Chapter twenty two
by @aysharano22
Letter data bashi ma bai samu damar karantawa ba to yana kwance ba lfy sai yau Lucas ya bashi da yaga ya fara samun sauqi, bai sake bata lokaci ba ya warwareta snn ya shiga karantawa kmr haka
"nasan lokacinda zaka samu takardar nan na dade da yin nesa dakai Ayaan, inaso kasan cewa ko kusa ba haushinka nakeji ba kuma ba laifinka nake gani ba domin duk abinda ya faru a tsakaninmu nice sila kuma nina janyo maka aikata hakan...bansan da wane ido zan sake kallonka ba don Allah ka yafemin snn ka roki Allah ma ya yafemin don ni bazan taba yafewa kaina ba kmr yanda bazan taba iya mantawa da abinda ya faru har mucigaba da rayuwa kmr yanda mukeyi a baya ba, sbd i ruined your life, na lalata maka rayuwa nasa ka aikata babban zunubi da kananun shekarunka, dukda kasancewar nice babba shekaruna basu amfanamin komai ba shiyasa kunya bazata iya bari nacigaba da rayuwa tareda kai ba, kuma indai har da gaske kana sona kar kayi yunkurin nemana don bazan iya hada ido dakai ba bayan abinda nayi maka...ina maka fatan alkhairi a duk wani abu da kasa a gaba Allah ya shige maka gaba ya zama gatanka ya hadaka da iyayenka...ina sonka sosai my beautiful baby boy pls karka damu kanka sbd ni kaji?, main bilkul theek ho jaayegi, aur Aapne mere liye jo kuch bhi kiya, uske liye boht shukriya"(i'll definitely be fine and thank you so much for all you've done to me).
Tun yana karantawa ya fara hawaye wanda rabonda yayi hawaye tun ranar da abin ya faru a tsakaninsu sai kuma yau...yanzu shknn Juwairiyya tayi mishi nisa kenan?...yanzu duk mafarkinshi na son kasantuwa tareda ita har tsahon rayuwarshi ya ruguje knn?...yanzu duk soyayya da yayi mata ko ince yake kan yi mata ya tashi a banza knn?...Oh Allah shikam ina zaisa kanshi ne ko zaiji salama?...ina zaisa kanshi ya samu sa'ida?...wnn wace irin jarabawa ce mai wahala haka?...wace irin qaddara ce wnn taketa faman bibiyarshi take kuma dagewa kan saita rabashi da farin cikinshi?.
Ranar yasha kuka kmr ba gobe saida ya sake shan drip don sake kwanciya yayi rigijib rashin lfy fiyema da wanda yayi a baya...bawan Allah Lee haka yayita dawainiya dashi yana kaishi asibiti da jinyarshi hatta kudin asibitin da magunguna shi yake siya shima duk yabi yayi wani firi firi to aboki kuma rabin ranshi ba lfy...saida ya sake kwana hudu asibiti bayan sati dayan da yayi a baya snn aka sallameshi dukda ba warkewa yai gaba daya ba yadai damu sauqi.
Haka suka tattara suka koma gida suka cigaba da gudanar da rayuwarsu suna zuwa makaranta dukda Ayaan kwata kwata ma yayi loosing interest kan karatun.
Bayan sati hudu suna fitowa daga class bayan sun kammala lectures dinsu suka hango Nusaiba daga can gefe tsaye da alama su take jira don tana ganinsu ta shiga dago musu hannu su kuma suka nufi inda take...lokacin six weeks kenn da faruwar abinda ya faru a tsakaninsu har snn kuma Ayaan ya kasa mantawa da komai...ya kasa believing cewa wai shknn Ju ta barshi rabuwa kuma na bar abada...ita kanta Nusaiba bayan sun karasa inda take da taga yanda Ayaan ya koma saida tayi hawaye don tausayinshi...gaisawa sukayi tace mgn take son yi dasu idan ba damuwa, Lucas yace ba komai su samu wuri su zauna sai suyi don haka suka nufi garden dake bayan school din suka zazzauna snn Lee yace mata"to muna jinki Nusaiba Allah dai yasa lfy"...kallon Ayaan Nusaiba tayi kafin ta dawo da kallonta ga Lucas tace"it's about Juwairiyya"...mutuminda tunda abun nan ya faru yana iya yini bai cewa kowa komai ba amma sai gashi da sauri ya hau ce mata"what happened to her pls?...where's she?...is she alright?"...duk a jere ya suburbuda mata tambayoyin baiko bata space din amsawa ba...kallonshi kawai Nusaiba take cikeda tausayinshi, tayi imanin cewa Ju bazata taba samun namiji da zai sota kmr yaron nan ba, dubi yanda ya lalace yayi duhu kmr ba Ayaan da kowa yake fadar kyawunshi ba...janye idonta tayi daga gareshi cikin ranta tana jinjina nauyin mgnr da zata fada musu dukda cewa batasan ya zasu dauketa ba itadai burinta a gyara ne ba a bata ba don haka ta fuskanci Lucas don bazata iya kallon Ayaan sa'adda zata fadi mgnr ba tasan yana iya sata kuka tsabar tausayin da yake bata.
Ba Ayaan din ba kadai hatta Lee zuwa yanzu a qage yake da yasan abinda ke tafe da ita don haka kai tsaye yace"kiyi mgn Nusaiba meya samu Juwairiyya?"...wani yawu ta hadiye da batasan yaushe ma ya taru mata a baki ba kafin a hankali kuma cikin nutsuwa tace musu"she's pregnant"...wani irin dokawa da zuciyar Ayaan tayi saida yakai hannu ya dafe kirjinshi don ji yayi kirjin kmr ballewa zaiyi tsabar bugunda take...Lucas ma zare idanuwa yayi hadda dora hannu akai cikeda tsagwaron shock yace"Jesus christ, pls Nusaiba i hope this is a joke"...girgiza kai Nusaiba tayi har snn bata yadda ta kalli inda Ayaan yakeba tace"well unfortunately it wasn't, it's the truth...she is 6 weeks pregnant, with your child"...ta karasa mgn referring to Ayaan da yanda kasan gunki haka ya sandare a wurin kawai processing kalmar pregnant ma yake acikin zuciyarshi ya kasa ganewa...like is this realy happening to him or he's in the middle of a dream?...is she really pregnant with his his child?..kenan idan da gaske ne hakan na nufin cewa zai samu 'da ko 'ya tareda Juwairiyya?...kenan zai samu somebody that he can call his blood?...shi sai yanxun ya tafi tunanin cewa duk rayuwarshi yayita ne da mutanen da bai hada jini dasu ba infact tunda yake bai taba gani ko sanin wanda suka hada alaqa ta jini dashi ba amma yanzu gashi Allah bashi...hakan na nufin kenan bazai kare rayuwarshi without blood relation ba domin duk abinda ta haifa zai iya bugan kirji yace wnn jinina ne kmr yanda a kullum kowa yake tutiya da jininshi ba kamar shi da yake tutiya da jinin wasu ba domin koda Umma ta haifeshi she's not his biological mother tunda bada egg dinta akayi producing dinshi ba.
Bature yayi gsky da yace blood is thicker than water don instantly Ayaan yaji he can do anything to protect that pregnancy dukda bata hanyar aure aka sameshi ba he don't care...da sauri ya dago ido yana kallon Nusaiba as ya riga ya gama making decision dinshi to keep the baby yace"pls where is she?..i need to see her, you need to take me to her now"...ya karasa mgn jikinshi kmr mazari tsabar matsuwa da yai yayi mgn da ita...daga ita har Lee kallonshi kawai suke an rasa mai bakin mgn saida Ayaan ya sake cewa"pls Nusaiba ina take?..i need to talk to her plsss"...ya karasa mgn yana hade mata hannayenshi alamar begging duk yabi ya sake rikicewa...ajiyar zuciya Nusy ta sauke kafin tace"zan kaika inda take but before then inaso kasan cewa Juwairiyya batasan nazo wajenka ba, she even tried to abort the pregnancy amma Allah bai yadda ba...da tasha magani taga bai zube ba shine yanzu take kokarin zuwa ayi mata evacuation, ni kuma tsoro nake ji mata coz i know how dangerous abortion is, and i don't want to loose my friend shiyasa na yanke hukunci inzo in fada maka koda zataji haushina"...mikewa sukaga yayi a zabure ya hau girgiza kai kmr zaisa kuka yace"no she can't do that, Juwairiyya will do no such thing to me she can't abort my baby"...mikewa Lee yayi yana dafashi yace"hey take it easy, everything will be fine"...ture hannunshi Ayaan yayi yana cewa"no Lucas she can't take it out, that's my only blood in this world, banida kowa tunda na tashi ban taba sanin wanda na hada jini dashi ba so she can't do this to me"...ya karasa mgn yana fashewa da kuka Lucas ya rungumeshi yana rarrashinshi...shi kanshi yana ganin jarabawa kala kala akan Ayaan saidai fatan Allah bashi ikon cinyesu gaba daya.
Da kyar ya samu ya lallabashi ya bar kuka daga nan kuma suka tafi asibitinda zaayi mata evacuation din don already tana can batasan nusaiba tazo ta fallasa mata ba...a wani office suka sameta zaune tana jiran Dr da zata mata abun su gama shiryawa kawai ganinsu tayi a kanta nan take tasha jinin jikinta...kallon Nusaiba tayi irin kallon tuhuma kafin ta dawo da kallonta ga Ayaan da dukda kokarin zubar mishi da ciki da take ganinta ba karamin sanyaya ranshi yayi ba sai yaji kmr yayi shekara da shekaru bai ganta ba...kmr mara laka a jiki haka ya shiga takawa zuwa inda take kawai sai ji tayi ya mikar da ita tsaye ya rungumeta da wani irin karfi ya fashe da kuka yayinda jikinshi keta karkarwa..tsit Juwairiyya tayi jinshi a jikinta ba karamin tayar mata da hankali yayi ba don ji tayi kmr babu tsoka ko daya a jikinshi sai kasusuwa sai kuma fatar data lullube kasusuwan tsabar ramar da yayi...batasan sanda ta rungumeshi ba itama tana hawaye, ko Allah yasan ba karamin missing dinshi tayi ba.
Pay 500 into 0013569116 Aisha Ahmad Tijjani Ja’iz Bank, sai a tura evidence ta ***.
Rano✨