SIRRIN ZUCIYA

Chapter twenty four

by @aysharano22

Juwairiyya kuwa zuwa yanzu dana sani take sosai na kazafin da tayi mishi saidai masu iya mgn sunce tsalle daya shike bata gari don haka itama ta riga ta bata al’amari da wnn mgn guda daya data fadama iyayenta wanda ba abinda yafi damunta kmr dropping out of school da akasa yayi sbd rashin mai daukar nauyin karatunshi, gara ita deferring shekarar gaba daya akayi mata tasan kuma tana haihuwa zata koma ta karasa abunta amma shifa shknn yayi asarar shekara biyun da yayi a makarantar kenan.


Haka Ayaan yasha wahala sosai da karancin shekarunshi duk ya fige ya lalace wnn kyan duk babu shi, duk wata bai taba fashin bada kudin rainon ciki da sukace saiya bada ba don aiki tukuru yake fita yayi ko dako ya samu yi yake indai zai samu dan wani abu a ciki, danma Lee na dan taimaka mishi dukda shima ba wani cikakken gata ne dashi ba.


Ciki na shiga wata tara babanta yace ayi cs a cire babyn don bazai iya jira har sai haihuwa yazo da kanshi ba, kudin cs din kuma sukace shi zai biya, lokacin ya shiga shekara ta 21 a duniya, hankalinshi ko ya tashi sosai don kudin nada yawa kuma baisan inda zaije ya samosu ba kawai saiji yayi Lucas yace mashi ai ya rigada ya biya, yayi mamaki sosai daya tambayeshi sai yace mishi filin gadonshi dake Ibadan yasa aka saida aka turo masa da kudin shine yaje ya biya kudin asibitin, abinda yayi saura kuma ya siya dan kayan baby wanda zasu fara amfani dashi kafin kuma Allah ya kawo wata hanyar…kuka sosai Ayaan ya fashe dashi ya durkusa har kasa yana masa godiya Lee shima ya fashe da kukan yana ce masa ya daukeshi ne tamkar dan uwan da suka fito ciki daya don haka kar ya sake mishi godiya duk abinda yayi mishi…Kuma har zuwa wnn lokacin ba mgn yake samun yi da Umma da Abba ba.


Ana gobe zaayi cs din saiga kiran Umma ya shigo wayarshi lokacin ma yana kwance ba lfy ko aikin ma kwananshi biyu bai fita ba…Lucas ne ya mika masa wayar don yana zaune kusa dashi ne bayan ya dawo daga makaranta ya samu ko abincin daya ajiye masa tun safe baici ba…yana ganin Umma ke kira yayi picking cikeda zumudi ya kara wayar a kunnenshi nan da nan saiga hawaye ya fara kuka yana cewa”Umma, umma kiyi hakuri, kiyi hakuri umma dan Allah ki yafemin nasan na zubar muku da mutunci amma wlh umma abin ba yanda aka fada muku bane”…maimakon yaji muryar Umman sai muryan Abba yaji a kausashe yace”tambaya daya zanyi maka Ayaan kuma inaso ka fadamin gsky”…da sauri yace”to Abba”…Abba yace”shin da gaske kayima yarinyar mutane ciki ko bakayi ba?”…hadiye yawu Ayaan yayi ya kasa cewa uffan…a dan fusace Abban yace”ba mgn nakeyi maka bane?”…da kyar ya iya bude bakinsa yace”da gaske ne abba amma wlh….“bai karasa ba Abban ya katseshi da fadin”babu wani karin bayanin da zakayimin abinda na tambayeka knn kuma ka bani amsa don haka yanzu inaso ka bude kunnenka da kyau ka saurari abinda zan fada maka”…yana share hawayen da sukaki tsaiwa kan fuskanshi yace”toh”…Abba yace”nasan dama kasan ni ba mahaifinka bane kawai na duba Allah ne na kuma duba Madina shiyasa na rikeka kuma Allah shaida ban taba banbantaka da yaran da na haifa a cikina ba amma yanzu da halinka ya fito fili bazan iya cigaba da rayuwa dakai ba Ayaan sbd yara mata gareni, inhar zaka iya raping mace to suma nawa ‘ya’yan zaka iya raping dinsu watarana, sbd haka daga yau na yanke duk wata alaqa da kasan kanada ita dani da kuma iyalaina…idan nace iyalaina ina nufin har Hajia Madina matata don kafi kowa sanin ita ba mahaifiyarka bace cikinka kawai aka sa mata ta haifeka amma kai ba jininta bane”…numfashin Ayaan har sama sama yaji ya farayi sbd tashin hankali, wnn wace irin rayuwa ce?…wane irin mummunan wasa ne haka qaddara takeyi da rayuwarsa?…jin shirun da yayi Abba yacigaba da cewa”don haka banason ko a waya inji ka kira daya daga cikin ahalina don wlh zanyi mummunan saba maka kuma zan dauki matakinda bazaima kowa dadi ba…idan ka baro india dama kasan inda zaka dosa ba gidana ba don na samu labarin an koreka daga makarantar, Allah ya bani ladan rikeka da nayi da gsky ba tareda cutarwa ba”…har snn numfashinshi bai gama dawowa daidai ba zuciyarshi har wani suya take gashi ko digon hawaye ya kasa zubarwa tsabar shock dinda ya shiga…muryar Umma ya jiyo a background tana kuka tana cewa dan Allah ya bata ko sau daya ne tayi mgn dashi ta karshe baiji me yace mata ba dai har zai kashe wayar sai kuma yaji muryar Umman nashi da kuka sosai tana cewa”Ayaan, Ayaan am so sorry, duk nice silar jefaka cikin wnn halin kayi hakuri na raboka da iyayenka…kayi hakuri na kasa zama uwa ta gari a gareka amma wlh Ayaan har cikin zuciyata nake sonka ban taba daukanka a matsayin danda ba nawa ba, kayi hakuri”…kasa cigaba da mgn tayi sbd kukanda yaci karfinta.


Sai a snn Ayaan da yayi poster a zaune kmr mutum mutumi ya dawo hayyacinshi yana canza wayar zuwa dayan kunnenshi har snn kuma ba hawaye a idanunshi sai bala’in zafin da yakeji cikin zuciyarshi yace”Umma stop crying pls, ki daina kuka ba ke ya kamata ki bani hakuri ba nine ya kamata in baki, niya kamata in baki hakuri for zubar muku da mutunci da nayi amma wlh duk abinda aka fada muku ba gsky bane wlh Umma banyi raping dinta ba”…bai rufe baki ba Umma tace”i know, nasan tarbiyyar dana baka Ayaan kuma na yadda da kyawawan dabi’unka dari bisa dari, nasan bazaka aikata abinda suka fada ba kuma inaso kasan cewa ko kowa na duniya zai juya maka baya kana da ni Ayaan, a kullum ina nan matsayin Ummanka karka taba cewa zaka dauki mgnr da abbanku ya fada bacin rai ne kawai”…tana rufe baki kafin ma Ayaan din yayi mgn yajiyo muryar abba a background yana cewa”tunda ni ban isa inyi hukunci kibi ba to ina mai tabbatar maki da cewa wlh kinji na rantse ko a waya naga yaron nan ya kiraki ko ke kin kirashi saina datse duk igiyar auren dake tsakanina dake, aiba mahaukaci bane ni da zan dauko rapist in kawoshi cikin ‘ya’yana da suke mata, wato a bawa kura ajiyar nama kou?..to billahillzhi bazai yiwu ba don a shirye nake in rabu dake matukar bazaki fita harkar yaron nan ba”.


Lumshe ido Ayaan daya gama jinshi tsaf yayi yanajin yanda Umma ta sake rushewa da kuka tana cewa”alhaji kaji tausayin yaron nan mana, bashi fa da kowa sai mu a duniya baisan kowaba a matsayin iyayenshi sai mu, ya kakeso yayi da rayuwarsa idan muka juya masa baya, yanzu da kai ka haifeshi zakace kar ya sake dawo maka gida ne, haba wnn wane irin rashin adalci ne?”…muryar Abban yaji ya fara bala’i sai kuma kitt yaji an kashe wayar…ya ajiye tashi a hankali yana dafe kanshi da yakeji kmr rabuwa zaiyi gida biyu tsabar ciwon da yake ga zuciyarshi da bata daina bugawa da karfi tana suya ba.


Lucas dake kuka wiwi don ya saurari kaf tattaunawar tasu ya matso da sauri ganin ba cikin hayyacinshi yake ba ya rikoshi a jikinshi da karfi yana cewa”Ayaan, Ayaan”…hannu Ayaan ya daga ya dora saitin zuciyarshi kafin ya samu ya bude bakinshi da kyar yace”mu..tu..wa..zan..yi”…da karfi Lee ya rungumeshi yana cewa”no bazaka mutu ka barni ba plss hang in there, just hang in there let me call an ambulance”…kafin ma ya dauko wayar daga aljihunshi ya sume masa a jiki nan ya fasa wani uban ihu yana cewa”Nooooo”.


House mates dinsu da sukaji ihun ne suka shigo dakin da sauri kowa yana tambayar abinda ke faruwa…kuka Lee yakeyi sosai yace musu”ku taimakamin mu kaishi asibiti he’s not breathing”…wani daga cikinsu ne ya kira amblance cikin few minutes ya iso har snn kuma Ayaan na sume kmr gawa a jikinshi…su suka taimaka mashi suka daukeshi suka saka cikin amblance shima Lee ya shiga sukayi asibiti wanda tun kafin su isa dama suka fara bashi first aid anan cikin ambulance din Lee nata kuka kmr numfashinshi zai fita…tausayin dan uwanshi yakeji sosai, cikin ranshi sai tsinewa Juwairiyya da iyayenta yake sbd duk su sukayi silar jefashi cikin wnn halin.


Suna isa asibiti akayi emergency room dashi yayinda aka bar Lucas a waje yanata zarya ko zama ya kasa yi sbd tashin hankali, bini bini zakaga yakai hannu yana goge tears da sukaqi dena sukuwa kan fuskarshi…tausayi sosai yake bashi yasan yanda bashida wasu iyaye a duniyar nan sai su Umma, baisan kowa a matsayin danginshi ba sai su yanzu gashi suma sun gujeshi kan laifin da basu ma tsaya sunji dalilin faruwar shi ba…yakai minti ashirin yana zirga zirga a bakin ward din ya kasa zaune ya kasa tsaye kawai sai addua yake Allah ya tashi kafadunshi kar ya mutu bai samu koda ganin babyn da ya sadaukar da komai nashi don yaga yazo dunia ba.


Bayan wasu mintuna likita dake cikin dakin ya fito nan kuma yace mishi ya kwantar da hankali don ya fita daga hadari yanzu amma ya zama dole ya ragema kanshi damuwa don yana gab da samun heart attack wanda da ace sunyi delaying kawoshi asibiti koda na mintuna kadan ne to da yanxu ba wnn mgnr ake ba don yana iya mutuwa.


Lee yaji dadi da wnn bayani sosai snn ya shige cikin dakin ya sameshi kwance yana bacci ansa mishi Oxygen ga kuma wasu machines da baima san na meye ba suma duk an makalasu a kirjinshi sai fitar da wani sauti din din din sukeyi. A hankali ya karasa kan kujera ya zauna yana kallon yanda ya koma kmr ba Ayaan dinshi ba kawai saiya rushe da kuka yanajin kmr yaje ya hallaka Juwairiyya for doing this to the person that loves her with all of his heart.


Mkewa yayi kmr ana tsunkurarshi ya fita daga dakin yana share hawaye, kai tsaye ya nufi ward da yasan zai sameta don anyi admitting nata cikin asibitin tun safe sbd early tomorrow morning zaayi mata cs.


Yana isa ya tura kofar dakin da karfi ya shiga ko bi ta kan mahaifiyarta dake zaune kan kujera baiyi ba ya wuce straight zuwa inda ya hangota…tana zaune kan bed da durmemen cikinta a gaba sai kallonshi take har ya karaso inda take dan taga kmr ba cikin hayyacinshi yake ba…mamanta ne ta taso daga inda take tana dubanshi tace”bawan Allah lfy zaka fado mana cikin daki haka ba sallama ba komai sai kace ba musulmi ba?”…juyawa Lee yayi ya kalleta da idanunshi da sukayi jajawur fuskarshi na bayyana asalin bacin ran da yake ciki yace mata”yes am not a muslim, kuma ba wajenki nazo ba don haka stay away kafin kice na miki rashin kunya”…ya juya yana cigaba da kallon Juwairiyya da zuwa yanxu cikinta har wani sautin qululu yake badawa tsabar tsoron daya bata don bata taba ganinshi cikin yanayi makamancin wnn ba…nunata ya shigayi da finger dinshi har snn idonshi bai daina shinning sbd hawaye ba yace”wallahi, wallahi Juwairiyya idan wani abu ya samu Ayaan ta dalilin wnn rashin imanin da kuke gwada masa saina kasheki da hannuna…nayi miki rantsuwa da Allah ne don ki fahimci ba barazana ko cika baki nakeyi ba, wlh idan na rasa shi ta dalilinki kema saina kasheki har lahira saidai nima a kasheni”.


Yana rufe baki mamanta data matso tana kokarin shiga tsakaninsu tace”malam bakada hankali ne?…mu zakazo kanayiwa barazana har cikin asibiti?”…juyawa yayi ya kalleta ya girgiza kai tareda sakin wani murmushin takaici kafin a fusace yace”na shigo din, kuma abinda yafi barazana ma zanyi muku kawai kuyi fatan kar wani abu ya sameshi…mutane marasa imani kawai kun shigo rayuwar yaro karami kun lalata masa ita kun tarwatsa masa mafarkinsa, kun rabashi da karatunshi kun rabashi da iyayenshi kun rabashi da farin cikinshi snn yanxu rayuwar tashi ma nema kuke saikun rabashi da ita kuma akan laifinda bakusan mafarinsa ba, bakusan gskyr al’amari ba kawai don kuna ganin kunada kudi shi kuma baya dashi?…kuna ganin ’yarku tanada gata shi kuma baya dashi?…to inaso ku kwana da sanin cewa kun zalinceshi domin bai aikata laifinda kuke zarginsa dashi ba, ’yarku karya tayi muku sbd wani mummunan quduri nata amma in the mighty name of Jesus zalincinku bazaiyi ajalinshi ba kuma da sannu zakuga karshenku tun kafin kubar duniya, alhakinsa bazai taba bari kuji dadin rayuwa ba”.
(Wayyo our Uncle Lee😭😭)


Pay 500 into 0013569116 Aisha Ahmad Tijjani Ja’iz Bank, sai a turamin shaida ta ***.





Rano✨