BURIN ZUCIYA Chapter 2
*BURIN ZUCIYA ❤️* *Arewapen@Ayshadansabo*
©️ Ayshat D'ansabo Lemu 🖊️
*FREE PAGE 2*
Ƙarfe sha ɗaya na dare motarsu ta shigo cikin estate ɗin.Sai da ya faka,Rash ta buɗe murfin motar ta fito,fuskarta cike da nishaɗi,yayin da zuciyarta ke sake cika da matsananciyar ƙaunarsa.
Sai da ya fito ya kulle motar,suka jera da juna. Rabin jikinta na manne a jikinsa,suna tafiya yana yi mata wasa,suna sakin dariya ƙasa-ƙasa. Idan ka ga yadda suke,za ka yi tunanin mata da miji ne sabbin aure masu matuƙar ƙaunar juna.
A tsakiyar falon suka tsaya,yana mai kai hannuwansa bisa ƙugunta,kansa ya ɗora a kafaɗunta yana raɗa mata wasu maganganu na iya shege,ita kuma tana kwasan dariya. Kafin ta juyo gaba ɗaya suka haɗa bakinsu wuri guda.
Sun jima a haka kafin ta zare jikinta tana nuna masa hanyar stairs. Cikin murya mai cike da salo na sace zuciya take faɗin:
"Yauwa ya Hisham,ka je ga Anty Sameera.Na san yanzu ma ta yi bacci.Indai Rash ce,ka san taka ce ana tare ai."Ta ƙarasa maganar tana nufar hanyar ɗakinta.Shi kuma kamar wani soko haka ya bita da kallo kafin ya juya ya nufi matakalan benen yana hawa.
Zuciyarsa fes take,cike da nishaɗi da shaƙuwa,domin Rash ta shayar da shi zumar da ya yi missing a tsayin sati guda da ba shi a ƙasar.Shi ya sa yau da ya dawo ya kasa daurewa har sai da suka kasance da juna.Sosai yarinyar take gamsar da shi tare da rikita shi a shimfiɗa fiye da Sameera.
Koda ya shiga room ɗinsa,kwance ya samu Sameera cikin kayan bacci masu kyau da suka bayyana surarta. Babu komai a jikinta banda rigar baccin.Ya sauke ajiyar zuciya yana nufar toilet.Bai jima ba ya fito.
Singlet kawai da boxer ya saka.Ya nufi bed ɗin tare da jan musu blanket bayan ya sanya ta a kirjinsa.Hancinsa ya kai yana shinshinar wuyanta zuwa ƙirjinta dake fitar da ƙamshinta mai daɗi.
Buɗe idanunta masu cike da bacci ta yi kaɗan.Jin ta a jikinsa ya sa ta sake shigewa cikin jikinsa,domin ta yi missing ɗinsa sosai. Wasanni ya fara yi mata masu rikita ta,tun tana cikin bacci tana jin sa har ta wartsake tana mayar masa da martani.Daga nan suka lula wata duniya ta daban...
⚡⚡⚡⚡⚡
Ƙarfe 10am na safe Surayyah ta fito daga ɗakinta,sanye take cikin skirt da riga na atamfa. Da alamu tayi wanka kenan ta shirya.Fuskarta simple kwalliya ce kawai a kwance a kai.
Babu kowa a cikin falon illa ƙamshin turaren ɗaki da ya cika kowane lungu da saƙo.Da alamu tuni Lami mai aikin shara da mopping ta yi aikinta yadda ya dace.
Kitchen Surayyah ta nufa kai tsaye domin neman abin da za ta ci. Kunun gyaɗa ta zuba a cup,sai ta zuba waina a plate guda biyu da miyan ganye wanda rabinsa naman rago ne da ƙashi.
Nan falo ta dawo ta zauna tana ci.Bata jima ba Mum ta shigo.Kallon Surayyah tayi tana faɗin:
"Auta wannan gayun duk na zuwa wajen koyan girkin ne? Ke da za ki je ki koyi aiki,wannan kwalliya ai yayi yawa Surayyah.Ko dai ƴar kwalliya gare ki ne bamu sani ba,amma ace mutum kullum cikin gayu da fente-fenten fuska."
Ta ƙarasa maganar tana wucewa ɗakinta.Sosai Surayyah take dariya,inda sabo ta riga ta saba da ƙorafin Mum ɗin akan yawan kwalliyarta.
Wanda ita yau sam ba ta ga wani kwalliya da tayi ba illa jan baki da powder,sai girarta da tayi masa caving.Don dai kawai ita ɗin mai kyau ce,shi ya sa ko tayi kwalliya kaɗan sai aga ta yi yawa.
Plate ɗin ta aje bayan ta kammala,ta koma ɗakinta domin ɗauko mayafi da jaka,don ƙarfe 11am har ya kusa,kuma class ɗin 11am suke farawa.
Takalmi da jaka na ALDO ta saka,waɗanda suke cikin kayan da Uncle B ke mata tsarabarsu idan zai zo hutu daga Turkey. A maimakon ta saka gyale kamar yadda ta so,sai kawai ta zari hijab ɗaya da ya dace da shigar jikinta ta saka.
Sosai hijab ɗin ya yi mata kyau.Tana son yafa veil,amma yawan kallon da take cin karo da shi na ƴan maza ne ke hana ta sakawa.Shi ya sa saka hijab ya zame mata jiki.
Idan ka ganta da gyale,sai a unguwar da za a kai ta a mota,ko za ta biki ko wani waje da ba za ta iya sanya hijab ba.
Ɗakin Mum ɗin ta nufa domin yi mata sallama sannan ta dawo.Ta fito tana takunta a nutse. Sosai Surayyah take da nutsuwa da kamun kai dai-dai gwargwado,domin Iyayenta sun ba su tarbiyyar Musulunci,ba su bar su kara zube ba.
Bata da rawar kai irin na ƴan matan zamani,musamman waɗanda suka gama jami'a suna ganin sun waye,idanunsu sun gama buɗewa.
Keke Napep ta tara bayan ta ƙaraso bakin titi.Ta shiga suka wuce kai tsaye inda take catering class.Ya kai ta ya sauke ta,ta biya shi kuɗinsa.
Ta shiga wajen tana addu'ar Allah ya sa yau su tashi da wuri,domin tana son zuwa wajen ƙawarta Mardiyya.
Ƙarfe uku suka tashi daga class ɗin saboda ba wani abu mai wahala suka yi ba.Cake ne,sai Savory donut da suka yi.
Ta yi sallama da Anty Hauwa mai koyar da su sannan ta fito.Tafiya take a hankali cikin takunta mai ɗaukar hankali.Sam ba a samun abin hawa a layin domin can cikin Gaskiya ne wajen.Koda ta fito bakin titi,cigaba da takawa tayi har ta fita ainihin bakin hanya. Sannan ta ja ta tsaya. Bata jima ba ta samu abin hawa,ta sanar da shi cewa gyallesu zai kai ta,suka tsadance ta hau.
Suna dab da isa gidan su Mardiyya ta kira ta a waya ta sanar mata gata nan zuwa.Hakan yasa tana shiga gidan,muryarta kawai Mardiyya ta ji ta fito a guje ta rungumeta tana faɗin:
"Oyoyo Bestie! Zuwan la'asar aka yi min,maimakon ki zo ki yini."
"Ok,baki gode ba kenan? To sake ni in je in gaida Mama sai na wuce gida abina."
Cewar Surayyah tana ƙwace jikinta.Mardiyya ta saki dariya tana faɗin:
"Ke fa banza ce Surry,daga wasa,mu je Mama Ta shiga maƙota ma bata nan."
Ɗakin Mardiyya suka nufa kai tsaye. Surayyah ta zauna cikin ɗaya daga cikin kujerun dake ɗakin tana faɗin:
"Wash Allah na,Mardy na gaji daga Almumtaz class nake wallahi.Wannan ɗan tafiyar da na yi zuwa bakin titi ba ki ji ƙafafuna ba."Mardiyya ta saki dariya tana faɗin:
"Ke dai wallahi raki ce dake Surry.Ni kam sam bana ganin nisan wannan tafiyar.Ƙawata,ni gani nake kullum sai ƙara wani fresh da kyau kike yi.Miye sirrin ne? Ko duk cikin kulawar Aliyu ko Nas ne?" Mardiyyah
Ta ƙarasa maganar tana kwashewa da dariya,wanda hakan ya ɓata wa Surayyah rai. Ta kai mata duka tana faɗin:
"Wallahi Mardiyya ki kiyaye ni.Uban Aliyu da Nas ne banza da baki da magana sai na ɓata rai.Wallahi Mardy na tsani ana min zancensu su duka.Aliyu ko jiya shi ya maida ni gida daga gidan Anty Safiya.Banza,sai wani zuba min magana yake wai mu dawo tamkar da, shi Wallahi ba zai iya daina so na ba."
Ta ƙarasa maganar da jan tsaki,fuskarta na bayyana jin haushinta sosai.
Hakan yasa Mardiyya zama serious tana duban Surry take faɗin:
"Surayyah ni kaina sha'anin samarin yanzu yana kullar min da kai matuƙa.Ba magidanta ba,ba kuma samari ba.Duk wanda ya zo akwai Burin Zuciyarsa a kanka.Mafi yawansu ma Burin Zuciyarsu ɗaya ne.Da zarar kin kasa ba su abin da suke so sai su janye jikinsu."Ajiyar zuciya Surayyah tayi tana mai lumshe idanunta,ta buɗe su akan Mardiyya kafin ta furta:
"Hmm! Ke dai Mardiyya ki bari kawai.Ni ina sha,ni kaɗai ce irin hakan yake faruwa da ni? Sai da na tattauna da ƴan mata da yawa na fuskanci soyayyar wannan zamanin ce ta lalace.Soyayyar shan minti ta zama ruwan dare wajen maza da mata.Abin na damuna Mardy,har ya kai zuciyata ta fara rinjayata da in bi sahu domin na gaji.Na gaji da korar samari ana cewa na ƙi fitar da mijin aure.Tun Mum da Baba suna ɗauke kai har sun fara min magana.Na gama degree amma na kasa fitar da mijin aure."Ta kai ƙarshen maganar tana sauke idanunta akan Mardy,wacce itama idanunta ke kan Surry. Maganganun Surry sun daki zuciyarta,domin abu ɗaya ne yake damun zuciyarsu.
Burin Zuciyarsu shi ne ba za su taɓa soyayyar shan minti ba.
Dafa kafaɗunta Mardiyya tayi tana faɗin:
"Surry kada ki karaya,har yanzu akwai sauran kamammamun maza.Ki sa a ranki lokaci ne bai zo ba,da Allah zai kawo mana daidai da mu.Kada ki bari son ki yi aure ko ɓacin ran sakarkarun maza yasa ki ba su jikinki don su amince su aure ki Surry.Ke na manta ma ban tambayeki ya kukai da Alhaji Sani ba?"Murmushin takaici Surry tayi tana kai hannu ta ɗauki cup ɗin da Mardy ta cika mata da lemun pineapple.Ta kai baki ta sha,sai da ta kusa shanye shi kafin ta aje cup ɗin tana watsa wa Mardy manyan idanunta dake rikita ƴan maza tana faɗin:
"Mardy kenan,shi ma ai duk tafiyar su guda.Ke ya ma fi su Aliyu fito min da maitarsa a fili.Domin shi har hotel ya yi min tayin wai mu je mu sha iska.Tun daga ranar na yi blocking ɗinsa bayan na aika masa da zagi."Ta ƙarasa maganar tana jan tsaki,yayin da Mardiyya ta saki dariyar takaici.Cike da zolaya take faɗin:
"Ke fa Surry kin san miye ne? Wannan ƙirjin naki da ƙugun ke saka su ruɗewa har su kasa danne maitarsu.Suna zaton duk budurwar da aka ce ta gama jami'a, ƴar hannu ce ta riga ta saba da soyayyar taɓe-taɓe da tsotse-tsotse."Mardiyya ta ƙarasa maganar tana dariya,yayin da Surry ta ja tsaki tana zabga mata harara.Kafin tayi magana wayarta ta fara ringing.
Ta ciro wayar,ganin Uncle B ne yasa ta shagwaɓe murya,wanda hakan ya sa Mardiyya tsura mata ido tana kallon yadda Surayyah ke amsa wayansa tamkar wani saurayinta da take mutuwar so.
Sun jima suna waya kafin su yanke.Surry ta aje wayar tana kallon Mardiyya take faɗin:
"Ya Malama wannan kallon fa? Uncle B jibi yana bisa hanya fa ƙawata.Nayi missing ɗinsa,na ƙosa ya dawo,ko ma dinga fita chilling.Ina ma zan sami saurayin da zai dinga shagwaɓani kamarsa Mardy.Ina ma kaina sha'awar auren wayayyen namiji mara girman kai kamar Uncle B.Burin Zuciyata bai wuce in samu namijin da zamu more ƙuruciyarmu ta hanyar nuna wa juna soyayya ta gaskiya ba."
Mardy tayi murmushi tana jinjina ƙauna da shaƙuwar dake tsakanin Surry da Uncle ɗinta.Abin har ya kusa yin yawa,amma sai ta kawar da abin da zuciyarta ke son jefa mata.
Ta dubi Surry tana faɗin:
"To Allah ya ba mu baki ɗaya.Ka auri mai son ka ai babban nasara ce Surry.Babu macen da za ta ce bata so a nuna mata kulawa da soyayya,sai dai idan bata samu ba."
Daga haka suka sauya salon hirar nasu har zuwa lokacin da Maman su Mardy ta shigo gidan.Bayan sun gaisa ne,Surry tayi shirin tafiya.
Suka fito tare da Mardy da za ta raka ta bakin titi ta samu abin hawa.Ba su yi tsayuwar minti biyar ba ta samu abin hawa,suka yi sallama ta tafi,ita kuma Mardy ta juya domin komawa gida.
Tunda keke napep ɗin da ya ɗauko ta ya shigo layinsu,ta hango motar Nas ce tsaye a ƙofar gidan su.Hakan yasa ranta ya ɓaci,ta haɗe girar sama da ƙasa.
Ta yi sallama da mai napep ɗin,ta fara takawa domin shigewa gida.Sam bata ko kalli motar ba,bare ta nuna ta san wanda yake cikinta.
Ganin da gaske take shigewa za ta yi,yasa Nas saurin fitowa ya nufeta.Har ta ɗaura hannu akan ƙofar gate ɗin tana shirin turawa ta shiga,shi ma ya kai hannunsa tare da dafe nata.
Hakan yasa ta saurin janye hannunta tana ja baya,ganin jikinsu sun ɗan goga juna,wanda shi sam bai damu ba.
Wani irin kallo ta watsa masa tana faɗin:
"Nas, miye hakan? Ina sha tuni mun raba jiha ni da kai,me kuma ya kawo ka ƙofar gidanmu a wannan yammacin?"
Ta kai ƙarshen maganar tana tsare shi da idanunta dake rikita nutsuwarsa.
Idanunsa fes a kanta,ya saki murmushi yana faɗin:
"Please baby ki aje wannan tambayar a gefe.Sanin kanki ne bazan iya rabuwa dake ba.Ina tsananin son ki Surry.Ke ce kike ɗaukar zafi akan abin da bai taka kara ya karya ba.Na rasa yaushe zaki waye baby,tamkar ba wacce tayi jami'a ba haka kike nunawa.Yanzu dai mu ƙarisa mota mu gaisa kinji sweetheart."
Nas ya ƙarasa maganar yana kashe mata ido.
Ƙarfin hali kawai Surry take yi,amma ta ji wannan kallon na Nas har cikin zuciyarta.Ta sani tana son Nas sosai,matsalarsa kawai abin da yake so a gareta ne ba za ta taɓa ba shi ba.Ba za ta taɓa amince masa ya cika Burin Zuciyarsa a kanta ba.Amma Nas yana cikin jerin mazan da suka amsa sunansu,suka kuma haɗa duk abin da ɗiya mace ke so.
Maimakon ta nuna masa karaya,sai ma ta sake tsuke fuska tana watsa masa harara kafin ta furta:
"Kaga Nas,babu inda zan je daga nan.Allah ya yi min tsari da sake shiga motarka.Don haka faɗi abin da ya kawo ka,ko yau ma bakin ka zo na baka ka tsotsa ko kirjin?Nas na sha gaya maka Burin Zuciyarka ba zai taɓa cika akan Surayyah ba.Don haka ka fita cikin rayuwata.Na tsaneka Nas,ba kuma zan taɓa canzawa ba.Ina nan a yadda ka sanni."Tana gama faɗin hakan ta juya da gudu-gudu ta shige gida,tare da bugo ƙofar gate ɗin har ya bada ƙara.Nas da ya bita da ido ne ya sauke numfashi yana cije lips ɗinsa da ƙarfi.Wutar soyayyarta na sake ruruwa a cikin zuciyarsa.
Haka ya nufi mota ya tasheta a guje,zuciyarsa na cike da takaicin kafiya da rashin fahimta irin na Surry, da har yau ta kasa ba shi damar su yi irin soyayyar da shi yake da burin yi.
⚡⚡⚡⚡⚡
"Ya Abdallah, barka da hutawa ashe kana nan. Na zagaya cikin gidan nan gaba ɗaya ban ganka ba.Tunda na iso Hajiya ta sanar min kana gida yau baka fita ba.Na je part ɗinka a rufe, sai yanzu zuciyata ta bani cewa yanzu haka kana garden kana hutawa,ilai kuwa."Matashiyar budurwar ta ƙarasa maganar tana zama bisa kujerar sakan da ta ƙawata wajen da Abdallah ke zaune.Ya miƙe ƙafafunsa akan dogon table dake tsakiyar kujerun.Wayoyinsa da car key ɗinsa ne zube bisa table ɗin,sai gwangwanin lemun Coke dake aje a gefe guda.Hannunsa na riƙe da wani magazine yana dubawa.Idanunsa ya ɗago ya sauke akan budurwar wacce take sanye cikin shigar riga da wando na gezner.
Rigar half buba ce,ta sha adon ɗinki na gaske,sai wandon wanda ya tsuke daga sama daga ƙasa ya yi faɗi.
Ɗinki ne da gogaggun ƴan matan zamani kan keta suturu masu tsada su yi.
Fara ce tas,sai dai bata da wani kyawun fuska mai ɗaukar hankali,amma tana da diri dai-dai gwargwado.
Kallo ɗaya za ka yi mata ka san gogaggiyar ƴar gayu ce,wacce hutu da jin daɗi suka taka rawansu wajen sake fito da ita.
Maida idanunsa yayi kan magazine ɗin dake hannunsa,ba tare da ya ce mata ko "ci kanki" ba.
Hakan ya ƙular da ita,ta sake cire murya tana faɗin:
"Yanzu Ya Abdallah,miye laifi na don nazo inda kake da har zan yi magana kai banza dani?"
Ta ƙarasa maganar muryarta na ɗan rawa kaɗan.
Wannan karon Abdallah ya aje magazine ɗin hannunsa,yana mai ɗago fuskarsa gaba ɗaya tare da kafe ta da manyan idanunsa da suke sake narkar da zuciyarta a soyayyarsa.
A hankali bakinsa ya motsa yana faɗin...
"Ai ban san laifin da kika yi ba da har za ki zo ki tambaye ni."
Ya faɗa cikin sanyin murya,idanunsa har yanzu suna kanta.
Budurwar ta ɗan yi shiru na wani lokaci tana kallonsa.Ta saba da halinsa,amma hakan bai hana ta jin haushin rashin kula da yake nuna mata ba.
"Ya Abdallah,ka san fa tun da na zo ban samu damar ganin ka ba.Shi ya sa na zo nan wajenka."
Ta ƙarasa maganar cikin wata murya mai nuna kulawa.
Abdallah ya sauke numfashi kaɗan,ya jingina bayansa da kujerar yana kallon gabansa."To kin ganni yanzu.Me kuma kike so?"Maganar tasa ta fito cikin nutsuwa,amma babu wani yanayi na fara'a a tare da ita.
Budurwar ta sake kallonsa tana murmushi kaɗan.
"Ni dai kawai nazo ne in zauna tare da kai."
Ta faɗa tana gyara zamanta.
Abdallah bai ce komai ba,ya koma kallon magazine ɗin dake hannunsa kamar yadda yake a baya.
Hakan ya sake ƙular da ita,amma ta daure ta yi shiru.
A gefe guda kuma,cikin zuciyarsa akwai abubuwa da yawa da yake tunani.Bai cika son yawan surutu ba,kuma bai cika son mutane su karanta abin da ke zuciyarsa ba.
⚡⚡⚡⚡⚡
A can gidan su Surayyah kuwa,tana shiga ɗaki ta zauna tana tunanin abubuwan da suka faru a wannan ranar.
Maganar Nas,maganganun Mardiyya,da kuma matsalar da take ganin ta shafi soyayyar zamani duk suna yawo a cikin kanta.
Ta sauke ajiyar zuciya tana kallon wayarta.
"Allah ka shiryar da mu,ka kawo mana abin da yake alheri."
Ta furta a hankali.
Daga nan ta aje wayar a gefe tana shirin sauya ka.......✍🏻