40
It's fatoumspassion IMSAL
Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM, INTENSE LOVE, EHSAAS and SCARRED.
Paid Book
Chapter 40
*Imsal*
Tun bayan da jirgin ya ɗaga sama yabar filin sauka da tashin jirage na Malam Aminu kano, Imsal ta nutsu akan kujerar ta tana kallon yadda garin Kano yake ƙanƙancewa ta jikin window.
Duk da ba wannan ne karon ta na farko da shiga jirgi ba, amman ji take yi komai na yau ya bambanta da yadda ta saba wani irin farin ciki da annashuwa ne acikin zuciyar ta.
A hankali ta jingina kanta da kujerar ta, tana kallon sararin samaniyar da suka shiga.
First class ɗin da Uncle Bello ya biya musu ya bambanta sosai da duk wani sashe na jirgi da ta taɓa hawa abaya, kujerun suna da faɗi sosai, kowacce kujera zaman kanta take, kamar wani ƙaramin ɗaki, akwai babban screen ɗin kallo agaban ta da wajen ajiye ƙafa tare da blanket da pillow masu mugun laushi, ga kulawa ta musamman daga air hostess ɗin dake attending to them.
Dan basu wani jima da hawa saman ba tazo tana tambayar Imsal,
idan akwai wani abu da take ɓuƙata?
girgiza mata kai kawai tayi tana mayar mata murmushi kamar yadda itama take mata.
Ganin bakin Imsal yaƙi rufuwa se murmushi take yasa Aunty Nadra cikin tsokana ta leƙota tana fadin
"Me ake kallo soon to be Hajiya?
Duk murnan tafiyar ce"
ɓoye fuskarta tayi tana murmushi cikin jin kunya.
Aunty Nadra ma murmushi tayi ta maida headphones ɗin kunnuwanta.
Se bayan kusan awa ɗaya da tafiyarsu aka kawo musu abinci.
Har zata ce bataci
sekuma ta tina da alƙawari da taima Hajiya haka dai ta ɗanci abinda zataci tasha ruwa.
A hankali ta ɗauko Qur'aninta daga handbag ɗinta ta buɗe, ta shiga karantawa cikin nitsuwa, wani irin nishaɗi taji yana mamaye ta na daban.
Se bayan kusan awa shida da tashinsu daga Kano sannan pilot ya sanar da su cewa suna gab da sauka a Madinah Al Munawwarah.
Nan take taji zuciyar ta na ɗauki da mugun son ganin Madinah garin Manzon Allah ﷺ, garin da Annabi ﷺ ya yi hijira zuwa gare shi, garin da ya karɓi musulunci lokacin da duniya ta ƙi karɓarsa.
Maida idonta tai zuwa kan window, ƙasa ta fara bayyana me ɗauke da fitilu, da gine gine da manyan tituna, tun tana ganin su ƴan ƙananu har suka fara ƙara girma.
jirgin yana fara tafiya saman titin filin jirgin Madina ta runtse idanuwan ta tana fadin
"Alhamdulillah."
Tana jin ƙwallar farin ciki na ƙoƙarin zubo mata, da sauri ta share.
sosai take jin kamar bata taɓa zuwa garin ba, koda yake ance duk zuwan da zakayi wannan shauƙin baya taɓa barin ka idan ka sake komawa.
jitake kamar a cikin mafarki take wai yau itace acikin birnin Madinah, garin da Annabi Muhammad ﷺ ya rayu, inda aka binne shi, garin da miliyoyin musulmai ke marmarin zuwa.
Fitowa sukai tana biye dasu Aunty Nadra, haka har aka kammala duk wasu ƙa'idojin filin jirgin da karɓar kaya.
kafin su fito zuwa babbar harabar filin jirgin, anan kuma suka tarar da direban da kamfanin Hajjin su ya turo ya tarɓe su.
Ya gaishe su cikin girmamawa, suka amsa ya ɗauki kayansu, tare da yi musu jagoranci zuwa wata baƙar mota mai matuƙar kyau.
Uncle Bello ne ya buɗe musu gidan baya suka shiga ita da Aunty Nadra, shi kuma ya shiga gaba.
Jingina kanta tai jikin glass, tana kallon ko ina, gashi barci yaƙi zuwa idanta, komai na Madina na ɗaukar hankalin ta.
saida sukai tafiya na dan lokaci kafin ta hango katafaren masallacin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, wani sashe na koren dome ɗin nan mai albarka ta soma gani, ta sa hannayenta tana dafa glass ɗin tana kallo cike da soyayya har suka wuce.
In few minutes motar su ta tsaya a gaban katafaren hotel ɗin da za su sauka, Anwar Al Madinah Movenpick, ɗaya daga cikin manyan hotel mafi kusa da Masallacin Annabi ﷺ.
Seda suka gama checking in sannan suka hau elevator zuwa floor ɗin da ɗakinsu yake, tun daga lobby ɗin hotel ɗin Imsal take bin komai da kallo, Luxury ne irin wanda ko Aunty Nadra da Uncle Bello da suka saba ganin manyan hotels har cikin States seda suka yaba, Marble floors ne masu sheƙi da manya manyan chandeliers, ga ƙamshin turaren oud mai sanyi na tashi ta ko'ina, ga mutane daga ƙasashe daban-daban na shiga da fita, wani irin farin ciki ne ya sake cika zuciyarta.
Koda suka isa floor ɗinsu wani staff ne ya buɗe musu presidential suite ɗinsu, Uncle Bello ne ya fara shiga, Aunty Nadra agefensa, se ita aƙarshe.
mamaki ne ya kama Imsal ganin suite ɗin nada girma sosai yana da babban falo guda ɗaya se ɗakunan kwana har guda uku, da manya manyan glass windows masu girma.
Su Uncle Bello ɗakin farko suka ɗauka, ita kuma aka bata na ƙarshe, bayan tashiga ɗakin nata ƙarasawa tai gurin window tana matsar da curtain ɗin gefe, wani irin daɗi taji ganin tana hango masallacin Annabi ﷺ tanan ɗin, fitilunsa suna ta haskaka ko ina kamar taurari, ga jama'a sunata kai kawo wasu na shiga wasu na fita, wasu kuma suna zaune suna karatun alƙur'ani.
Ta daɗe agurin sosai kafin ta saki curtains ɗin ta koma ciki.
Wanka ta shiga toilet tayi ta fito, ta saka wata plain baƙar abaya mai kyau tai Rolling mayafin akanta, kafin ta ɗauko wayarta daga cikin handbag ɗinta.
WhatsApp ta shiga tai connecting WiFi, Rayyan tafara ƙoƙarin kira dan so take ya haɗa ta da Hajiya ta sanar mata sun sauka lpy.
amman se taga bama ya online kwata-kwata, mayar da akalar kiran tayi zuwa wayar Daddy aikam tana fara ringing ya ɗaga cike da farin ciki nutsuwa tace
"Assalamu Alaikum Daddy."
Shima ɗin tanajin muryarsa da alamar jindaɗi ji daga gare ta acikinta yace mata
"Ameen Wa Alaikummussalam Imsal,
Kun sauka lpy?"
Jinjina kai tayi kamar tana gaban shi tace
"Eh Daddy Alhamdulillah."
Yace
"Ya gajiyar hanya?"
A hankali tace
"Tabi lafiya Alhamdulillah"
Shiru Daddy yayi na ɗan lokaci kafin yace
"Yaya su kawun naki?"
Tace
"Suna ɗakin su,
ko nakai musu,"
Yace
"A'ah Imsal kice musu dai ina musu Allah ya huta gajiya,
idan Mummy ɗinki ta dawo zance mata kin kira tun ɗazun take neman ki bata samu ba,"
Cikin farinciki tace
"Mummy ta dawo daga Abuja?"
Lumshe ido Daddy yayi daga ɗaya ɓangaren yace
"A'ah nine dai naje can,"
Da ɗan mamaki tace
"Daddy hope everything is well,"
Muryarsa aƙasa yace mata
"Yah all is well alhmdlh,
Allah ya ƙarbi ibadu, let me go,"
Ya faɗa cikin gajar ce maganar.
Jin haka yasa Imsal ma tace mai
"Ameen,
se anjima Daddy,"
Ta katse wayar.
Tana ƙoƙarin kiran Natasha taji nata kiran ya shigo ta ɗaga tana faɗin
"Har kin fara missing ɗina na sani,
irin wannan kira haka daga sauka,"
Natasha daga ɗaya ɓangaren turo baki tai kamar tana gaban ta tace
"Oh danma kinga andamu dake se nama kashe wayar,
kule?"
Da sauri Imsal tace
"haba mana,
ba chass ba,
ƴar ƙanwata da wasa nake maki,
Toh na sauka lafiya alhmdllh nasan tambayar da zakimin kenan,"
Natasha daga ɗaya ɓangaren tace
"ni bashi zan tambaye ki ba ,
kinje gaban Ka'abar,"
murmushi Imsal tayi tana faɗin
"Toh Madinah muka fara sauka ma ai,"
Daga ɗaya ɓangaren Natasha tace
"Toh yaushe zaku tafi Makkar,"
Tace
"I don't really know but maybe in three days,"
Jinjina kai tayi tana faɗin
"Idan kinje masjid ɗin annabi ma kimin addu'ar karki manta,"
Imsal tana murmushi tace
"bazan manta ba,
Kina ina wai?
naji Daddy yace min yatafi Abuja,
Koda ke yatafi"
Natasha cikin mita tace mata
"Ina fa,
gidan Hajiya ya dawo dani,
tana nan ta fara damuna Allah,"
Imsal gano drama ɗin zaman Natasha ta farayi da Hajiya,
ba ita atsakiya,
kawai tafara dariya,
cikin ƙulewa Natasha tace
"yah Imsal dariya ma kike min ko,"
Imsal ƙunshe dariyan ta tai tana cemata
"haba ni na isa,
ɗan kai mata wayar mana mu gaisa,
ko ki temaka ki buɗe mata WhatsApp semu ringa wayar ta can,"
Natasha tace
"Bafa zankai mata ba,
bakisan metamun ba ɗazun akan zanga lefenki,
Kuma Hajiyar ce zata wani iya WhatsApp kema dai kin yaudari kanki ne kawai,"
Imsal tace
"Please kai mata,"
Natasha tace
"Nifa bazan kaiba sedai kiyi,"
Duk da yadda Imsal ta kaɗa ta raya Natasha ƙin kaiwa tai daga ƙarshe tama kashe data ɗinta.
Bayan sun gama ta kira Mummy, jin bata online ya saka ta ajje wayar, kawai ta miƙe daidai nan kiran Farouq ya shigo harta ɗauka zata ɗaga se kuma wata zuciyar tace mata karki ɗauka.
ajje wayar tai tana saka takalmanta daidai ana kiran sallar maghrib, jin kiran sallar tai kamar acikin ƙirjinta akeyi daga masallacin Manzon Allah Sallallahu saboda yadda yake ratsa ƙirjin ta ta lumshe ido.
tana bi gently har aka kammala, sannan tayi azkar ɗin da akeyi after.
daidai Aunty Nadra tana turo ƙofar ɗakin itama ta shirya cikin wata brown abaya plain me faɗi sosai, tana murmushin tace "ai dama nace ma kawun ki,
kina da hinma,
har kinyi wanka kinyi alwala ko?
wai cewa yake abarki ki fara hutawa kici abinci zuwa isha sekije masallacin,"
da sauri Imsal ta nufo bakin ƙofar inda take tana faɗin
"ni bangaji ba,
Aunty zan iya zuwa masallacin aiba nisa," murmushi Aunty Nadra ta sake yi tana dafota tace
"nasani Imsal,
nima haka nace mai muje kawai,"
Jinjina kai tayi tana murmushi suka fito tare,
hannunta cikin nata,
Uncle Bello na zaune saman couch yana jiran su da dan mamaki yace
"Imsal har kin gama,
zaki iya?"
jinjina masa kai tayi tana murmushi yace "toh kumuje ko,
kar atayar da sallah,
kinyi alwala ko?"
jinjina mishi kai ta sake yi suka fito tare, elevator suka hau ya sauko dasu ground floor, suka fito waje sannan suka fara takawa da ƙafafuwansu zuwa masallacin Annabi ﷺ, duk inda ka kalla Mutane ne, ƙabila iri-iri, yare kala-kala tun daga farare, faƙaƙe, larabawa, turawa, indiyawa, da ƴan Africa kamar mu, kowa da kalar harshen sa amman duk manufarsu iri ɗaya ce acikin zuciya wato bautar Allah.
Koda suka isa ƙofar masallacin, Imsal gani tai mosque ɗin ya ƙara girma da haɓɓaka ba kamar sanda tazo da farko ba, ga dubban mutanen dake shiga, wani irin shauƙi takeji aranta tinawa da cewa wannan shine masallacin da Annabi ﷺ yayi sallah a cikinsa, sannan shine masallacin da sahabbai suka rayu a cikinsa, jitai ƙwalla na taruwa a idonta. Aunty Nadra ganin haka ta ɗan dafata tana faɗin
"Imsal are you okay,"
Da sauri tana murmushi ta jinjina mata kai, tace
"Yeah,
muje Aunty,"
Tare suka shiga cikin haramin,
tana jin wani sanyi na ratsa ta.
Shiru tai na wasu daƙiƙu tana kallon haramin, Mutane ne kawai take gani tako ina fiye ma da wanda ta gani awaje, har anfara haɗa sahu jin za'a tada sallar anayin iqama,
Aunty Nadra ta jata suka wuce inda mata suke, Uncle Bello yayi ɓangaren da maza sauke suka bi sahu aka tayar da sallar maghrib, koda suka idar bata tashi daga inda take ba daga ita har Aunty Nadra qur'ani suka ɗauka suka fara karantawa har aka kira sallar isha'i, sukayi.
bayan da aka idar ne mutane da yawa suka ɗan fara fita, amman har lokacin Imsal ko yunƙurin tashi batai ba, saboda nutsuwar da take ji ta samu, wacca bata taɓa samun kanta a cikinta ba, tunda take.
Ganin ta cigaba da karatun har sun kusa shafe awa ɗaya da rabi yasa Aunty Nadra kallan ta tana faɗin
"Malama Imsal"
Ɗagowa Imsal tay tana kallonta,
Message ɗin da Uncle Bello ya turo mata ta nuna mata tana faɗin
"Yace yunwa yakeji inkuma yatafi ya barmu ne toh, nima kuma yunwar nakeji"
Murmushi Imsal ta ɗanyi,
se yanzun ta tuna gaba ɗayan su rabon su da abinci tun a jirgi amman sam ita bataji taji yunwar ba ko kaɗan.rufe qur'anin tayi tana yin addu'a ta miƙe tana faɗin
"Tohm Aunty muje,"
Miƙewa Aunty Nadra tai, suka nufi hanyar fita, tana sake bin masallacin da ido ita ji take kamar ta kwana anan.
A waje suka samu Uncle Bello suka fito tare gaba ɗaya, Duk da darene amman sanda suka fita gani tai kamar ma rana ce dan akwai haske ta ko'ina, haka ma al'umma sai kai kawo sukeyi, ga masu siyar da misbaha da turare da dabino nata cinikayyar su, komai na garin is so peaceful babu hayaniya ko kaɗan.
A haka ta ringa kalle kallenta har suka ƙaraso hotel ɗin suka hau elevator zuwa floor ɗinsu Aunty Nadra nataiwa Uncle Bello complain ɗin rashin samun Hajiya Nafisa awaya.
Suna shiga aka kawo musu abinci mai rai da lafiya da Uncle Bello ya musu order, anan falon suka zauna sukaci dukda ba wata yunwa takeji ba haka ta daure taci, dan kar suyi mata faɗa, dan taga yadda Aunty Nadra ke kallonta closely.
seda suka gama ta koma ɗakinta,
suka wuce nasu sannan ta farajin gajiyar tafiyar da sukai ajikinta.
Amman ƙin kwanciya tai,
ta wuce bakin window tana cigaba da kallon masallacin da jama'ar dake ta shiga suna fita daga cikinsa, kamar me tsoron inta kwanta tai barci zataga mafarki takeyi.
se ƙarfe biyu sannan ta shiga toilet ta ɗauro alwala ta fito tai nafilfilin data sabayi duk dare, tai addu'o'in ta wanda tana cikin yi barci ya kwashe ta.
bata ƙara sanin inda kanta yake ba seda taji kiran sallar asubah,
da yake tasa abin aranta kuma ta saba tashi ana fara kiran take jinsa har tsakiyar ƙirjinta.
Miƙewa tai tana ɗan kallon ɗakin da take addu'ar tashi daga barci tayi tana ɗan miƙa ta nufi wurin window ta janye curtains ɗin, murmushi tai ganin haramin, wata irin nutsuwa taji aranta, ta wuce toilet a gurguje tai wanka ta wanke bakinta ta daura alwala ta fito ta shirya cikin doguwar rigar ta plain purple me kyau ta zira hijab ɗinta me ɗan kauri har ƙasa fari tas ta fito.
Bata jima afalon ba su Uncle Bello suka fito, tare suka wuce haramin don yin sallar asuba, anata shigowa tako ina.
Bayan an idar da Sallah,
zama sukai,
sukai azkhar da karatun Alqur'ani har seda rana ta fara fitowa sannan suka koma hotel ɗinsu, sukai breakfast kowanne daga cikinsu ya shige ɗaki dan samun hutun daya kamata.
seda akai kiran azahar sannan suka koma Masallacin, har akai la'asar suna can, koda Aunty Nadra tace su koma hotel su dawo da maghrib ƙi tayi tace mata ta gane hanya taje kawai ta taho.
kyaleta tai ta taho abinta,
itakam Imsal wani daɗi taji haka ta ƙarasa wunin ranar cikin mosque, tana zikirori da karatun Alqur'ani da addu'o'in ta har seda akai maghrib.
Aunty Nadra ta dawo sukai maghrib da isha'i tare, se wurin karfe goma saura suka koma hotel ɗin,
Uncle Bello yana tsokanar ta yace
"ya zata kwana zatayi acan ai,"
Murmushi tayi tana ɓoye fuskarta, jikin jin kunya.
Aunty Nadra tace
"ki kira Barrister,
tun ɗazun take kirana tana neman ki,
kina masallaci bata sameki ba,"
Jinjina mata kai tayi,
Aunty Nadra taɗan yin jim kafin tace
"Bani number Abdullah ta South Africa in kina dashi inata kiransu bansamu ba daga shi har uwar,"
A sanyaye tashiga karanta mata number up head danta riga ta haddaceta kallo ɗaya takema number duk tsayinta ta rike musamman idan lambar wanda yakeda wani gurbi na musamman azuciyarta ne.
Ganin se ƙasa dakai take alamar jin kunya Aunty Nadra bata wani nuna mata mamakin jin ta haddace number tasaba tana gama rubutawa ta shige.
Imsal kam bayan ta ɗan taɓa abincin da aka ajje mata wuce wa ɗakinta tai.
Seda ta farayin wanka sannan ta dawo ta ɗau wayarta ta kira Mummy,
Kamar kwa jira take tana online tai picking,
Cikin ɗan faɗa take cewa
"Wato kin kira kowa kinsan da kowa banda ni dana haife ki ko Imsal?
ya miki kyau,"
Shiru Imsal tai dan batasan me zatace mata ba, jin daga kira tafarai mata faɗa kamar dama asaman take.
Jin tayi shiru Mummy ta ɗaura da
"bakya jina ne,"
Asanyaye Imsal tace
"Ina wuni Mummy,"
A hassale Mummy tace
"Lpy,
tunda se yanzun kika tuna dani,"
Gently Imsal tace
"Kiyi haƙuri Mummy na kira jiya bakya online ne,"
Tace
"yau kuma da kika tashi meya hanaki sake kira?"
Ahankali Imsal tace
"Kiyi haƙuri Mummy,"
Cikin son a zauna lafiya kawai.
Mummy cikin jin daɗin yadda take feeding ego ɗinta tana bata haƙuri tace,
"Ya kuke?"
Tace
"Lpy lau Alhamdulillah Mummy,"
Ciki ciki tace
"Toh Masha Allah,
Mubeena ta kira ki kuwa,"
Da ɗan mamaki Imsal ta girgiza kai tace
"A'ah Mummy,
Naji aunty ma tace bata samun su fatan komai lafiya"
Maimakon ta amsa mata tambayarta,
Se tace Cikin bugar ciki tanason tasan ko tasan halin da Abdullah ke ciki .
"Mamarsu fa ko Rayyan?"
Girgiza kai tayi alamar a'ah,
Tace
"Kinsan me Imsal,
Kawai ki kashe wayar ki,"
Cike da rashin fahimta tace
"Mummy in kashe waya kuma?"
Tace
"Eh kinga karta dauke miki hankali daga yin ibada,
In zamu miki magana kawai se muyi contacting ɗinki ta wayar Uncle ɗinki ko Nadra,"
Ba tare da tunanin komai ba Imsal tace
"Toh Mummy, zan kashe,"
Cikin jin daɗi Mummy tace
"Yauwa Allah yayi miki albarka,
Ya karɓi ibadu, yaushe zaku wuce Makka,"
Imsal tace
"Jibi in sha Allah,"
Mummy tace
"toh Allah ya kaimu seda safe,"
A hankali tace
"Allah ya tashemu lafiya,"
Tana katse wayar.
Imsal ta ɗanyi shiru tana tunani, har zata kashe wayar se kuma ta tina batai magana fa da Hajiya ba har lokacin.
wayar Rayyan ta sake kira cikin Sa'a ta shiga amman beyi picking ba se message da taga ya turo mata
"How far?"
Da mamaki take kallon dry message ɗin,
How far? fa itace blood ɗinta kece mata haka? tayi tafiya me nisa haka?
A sanyaye ta shiga mai typing,
"Ina wuni blood,
Ykk,
yasu Hajiya,
Dama so nakeyi nayi magana da ita dan Allah ko zaka haɗani da ita,"
Gani tai ya fara typing,
Se kuma ya tsaya,
Se ya ƙara farawa sannan yayi sending
"All good,
Bana gida."
Abinda kawai yasa mata kenan taga ya tafi offline.
tagumi ta rafka tana kallon message ɗin nasa zuciyarta najin ba daɗi, ta shiga DM ɗin Mubeena gani taima kamar rabonta da online tun kwana huɗu da suka wuce.
Scrolling up ta farayi,
tana kallon chats ɗinsu na baya yanayin shaƙuwar su da yadda Mubeena ke bombarding DM ɗinta da voicenotes da funny videos iri iri amman yanzun se sufi sati ma basuyi magana ba.
wani irin kewar ƙawar tata taji tana yi kawai ta mata dropping message ta sauka online ɗin, kamar yadda Mummy ta shawarceta kashe wayarta tai don tai focusing akan ibadarta baki ɗaya.
Washegari da safe bayan sun dawo daga Sallar asubah Uncle Bello ya sanar dasu yau zasuje ziyarori, sosai Imsal tayi murnar jin haka, wanka sukai suka shirya acikin motar hotel suka tafi,
Guri na farko da suka fara zuwa shine Masallacin Quba, masallacin farko da aka gina a musulunci, gurin da Annabi ﷺ yake zuwa, sannan yana son zuwa can duk ranar asabar.
Sallah sukayi raka'a biyu, tare da addu'a sannan suka fito.
Daga nan suka wuce yankin Uhud, tun daga nesa Imsal ta hango babban dutsen.
Cikin ƙarin bayani Uncle Bello yace mata
"Imsal wannan shine Uhud kin hangoshi ko,"
dan yasan lokacin da Imsal tazo da Mummy bata wani barta ta sake tazo ziyara ba kamar yadda akeso saboda ciwanta da yayi wani irin tashi kusan shekara hudu da suka wuce.
Jinjina masa kai tayi tana murmushi, cikin jindadi saboda dutse ne wanda ta daɗe da jin labarinsa shekara da shekaru cikin sira, tun tana ƙarama bama ta iya karatu ba Mahaifin Abdullah Sheikh Suhail ke zaunar dasu su uku ita, Mubeena, da Natasha yana basu tarihin manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama da sahabbansa, kuma tun daga lokacin tasan dutsen, dutsene da sahabbai suka yi yaƙi a gefensa, dutsen da sayyadina Hamza bn Abdulmuttalib رضي الله عنه yayi shahada a kusa da shi.
Koda suka isa cikin nitsuwa ta fito daga cikin mota da Aunty Nadra agefenta, ta shiga kallon dutsen, tanajin kamar tarihin yaƙin Uhud na dawo mata daki daki saboda tarihine da taji ba sau ɗayaba, ba sau biyu ba, tana tina yadda maharba suka sauka daga gurinsu, da yadda jarabawa ta afkawa musulmai, da yadda Annabi ﷺ ya ji rauni.
Rintse idonta tai tanajin wani irin rauni da shauƙin soyayyar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam da sahabbansa dake ratsa kirjinta tana tina duka sacrifices ɗin da sukayi dan ɗaukaka kalmar Allah.
Nanma basu wani jima ba suka wuce zuwa Baqiyya, tun kan su ƙarasa Uncle Bello ya shiga yimata bayani yace
"Anan ne aka binne dubban sahabbai, tare da iyalan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam da yawa"
Jinjina masa kai tai alamar ta gane.
Washegari da safe ta kama bakwai ga wata ranar ya kama zasu wuce Makkah duk da tana son zuwa Makkah amman ji take yi kamar karta bar Madinah saboda akwana ukun da sukayi sosai takejin zuciyarta ta samu nutsuwar data daɗe bata samu ba,
Tanaji kamar zata tafi tabar wani ɓangare na zuciyarta anan.
Dan koda daddare da Uncle Bello ya shigo ya sanar da ita da safe zasu wuce Dhul Hulayfah, anan zasu yi niyyar Umrah saboda tamattu'i zasuyi, kasa kwanciya tayi daga ƙarshe dai masallacin ta wuce tayi nafilfili kafin ta dawo hotel ɗin.
kwata kwata barcin two hours tai akai kiran sallar asubah, suka sake komawa mosque sukai Sallah kafin su dawo su fara shiri.
Bayan sun gama breakfast suka sauko lobby tare, an riga an sauko musu da kayan su.
Already driver na jiransu,
Uncle Bello na gama checking out suka fito zuwa parking lot.
Driver ɗinsu already yana jiran su.
Imsal ce ta fara shiga bayan motar idonta akan wayar Aunty Nadra data bata suna video call tare da Natasha da Hajiya, tana ɗan murmushi kasa ƙasa, har ta zauna tana kallon wayar ta.
Aunty Nadra na waje suna magana tare da Uncle Bello, gaba daya hankalin ta na kan wayar, amman tana jin sanda aka buɗe ƙofar motar aka shigo tinaninta Aunty Nadra ce, hakan yasa tai sallama dasu ta kashe dan tabata wayarta, amman jin familiar ƙamshin turare wanda be mata kala dana Aunty Nadra ba yasa ta jiyo da ɗan mamaki dan batai tsammanin ganinsa a irin wannan lokacin ba.
Ɗage mata gira daya taga yayi yana faɗin
"Hey Lulu,"
Idonta na sauka cikin nashi yana gama gyara zamansa agefenta amman ba daf ba, sanye yake cikin farar jallabiya da farar hula yadda kasan wani Sheikh ɗin malami shigar ta mugun karɓar sa sumarsa tayi luf luf kamar wani baƙin balarabe.
tsabar mamaki ma kasa magana tai for the first time tin zuwanta Madina taji wani abu ya ɓata mata rai.
ta ɗauke idonta daga kallonsa, shikam gogan naku murmushi yake yi kamar ma besan me takeyi ba,
Cikin tsokana yace mata
"Surprise,
Ai dama nace miki sena biyoki,"
Cikin kulewa tace
"Duk dai ibadar da akayi badan Allah ba, dan wani ba karɓaɓɓiya bace ba,"
Hararar wasa ya galla mata yana faɗin
"If your the god,
innayi karki amsa,
Rude"
Shima ya ɗauke kansa daga kallonta irin yayi zuciyar nan,
Ƙwafa kawai tayi.
Daidai Aunty Nadra na leƙosu ta taga,
cikin tsokana tace
"Imsal kinga mutumin naki ya biyo mu ko?"
Kwabe fuska tai kamar zatai kuka tana kallon Aunty Nadra, wacca ke mata dariya dan ita kaɗai ta fahimci bata shiri da Farouq ko kaɗan.
Juyawa yayi yace ma Aunty Nadra
"Niba itafa na biyo ba aunty,
ibada nazo yi nima,"
Ƙasa ƙasa Imsal tace
"Kadai ringa jin tsoron Allah."
Murmushin yayi dimples ɗin both cheeks ɗin shi na loɓawa,
ya juyo gare ta batasan ya jiba shima ƙasa ƙasan yace mata
"Da tsoron ki zanji wife."
Banza tamai bata sake mai reply ba har aunty Nadra ta shigo,
da yake motar me baya biyu ce babba kuma, suna can karshe seya kasance Aunty Nadra ce atsakiya se Uncle Bello gefenta gaba kuma driver ne shi kaɗai babu kowa agurin me zaman banza.
Haka driver yaja suka ɗau hanya,
Ƙasa ƙasa Farouq yayi leaning wurin kunnenta yace
"Amman fa kin ƙara kyau."
Ɓata rai ta sakeyi tana roƙon Allah yayi nata maganinsa kada ya lalata mata aikinta bataji ba, bata gani ba.
Shikam ganin taƙi kula shi ta maida hankalinta kan window tana kallon hanyoyin Madinah yasa ya lumshe ido yanajin wani irin farin cikin kasancewar ta tare dashi haka.
Seda suka fara fita daga birnin ya buɗe idanuwansa yana ɗan kallonta ahankali yace mata
"Lulu."
Banza tamai kamar bada ita yake ba ya sake cewa
"My luuu."
In kin tanka Imsal ta tanka
Yace
"Future wife."
Da sauri ta juyo,
Cikin ƙoƙarin controlling temper nata tace masa
"Farouq!"
Yace
"Na'am Lulu."
Tace
"Wallahi idan baka yi shiru ba..."
Kanta ƙarasa ya katse ta cikin daring nata yace
"Zaki mene?"
Hada kai da gwiwa kawai tai,
hawaye na zuwar mata dan bataso ya ɓata mata duk burin da taci nayin aikin hajji yadda ya kamata.
Aunty Nadra ce ta juyo,
Strictly ta kalleshi ta faɗin
"What happen?
naga kamar tana kuka?"
Ɗaga hannayensa yayi in surrender yake fadin
"Nothing aunt you can asks her,
Lulu stop being a crying baby,
me na miki please,
bakyau sharri fa,"
Banza tai masa,
Uncle Bello ne ya juyo yana kallonsu,
Yace
"Imsal ɗago ki faɗamin meya faru kike kuka?
meya miki?"
Cikin sangarci ta ɗago tana faɗin
"Ba shine yake ta sani ɓacin rai ba, kuma yanata jana da faɗa bayan aikin hajji zamuyi karya lalata min,"
Gaba ɗayan su wata irin dariya ce tazo musu, saboda yadda tai maganar, dan Aunty Nadra da Farouq seda sukai,
Uncle Bello ne ya dake yana kallon shi cikin faɗa yace masa
"Farouq ba ruwanka da ita, idan kace takurama ƴata zakai zamu raba tafiyar nan, kayi taka muyi tamu, aikasan hanya."
Ƙunshe dariyar sa yayi yana faɗin
"Okay,
Okay I'm sorry luuu,
Bazan sake ma cewa komai ba,
I promise kibar kukannan kinsan banaso ko,"
Ya ƙarasa faɗa yana leƙata,
jinginar da kanta tai a window tana share hawayen tana tura baki kamar wata ƙaramar yarinya.
Bayan kusan minti talatin suka isa Dhul Hulayfah, Miqat ɗin mutanen Madinah kenan, anan ne duk wanda ya taho daga Madina zuwa Makka yake ɗaukar Ihrami,
Anan ne kuma suke niyyar yin Umrah.
Fitowa sukai daga motar, Aunty Nadra da Imsal suka shige cikin masallacin suka nufi ɓangaren mata dan yin alwala suma su Farouq sukayi nasu ɓangaren.
Bayan sunyi alwala suka ɗaura niyya suka ɗan geggyara wa suka fito.
A can wajen motar suka tarar da Uncle Bello da Farouq suna jiransu, har sun shirya sun sauya kayan dake jikinsu zuwa ihrami, fararen zannuwan nan guda biyu.
For the first time taga Farouq simply yadda yake ba agogon alfarma, ba suit, babu does shiny expensive shoes, his just him, duk kuɗinsa duk matsayinsa da manyan mutanen dake ƙarƙashin sa.
Lura da kallon da take masa yasa ya ɗan gyara tsayuwar sa yana faɗin
"I'm I that fine,"
Kallon da Uncle Bello ya mai yasa ya ɗan nitsu yana faɗin
"Toh sorry nayi shiru,"
Kafin ya faki idon shi ya ɗanyi mata muah da bakinsa yana kashe mata ido ɗaya, ɗauke kanta tai daga gareshi kamar bata ga meya aikata ɗinba.
Da kansa ya buɗe musu mota suka shiga, tare da ɗaura niyyar yin Umrah.
Uncle Bello nasake tunatar dasu kan su yawaita yin talbiyah,
Nan take kuwa suka fara.
"Labbaykallahumma labbayk
Labbayka la sharika laka labbayk
Innal hamda wan ni'imata laka wal mulk
La sharika lak."
Wani irin sanyi ne Imsal taji yana ratsata, ta maida kanta jikin kujera, tana maimaita talbiyah akai-akai.
Hanyar Makkah suka nufa, wacca a irin wannan lokacin zaka ga motocin alhazai, da bus bus suna ta wucewa,mutane ta ko ina daga kowanne sassa na duniya suna tahowa da purpose guda ɗaya wato cike rukunin addinin su.
Seda sukai tafiya me tsayi, sannan Farouq ya kalleta a hankali yace mata
"Mun fa kusa shiga Makkah,"
Ɗagowa tai tana kallonsa, cikin mamaki irin ya akai ya gane ɗinnan?
dan bama tai expecting yana daga cikin mutanen da suke zuwa saudiyya ba da har ze iya tantance hanyoyinsu,
sharewa kawai tayi a tinaninta shaci faɗa kawai yayi aiko cikin ƙanƙanin lokaci taga ta fara hango fitilun garin da Manyan gine gine.
Ɗan kallonsa tai da ɗan mamaki ya ɗage mata gira ɗaya,
irin I told you so ɗinnan yana maida kansa baya ya lumshe ido har suka shiga cikin garin Makkah.
Hotel ɗin da suka kama direct suka wuce wanda yake daf da harami kamar yadda wancan da suka zauna a Madinah yake.
katafaran hotel ne da yake ƙarɓar alhazai daga kowana sassa na duniya.
cikin girmamawa staffs ɗin suka tarbesu, aka ɗauki kayansu zuwa floor ɗin da ɗakunan su yake, suite suka kama kamar yadda sukai a Madinah susu uku, se shima Farouq nashi daban.
Aunty Nadra ce tace su huta kaɗan dan nan da lokaci kada zasu wuce masallaci.
Farouq nasa suite ɗin ya shige,
suma suka shiga nasu,
Imsal ta shige ɗakin da Aunty Nadra ta nuna mata a matsayin nata,
Allah Allah kawai takeyi ta ganta agaban ka'aba.
It's fatoumspassion
Don't forget to
Like
Share
Comment
Vote