Hawayenmu

Chapter 6

by @sadiyaabdulrazak954

*HAWAYENMU*



         BY
SADIYA ABDULRAZAK 


PAGE 6


  Fasila ba ta ɗauki wayar ba, sadda ta ga miss call ɗin ta kira kuma Hafsan ba ta ɗaga wayar ba, saboda ta fara shawarar kar ta faɗa mata, ta jira ta yi hankali ta san 'yancin kanta tukunna.

 Da yamma Sa'eed yana gida baban shi ya kira shi a waya ya ce masa idan yana nan zai zo gidan nasu, Sa'eed ya ɗan roɗe saboda ba ya zuwa gidan nasu, ya ce "Amma Daddy lafiya kuwa? Idan wani abun ne sai na zo".

"Ina son ganinku tare da matarka ne, kuma ku biyu kawai ba a gaban iyayenku ba".

"To shikenan Daddy sai ka zo, Allah Ya kawo ka lafiya".

Ya amsa da Amin.

Sa'eed ya je ya samu Fasila wacce take kitchen, ya ce "Mine!"

Ta juyo tana amsawa.

"Kin ji Daddy yana hanya wai zai zo gidan nan, yana don magana da mu".

Gabanta ya faɗi ta ce "To Allah Ya sa lafiya".

Ya amsa da Amin.

Ya koma falo, ita kuma ta ƙarasa miyar tuwon ta shirya komai a dining, ta koma ɗaki don yin wanka, tana cikin wankan ya ƙaraso gidan, ta shirya ta yafa mayafi ta fito.

Ta zauna a ƙasan kujerar ta gaishe shi, ya amsa, sannan ta je ta kawo masa tuwon da drink, Usman ya ce "Dama na zo na tattaunawa da ku ne a kan matsalolin da na ji suna faruwa, Hadiza ta ce Fasila ba ta gaishe ta haka ne?"

Fasila ta sunkuyar da kai ta ce "Daddy ina gaishe ta wallahi, jiyan da na je waya take yi kuma na jira ba ta gama ba shi yasa na tafi".

Usman ya ce "Hadiza ai uwarki ce ko da ba Sa'eed kike aure ba, don kin zauna kin wuni a ɗakin ba komai ba ne, ya kamata ki jira ta, tun da idan babarki kika samu tana waya dole za ki zauna ki jira ta".

"Haka ne, zan kiyaye in sha Allah, a yi haƙuri".

"To ma sha Allah! Magana ta gaba ina so na ji ko akwai wata matsala da kuke samu tsakaninki da mijinki, akwai abubuwan da yake yi miki na rashin kyautawa?"

Ta girgiza kai "Babu komai".

"Sa'eed kai kuma fa? Akwai wani abu da take yi maka wanda ta ƙi gyarawa?"

"Babu komai Daddy, ni dama kawai yadda ba ta jituwa da Momy ne, sannan Humy ma ba ta jin daɗinta, shi ne ba na so".

"Yanzu ta ce za ta gyara, bayan shi sai me?"

"Babu komai" Ya faɗa a fili a ransa kuwa cewa yake duka ta daina burge shi.

 Usman ya ce "Mene ne asalin dalilinka na son ƙara aure?"

Da sauri Fasila ta ɗago ta kalli Daddyn, zuciyarta ta yi wani irin bugawa da ƙarfi, sai kuma ta kalli Sa'eed don jin amsar da zai bayar.

Sa'eed ya ce "Daddy kawai ina da ra'ayin zama da mata biyu ne".

"Sannan momynka ma tana so ka ƙara ko?"

"E haka ne".

Usman ya ce "Ƙarin aure ba haramun ba ne, indai za a yi adalci, kuma ba a yi shi don cin zarafi ga uwargidan ba, don haka babu wanda zai hana ka ƙara aure, sai dai ka sani Fasila ƙanwarka ce, kuma 'yata ce, ni babanta ne, ba zan ɗauki cin zarafin 'yata ba don za ka ƙara aure, idan ta kawo ƙararka ba za mu wanye ƙalau ba".

Ya kalli Fasila "Fasila ni a matsayina na mahaifin Sa'eed kuma babanki na zo na ba ki haƙuri kan cewa Sa'eed zai iya ƙara aure nan gaba, don Allah ki kwantar da hankalinki, kar ki damu da aurensa, dama ita rayuwa ta gaji haka, ba komai mutum yake samu yadda yake so ba, ki ƙaddara haka Allah Ya tsara zai zauna da mata biyu, sai dai ban ce ki yarda da cin mutunci ba, na tari zancen ne don kar ki fara ji daga bakin babarki, saboda kin ga irin zaman da suke yi da babar mijinki duk da sun girma ba su fasa ba, kar ki yarda tsakaninsu ya gurɓata rayuwar aurenku da kuka gina ta da sahihiyar soyayya tun ƙuruciya".

Kai kawai take gyaɗawa, ta kasa buɗe baki hawaye kuma tuni ya wanke mata fuska.

"Fasila ƙarin wannan ba wai an ce yau ne ko gobe ba, ko ya tabbata ko a fasa tun da manya ba su shiga ciki ba tukuna, don ni Sa'eed bai taba min zancen ba ma sai jiya babar shi take faɗa min..."

Sa'eed ya katse shi da faɗin "Daddy da gaske ne kuma zai tabbata in sha Allah, dama ina da shirin faɗa maka ɗin, don nan ba da jimawa ba za a tura in sha Allah".

"To shikenan Allah Ya tabbatar da alkhairi, Fasila na san kina son mijinki, kin san kuma Hafsa ba son aurenku take yi ba, idan kina yawan kai mata ƙarar mijinki zai saka ta kara ƙin auren ne kawai, kin ga kuma za ta tsani mijinki ƙila ma ta so ku rabu, ke kuma kin ga ba za ki so haka ba tun da kina son mijinki, a maimakon ki faɗa mata ko dinga faɗa min idan wani abu ya faru, ki kira ni a waya ni zan zo har gida na sasanta kuma ba zan yarda Sa'eed ya wulakanta ki ba".

"Kai kuma Sa'eed Fasila amana ce aka ba ka, kuma ka fi kowa sanin wahalar da ka sha kafin ka same ta, don duk mun fitar da rai da za ka rayu, nan aka dinga saka maka oxygen saboda so, da ƙyar ka same ta, zan yi mamaki idan aka ce za ka wulaƙanta ta don ka ƙara aure, kuma ba zan barka ba, don haka ka kiyaye".

"In sha Allah Daddy ba za a samu matsala daga gare ni ba".

"Alhamdulillah, Allah Ya sa, Fasila ba ki ce komai ba".

Da rawar murya ta ce "Na gode Daddy"

Sai ta tashi ta bar falon da sauri, Usman ya ce "Ni zan tafi, ka bi ta ka rarrashe ta kuma ka ba ta haƙuri, idan ta yi gadon rigimar babarta zan ce maka sorry". Ya ƙarasa maganar da murmushi

Shi ma Sa'eed murmushin ya yi ya ce "Zan jure in sha Allah".

"Yawwa ka riƙe amana sosai Please, ba na son ƙananun rigima, idan ka yi wa Fasila ba daidai ba ni ma ba za a ga daidai a gidana ba, tun da babarta tana bayanta, ni ma ina bayanka, don ƙara aure ba haramun ba ne".

"Haka ne Daddy, za a zauna lafiya ma in sha Allah".

Ya raka shi har waje ya shiga motarsa ya tafi, ya koma cikin gidan, maimakon ya je ɗaki wajen Fasilan sai ya zauna a tsakar gida inda yara suke wasansu.

 Fasila kuwa a bazata ta ji zancen auren, duk da ta san babar shi tana so ya ƙara bai taɓa zaton zai ƙara ɗin ba, ba ya nuna mata nan gaba zai ƙara aure, ko zargi ta yi zai ce ba haka ba ne, sai ga shi yau a gabanta yana cewa ya shirya aure nan ba da jimawa ba, wai ita ce za ta zauna da kishiya? Ita ce za ta raba Sa'eed ɗinta da wata? A ce Sa'eed zai yi irin rayuwar da yake yi da ita tare da wata? Ƙirjinta ya cunkushe, kuka ya ƙwace mata ta shiga yi ba ƙaƙƙautawa, ƙarshe sai da yaran suka shiga ɗakin suka ganta tana kuka, suka shiga damuwa, suka je suka faɗa masa.

 Ya tashi ya je ya same ta, shigowarsa ba ta saka ta tsagaita da kukan ba, ya tsaya yana kallonta, kafin ya kira sunanta "Fasila".

Ba ta amsa ba.

Ya cigaba "Tun da nake da ke na taɓa yi miki alƙawarin ba zan ƙara aure ba ne?"

"Ba ka yi ba, amma ni ma ban taɓa yi maka alƙawarin zan iya zama da kishiya ba".

"Ke za ki saka a ranki kishiya zan yi miki, ni dai ban ce zan yi miki kishiya ba, zan ƙara aure kawai, idan kin ga dama babu ruwanki da ita, sai kin ga dama ma za ki ganta, tun da ba gida ɗaya za ku zauna ba".

"Amma ka haɗa shimfiɗa da ita ba sai na ga dama ba ko? Ni ba zan iya sharing ba, ina da kishin da ba zan iya ba, don haka sai dai ka zaɓa zama da ni ko zama da wata, idan har sai ka ƙara aure to ka sake ni kawai tun yanzu".

"Ok kenan saboda mahaifina bai isa da ke ba duk abin da ya faɗa miki yanzu ba ki ji ba? Me yasa ba ki ce na sake ki a gabansa ba?"

"Ni dai na faɗa maka, ka zaɓa kawai saboda ba zan zauna da kishiya ba".

"Ke ba ki isa ki ba ni zaɓi ba, ra'ayina shi zan bi, idan kin so daga ranar da na yi aure kar ki sake yarda da ni a shimfiɗa, abin da kike taƙama da shi ɗin wallahi manage nake yi dama".

Ya juya ya fice daga ɗakin, ya barta da sakakken baki ido kamar zai zazzago don mamaki da firgici.