BURIN ZUCIYA(Short Story)

BURIN ZUCIYA Chapter 1

by @ayshadansabo

*BURIN ZUCIYA ❤️*
Arewapen@ayshadansabo

©️ Ayshat Ɗansabo 📚

Ina mai farawa da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinƙai.

  *Free page 1* 

Wata baƙar mota ce ta tsaya daidai gate ɗin wani gida.Kallo ɗaya za ka yi wa gidan ka gane cewa gida ne na masu rufin asiri ne gwargwadon hali.Ko da motar ta tsaya,sai da aka shafe tsayin mintuna biyar kafin murfin motar ya buɗe.Wata kyakkyawar budurwa ce ta fito sanye da hijab,wanda ya ɓoye asalin ƙirar jikinta da Allah Ya yi mata.Sai kyawun fuskarta kaɗai zan iya misaltawa.Sosai take da kyau duk da kasancewarta baƙar fata,irin wadda turawa ke kira da black beauty.
Shigewa tayi cikin gidan kai tsaye,yayin da motar ta juya ta bar layin baki ɗaya.Da sallama ta shiga cikin gidan mai ɗauke da ɓangarori biyu madaidaita; ɓangare guda na mahaifinsu ne,sai ɗayan na mahaifiyarsu wanda yake haɗe da ɗakunan su a ciki.
A babban falon ta ajiye jakar da take rataye a kafaɗarta,sannan ta zauna cikin kujera tana cewa:

“Wash, Allah na.”

Wata farar mace ce ta fito daga wani corridor ta sauke idanunta akan budurwar,kafin ta ƙaraso cikin falon tana cewa:
“Surayyah,sai yanzu kike dawowa? Ina ta kiran wayarki baki ɗaga ba ai.”
Budurwar da aka kira da Surayyah ta dubi matar wacce ga dukkan alamu ita ce mahaifiyarta,saboda kamanninsu ya yi yawa sosai.Bambancin su kawai ita matar fara ce,ita kuma Surayyah baƙa ce.

Murmushi ta saki tana cewa:

“Wallahi Mum,wayata tana silent ne shi ya sa.Kuma Anty Safiya ce ta tsaidani wai lallai in jira Aliyu ya sauke ni. Yanzu haka shi ya maidoni.”Ta ƙarasa maganar da shagwaɓa sosai,wanda ya sa Mum ɗin sakin murmushi tana cewa:
“Surayyah kenan, ita dai Safiya tana son ki da Aliyu.Gashi ke kuma ba kya ra’ayinsa.Na rasa meye aibun Aliyu da ba ki son shi,auta.”
Surayyah ta taɓe baki tana miƙewa tare da ɗaukar jakarta tace:
“Mumy kenan, ba za ki gane ba.Ni kaɗai na san Burin da ke zuciyar Aliyu a kaina.”
Tana gama faɗin haka ta nufi corridor zuwa ɗakinta.
Bayan ta Mum ɗin ta bi da kallo tana sauke ajiyar zuciya.A fili ta furta:
“Allah dai Ya nuna min mijin auranki,Surayyah.Na rasa me ya sa kike korar duk masu zuwa gareki da sunan so,sai an yi magana ki ce ba mu san Burin zuciyarsu ba.Ko mene ne Burin zuciyar nasu a kanki?”
Ta ƙare maganar tana tambayar kanta,sannan ta tashi ta fito ta nufi ɓangaren Babansu Surayyah domin kintsa shi,don ya sanar mata yana bisa hanya.
A can ɗakin Surayyah kuwa,hijabin jikinta ta cire.Nan take surar jikinta ta bayyana cikin straight gown ɗin da ke sanye a jikinta wanda ya bayyana irin halittar da Allah Ya yi mata.
Domin tana da kyau sosai; ko mace da wuya ta yi mata kallo ɗaya ta ɗauke kai.Tana da tsayi,amma ba sosai ba.Ba ta da jiki sosai sai dai kirjinta da ƙugunta da suke a cike sosai.
Za a iya lissafa ta cikin jerin kyawawan 'yan mata na musamman.Ɗankwalin kanta ta zame,baƙin gashinta da ta ɗaure da band ya bayyana.
Zama tayi a bakin gadonta tana zaro wayarta da take ta rawa a cikin jaka.Ganin sunan Uncle B ya sa ta ɗaga wayar tana cewa:
“Hello Uncle B.”
Daga ɓangaren sa ya amsa mata da:
“Surryn Mama, ya kike?Yau kwana uku kin bar Uncle ɗinki kina fushi da shi saboda ya hana ki ɗora hotuna a status ko?Haba Surry,kin san Uncle ɗinki mai son ki ne, ba zai so abin da zai cutar da ke ba.”
Murmushi tayi kamar yana gabanta,kafin ta shagwaɓe murya tana cewa:
“Shikenan Uncle,ya wuce.Amma Uncle B,hoton da na ɗora ni ban ga wani aibunsa ba.Da mayafi a jikina fa.Da kai ba uncle ɗina bane, sai in ce kishi kake.”
Ta ƙare maganar tana sakin dariya. A ɓangaren Uncle B kuwa ya sauke ajiyar zuciya,domin ko kaɗan ba ya so Yarinyar ta gano Burin zuciyarsa a kanta.
Sai ya kawar da maganar ta hanyar tambayar ta Mum.Ta sanar masa kowa lafiya.Sun ɗan jima suna hira kamar yadda ya saba kiranta domin ya ji muryarta a ko yaushe.
Daga ƙarshe ya sanar mata cewa cikin kwana uku zai dawo Najeriya.Ajiye wayar tayi bayan sun kammala,tana sakin murmushi.Zuciyarta na jin daɗin yadda Uncle B ɗin yake tsananin ji da ita tare da shagwaɓata da yake.
Kowa a cikin friends da danginsu ya san irin kusanci da son da Uncle B ke mata.Sau da yawa ta kan yi nazari,cewa da ace bata san dangantakar da ke tsakaninsa da Mum ba,ita da kanta da za ta saka shi cikin jerin samarin da suke zuwa gareta.Shigewa toilet tayi domin ɗauro alwalar la’asar da ake ta kiran sallah.

⚡⚡⚡⚡⚡

Kwance yake a katafaren falon mahaifiyarsa,ya lula cikin duniyar tunani wanda ya fara zama masa jiki.Kullum tunaninta yake yi; da shi yake kwana,da shi yake yini.
Tun da ya ɗaura idanunsa a kanta,bai sake samun hutu da sukunin zuciya ba.Da zarar ya kasance shi kaɗai,tunaninta yake da ya zame masa abokin hira.
Sau ɗaya ya gan ta,amma ta gama tafiya da duk wani nutsuwarsa.Bai taɓa cin karo da yarinyar da ta tafi da zuciyarsa haka ba sai ita.
Ga shi yau kimanin watanni uku kenan da haɗuwa da ita,amma bai sake cin karo da ko me kama da ita ba.
Lokacin da suka haɗu a Mangal Plaza,yana shirin yin wani abu,sai motarsu ta bar wajen. Tun daga ranar bai sake ganin ta ba,sai hoton surarta da fuskarta da ya kasa ɓacewa daga tunaninsa.
Fitowar Hajiyarsa daga ɗaki ta dawo da shi hayyacinsa.Ta ratso cikin falon tana sauke idanunta a kansa tare da kiran sunansa:
“Abdallah,yanzu ba za ka cire duk wani tunani a cikin zuciyarka akan Yarinyar da ba ta ma san kana yi ba ko? Na sha gaya maka addu’a za ka yi,Allah Ya sake haɗa ku inda akwai alheri.Amma ka daina sawa zuciyarka yawan tunani,Autan Hajiya.”
Ta ƙare maganar da zolaya tana tsare shi da ido.
Hakan ya sa ya sauke hannunsa yana murmushi kaɗan,sannan ya ce:
“Wallahi Hajiya,yarinyar ta gama tafiya da zuciyata.Ban taɓa tunanin haka soyayya take ba.Ko dai wulaƙancin da nake wa ƴan mata masu kawo kansu gare ni ne ya sa Allah Ya jarabceni da zazzafar sonta,bayan bata ma san ina yi ba Hajiya.”
Ya ƙare maganar cike da shagwaɓa tamkar ƙaramin yaro.
Hajiya tayi dariya tana cewa:
“Ka dai roƙi Allah,shi ne zai sake haɗa ku.Ni dai ka kwantar min da hankalinka,Auta.Ka san ba na son damuwarka.”
Hajiya Halima ta ƙare maganar tana sakin murmushi,yayin da Abdallah ya miƙe yana cewa:
“Hajiya,bari na je na yi wanka.Ina so na fita wajen Alhaji Sambo, akwai abin da za mu tattauna.”
“To Abdallah,Allah Ya ba da nasara.Idan za ka dawo zuwa yamma,ina son ka taho min da wannan furar,ya yi min daɗi sosai.”
Sai da ya yi murmushi kafin ya furta:
“An gama Hajjaju,zan ma haɗo miki da kaza.” Daga haka
Ya fice yana nufar ɓangarensa,zuciyarsa na tunanin cewa ina ma ace yana fita ya sake haɗuwa da pretty ɗinsa kamar yadda ya raɗa mata a zuciyarsa.
Wanka yayi ya shirya cikin ƙananan kaya da suka yi masa mugun kyau.
Abdallah kyakkyawan matashi ne mai kyakykyawar hali ga kyau,kuma yana da dukiya sosai.Yana cikin sahun maza na musamman.Yana da nutsuwa da kamun kai matuƙa.
Sam ba shi da rawar kai irin na matasan zamanin nan.Kuɗi da wayewarsa ba su ruɗe shi ba,sai dai yana da tsare gida da miskilanci sosai.
Idan ka ji dariyarsa,to yana tare da Hajiya ne ko kuma Yayarsa Hafsatu.Amma ƙannensa biyu da suka rage suna ɗan jin tsoronsa saboda baya sake musu fuska.
Fari ne shi,amma ba sosai ba;hutu da jin daɗi sun sa fatarsa ta zama mai kyau sosai.Ɗan gayu ne na ƙarshe,wanda ya san yadda zai tsara sutura,turare da takalma masu kyau.
Da ya fito,motarsa ƙirar Lexus ya nufa ya shiga. Mai gadi ya buɗe masa ƙofa yana yi masa fatan dawowa lafiya.Hannu kawai ya ɗaga masa sannan ya fice yana tuƙinsa cikin ƙwarewa.
⚡⚡⚡⚡⚡

Suna zaune suna cin abinci a ɗakin cin abinci.Mutane uku ne tare da ƙaramar Yarinya mai shekaru biyar.
Wata matashiyar mace ce wadda ba za ta kai shekaru ashirin da biyar zuwa ashirin da shida ba.Tana sanye cikin matsatstsen siket da riga na lace,wanda ya fito da kyawun surar jikinta.
A gefenta akwai wani kyakkyawan matashi,da alamu mijinta ne,sanye cikin jallabiya mai launin ruwan madara wadda ta yi masa kyau sosai.
Kallo ɗaya za ka yi masa ka gane cewa masu gidan rana sun zauna.Fatarsa tana da kyau sosai,saboda hutu da jin daɗi sun sauya yanayinsa.
Daga kujerar da ke fuskantar su,Rasheeda ce zaune sanye da riga mai kyau wadda ta bi jikinta tare da bayyana dukkanin ƙirar jikinta.
Tana da kyau sosai,fara ce mai ɗauke fatar jiki mai kyau.Tana da gashi sosai dabya sauko har tsakiyar bayanta.
Suna cin abincin cikin nishaɗi suna jefa hira lokaci zuwa lokaci.Hisham da Rasheeda suna satar kallon juna suna yi w juna murmushi.
Tun lokacin da Hisham ya ga shigar Rasheeda,ta fi ɗaukar hankalinsa fiye da yadda ya kamata.Ita ma ta fahimci hakan,shi ya sa take ƙara nuna kwarjini idan suna tare.
Anty Sameera kuwa ba ta kula da su ba,domin hankalinta yana kan wayarta tana hira da ƙawarta Zainab.
Rasheeda ce ta fara tashi tana cewa:
“Alhamdulillah,ni kam na ƙoshi.”
Ta sauke idanunta a kan Hisham,shi ma idanunsa suna kanta. Ta yi murmushi sannan ta tashi.
Sameera ta ɗago tana cewa:
“Dadyn Husnah,mu tashi ne ka ƙarasa? Ni ma tuni na ƙoshi.”
Ta faɗa tana gyara Husnah da ke jikinta,wadda bacci ya fara ɗauka.
Hisham ya dubi Husnah cikin kulawa,sannan ya ce:
“Eh, mu tashi.Yau ma ba mu yi hira sosai ba.Yanzu zan fita, za mu haɗu da wani abokina a Area 2.”Ya ƙare maganar yana miƙewa tare da ɗaukar Husnah daga hannun Sameera.Sameera na gaba,yana biye da ita har suka ratso cikin falon.
Rasheeda ce zaune tana hira a waya.Jin takun su ya sa ta ɗago manyan idanunta ta sauke akan Hisham.Shi ma hankalinsa yana kanta,sai ya kashe mata ido tare da yi mata wani alama.
Ganin hakan sai ta saki murmushi sannan ta miƙe tsaye.
Sameera da ta kusa haye matakala ta juyo,a lokacin da Hisham ya fara hawa,ta ce:
“Alright Rash,sai kin dawo.Amma kada ki kai dare sosai, don Allah.”
“Karki damu Anty, bari na je.”
Rasheeda ta amsa sannan ta nufi ɗakinta wanda yake a ƙasa.
Ba ta daɗe ba ta fito ta ɗaura ƙaramin mayafi a kanta,hannunta ɗauke da jakar hannu,sannan ta fice.
Cikin mintuna goma sha biyar,Hisham ya sauya kayan jikinsa zuwa riga da wando na Burberry.Ƙamshinsa mai daɗi yana tashi,ya ɗauki makullinsa da wayoyinsa sannan ya fice.
Kafin ya fita,ya yi wa Sameera sallama wadda take zaune a gefen gadonsa.
Tsaye take tana latsa waya,ba ta ji takunsa ba sai da ta ji saukar numfashinsa kusa da wuyanta.
Hannayensa biyu ya kai kan ƙugunta sannan ya yi mata sumba a wuyanta.
Ta sauke ajiyar zuciya tana yin gaba,shi kuma yana biye da ita har suka isa wajen motarsa.
Daga nan suka bar estate ɗin.....✍🏻