JODAH

01

by @sadisakhna


_____👑 *JODA* 👑_____


             




Na 


*Sadi-sakhna*


Ƴar mutan Jama'are




*JINJINA*


THE TRIO OF TALES 

(3⃣ minds, 3⃣stories,1⃣Journey) 


JODAH by sadi-sakhna

DAAÆŠIN ZAMA by seemawrites

ƘARFE ƊAYA BAYA AMO by gureenjoh


Wannan tafiya da zamuyi Allah ya haÉ—a kawunanmu ya kaÉ—e fitina da Sabani a tsikanunmu. Jinjina my Triple tales.



*GAISUWA*



Ga ɗaukacin Iyaye sannunku da ƙoƙari Allah yaƙara haɗa kan zuri'armu bisa hanya madaidaiciya.



*GARGAÆŠI*


Ban yarda a yanki wani sashe na littafina ba,ƙirƙiratace ni naje nayi bincike na tara bayanai na,dan haka ɗaukamin wani yanki na littafina bada yarda ta ba ban amince ba.



*ƘARIN HASKE*



Wannan labarin zai aukune a wasu shekaru da suka wuce a nahiyar africa,zan ambaci gurare masu ban mamaki,saidai bawai ƙirƙira nayi ba face dama sun wanzu a lokacin iyaye da kakanni. Ba shaci faɗi nayi ba.Domin gudun rashin fahimta ga kaɗan daga labarin waɗannan Dauloli (empire) da zasu zo inshaallah a cikin wannan labari na Joda.




Ƙasar africa a wannan ƙarnin nahiya ce data riƙe kambu na ƙarfin mulki da tashen arziƙi,wanda mafi yawan abinda ya kasance abin tunƙahon wannan nahiya shine zinare,da Allah ya albarkaceshi a ƙarƙashin ƙasar wajen.


Wannan nuna mulki da isa na ƙarfin izza ya wanzune a tsakanin jiga jigan dauloli guda Huɗu.



 ðŸ‘‘ *DAULAR MASAR (EGYPT EMPIRE)*  👑


Daular Masar DaÉ—É—iyar daulace data Wanzu cikin izza Æ™arfin kasuwanci,noma da sauransu. Inda ta zaba babbar cibiya na gudanar da kasuwanci tsakanin Sin(china),Indiya da kuma Yamen.  


Masar ta shiga Daular Musulunci ne a shekara ta 640–642 Miladiyya, lokacin da rundunar Musulmi ƙarƙashin Amr ibn al-ʿAs ta kwace ƙasar daga Roma (Byzantine). Wannan ne ya sa Masar ta zama ɗaya daga cikin muhimman cibiyoyin Daular Musulunci.



👑 *DAULAR GHANA* 👑



Daɗaɗɗiyar daulace data kafu Tun a shekarar 300C.E, Mutanen soninke sune suka kafa wannan daula,Tayi tashen fitar da ɗanyen zinare daga ƙarƙashin ƙasa na tsawon lokaci da zamani,inda har tasamu mulki daga sarakuna 144 a lokacin.


Addinin wannan yanki shine bautar gumaka,sai daga baya wajen 740CE aka fara samun yaÉ—uwar addinin musulunci a cikinta.


Mutuwar Daular Ghana ta farane wajajen 1328CE inda Daular mali mai biye mata baya ta mamayeta bisa jagorancin sarki Abu bakr, a ƙarni na 11th.




👑 *DAULAR MALI* 👑




Daular mali itace ta biyu bayan Daular ghana,duk da cewar daular ghana tafita daɗewa tana damawa da ragamar iko,saidai itakuma tafi daular ghana yawan arziƙi da kuma tashe a faɗin duniya.


Daular mali ta wanzune a ƙarƙashin jagorancin Sarki Mansa Fasih,wanda yakasance mutumin daya riƙe kambun wanda yafi kowa a ƙudi a zamaninsa,wanda har a yau ana ganin masu kuɗin yanzu basu kama ƙafarsa a dukiya ta zallan ɗanyen zinare ba.


Daular mali daula ce ta musulinci,wacce tayi babban aiki wajen yaɗa addinin musulunci a yammacin africa da kewaye. Saidai itama tayi ƙasane sakamakon Mutuwar Sarki mansa Fasih,wanda Sarki Sunni Ali wanda yakafa Daular Songhay ya cita da yaƙi a ƙarni na 16th.




👑 *DAULAR SONGHAY* 👑




Wadda itace daula da ƙarshe,duk da batakai sauran taka madafun iko da daɗewa ba saidai itama ta taka muhimmiyar rawa wajen mallakar dukiya da kuma iko mai ɗumbin yawa.


 A Æ™arni na 14 daular Songhay tana Æ™arÆ™ashin daular mali ne,bayan da tayi raunine itama ta samu nata madafar ikon a Æ™arnin 15, bisa jagorancin Jarumin sarki Sunni Ali,É—an addinin musulunci Æ™arÆ™ashin koyarwar Sunni. Wanda kafin haka kuma mutanene su masu yarda da bautar magabata ko kuma iskokai.


Daular Songhay tayi tashenta ne ta ƙare a tsakanin ƙarni na 15 zuwa na 16,hakanne yasakata zama daular mai gajeren Zango in an dangantata da sauran daulolin.


Daular Songhay shine yammacin africa a yanzu wanda ya haÉ—a dasu Nigeria,Niger,Chadi,Cameroo da sauransu.






...................👑*Sharar fage (prologue)*👑




Nahiyar Africa a shekara ta 728AH. Bayan hijira na fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW) wanda yayi daidai da 1327-1328CE.  Na miladiyya haihuwar annabi isah (AS).




.......A rayuwa Allah yayiwa ɗan adam baiwa, baiwa ta yayi tunani,yayi nazari sannnan yayi tafiya a tsaye batareda ya kifa gwiwoyinsa da hannyensa ba,domin ɗaga darajarsa fiyeda ta sauran halittu. Ya fifitasu akan komai daya halitta,ya basu ikon yin mai kyau domin ya saka musu,haka kuma shi mai yafiyane idan suka saba masa kuma suka dawo gareshi....... To amma mai zai faru idan su wannan halittun a cikinsu suke ƙasƙantar da wasu sashen daga cikinsu zuwa matsayin da yafi na dabbobi ma muni...!!

Shin sun manta cewar idan Allah yatashi yin baiwarsa da É—aukakarsa yakan É—aukaka wanda yaso koda kuwa ku kuna ganinsa a bakomai ba, sai hakan kuma daga karshe yazama hassada da tabewa.




******




Hantsi mai haɗeda shuɗin launi na sararin samaniya,garine mai ɗauke da gini na laka da akayi su da ɗanyar ƙasa da kuma itacen giginya domin ƙara karfin ginin.




Cikin Garin Adik wanda Babban garine a ƙarƙashin Mulkin Soghay, kuma shine na biyu bayan Garin Goa inda Daular Songhay take.




Babbar fadar sarki a cikin garin Adik tafi kowanne fada girma ƙayatarwa dakuma girman mamayar ƙasa. A cikin fadar wani bangare dayake ɗauke da fili mai dauke da farar ƙasa mai laushi an shareta abin gwanin ban sha'awa.




Yarane ƙanana da bazasu wuce shekara bawai ba zuwa takwas,dariya suke suna bulawa wata yarinya a gefensu ƙasa wacce zata kai shekara goma sha biyu ita,domin ta ɗan girmesu a tirinyar jiki amma kuma daga yanayinta hankalinta ma bai kai nasu ba.




Idan suka ɗebi kasa suka watsamata sai ta saka kuka tamkar asara,su kuma hakan sai yasa su sheƙe da dariya cikin farinciki. Tana gefe a zaune gabaɗaya sun wanketa da ƙasa itakuma ta bare baki tana ta kuka.




Can bayan wani ɗan lokaci fuskarta tayi kaman dodo,hawaye ya haɗu da ƙasa tayi buju buju da ita.




ÆŠaya daga cikin yaranne tace.




"Joda Aga agaaaa"




Tana cikin kuka tayi maza tace "Aga" cikin wauta.




"Agah waye zata iya shiga cikin jejin can ta É—aukomin takalminaaa ?"




"Niii CoÉ—a"




"To jeki ki É—aukomin sauri ki dawo yanzu zan baki kifi na idan babana yakawomin daga ruwa"




Da sauri ta tashi ta kaÉ—e jikinta ta nufi inda yarinyar ta nuna mata bigizim bigizim. Jeji ne inda ake noman su giginya kwakwar manja da sauran manya manya bishiyoyi irin Goro da sauransu saboda niimar wajen yana kusada kogin Niger,sai hakan yabawa yanayin garin sanyi da lumshi.




Batareda shayin komai ba ta nufi dajin,burinta tayi abinda aka sakata yazama ita tayi nasara,kuma za'a bata kifi. Ta manta kargaÉ—in da akayiwa yaran karsu bar cikin masarautar. Saboda hatsarin faÉ—awa hannun masu kamen bayi da kuma naman daji masu hatsari.




Tun tana shiga tana kallon bishiyoyi da sukayi kama dana kowanne daji,har ya zamto ta fara yin karafkiya da duhuwar daji mai ɗauke da bishiyoyi masu launi kala kala. Abinka da ƙananun shekaru haɗeda yarinta da wauta maimakon hakan yabata tsoro ko ya ɗarsa fargaba a cikin ranta,saima ya ƙara ƙayatar da ita tareda saka shauƙi a cikin ranta.




Tafiya take da sassarfa tana Æ™ara gudun tafiyarta. Wata akwalkwala (malan bude littafi) ne ya iyo Æ™asa Æ™asa yana walwali a samanta daidai yanda  hannunta zai iya tabawa.  Aikuwa hakan yayi tasiri wajen jan hankalinta matuÆ™a,inda tafara binsa da gudu tana Æ™yalÆ™yala dariya,shikuma yacigaba da janta izuwa zuciyar dajin.




Takai wani lokaci tana bin Akwalkwalar zata kama,amma sam taƙi bata damar yin hakan, sai ta kusa kamata sai ta sake yin sama da kaɗan. Dariyarta ta fara sararawa alamun gajiya sun fara bayyana a jikinta. Waigawa tafarayi da alamun tanason komawa da baya. Rau rau tayi da ido zata fara kuka,jin dajin tsit babu sautin bil'adama ko guda ɗaya,sai kukan tsintsaye,rausayar bishiyoyi da kuma sautin ƙananun halittu masu ban al'ajabi da babancin Halitta fiyeda na waɗanda muka saba gani.



Wani haske tagani a cikin wani kogo da kuma sautin motsin mutum,da sauri kuwa batareda ta sake tunani na biyu ba ta nufi wajen.



Kai tsaye shiga tayi tana Æ™arewa wajen kallo. Abincine akan tebur an ajiye tamkar ana jiran baÆ™o yazo yaci. Cikinta ne taji yayi Æ™ara alamun yunwa ta gara mata,domin rabonta da abinci tun gurasar da suka hau layi aka raba musu. Da sauri ta nufi wajen zata saka hannu itama taci. Saidai taji an riÆ™e hannunta caff. Juyawa tayi da mamakin waye? .....Wata mace tagani  dattijuwa a matakin Æ™arshe na shekarunta,tana sanye da farin saÆ™i amma kuma fess da ita. Ba kaman ita ba da takeda baÆ™ar fata da kuma Æ™ayan saki masu matuÆ™ar dauÉ—a.




Murmushi tayi mata wanda baya bayyana Æ™yama ko kaÉ—an. Jan hannunta tayi zuwa Æ™uryar É—akin,inda wani kofin Duma yake ajiye da tsimi a cikinsa. 




"Sam abubuwan dasuke wajennan bakya buƙatarsu a yanxu,keɗin makulline wanda sai yayi tafiya mai nisa da take cikeda ƙalu bale kafin yakai ga buɗe ƙofar ƙaddarar da take gabansa. An haifeki da baiwa ta Fasihmman wanda wani ƙashi ya tosheta sanadiyyar haihuwarki da Mahaifiyar ki tayi a tsaye saboda firgici na halin yaƙi. Karbi wannan ruwan kisha,zai taimaka miki wajen warkar dake sannan ya taimakawa ƙarfin tunaninki. Wannan shine iya abinda zan iya biya daga taimakon da Mahaifinki Yayimin batareda yasani ba"


Hallau da murmushi akan fuskarta ta tsiyanyo ruwan ta miÆ™awa Joda. 




Batasan mai take faÉ—aba ballantana tasan mai take nufi,sakamakon an haifeta da shanyayyen tunani,sai anyi magana goma kafin tagane É—aya. Karba tayi kawai tashanye saboda Æ™ishirwar da takeji. 



Yana shiga cikin bakinta ta zefar da kofin tareda tsallara wata ƙara mai ƙarfi,dafe kanta tayi tana kallon matar wanda a hankali take Dusashewa daga idonta,a wani bangare kuma wata duniyar tana bayyana. Muryar mahaifinta take jiyowa sama sama, daga nan batasan mai yasake samun ganin ta da jinta ba....


*********




*Harƙa ta (1)*👑




"Ranki ya daɗe Keita Sunjata Mansa ya dawo daga yaƙin sa na farko daya jagoranci dakarun yaƙi guda Dubu biyar a karo na farko a zuwa filin dagarsa,har ila yau cikin ƙananun shekarun da basu wuce goma sha biyar ba.........Babban daddaɗan labarin shine yayi nasarar,da tunda aka kafa masauratar mali wani ɗan jinin sarauta bai taba yinta ba a irin shekarunsa"



Cikeda zumuɗi baƙin bafaɗen ya faɗi a gaban matar wacce take cikin ƙaya na ƙasaita daga sama har ƙasa anyi musu ado da ɗanyen Zinare mai ɗauke dukkan idon mai kallo.



Kyakkyawace fatar ta kalar Cakuleti,an tafke dogon baÆ™in gashinta mai É—auke da halittar tauri da Æ™arfi irinnamu na Æ™asar africa,saboda gyaran dayasha sai cikarsa a cikin kanta yaÆ™ara mata wata izza mai bada razani a zuciyar na Æ™asada ita. Kaifin idonta a tsaye yake da idan mutum ya kalleshi zai iya É—auka cewar cakarsa tayi da allura a cikin nasa idon. 



Juyowa tayi ta kalli bafaden dake durƙushe a gabanta tamkar ɗan tsaki a gaban giwa,biyyayya zayyi iya iyawarsa don kada ta murƙusheshi. Wani hamshaƙin murmushi tasake kafin tafara magana cikin izza.



"Yakai Yahuza wannan ba wani labari bane mai ɗauke da abin mamaki,saidai yana ɗauke da dadin ji. A yanda na raini ɗana banajin yanada tsara a cikin yayunsa ma ballanatana kuma na ƙasansa,muɗin Ahalin Ghazzz jinin Sadaukantaka ne da kuma Dagiya akan abinda muke muradi. Burina shine ɗora ɗana akan karagar mulki,koda kuwa hakan zai zamo sanadin numfashina bazan taba damuwa ba,dan wannan shine muradin Ahalina"



Shidai wanda yakawo labari daddaɗa maimakon yasamu yabo da kuma kyauta sai ya ƙare da samun razani da firgici na sautin amonta.



"Me kake faɗa,Keita Sunjata ɗa ga Musso Lazeerah yayi nasara akan yaƙin da Sarki ya turashi?"



"Eh hakane ya Shugabata yayi nasara dagaske,yazunnan ma zakiji busa da amo yafara tashi nan bada daÉ—ewa ba"

Ragwaf tayi ta faɗa kan wani babban matashi mai matuƙar laushi da akayishi da silki.

"Inkuwa hakane to tabbas akwai chakwakiya a lamarinnan,domin hakan yana nuna yashirya yin Fito na fito da Keita Kamarou kenan,tabbb aikuwa Musso Shuwarah bazata taba bari a bashi lambar yaboba. Maza je ki ƙiramin Keita Hamad nasan yana can yana baccin Asara Ohhh Allah ni yazanyi da wannan yaronne,babu abinda nakeso illah nima naga nawa yana ciki ana damawa dashi,amma abin sam yaci tura kwata kwata bayason dagewa ya kara da yan uwansa. Ga sauran matane sukam ba'a tasu. Yazo yaji abin kunya ɗan uwansa dasuke sa'a ɗaya yaje yayi abin arziƙi shi yana can yana baccin asara"

Da sauri Baiwar da aka bawa aiken ta nufi wani sashe a cikin Danƙareriyar masarautar domin ƙiran wanda aka ƙira da Keita Hamad ɗin.

Zuwa take tana dawowa tacika tayi famm da ita,Itama hamshaƙiyar mata ce tagani ta faɗa. Idonta yanada kaifin Basira shu'umanci da kuma makirci,amma baikai Na Musso Lazeerah izza da Gizo ba. Duk da a yanayin shekaru ta girmeta sosai.

"Tabbas idan wannan zancen gaskiya ne cewar Keita Sunjata yayi nasara a yaÆ™in da Sarki Mansa ya turashi to kuwa hakan yanuna Musso Lazeerah so take tayi takara dani. Da alama wuyanta yafina waccar Lusarar kauri (Musso Aimanah mahaifiyar Keita Hamad) dani zatayi zancen. Har yanxu na gagara gamawa da wancan Æ™aramin Zakin, ita kuma zata shigamin É—aya Æ™ofar hancin? Babu wanda zayyi sarautar Daular mali sai ÆŠana Keita Kamarou." 

A zaune yake akan Karagar mulki a Babbar Fadarsa dake tsakiyar Cikin gidan sarautar a gini mafi tsayi. Zuciyarsa dakuma Fuskarsa cike suke da ɗokin dakon isowar Gwarzon matashin dannasa daya tafi Yaƙi wata uku da suka wuce. Kuma labari ya iskeshi cewar yana kan iyaka ɗauke da tutar Ƙasar a hannunsa da kuma ta Abokan gaba.

"Gaisheka wanda Zinare ke duƙa masa,gaisheka mai daular data haska ko ina da haskenta,gaisheka uban Zaratan Jarumai"

"Ai wato ina cikin farinciki da dakon isowar wannan Matashin Jarumi. Lokacin dana turashi ban taba tunanin zai dawo da wannan nasarar ba. Lallai yaƙara ɗaukaka suna na a nahiyar nan "

*********

"Dan Allah Aminatou kiyi shuru haka,idan kina kukannan da wanne zamuji ne,da halinda take ciki ko kuma da yanayin dake kike ƙoƙarin jefa kanki ciki?"


Jan majina tayi ,ganin bazai kaita ba tasaka bakin Zanin saƙinta ta goge. Kallon mijinnata Tayi Kalamudeen wanda fuskarsa ta bayyana damuwa sosai.


Su bayine wanda su kansu bazasu ce ga Asalinsu ba, Aminatou Æ´ar nan Adik ce anan ta tashi tun tana yarinya cikin Fada tana hidima. Shikuma Kamaluddeen Bamisrene da aka kamoshi a kamen bayi tun yana yaro matashi. Kasancewar yanada Æ™irar jarumta,hakan yasa yasamu nasarar shiga jerin Dakarun masarautar,har aka bashi damar yin aure kuma ake bashi wani abu.  Dama saboda Aminatou yadage yakai matsayin dan haka babu daÉ—ewa suka nemi alfarmar a barsu suyi aure, kasancewar dukkansu bayin fadane basu samu wata tangarÉ—a ba a tafiyar.


Anan sashen Bayi yabada kuÉ—i aka nuna masa Filin dazayyi bukka. Da murna da farinciki Abokansa suka Tayashi yayi musu bukka biyu da makewayi. 


Rayuwar farinciki suka fara ginawa mai cikeda yarda da amana,Aminatou yarinyace mai nutsuwa da hankali ko kaÉ—an halayyar Bayi mata na cusa kansu ga Æ´aÆ´an manya dan samun abin duniya bai dameta ba,duk da kuwa abinda yazama ruwan dare kenan a Tsakanin bayin fadar.


Idan suka tashi da safe Zata gyaramusu muhallinsu shikuma idan yana gida babu fita filin yaƙi to sai ya tafi wajen horo. Itakuma sai ta tafi wajen nata aikin,Uwargidan Sarkin Sunkia Salamah Itace Uwargijiyar ta.


A haka rayuwa tacigaba da gara musu Harta Samu cikin Joda. Farin ciki a Wajen Kamaluddeen ba'a misaltawa,kowa ya haɗu dashi sai yayi masa labarin za'ayi masa haihuwa,duk da in yatuna ƙangin bautar da ɗansa ko ƴar sa zaizo ya fuskanta a hannun masu ƴan ci,hakan yanasa yaji babu daɗi. Kuma yanasakawa yaƙara Jajircewa wajen ganin yataka wani matsayi ko domin iyalansa suyi alfahari da hakan.


Cikin Aminatou bakwai ta haifo Joda saboda tsananin tashin hankalin harin da Daular Songhay takawomusu,saboda tana kallon suna so su fita daga takunkumin data saka musu. Ƙarar Nakiyar yaƙi razani da gudun ceton rai a haka Aminatou ta haifi Joda a tsaye babu damar zama.


An gama yaƙi hankalin wasu yakwanta,Daular Soghay ta sake ɗaure su tamau fiyeda na da. Wanda yazamana ko sunan ta a ƙira a kunnen ɗaya daga cikin ɗan Masarautar to sai hantar cikinsa tayi kuka ta kaɗa.



Ga wanda nasu yamutu sunyi kuka,wanda suka razana ma hankali yakwanta amma ga Aminatou lafiyar jinjirarta ta rasa wanda batasan ranar dawowarsa ba. Sai bayan anyi suna dukka babu shiri domin ba'a tsammaci tarbarta zuwa cikin duniyar a wannan lokacin ba. Sai kuma suka fara gane batayin kuka sosai,sannan kallonta ba daidai yake ba. Basu kawo hakan a matsayin wata matsalaba,sai suka Allaƙa hakan da haihuwarta da tsirarun watanni ne yakawo hakan. Babu wanda yayi tunanin zata rayu ma Fasihmman a lokacin yaron dabai cika wata tara ba bai fiye Rayuwa ba.



Bayan shekara biyu sai abubuwan suka ƙara ta'azzara,batayin abubuwa kaman sauran yara,kallonta yana jinkirtawa yayinda karshashinta ma bai kai yanda ake gani a wajen yaro lafiyayye ba. Babu tafiya babu rarrafe babu alamun gwada magana har saida takai shekara Huɗu kafin tayi tafiya,sannan tafara gwada ƙiran baaba da Umma,sai yawan dariya da tafa hannu kawai.



Da farko Aminatou ta ɗauka yarinta ne,amma ganin ƴar tata girman jiki kawai take karawa amma banda hankali sai abun yafara damunta sosai,sannan a tsakanin bayi an fara jefar ƴar tata da kalmar wawuya,abin yafarayi mata ciwo duk da kuwa itama tasan zancennasu haka yake. Hankalin ƴar tata sam baya ƙara girma,yara ƙanana data girmesu sai suyi ta sakata aiki kokuma su daketa. Kullum cikin kuka take ko kuma dariya ba saurarawa.



Shawara tayi da Mijinta akan zata fita nema mata magani wani dare suna zaune ita kuma joda tayi bacci a gefensu.



Hawayen idonta ya share mata cikin nutsuwa yasan dole abin zaiyi mata ciwo,shima bai taba tunanin haka rayuwar Æ´ar da yayi kwaÉ—ayin a haifamasa zata kasance ba. Gashi da alama ita kanta ta samu matsala dan ko barin wata bata sake ba shekara biyar kenan.



"Aban Joda kabarni naje nema mata magani,Æ´ata batada lafiya rayuwa a halinda take ciki zaiyi mata wuya a wannan duniyar,da mai wayo ma wahala yakesha ballantana ita da batasan ma tukun a duniyar da take ciki ba. Yanzu haka yau yaran bayi maza su uku nasamu sun tube mata kaya wai zasuyi mata wanka tayi datti AbanJoda .......ka dubamin wannan lamari tun yanzu ma kenan inaga idan ta girma surar mace ta bayyana a jikinta,taya zata kare kanta kenan idan bana kusa,nima rayuwata ba tawa bace taya xan kare tata rayuwar."



"Bakya bukatar kare rayuwarta Aminatou Allah da yayita shine yake bukatar kareta,sannan zamowarki uwa hakan kar yasaka ki manta da cewar Koda kece bakida lafiya bakida ikon fita nemawa kanki magani ballantana harki samawa wata magani. Mu ba ƴaƴa bane,muna a karkashin ikon shugabanmu ne,saba musu dayin abinda yakasance ra'ayinmu abune daya sabawa doka kuma zai jawo hukunci mai tsanani. Dan haka ina roƙarki dakiyi haƙuri ki karbi Joda a yanda Allah yayi niyyar yabamu ita,ki bata kulawa kuma kiyi mata addu'a iya iyawarki,bakisan wacce irin baiwa Allah ya ajiye a cikin rayuwarta ba"



Maganganun Kamaluddeen sunyi tasiri a ranta,amma hakan bai hanata cigaba da kuka ba tana ƙara rungume ƴar tata wacce take bacci kaman matacciya batasan wacce wainar ake toya ba.



Haka rayuwar ta cigaba da wainawa cikin haÆ™uri da dogaro da Allah har Joda takai shekara Goma a duniya,maganar ma bata fita sosai ballantana akai ga yin karatu,kaya ma sai an saka mata ta É—aÉ—É—aure mata saboda karya sunce ko yara su cire mata. Ga aikinta na uwar É—akinta,a haka babu yanda ta iya take barinta da sauran yara bayi ta tafi aikin,suma ana sakasu É—ebo makamashi da karantarwa akan yanda zasu tafiyar da iyayen gidansu idan sun girma da sauransu. 



Kaman jiya tana cikin aiki bayan ta dawo tanata nemanta amma bata ganta ba,tazo bata ɗan abincin rana data ragomata,saboda tasan ko an basu abincin yara ƙwacewa zasuyi,su barta tayi ta kuka ga yunwa.



Wata maƙwanciyarsu Khadi'atou ta tambaya ganin tana zaune da nata yaran su uku suna cin abincin data zo dashi.


"Uhm nace Khadi'atou shin kinga Joda kuwa,tun É—azu nake duba sashennamu amma banganta ba,kuma nasan bata saba yin nisa ba saboda tasan ina dawowa na bata abinci"



"Tabb kiji Aminatou ta wani zance,wai tasan kina dawowa,yarinyar da ana mata magana ta manta itace zatasan wai zaki dawo,dama su Sule ne ke tarota idan tayi waje su kuma an sakasu É—ebo abincin dawaki acan gidan Shamaki yau,sun fara kama aiki suma"


Hawayen idonta ta matse tareda haÉ—iyar yawu, kowa a wajen kallon tunkiya yakeyiwa Æ´ar tata,shiyasa taso ta dunga zuwa da ita wajen aiki,amma tasan koda wasa uwar bayi bazata bariba,tunda dokace bazasu je da yara ba,saboda karsu hanasu yiwa iyayen gidansu hidima yadda ya dace.



Ganin babu ita babu alamunta a da'irar tasu yasa ta tafi wajen bada horo domin sanar da kamaluddeen, tun daga É—an nesa daya kanta tana sauri zata iso babu alamar kwanciyar hankali a tareda ita shima ya isa gareta. Kafin yayi magana tafara É—aga hannu tana faÉ—amasa.



"Jodah jjjjodah Banganta ba AbanJoda......nnnaayi ta dubawa banganta ba bansan yanzu haka a wanne hali take ciki gashi bataci karin kumallo bama sosai,dan turata karbar gurasa nayi bamu tashi da abinci ba jiya....ka taimakeni mu nemota......."



"Ki dakata haka ki nutsu za'a sameta Insha'allahu kije gida barina tambayi Su Umar saisu rakani mu dubata bazatayi nisa ba da izinin Allah"



Duk maganar ta baisa hankalin ta ya kwanta ba sude kawai sunyi gaba sun barta a wajen tana sauke numfashi.



Suna cikin tafiyane Yarinya Æ´ar gidan Khadi'atou  Salma wanda suke cin abinci ÆŠazu tacewa kamaluddeen..



"Aban Jodah batanan fah tashiga Daji "



Juyawa yayi ya kalleta cikin É—aure kai,mai zai kaita daji kuma?"



"Uhmm dazune muna wasa Sibrah ta aiketa wai ta ɗaukomata takalminta zata bata kifi,kuma ƙarya take babu takalminta a jejin kawai ta turata"



Tashin hankalin sa karuwa yayi ta gudu yayi hanyar data nuna masa batareda ya faÉ—awa kowa ba.



Yayi tafiya mai nisa kafin yaganta a tsakiyar wasu bishiyoyi tana jujjuyawa ta dafe kanta,idonta yayi Jawur alamar wani abu babba yasameta,gefenta kuma wani kofi na Duma da sauran wani baƙin ruwa a ciki,kallo ɗaya yayi masa kafin ya maida hankalinsa zuwa kanta.



Cikin razani ya ƙira sunanta sannan ya tareta ganin zata faɗi,sume ya ɗaukota yana tafiya kansa cunkune da abubuwa kala kala,shin mai yafaru ya tambayi kansa tambayar da bashida amsarta. Hakan yasa ya ƙuduri binneta a cikin ransa har abada,tunda babu wata mafita dazai haifar,koma waye yayi niyyar cutar da ita Allah yafishi,yasan in yafaɗawa Aminatou ma hankalin ta kawai zata ɗaga,inma neman mafitane saidai ya nemo da kansa.



Tun daga nesa ta hangoshi rikeda Joda kamar matacciya a hannunsa,ta gudu da tareshi muryarta na rawa tana tambayarsa mai yafaru,bai bata amsaba sai wuce ta kawai da yayi yashiga bukkar tasu,mutane sun taru suna ta tayasu alhini.



Bayan ya shimfiÉ—ata ya É—aga kai ya kalli Aminatou wacce take tsaye a kansa tana sallalami.



"Ki kulada ita barinaje na roƙi Babawuro mai Aikin jinyar mayaƙa alfarmar ya dubata tunda muna ɗan shiri dashi"



"Toh amma kanaga zai yarda ya dubatan,bazamu nema a wani wajen ba,kar hakan yajawo maka matsala kokuma shi?"



"To ya zamuyi Aminatou munada mafitane dayawuce hakan,rayuwar bawa ba abar kulawa bace idan ya mutu ma makansa ne,kedai ki bari zan gwada tambayarsa,shima ai nayi masa alfarmomi dayawa"



"To shikenan Allah yabada sa'a"



Daga haka ya fita ya barta tana jujjuyata kaman gawa. Kusan kamar Rabin sa'a sai gashi yashigo da wanda aka ƙira da Babawuron,Baƙin mutum ne mai ɗan jiki yanada gashin baki duguzu duguzu,da kayan fata a cikin na warki.



Kai tsaye shiga yayi cikin bukkar,ganin haka itakuma Aminatou ta fito tana leƙasu daga waje,duddubata yayi na ɗan wani lokaci kafin yafito da wani ganye kala kala guda uku ya mikawa Aminatou akan ta daka masa.



Da gudu ta karba ta É—auko turminta na dutsi tafara gurza masa,bayan yayi laushi ta zuba a É—an kwano ta mika masa. Ruwa yasa aka kawo masa yajigasu kana ya É—aga kan Joda ya É—uramata.



Kamaluddeen ya kalla kana yace....



"To abin ya daure min kai,banga wani rauni a jikinta ba,sannan babu wata alama ta guba a jikinta,kuma dumin jikinta ma daidai ne. Saidai maganin dana bata zai ƙarawa garkuwa jikinta ƙarfi,da alama gangar jikinta tashiga wani hutune idan Allah yayi ikonsa zata iya tashi,idan kuma bata tashiba to gaskiya ni babu abinda zan iya. Mutum ɗayane zai iya taimaka mata wanda na taba jin labarin yana farfaɗo da mutum daga suma shine babban Likitan fasar Daular mali,shima kuma ance iya ƴaƴan masarsutar kawai yake dubawa. Ko mu nan bamuda shi,in mutum bai tashi ba da wata ɗaya binneshi kawai akeyi,idan kuma bawa ne da sati ɗaya za'a binneshi. Inba haka ba kuma wani bala'i zaisamu ƙasa. Dan haka kucigaba da addu'a Allah yasa ta tashi nan da kwana bakwai idan ba haka saidai kuyi haƙuri da ita gaskiya"



Yana gama faÉ—in haka yasaka kai yabar É—akin,hakan ma babban taimako yayi musu ,vanda haka waye ke yiwa bawa magani in badai Æ´an uwansa bayi ba.



Kuka Aminatou ta rusa tareda zubewa a wajen.



"Aban Joda munshiga uku,yanzu yazamuyi idan bata tashi ba,gaskiya yafaÉ—a ko bamu binneta ba doka bazata barmu ba"



"Insha'allahu ma zata tashi,amma idan bata tashi ba saidai Ayimin duk abinda za'amin amma bazan taba binne ƴata da ranta ba,wannan alƙawari na ɗauka saidai bayan raina ma'ana bana numfashi"


*********