Chapter twenty three
by @aysharano22
Janyewa yayi daga rikon da tayi mashi yace “Ju meyasa zakiyimin haka?, meysa zakiyi punishing dina kan laifin da…..”.
Bata bari ya karasa ba ta rufe masa baki tana hawaye don tausayinshi, tayi Amanna Ayaan na sonta so na haqiqa amma kuma qaddara bai zama lallai ta bari su kasance tareba duba da matsalolin da suke samu one after the other tunma kafin su fara dating…ga kuma 4 years age difference dake tsakaninsu tasan bai zama lallai ma a barta ta auri yaronda ta bama good shekara hudu ba plus he’s just so young, just 20 years old ita kuma 24 so ta yaya zaa bari suyi aure har su rayu tare rayuwa na har abada?.
Tasan ita ko yau ta samu miji zatayi aure amma Ayaan nan da shekara biyar ma bai zama lallai a barshi yayi aure ba sbd yayi qanqanta…bude kofa akayi Dr ta shigo tana ce mata if she’s ready tazo suje a fara nan kuma hankalin Ayaan ya dawo jikinshi ya tuna aika aikan da take shirin aikata masa don haka ya dago sake dubanta da sauri ya kama hannunta yana dubanta da idanuwanshi da sukayi jajir cikeda tashin hankali yace “you can’t do that Ju, you will not do this to me”…zame hannunta tayi daga cikin nashi tana kauda kanta daga gareshi tace”am sorry, but i have no choice”…sakin hannun nata yayi da sauri ya ya canza yanayin fuskarshi still kuma yana cigaba da dubanta yace”dan girman Allah kiji tausayina Juwairiyya karki zubda cikin nan, remeber banida wani blood relation a rayuwata this is the only blood i have, karki rabani dashi dan Allah”…da kallon mamaki da takaici take binshi tace”really Ayaan…wato har wani murna kake zaka samu blood kmr bakasan ta hanyar da aka samu blood din ba?..well idan ka manta bari in tuna maka, blood din da kake so a bari ba dan sunnah bane shege ne, mara uba ne snn…..“toshe mata baki yayi da sauri don bazai iya cigaba da sauraran wnn munanan maganganu akan jininshi ba even though its true yace mata”na sani ba mantawa nayi ba, amma meye laifin yaron a ciki?…duk abinda ya faru tsakaninmu ba laifin shi ko ita bane don haka bai kamata sin dinmu ya shafeshi ba…bai kamata ki aikata kisan kai ba sbd laifinshi yana iya zarce laifin tarayya da mukai ba tareda aure ba”…murmushin takaici ta saki ganin yanda ya dage kan bazata zubar da ciki ba wato shi baya gudun abun kunya tace”let me tell you something Ayaan idan kai baka gudun abun kunya ni ina gudunshi…idan kai baka tunanin yanda barin wnn cikin zaiyi affecting parents dinka ni ina tunanin haka sbd babana politician ne, labarin cewa ’yarsa tayi cikin shege ta haihu zai iya kawo baban nakasu a siyasarshi, snn nima ban shirya barin abin kunya da zaa yita min gori har ‘ya’ya da jikoki na ba don haka bazan bar wnn cikin a jikina mutane suna ganin ina gilmawa dashi bayan sunsan ba aurene dani ba, ban shirya barma kaina da iyayena wnn abun kunyar ba so am taking it out”.
Ganin lallami fa ba lallai yayi tasiri a kanta ba ya mike tsaye yana dubanta wnn karon fuska a matukar daure kmr ba shine ya gama mata magiya yanzun ba yace”ni kuma a shirye nake da inyi rigima da duk wani mai hannu cikin yunkurin zubar min da ciki, ciki harda ke da asibitin nan dama duk wanda ke goyon bayanki”..da mamaki kwarai ta tsaya kallonshi don zata iya rantsuwa tunda suke bata taba ganinshi a haka ba…daure nata fuskar tayi itama kafin tace”ni kuma banga wanda ya isa ya hanani ba tunda ciki a jikina yake ni nake da hakkin da zan barshi idan inaso ko kuma in zubar dashi idan banaso”…kai kawai ya gyada yana kallonta kafin ya juya ya fita don tuni Dr da tazo yi mata mgn ta tafi.
Kai tsaye ya nufi inda suke, ko me yace mata oho sudai sunga ta biyoshi har office din tana bashi hakuri cikin Hindi tana cewa basu san matarshi bace ita…cikeda takaici Ju ke kallonshi ganin karyar da yaje ya shirga musu, Lucas da Nusy dai ba wanda yace uffan tun dazu sun zama yan kallo a tsakaninsu.
Haka Ayaan ya damki hannunta ya shiga janta suka fita daga office din…duk yanda Ju keta kokarin kwace hannun kasawa tayi don ba karfinsu daya ba…daga karshe ma daukanta cak yayi da yaga tana bata mashi lokaci plus wnn turjiyan da take sai yake ganin kmr cikin na iya zubewa tunda dama tasha maganin zubar da ciki.
A takaice sunfi sati suna rigima akan zubda cikin, duk wani kokari na Ju ta kasa gane yanda Ayaan yakebi yake lalatashi, gashi lokaci sai kure mata yake bataso cikin ya girma sbd wahalar fita zaiyi don haka ya zama dole tasan abinyi da wuri don da gske har yanzu bataji zata iya barin cikin nan ba.
Ana haka kwatsam saiga mamanta da sisters dinta sun kawo mata ziyara, nan fa hankalinta ya sake tashi don bata taba tsammanin zuwansu ba, ita yanzu ya zatayi idan mamanta ta fahimci tanada ciki batasan tuni ta gane ba. Koda ta tsareta da tambaya kuka ta fashe mata dashi ta rasa karyar da zata shirga mata kawai sai tace ita batada wani ciki…haka mamanta tasata a gaba sukaje asibiti akayi scanning kuma ya tabbatar mata da cewa tana daukeda ciki har na tsahon sati bakwai.
Hankalin mahaifiyarta ba karamin tashi yayi ba taji tayi dana sanin kawota kasar waje karatu aikuwa ba shiri ta kira mahaifinta dake Germany ta fada mashi shima kafin kace me sai gashi a India don idan mgnr cikin nan ya fasu qimarshi sai tafi ta kowa tabuwa matayinshi na dan siyasa. Haka dai suka sanyata a gaba suka matseta saita fadi wanda ya mata ciki ita kuma sbd ta wanke kanta tace musu ai wani ne yayi raping dinta bayan ya bata kwaya tasha…nan fa ran babanta ya baci yace koma waye yayima ’yarshi haka sai yaga wanda ya tsaya masa.
Bawan Allah Ayaan na gida yasa akaje har gidan aka kinkimeshi akayi police station dashi, saida ya kwana uku suna gana masa azaba duk a sunan yayi raping dinta don su rape ba karamin case bane a can basu san cewa sam mgnr ba haka yake ba and nobody is willing to listen to his own side of the story…shikam shock ma kadai ya isheshi don bai taba zaton Ju zata iya yi masa irin wnn sharrin ba…ita kuma tayi haka ne don ta fitar da kanta sai kuma don haushin yanda ya hanata zubda cikin har iyayenta suka san dashi wanda daya bari ta zubar da kimarta bata ragu a idanunsu ba so she has no choice than to lie ko don ta steratar da kanta da kuma kimar mahaifinta.
Lucas bawan Allah shi kadai ne ya shiga tashin hankali mara misaltuwa haka yayita faman sintiri tsakanin gidansu da Police station shi kanshi bai taba zaton Ju can do this to Ayaan ba.
Bayan an fito dashi kuma baban Ju ya nemi number Abban su Ayaan din da kanshi ya kirashi ya sanar dashi cewa ga danshi nan yayi raping ’yarshi a india, aikam shima ba karamin tashin hankali ya shigaba hakama Ummanshi da taji kmr tayi tsuntsu ta biyoshi india…duk wnn abun da suka masa bai ishesu ba saida suka cigaba da yunkurin zubar da cikin, nan kuma Allah ya nuna musu ikonsa don sau biyu tana shan magani cikin yaki fita sai uwar wahala da takesha dole haka suka hakura don likita ya tabbatar musu da cewa idan ta sake yunkurin zubdashi tana iya rasa rayuwarta in the process don haka ba don sunaso ba suka hakura da zubarwa tareda sharadin tana haihuwa zai karbi abinshi don ’yarsu baza tayi rainon shege ba, yace ba komai idan an haifa din a bashi shi zai rike abinshi.
Hatta scholarship dinshi saida mutumin nan ya shiga ya fita yasa akayi terminating, ya zamana bashida mai sponsoring karatunshi gashi har sun kusa gama level 2 dole yayi dropping out ya shiga ’yan buge buge yana neman kudi don makudan kudi suka yanke masa wai ya dinga biyanta kudin rainon cikin da take masa…bawan Allah Ayaan bai taba sanin yanada juriya da karfin hali har haka ba saida wnn qaddara ta afka mashi.
Ga abbanshi ya daina daukan waya idan ya kirashi Umma ma ba koda yaushe take dauka ba balle kuma sisters dinshi, abun duniya duk ya taru ya mishi yawa Lucas ne ya zama his only support a wnn lokacin…daidai da lokaci daya bai taba gajiya da taimakonshi ba walau da shawarwari ne koda kudi koda rarrashi da karfafa masa guiwa da mgn mai dadi, shi kadai ya zama gatanshi lokacinda rayuwa tayi masa zafi a duk fadin duniya.