Chapter 04
by @teemerheart
Hakika anyi babban rashi a familyn nan don duk wanda ka gani fuskan shi cike take da jimami da damuwa rashin Hajiya kaka. Jana’iza Karfe goma za ayi saboda abba da Yaya Usman sun taso ba karmi tashi hankali su Aunty suke ciki ba.Asmirah ko ba a magana don tunda aka fada mata banda kuka babu abinda take yi ko fitowa wa daga daki batayi bah.
Karfe goma dae dae aka gudanar da sallar
Jana’iza aka kae Hajiya kaka gidan ta na gaskiya( idan tamu tazo Allah yasa mu cika da Imani Ameen).
Bayan kwana uku akayi addua da sadakan uku da bakwa. Da misalin Karfe takwas Abba ya tara kannen sa duka a parlor yayi musu nasiha da surike zumunci don Allah sannan suna hakuri da juna kuma surike tarbiya da Iyayen su suka basu sai kuma batu na karshe shine batu akan Asmirah shi yana so ya dauke ta ya hada da yaran sa ya rike gaba to amma yanzu tana ajin karshe bai kamata a tsaida mata da karatu ba a Wannan gabar.
Aunty ta daura da fadin “Mungode sosae yaya Ubangiji Allah ya cigaba da kare ka ya kuma jamana nisan kwanan ka hakika munyi rashi na iyayen mu amma mun gode wa Allah daya bamu yaya wanda ya kasance tamkar uba a gare mu, Allah ya yiwa iyayen mu rahama “
Da Ameen duka duka amsa
“ sai kuma batun Asmirah ina ga ta dawo gida na sai ta cigaba
da zuwa makaranta daga nan Ina ga zaifi amma fa a nawa tuna nin fa yaya” Aunty ta fada
“ Aaa hakan ba zai yiwu ba Hafsat sam duk yawan mu ace Kina mace kece zaki dauki yar ki da take marainiya ina ai mutunci mu zae zibe sam Wannan ba shawar bace ku yaya ka gani Usman” Abba ya Karasa fadin yana duban yaya Usman
“ Dama ni jira nake naji daga bakin ita Hafsat din amma ni a gani na ma zai hana ta dawo gida na da zama tunda ni a gari nake” yaya bukar ya fada
“ Nima nayi Wannan tunanin Ubangiji Allah ya bamu ladan zumunc”Yaya Usman ya Fada
Da Ameen dukan su suka amsa.Aunty ko har kukan sanda tayi saboda yanda yan uwan ta suka nuna soyayyar su ka Yar ta,tai ta musu addu’oi da fa Dan Alkhaeri.
Kuwa yayi na’am da shawar da yaya bukar ya zo da ita kuma duka sun tsaya kan ta.Sai da Abba yace Iya shekara daya zatayi a gurin yaya bukar da zarar ta kammala karatun ta zai samar mata makaran ta a kaduna sai ta koma Chan da zama.
Abba ne ya umarci maman sadeeq da taje ta kira Asmirah da to ta amsa tare da mikewa ta nufi tsakar gida.A zauna ta hango ta ita kadai ta tafi duniyar tunani don ga dukkan alamu bata ma sanda futuwar ta ba ma sai Kawae ji tayi an taba ta a razane ta juyo. “Maman Sadeeq yaushe kika fito ko motsin ki banji bah “
“Ina zaki jini kin tafi duniyar tunani,tashi maza muje su yaya Muhammad suke kiran ki”
“Ni kuma Allah yasa laifi nayi ba maman Sadeeq zuciya na har ya tsinke wlh”
“ Ba laifin da ki Kayi kinji maza tashi muje kar suga mun dade” Maman Sadeeq ta fada tare da rike hanun ta suka nufi parlor
Cikin nutsuwa tayi sallama,sai da aka amsa mata sannan tashiga parlor ta zauna a kasa tare da gaishe ta iyayen nata,suka amsa mata cike da tausayawa a gareta hakika ta shaku da Hajiya kaka shiyasa da ka ganta zaka san tana cikin tashin hankali da damuwa sosae. Abba ne ya mai da duban sa gare ta tare da fadin “ Asmirah dago kanki ki kalle ni dukan mu nan iyayen ki ne ba wanda zai gan ki acikin damuwa kuma yayi farin ciki hakika munyi babban rashi sai dai Ubangijin da ya bamu ita kuma ya karbe ta ya fimu sonta,a yanzu haka babu abinda tafi bukata daya wuce addua Allah Ubangiji ya jikan ta da rahama”da Ameen duka suka amsa Asmirah kuwa banda hawaye babu abinda idon ta ke zubarwa.Sannan ya daura da fadi “ mun yanke Sharwa da sauran iyayen ki zaki koma gida kawun ki bukar da zama zuwa ki karasa karatun ki sai ki dawo kaduna ki cigaba achan in Allah ya yadda” ba karamin bugawa zuciyar ta tayi ba lokacin daya ambaci gidan Yaya bukar ita a duniya ma in Kawae gidan da ko aiken ma bata so ayi yawuce shine za ace ta koma chan da zama ina sam zuciyar ta bazata Iya dauka bah Innalillahi wa Inna ilaehirraji’un.
“Kin yi Shiru ko ba dake ake magana bane Asmirah” Aunty ta fada
“A’a kin ga kyaleta tashi ki je ciki Allah yayi miki albarka”yaya Usman ya fada.
Banda kuka babu abinda take yi a kan gado da tunani ya Zata fara rayuwa a wannan gida tare da matar gidan,Yaya bukar kam bashi da matsala to amma matar sa ita ce babbar matsalan gidan mata ce wacce take da fuska biyu indai ka ganta baza ka taba ce wa tana da matsala ba amma mundi kaje gidan ta anan ne zaka gane wacce ce ita saboda Asmirah ta taba zuwa gidan tayi sati biyu a lokacin ta Hajiya kaka tayi tafiya a nan ne tasan halin ta.
Bayan sun gama tattaunawa a tsaka nin su,suka yi sallama saboda gobe da wuri zasu kama hanya in Allah ya kaimu.Aunty ne dasu Maman Sadeeq suka shi daki suka tarar da ita tana kuka,dafa kafadar ta maman Haidar tayi tare da fadin “Hakika mun su daukar ki Asmirah amma ba yadda muka iya da umarni yaya Muhammad saboda tamkar uba yake a gare mu kuma insha Allahu muna da yaki nin yaya bukar zai rike ki tamkar yar da ya haifa a cikin sa haka kuma matar sa” dago Kai kawai Asmirah tayi ta dube ta tare da fadin “ maman haidar wallahi tsoron zama a gida nakeyi ban San taya zan fara bah”
“ Kiyi addua kiji ya’ta babu abinda zai faru insha Allah,Allah yana tare dake “maman Sadeeq ta fada tare da goge mata hawayen dake idanun ta.
Aunty ne ta daura da cewa “ kiyi hakuri Asmirah ni mahaifiyar kice yadda kike min biyayya insha Allah Nasara na tare da ke a Duk inda kike babu abinda zai same ki.Allah yayi miki albarka”
Da Ameen duka suka amsa “ Gobe da yamma insha Allahu zamu Kai ki gidan,don haka ki samu ki hada Kayan ki a nutse kar kiyi mantuwa” Aunty ta fadi tare da juyawa izuwa parlor daure wa Kawae ta Kayi abun ba karamin taba mata zuciya ya ke yi bah Allah ma ya sani yadda take son Asmirah taso ace ita ta dauke ta sai dai ba yadda ta Iya kuma tana rokon Allah ya bata kariya a Duk inda take ya kuma tsare da daga sharin mutum da aljan.