoqarin ceton rayuwarta amma inaa tuni rai yayi halin sa,lokacin da doctors din suka fito kasa magana suka yi ganin sunqi cewa komai yasa Husnarh ta sha gaban su tace doctor ka fada min ya jikin yar uwa ta yake,yayi shiru bai ce komai ba lab coat din shi ta kama tana jijjigawa tace doctor me kayi ma yar uwata ka fada min me kayi mata ta fada tana kuka mijinta ne ya qaraso ya riqe ta yana patting bayan ta,a hankali likitan ya fara magana calm down madam ya kamata ki nutsu ko dan abinda ke cikin ki kar ki cutar da  shi, toh naji amma kayi ma Allah ka fada min halin da yar uwata take, ke musulma ce kuma ina da tabbacin kin yarda da qaddara me kyau ko akasin hakan and rayuwa da mutuwa duk suna hannun Allah ne kiyi haquri Allah yayi mata rasuwa,yana gama magana taji kaman an saka mashi an soki zuciyarta,luuuu tayi baya zata fadi mijinta ya riqe ta, a lokacin ta nemi kuka amma yaqi zuwa sai a lokacin ta fahimci idan tashin hankali yayi tashin hankali kukan ma neman sa ake a rasa,suka gama duk wani cike cike da ya kamata aka basu gawarta suka taho tun a lokacin da aka sanar da mutuwarta mijinta ya kira waya ya sanar da maku santanta,bayan sun koma gida aka yi mata sutura aka tafi aka rufe ta a gidanta na gaskiya,tun bayan da aka dawo daga binne ta step sister dinta da step brothers dinta suka ce to su zasu tafi baza su zauna zaman munarfici ba wata a cikinsu ne ta kalli Husnarh tace naji ance wai ke ta barma wasiyyar kula sa jinjirin da ta haifa toh Allah ya baki wuyan dauka don dama tasan babu wanda zai mata rainon danta tunda mu ba bayinta bane muma muji da namu,bayan sun gama fadin hakan suka kada kai suka tafi,tun bayan mutuwan Saudart Husnarh ke kula da jaririn da ta haifa,ranar da ta kama sati daya da haihuwa aka rada ma yaro suna Usman ake kiran shi Zannur,mijin margayiya Saudart yana matuqar jin tausayinta saboda ga ciki tana fama dashi ga raino amma a haka bata taba nuna ta gaji ba ko da kuwa sau daya,mahifiyar mijin Saudart da kanta tazo gidan Husnarh aka ta bata Zannur ta cigaba da kula dashi saboda ita ma tana buqatar me kula da ita amma taqi tace ai ita yanxu ta tsufa bai kamata a dora mata dawainiya ba idan ba'a kai mata me kula da ita ba aikuwa ba'a dora mata dawainiyar kula da jinjiri ba,duk yadda taso karbar Zannur Husnarh ta bata haquri,ganin ta dage yasa tace toh shikenan Allah ya mata albarka ya kuma sauke ta lafiya tace Ameen,tun daga nan idan akayi sati haka tsohuwar nan zata zo ganin Zannur ta kuma taho masa da madara da kayan sawa,ana haka har cikin Husnarh ya shiga watan haihuwar shi tun daga lokacin da ta shiga watan haihuwar ta kullum tana cikin faduwar gaba,cikin iko na ubangiji wata ranar lahadi da daddare ta fara naquda zuwa washe gari litinin da asuba ta haifo santalelen danta itama,tun bayan haihuwar Husnarh abubuwa suka fara yi mata yawa,ga kula da Zannur ga kula da yaron ta,gashi ba wani shekaru ne da ita ba,ranar suna aka rada ma yaro suna ALIYU ana kiran shi da HAYDAR,ganin haka yasa mijin margayiya ya fara neman aure a nan ne kuma ya hadu da wata mata me suna Ruqayya ya aure ta bayan auren su da wata biyu ya buqaci Husnarh ta bada Zannur domin Ruqayya ta cigaba da kula dashi ita ma ta huta, a nan tayi tsalle ta dire tace ita bata san zance ai bata ce ta gaji ba,sai da aka kai ruwa rana sannan Husnarh ta yarda ta bada Zannur shima da sharadin za'a na kawo mata shi duk weekend,duk lokacin da za'a kawo mata shi weekend sai taga kaman tabo a jikin shi wani lokacin kuma kaman shatin bulala tun bata maida hankali akan abin har hankalinta ya fara zuwa wurin wata rana sai taga kaman qunar wuta a hannun shi,hakan yasa lokacin da ta maida shi gida tace Ruqayya ni naga kaman qonewar wuta a jikin Zannur garin yaya ya qone?sai ta fara kame kame tace ranannan ne na aje kaskon turaren wuta da garwashi a ciki ya sa hannun shi a ciki kin san shi da qiriniya, bawai don ta gamsu da abinda ta fadi ba tace a'a fah Zannur baya da qiriniya wannan wauta ce ki rinqa ajiye garwashi bayan kin san akwai qaramin yaro a gidan gaskiya ki kiyaye, tana ta kame kame tace in shaa Allah baza a sake ba,bayan Husnarh ta fita tace yen yen yen tana wani yi man fada kaman wata babata mata sai shegen shishigi ke ba yar uwar su ba ba komai ba sai shegen shishigi dani kike zancen,a haka har Zannur ya cika shekaru uku a duniya wata rana an kawo mata shi weekend tazo zata yi masu wankan bacci shi da HAYDAR taga shatin quna a bayan shi,bata ce komai ba ta bari sai da ta zo tana shafa masu mai tace yaron mamanshi menene ya sameka a bayanka yaro babu wayo yace aunty ce ta sa abin cin abinci a akan wuta shine ta sa min abin cin abincin a baya na ni kuma nayi ta kuka kuma tace idan na fada ma daddy sai ta yanka ni ni kuma naji tsolo ban fada mashi ba,shikenan yaro na amma daga yau duk wanda yayi maku wani abu ko kai ko dan uwanka ka fada man kaji toh Mamy that's my boy high five ya bata hannun shi suka tafa ko baban HAYDAR bata fada ma ba saboda tasan zai ce mata a bi komai a hankali sai da ta bari dare yayi kuma tana da tabbacin baban Zannur ya dawo sannan ta dauki waya ta kira yan sanda ta shigar da report sannan ta basu address din inda zasu zu tana gama kiran su tace ma baban HAYDAR zasu shiga maqota yace mata a dawo lafiya,a qofar gida ta tsaya har yan sanda suka qaraso sannan tayi leading dinsu zuwa cikin gidan,suna zaune a parlour suna kallo suka ji sallama,izinin shigowa suka bada Husnarh ce ta fara shigowa sannan yan sandan suka biyo bayan ta,miqewa tsaye yayi yace maman yara lafiya?ta hade rai tace lafiya qlau wurin matar suka zo, maman yara kaman yaya wurin Ruqayya suka zo ban fahimta ba? Eh yanxu xanyi maka bayanin da zaka fahimta kwantar da hankalin ka, Zannur ta kamo ta bude bayan shi tace ina fatan ka san menene wannan,wannan ai kaman quna ko? Eh dan quna quna ce amma ba wai qonewa ce ta tsakani da Allah ba qona shi aka yi,matar ka ta saka spoon akan wuta yayi zafi ta dauka ta saka shi a bayan wannan dan alhakin kuma tace idan ya fada maka zata yanka shi,toh kafin ta kashe man da ni zan dauki matakin da ya kamata akan ta kaga officer ku tafi da ita duk wani bayani daga baya sai ayi shi a station din,zai yi magana tace baban Zannur kar ka bari kaima ka shiga cikin black list dina don wallahi ba zata yi maku dadi ba ka bari su tafi da ita duk abinda za'ayi sai ayi daga baya,ganin ranta ya baci sosai yasa yace shikenan toh amma ayi man alfarma na kawo ta da kaina tace wannan kuma ba matsala,haka kuwa aka yi ta koma gida ta kwantar dasu sannan tace me aikinta tana kula dasu,dakin mijinta ta wuce tayi masa bayanin abinda ke faruwa yayi ta fada akan dalilin da yasa ta kira yan sanda haquri ta bashi tace yanxu dai muje ka kaine station din mu gama abinda za'a yi,haka ya dauketa suka tafi station din,lokacin da suka je sun tarar ana tuhumar Ruqayya akan qarar ta da aka kawo, babu kunya ko alamar tsoro a idanun ta tace eh ta aikata ai ita da aka tashi auranta ba haka aka ce mata raino zata zo yiba,don haka su shirya ganin abinda yafi haka daga gareta idan har ya zama ita ce zata na kula da Zannur,sannan ta dauki waya ta kira brother dinta C.P suna gama waya tace masa toh yaya,mintuna biyu sai ga D.P.O ya fito yana zuwa yace suyi haquri order ya samu daga sama akan cewa ayi watsi da case din don haka suyi haquri,abin yayi matuqar taba ran Husnarh ta dauki waya ta kira surukar margayiya ta fada mata duk abinda ke faruwa,sosai itama ranta ya baci tace mata shikenan gata nan zuwa gidan nashi a daren nan,bata cewa kowa komai ba suka hau motocin su suka dauko hanyar dawowa gida,a cikin motar ta cewa baban HAYDAR,idan sun qarasa zata tsaya gidan su Zannur yace mata saboda a qara yin wani tashin hankalin ko?ke baki son a zauna lafiya,wannan halin gaba daya ba naki bane kin dakko kin ara kin yafa,ita dai bata mashi musu ba tace Allah ya huci zuciyar ka ranka ya dade dama kakar Zannur ce ke son magana damu,amma idan kace bazan jeba babu matsala sai na bata uzuri kawai, a'a ba sai kince mata komai ba amma don Allah banda tashin hankali tayi dariya tace in shaa Allah,a qofar gida ya ajiyeta sannan ya shiga da motar cikin gida, tana shiga ta tarar suma sun qaraso ita ake jira ta tsugunna ta gaishe da hajiya sannan ta nemi wuri a qasan carfet ta zauna,hajia ta tambayin ba'asin abinda ke faruwa Husnarh tayi mata bayani bayan ta gama ta kalli shi tace Abdullahi abinda ta fada gaskiya ne ya sunkuyar da kanshi qasa kaga ba cewa nayi ka sunkuyar da kai ba kaman tsohon munafiki amsa nake son ka bani,eh haka ne hajiya,toh masha Allah Abdullahi! Na'am hajiya Abdullahi! Abdullahi sau nawa na kira sunanka?sau uku hajiya toh da kyau abinda nake so da kai yanxu ba sai anjima ka saki wannan munafukar figaggiyar matar taka don wallahi idan har ni na haife ka ba daga sama ka fado ba,ban yadda ta kwana da igiyar auren ka a kanta yau ba,nima hajiya ba zan iya cigaba da zama da ita ba bata san jini na ba amma da kin bari zuwa safiya yanxu kusan qarfe tara da rabi na dare nefa,bai dameniba ko karfe dayan dare ne dole yau ka sake ta,toh shikenan hajiya yadda kika ce haka za'a yi Ruqayya kije gida na sake ki saki daya,a gigice ta miqe tace dama Abdallah zaka iya saki na?don Allah ka ceman mafarki nake yi wallahi ina son rayuwa da kai don Allah kace man wasa kake yi ba dagaske kake ba, bakya sona kuma ba kya son rayuwa dani tunda bakya son jini na,goge hawayen idanunta take yi amma sunqi tsayawa tace irin sakayyar da zaka min kenan ko Abdallah,babu komai idan ka rabu dani dubunka zasu zo kuma kaima ka sani in banda soyayya na fi qarfin level din ka talk less of auren ka,kaima ka sani alfarma nayi maka na aure ka,to tunda alfarma kika yi masa yanxu ai sai ki je ki auri wanda yake dai dai da level din naki cewar hajiya,bata qara cewa komai ba tayi hanyar waje,tun daga wannan rana komai na kula da tarbiyar Zannur ya dawo hannun Husnarh,duk wata kulawa da zata ba HAYDAR ita take bama Zannur,sun taso kaman yan biyu komai nasu tare hatta da school iri daya ake saka su,ba'a taba banbanta tsakanin ALIYU da Usman kaya ma iri daya suke sakawa,sai a lokacin da suka fara girma ne sannan suka dena saka kaya iri daya, shi kanshi HAYDAR yayi man sadaukarwar da har abada bazan taba iya biyan shi ba yanxu don Allah Lateefah ki fada mun nayi laifi idan na dauki matsalar HAYDAR na saka ta a cikin raina har tana damuna?nasan ke kawai kina mana kallo ne na abotar mu ce tayi qarfi sosai shiyasa muka shaqu sosai da Mamy, amma ba haka bane, nayi maki uzurin rashin sani,amma duk wanda ya san cikakken labarin rayuwarmu ba zai taba ganin laifi na ba,Allah sarki Mamy,ban san meyasa ba kawai naji ina qaunarta tun kafin nasan irin sadaukarwar da tayi maka amma yanxu wallahi qimarta ta ninku akan yadda nake ganinta da,Allah ya saka masu da alkhairi ya biya su da gidan aljannah for all they have done to you murmushi yayi yace Ameen....................................
Suna fitowa tace don Allah kuzo ku raka ni bazan iya tafiya da ya Sadeeq mu kadai a mota ba zulaikha ce ta sa dariya tace tabbb rufa mana asiri kar kisa yaya yayi kwallo damu iya kacin mu bakin mota mu juyo Nafeesah da Hannah ta kalla with pleading eyes kafin tayi magana suka juya mata baya,Zulaikha ce kawai ta qarasa rakata har bakin mota sannan ta bude mata front seat, tace mata bye tana daga mata hannu, suna ganin motar ta fita daga gidan suka sa dariya Hannah tace ina ma ace ina cikin motar nan na kalli drama gaba dayan su suka fashe da dariya kaman wanda suka samu tabin qwaqwalwa......................