JODAH

02

by @sadisakhna


 

  _____👑 *JODA* 👑_____ 

 

              

 

 

 

Na  

 

*Sadi-sakhna* 

 

Ƴar mutan Jama'are 

 

 

 

 

 

 

 

THE TRIO OF TALES  

(3⃣ minds, 3⃣stories,1⃣Journey)  

 

 

 

*HarÆ™a ta (2)*👑 

 

 

 

 

 

 

 

"Dan Allah kici abincinnan kada yayi sanyi kinji" 

 

 

 

"Nakoshi ko naci ma amansa zanyi Aban Joda,zuciyata ta kasa sukuni ji nake kaman zata buga ta fashe. Bantaba sanin inason ÆŠiyata ba duk da lalurar datake É—aukeda ita sai yau,ita kaÉ—ai ce wacce nake gani a matsayin cigaba na zuri'h ta,babu wanda yake É—aukeda jini na sai ita,amma inaji inagani saboda dogaro da jahilci da kuma Al'ada za'a binne min ita tana numfashi,dama haka umman zakir taji da aka kashe mata É—anta?" 

 

 

 

"Dan Allah kidaina wannan sambatun haka,nace miki babu wanda zai kashe mana ita ki kwantar da hankalin ki kinji" 

 

 

 

"Uhmm tohh mai zakayi,wanne mataki zaka É—auka ka faÉ—amin ko raina zaiyi sanyi" 

 

 

 

"In lokacin yayi zaki sani kedai ki tashi kici abinci ki tafi aiki kar a zargi wani abu,naji su Umman Sule ma sun zunÉ—enki É—azu jiyama bakije aiki ba" 

 

 

 

"Wanne aiki akeso naje Æ´ata tana wannan halin mai kamada mutuwa,wai mu ba mutane banene,ko dabba Æ´ar ta batada lafiya inaga ba'ayi mata adalci ba idan akace ta tafi aiki,ni ba inda zanje" 

 

 

 

"Meyasa kikeda rikicewane Aminatou,nasan halinda kike ciki babu daÉ—i,amma bazaki yarda dani ba kiyi abinda nace,kinfiso ki sake jawo hankalin kowa kan abinda muke ciki ne. Idan kin yarda dani kitashi ki tafi aikinki,kekanki kinsan dabba ma tafimu a wanann rayuwar,Allah ne kaÉ—ai yake kallonmu a matsayin bayinsa masu daraja,amma ba Æ´an adam yan uwanmu ba." 

 

 

 

A haka jiki kaman babu laka tana waiwaye tana kallon Joda dake kwance kaman mai bacci har ta fice daga cikin É—akin. 

 

 

 

 

 

Cikin harabar Fadar ta shiga,kana tabi wani lungu dazai kaita Turakar  Garka (Gimbiya)Hamdiyyah. Matace Mai haÆ™uri da Sanyayawa na Æ™asada ita,saidai Jakadiyarta  kuma batada mutumci ko kaÉ—an,duk inda tasan inta bi zata taka wani to nan take bi.  Yauma a tsaye take da jajayen kayanta anyi musu ado da kalar baÆ™i irinna sauran bayi,itakuma nata da ja ajiki yana nuni da shugabanci. 

 

 

 

Tunda suka haÉ—a ido da Aminatou daga nesa gabanta yabada sautin dummm domin tasan ita da ita Allah ne kaÉ—ai zai rabasu. Cikin sanyin jiki ta Æ™ariso inda take a tsaye tana sunkuyar dakai,yayin da itakuma take binta da wani kallo kaman taga É—an tsako. 

 

 

 

"Da izininwa baki zo aiki ba jiya,kodan kunga uwargijiyarmu bata damuwa shiyasa kuke cin karenku babu babbaka. Da akayi mana alfarmar zama wani sashe mu Æ™irashi da namu sannan mu taho aiki da safe shine yabaku damar yin yadda kukeso? Wata Æ™asar zaku samu hakane. Zakuwa ki fuskanci naki hukuncin" 

 

 

 

"Kiyi haÆ™uri Jakadiya wlh É—iyata ce batada lafiya,shiyasa bansamu damar zuwaba dan Allah kiyi haÆ™uri kiyimin rai" 

 

 

 

"Dan Æ´arki batada lafiya shine bazaki zo wajen aiki ba,kin manta da ko kece bakida lafiya dolene kizo ballantana wata Æ´arki? Lallai kun samu Æ´anci bayinnan." 

 

 

 

Kallonta Aminatou takeyi cikeda Æ™unan rai,saikace itama ba baiwar bace,wannan da itace sarauniya da tuni ta gasa kowa ta cinye. 

 

 

 

"Wai ma wacce Æ´ar kike tunani,badai wannan tunkiyar Æ´ar taki ba da batada maraba da mutumtumi,wannan idan tamutu ma aikin huta zakiyi aikinki cikin nutsuwa,nima kuma zan huta dajin uzurinki a kullum" 

 

 

 

Wani É—aci Aminatou taji ya ziyarci maÆ™ogaranta, babu abinda ta tsana irin a Æ™ira Æ´ar ta da wannan Æ™asÆ™antaccen sunan,shin meyasa mutane suka manta da cewar itama uwace,idan suka Æ™ira Æ´ar ta da sunan zataji babu daÉ—i? 

 

 

 

Cije bakinta tayi idanunta sun kaÉ—a sunyi jawur,gabaÉ—aya kunnuwanta sun daina ji ballantana tasake jin wata kalma daga bakin Jakadiyar.  

 

 

 

Firgit ta dawo hankalinta jin ihun da Jakadiya take mata. 

 

 

 

"Wannan kallon da kikemin fah,ba tunkiyar bace ko Æ™arya akayi ai gwara tunkiya ma za'a kaita kasuwa a sayar ko yanka,itakuwa fah dakike ta É—awainiya da ita wani amfani zatayiwa kanta balle kema ta amfaneki,sai wahala dakike akanta wasu ma kina damunsu" 

 

 

 

"Jakadiya duk abinda zaki faÉ—a dan Allah ki daina Æ™iran Æ´ata da wannan sunan banaso,kuma da kike zancen amfani sai É—anka yanada amfani zaka soshi,sannan akwai wanda in Allah yayi niyyar azurtashi da É—a yake zabar wanda zai bashi ne. Abinda Allah ya jarabci Æ´ata dashi Jarrabawata ce kuma na karba hannu bibbiyu,na yarda Allah yanada kallona kuma zaimun Fasihnya da mafi kyansa a duniyarnan ko kuma a lahira" 

 

 

 

"Iyeee lallai ke kinsan wanne kuskure harshenki yake faÉ—a,lallai kin Æ™ira mutuwarki ko kuma azabarki,ke zo nan je ki Æ™iramin Sarkin zagi yanzunnan . Kice yazo yayiwa wata baiwa hukunci na bulala hamsin,ya taho da dorinarsa" 

 

 

 

Da rawar jiki wata mai kaya irinna Aminatou ta matso jinjina kai alamar karbar saÆ™on kafin tasaka gudu zuwa wani bangaren. 

 

 

 

Ita dai Aminatou tana tsaye a wajen ga rana tana cikinta ta haÉ—a gumi,ga tunanin halinda Æ´ar ta take ciki sannan kuma ga kallon zakici Æ™wal ubanki É—innan yau. 

 

 

 

Duguzun duguzun ya shawo kwana da wata Jar babbar rigar saÆ™i a jikinsa yana jijjiga wata Æ™atuwar dorina a hannunsa,bayansa kuma wacce aka aika ta Æ™irashi tana binsa da sauri sauri. Taraddadin dayake cikin zuciyar Aminatou na tunanin halinda Æ´ar ta take ciki ya zarce cin wata fargaba da hukuncin da Jakadiya ke shirin yi mata. Ji take idan da in anyi mata wannan dukan Æ´ar ta zata tashi to ashirye take ta Æ™arbi ninkinsa ma. 

 

 

 

Yana isowa wajen ya washe baki da suka haÉ—a ido da Jakadiya,itakuwa ganin kallon dayake mata yasa tayi fari da ido sai kace wata yarinya sannan tayi wata Æ´ar rausaya. Don kowa yasani Sarkin Zagi na É—aya daga cikin wanda suke zawarcin Jakadiya bayan mutuwar mijinta a fagen yaÆ™i. 

 

 

 

"Jakadiya sai anganki aga Gimbiya,idan ba a ganki ba babu mai ganin gimbiya,taka lafiya idaniya Mikiya mai kulada dukkan komai" 

 

 

 

Ƙirarin duk da mai cika ma'ana ba amma babu laifi yataka rawar gani wajen fasa kan jakadiyar,take kuwa taji ta kamar a saman gajimare. 

 

 

 

"Kaga ba wannan ba, wannan baiwar nakeso ya saitamin ta dawo kan hanya,wai har ni nayi zafin da zata dunga maidamin magana akan wata shanyayyar Æ´arta da ko kaÉ—an bata kama hanyar shiga sahun mutane ba" 

 

 

 

"Ehhh lallai ta tafka babban kuskure dole a ladabtar da ita tagane iyakarta" 

 

 

 

Jijjiga bulalar yasakeyi tareda zare ido ya turbune fuska kaman bashine yake kafa fadarsa a wajen Jakadiya yanzu ba. Tsawar daya dakawa Aminatou ne yakasa hantar cikin ta ta kaÉ—a jikinta yafara mazari. Kafin tayi wata wata taji ya zage ya zuga mata bulalar hannun nasa. 

 

 

 

Cikin gigita ta tsugunna a gabansa ta É—aga kanta sama tana kallonsa,hannayenta dukka suna gadon bayanta tana Æ™oÆ™arin sosa inda bulalar ta kwanta a jikinta. 

 

 

 

"Kwanta kwanta!!! Ki Æ™arbi hukunci Æ´ar jakar uba,daga kunga anayi muku sanyi sanyi saiku fara raina na gaba daku ko?" 

 

 

 

"Kai kai la'ilah mai nene haka mai tayi maka kake mata wannan dukan kaman kasamu gardi É—an uwanka" 

 

 

 

Denti Hamdiyyah ce take maganar tana leÆ™owa ta turakarta jin hayani a Æ™asan tagarta. 

 

 

 

Cikin sauri yaja da baya ya tsugunna jikinsa yana mazari yana zazzare ido. 

 

 

 

"Ranki yadaÉ—e Jiminar Æ™asar Adik,wannan baiwa rashin kunya tayiwa na gaba da ita,wanda idan aka barta ta hanyar zuba mata ido zata iya fara maidawa manyan na sama sosai magana" 

 

 

 

"Wannan ba Aminatou bace,a sanina tunda tatashi a masarautar nan bantaba kamata da rashin kunya ba,ko kuma naji labarin wani yakamata tayi masa ba.....saidai idan wani abunne yafaru daban. Kuma an faÉ—amin tunba yau ba kuna Æ™iran Æ´ar ta da sunaye na Æ™asÆ™anta,idan yau ma abinda kukayi ne to kuwa babu wata uwa dazata jure hakan. Ke Jakadiya ki gyara wajenann komai yakoma yanda yake. 

 

 

 

Ke kuma Aminatou mai yake faruwa?" 

 

 

 

Tsayawa tayi da murje murjen bulalan da sarkin zagi ya shimfiÉ—amata a baya jin Denti Hamdiyyah tayi mata magana. Allah yagani jininta ya haÉ—u dana matar,wannan dalilinne ma yasa sauran bayin suke hantararta ganin ana bata Abubuwa su ba'a basu. Kuma tafisu gaskiyane da riÆ™on amana,sannan ga aiki tsakani da Allah shiyasa Uwargijiyar tasu takeson aikinta har taki yarda ta saida ita ko kuma kaita wani bangaren daban. Da Æ´arta tayi aure ma taso tafiya da ita,amma ta hana saboda tanajin daÉ—in aiki da ita,kuma tasan Aminatou bazata so hakan ba,tunda tanada aure kuma ga Æ´a mai laluri. 

 

 

 

A cikin nutsuwa ta zayyana mata abinda yafaru,duk da kuwa tana cikin halin ciwon bulalun data farasha. 

 

 

 

"Ayya Allah sarki Allah yabata lafiya,ki tashi kije maza ki kulada ita harta samu lafiya saiki dawo na baki dama. Kekuma Jakadiya kishigo ciki inkin gama inada magana dake,sannan karki sake É—aukan hukunci a hannunki a sashena,idan wani abu yafaru kizo ki faÉ—amin,bawai ki Æ™irani wani can da baisan ciwon kansa ba yazo yana yiwa bayina hukunci ba." 

 

 

 

Da sauri jin abinda Denti Hamdiyyah tafaÉ—a Aminatou tatashi tsaye zumbur takaÉ—e jikinta tareda yin Godiya sosai sannan tayi hanyar gida da sauri,ko takan su Jakadiya bata Æ™ara bi ba. Kamar kaza mai Æ´aÆ´an daka É—aure kuma aka saketa tabi bayan Æ´aÆ´anta. 

 

 

 

Tana gama faÉ—ar hakan takoma ciki bayan taÆ™arewa Sarkin zagi kallon kaman taga mahaukaci,badan mugunta da shiga sha'anin bayi bata dameta ba ta tuni ta sutaleshi shima tasaka na gaba dashi sun hukuntashi. Dandai batason bayi suyita yamiÉ—iÉ—i da sunan ta kaman sauran abokan zamanta ne. 

 

 

 

Tana wuce kuwa sarkin Zagi yaja ajiyar. 

 

 

 

"Ke Jakadiya wannan wacce baiwa ce da uwargijiyarki ta muzantamu a gabanta haka?" 

 

 

 

"Hmmm kaima ka faÉ—a,ai inaga bakaga komai bama,mu nan bayinda muke sashennan muna ganin abu,nice da kujerar Uwar bayinnan amma in a gaban Denti ne waccar munafukar har ta fini,kanaga hukuncin da akayi mata yasa da samu sassaucin da kowacce ta haihu bata samu ba? Ni kullum bincike nake na kamata da laifin da zaisa na kawar da ita dukkama,gata da iyayin addini kaman ta É—auro masallaci a kanta,ko abu muka raruma aka raba da ita sai taÆ™i Æ™arba wai ba haƙƙinta bane,da alama ma zuwa take tafaÉ—i mun É—iba,shiyasa itace da gaban goshi,komai mukayi ba'a kallo sai nata" 

 

 

 

"Ehh naga zahiri kam,gashi an muzantamu muna shugabanninta a gabanta,gaba ta ganmu ma dariya zata farayimana...dolene mu É—auki matakin maganinta a masarautar nan,dan irinsu barazana ne ga É—an matsayinnan da Allah yabamu ya É—oramu akansu" 

 

 

 

Wata baiwa ce da suke danga É—aya da Aminatou ta matso inda suke tana É—an sosa kai alamar rashin gaskiya,Sarkin zagi ne ta kulada ita yace. 

 

 

 

"Ke kuma miye kike sussunne kai kaman an kama tsohuwa tana satar itace?" 

 

 

 

"Uhmm Ran sarkin Zagi ya daÉ—e,dama nace nasan wani labari da in kukaji zai taimaka muku kuyi maganin Aminatou muma ko zamu samu mu samu shiga idan batanan" 

 

 

 

"Lallai shiga manya ke asuwa,kedai faÉ—i ko hakan zaisa na fara É—an É—agamiki Æ™afa a wani abun,ko kuma in labarin yanada matuÆ™ar amfani a wajenmu na iya maidaketa wajena" 

 

 

 

Jin abinda Jakadiya ta faÉ—a yasa da sauri kaman an sakawa recorder memory tafara zayyano labarin halinda su Aminatou suke ciki. Shuru sukayi suna saurarenta harta kai aya. 

 

 

 

"Kai Sarkin Zagi wannan fah babbar damace dazan kawar da wannan baiwar,tabbas wannan labarine mai daÉ—i. Dan kuwa indai wannan magana ta kai kunnenta Uban doka dolene a zartar da hukuncin binneta indai har bata tashiba a gobe. Kai bama ga ita kaÉ—ai ba inmunyi wannan aiki babbar shahada fah mukayi na kubutar da garinmu daga iftila'i,dan barin yarinyar nan a kwance dama ga tabin hankali babu motsi kaman gawa na tsawon lokaci babbar matsalace,kuruwarta yawo zata dunyi mana a saman gari tasaka a hanamu ruwa,dama ga damina ta gabato" 

 

 

 

"Kaii kumafah zancenki haƙƙun,wannan ai ba abin boyewa bane,koma waye ba itaba dolene a zartar masa da hukunci kaman yanda akeyiwa kowa,kema menene ma sunanki idan wannan hukunci ya tabbata kinada babbar kyauta. Yanzunnan zanje ga Maga É—aki,shi suna shiri da Uban doka,zai mika wannan lamari kotu a gobe ba sai an jinkirta ba." 

 

 

 

"Shikenan kaga muma mun huta bibiyar da take yiwa yaÆ´anmu kalan ta koya musu dolantaka,Æ´a kaman an toshe mata Æ™ofofin hankali,tana tafe tana haÉ—a hanya da dalalar yawu" 

 

 

 

A bangaren Aminatou kuwa wani daÉ—i ne yajiyarci zuciyarta jin an bata damar taje tayi jinyar Æ´ar ta batareda tazo aiki ba. 

 

 

 

A zaune ta iske kamaluddeen yana shafe jikin Joda da tsumma mai damshi,idanuwansa cikeda damuwa da zullumi,bashida burin dayawuce Æ´ar tasa ta tashi,koda kuwa zatayi masa wannan dariyartata da dukkan Æ™arfinta,yayi kewarta sosai. 

 

 

 

ÆŠaga kai yayi ya kalli Aminatou wacce take tsaye a bakin kofa hannunta riÆ™eda asabarin(labulen da akayishi da zana) dayake rataye a jikin Æ™ofar saboda yakare hasken rana shigowa ciki. 

 

 

 

"Yana ganki kin dawo harkin gama aikin?" 

 

 

 

Kwashe abinda yafaru tayi tafaÉ—awa mijinnata,yana jinta har saida takai Æ™arshen bayaninnata kafin ya numfasa kana ya haÉ—a da cewa. 

 

 

 

"Wani lokacin kina da zuciya Aminatou kuma hakan yakan kaiki ki aikata wani abu da in yajuyomiki baxakiji da daÉ—i ba. Sanin kanki ne mutanennan Æ™iris suke jira su tozartamu saboda damar da Allah yabasu akanka,yanzu badan kin samu uwargijiya mai Mutunci ba mai kike tunanin zai faru?........." 

 

 

 

Tasan abinda yafaÉ—a gaskiya ne,ita kanta tasan bata iya rike fushinta indai akan zagin da akeyiwa Æ´ar tane,ita dai tunda tasamu am bata wannan Æ´ancin babu wanda yakaita farinciki a yanzun,gabaÉ—aya ta nemi zogin bulalar da sarkin zagi ya naÉ—a mata ma ta rasa. Dan kar a yita jan maganar yasa ta É—aukowa kamaluddeen wata hirar daban. 

 

 

 

"Dana shigo na kalli kana kallonta cikin damuwa da alamar kamar mai nazari kuma,shin wani abune yafaru dana tafi?...." 

 

 

 

"Ahah ko É—aya,kawai dai ina tunanin wacce mafita zan samu ne,nace ki barmin komai a hannuna zanji dashi amma alamu yana nuna zan gaza karbar yardar dazaki É—oramini,lokaci dai tafiya yakeyi,ji nake kaman idan dare yashiga to karya waye,idan kuma gari ya waye to kar dare yakuma lullubeshi,duk wasu sa'o'i da daÆ™iÆ™u da suke wucewa ji nake kaman na jawosu su tsaya cakk a taredani. Banajin zuciyata zata iya jure saka Æ´ata da ranta a cikin rami na binneta kawai domin abinda wani ya yarda dashi na jahilci Aminatou. Hakan ba daidai bane kuma son kaine,mutum mutum ne miyasa in fushin kar wani bala'i ya afkune bazai hau kan kowa ba sai bawa.? Akwai É—a sarkin garinnan da yayi jinyar doguwar suma babu wanda ya binneshi har saida ya shekara biyu ya mutu dan kansa,sai mune idan muka samu wannan matsalar za'a kasa haÆ™uri damu a kawar damu. Bamu É—orawa jinyar Joda kowa ba,mun yarda zamuyi abinmu meyasa zasu rabamu da ita koda bamason hakan. Jiya da daddare naje wajen Abokaina nakejin Ashe Babawuro ya faÉ—awa kowa zancen Æ´ata sauranta kwana biyu a duniya,na yarda dashi har hakan yasa yasan halinda muke ciki,bansan miyasa ya zabi yayimin haka ba. Bamuda ishashshen lokaci komai ma zai iya faruwa." 

 

 

 

Zuwa lokacin kuka Aminatou takeyi shabe shabe kaman mai zaman makoki. Matsowa tayi ta dafa mijinnata tareda sako kanta ta kafaÉ—arsa tana kallon jodan itama,wacce take kwance kaman mai bacci,amma ta gagara farkawa yau kwana shida. Tunda ta kalli halin karayar zuciyar da mijinnata yake ciki tasan abin ba Æ™arami bane,yanemi mafita iya iyawarsa ya rasa. 

 

 

 

"Aban Joda to yanxu yazamuyi kenan,shikenan muna gani za'a binneta gobe idan bata tashi ba?" 

 

 

 

Shuru ne ya ratsasu,babu abinda yake tashi sai sheshsheÆ™ar kukanta da kuma ajiyar zuciyarsa. Wasi wasine a zuciyar mai bata amsar,wanda lalume yake da neman shin wacce mafita kwakwalwar tasa zata miÆ™o masa domin yasamu yabata?.....kwatsam wata kalma ta fito daga bakinta wacce ta razana shi har saida hantarsa ta kaÉ—a,bai taba tunanin zata faÉ—i hakan ba. 

 

 

 

"Aban Joda mu tattara kayanmu mu É—auki Æ´ar mu mu gudu daga garinnan a darennan" 

 

 

 

Diff yaji kamar kunnensa sun daina aiki,mai take cewa?  Guduwa?  Ko kaÉ—an shi hakan baizo ransa ba,zatonsa roÆ™o zayyi tayi har a jishi a karba a Æ™yale masa Æ´arsa da ranta. 

 

 

 

"Ya ilahi Aminatou kinsan mai bakinki ya furta kuwa,guduwa fah......idan aka kamamu fah dukka zasu kashemu mu ukun,sannan a rataye gawarmu ana jifanta a tsakiyar gari har rana ta narka namanmu da kitsenmu ya zagwanye yabar kashi"