Chapter 7
*HAWAYENMU*
BY
SADIYA ABDULRAZAK
PAGE 7
GIDAN MUKHTAR
Tafiyar Maimuna ta ƙara masa kusanci sosai da Halima, don da ba shi da damar wayar dare da ita, indai ya dawo gida shikenan, amma yanzu sai sun kai sha ɗaya suna waya, haka kullum sai ya je zance, don dama yana ɗaga ƙafa ne saboda kar ya sosa ran Maimuna, kullum jaddada mata yake ta zauna lafiya da Maimuna saboda tana sonta, ba ta kishi da ita, ita ma kar ta yi kishi da ita, ko bai faɗa ba ita ma Halimatu har ranta take jin ƙaunar Maimuna, ta yi alƙawarin ba za a taba samun matsala daga gare ta ba, don ita gani take aurenta kadai ma da Mukhtar zai yi ai ya taimaka mata ne, to bare kuma ga kishiya ma tana ƙaunarta, ji take kawai ita ta samu canjin rayuwa, za ta rabu da uƙubar matar uba, ko da iya ɗebo ruwan asuba da za ta daina ta ji daɗi.
Duk wasu shirye-shirye an gama shi, bai yi niyyar a yi wani event ba, amma Maimuna ta ce sai an yi, kuma tana daga can ta yi order kayan da za su saka duka aka kai ɗinki, sai dai kawai ta ce masa ya saka kuɗin abu kaza, auren ya rage sati ɗaya cif ta dawo ƙasar, ba iya Halima ba har Umma da Baba ta yi wa tsaraba, sai dai tana cikin da baƙincikin gwal ɗin da aka siyawa Halimatu.
Yana zaune a falo ta ɗakko ɗankunnen ta miƙa masa tana murmushi ta ce "Ga ɗankunnen ƙanwata nan, ina taya ta godiya".
Ya karɓa yana murmushi ya ce "Ai kuwa ya yi kyau".
"Ai ya fi nawa kyau ma, don da na je shi kadai ne irinsa a wajen, so na yi muku anko, sai kuma ya zama shi kadai ne design ɗin, shi ne na ɗaukar mata ni na haƙura".
Cikin jin daɗi ya ce "Matar nan fa nema kike ki fi ni son yarinyar nan".
"Sosai nake sonta kamar yadda nake sonka, kuma farincikinka shi ne nawa, don haka duk abin da kake so ni ma ai dole na so".
"Ina godiya sosai, Allah Ya haɗa min kanku".
"Ameen, ni dai yanzu mota ce ta rage min, tun da ka kai ni Umara".
"Kar ki damu za a siya in sha Allah, ko don idan za ku fita ba sai dole na zo na kai ku ba, nan da wasu watanni dai za mu je Umara da Halima, don haka mota sai dai ku yi haƙuri sai next year".
Kalmar ku yi haƙuri ta dake ta, wato nufinsa motar su biyu zai siyawa ba tata ba ce ita kadai, lallai da sake. Amma ba ta nuna ba ta yi murmushi ta ce "Allah Ya nuna mana".
"Sai maganar event, Ku an gama ɗinkinku ka ni ce zan kai size ɗina gobe sai a dinka a hada a karɓo, don Allah ka kama mana waje me kyau sosai, ina so mu haɗu sosai mu ja magana".
A ɗan sanyaye ya ce"Amma dai Maimuna na yi zaton za ki haƙura da zuwa event ɗin nan".
Ta canza fuska ta ce "Me yasa?"
Ya ɗage kafaɗa "Ba komai, shikenan idan za ki je".
"A'a ka nuna ba ka son zuwana, ba damuwa in sha Allah ba zan je ba, ni a zatona ɗaya ne, komai tare mu dinga yi, ashe kai ba haka ba ne a wajenka, shikenan na gode". Ta tashi ta nufi ɗakinta tana kukan da babu hawaye.
Ya bi ta da sauri yana kiran sunanta, ya riƙo hannunta "Ki yi haƙuri don Allah ni fa ban faɗa da wata manufa ba, kawai na ga za a yi ta nuna ki ne ana cewa ga kishiyar amaryar".
"A'a kar ma ka waske, ka ce dai kawai ba ka so a nuna ni a ce ga matarka, saboda ni na girma yanzu, za ka auri karamar yarinyar 'yar Candy to marriage, ita ce ajinka".
Ya rikice ya ce "Haba Maimuna wallahi ba haka ba ne, tun da kin fassara abun shikenan ki yi haƙuri sai ki je ɗin, ni ban faɗa da wannan manufar ba Allah Ya sani".
"A'a ni kam na haƙura ba zan je ba, ku je kawai ku yi abunku".
"Ai kuwa indai kika fasa sai dai a fasa event ɗin bakiɗaya".
Da ƙyar ya lallaɓa ta ta haƙura za ta je.
Ta ce"Kawo ɗankunnen sai na haɗa da kayanta".
"A'a zan ajiye a ɗakina, sai ta tare zan ba ta, kin san yanzu gidan baƙi ne za a yi kala-kala, kuma ita kanta ba ta da nutsuwar da za ta adana".
"Haka ne, Allah Ya kaimu".
"Ai kin huce ko?"
Ta yi murmushi "Dama ban yi fushi ba, ai bikinka ne, tun da ba ka gayyata ta me zai kai ni".
"Ki yi haƙuri suɓutar baki na yi wallahi".
"Ya wuce a bar zancen".
Tun daga ranar ta fara zuwa wajen gyaran jiki, ana gyara ta ciki da waje, don magungunan mata da ta sha tun da tale ba ta taɓa shan irinsu ba, tun da ta je gidan su Halima ta tarar ƙawayenta suna shafe ta da wani haɗin dulka local ta ji daɗi a ranta, ita kuma ta saka a ranta za ta yi gyaran da ya fi nata.
Ana saura kwana uku ɗaurin aure aka yi jere, a ranar ne kuma Maimuna ta kai mata kayan fitar bikin, ta ja Umma gefe ta ce mata "Umma kun gyara Halimatu kuwa su maganin sanyin nan da maganin mata?"
Umma ta taɓe baki ta ce "Ni ba ta wannan nake ba, ba ji dai kanwar babarta tana cewa gobe za ta dafa mata kaza".
Farinciki ya kama Maimuna ta ce "Ai Umma da ta barta indai ba ta yi ba, don kaya suna nan da yawa na siya mata, ingantattu ma kuwa, kayan haɗin kazar ma na yi order ina jira a kawo shi to tun daga Nijar ne sai ranar ɗaurin auren kayan za su zo, kin ga sai na dafa mata ana kawo ta zan saka ta a ɗakina ta ci kafin ya shigo gidan".
Umma ta ce"Oh! Ni Maimuna sai ka rasa ke wace irin mace ce, kai Allah Ya miki albarka Ya saka miki da gidan aljanna, Allah Ya sa dai yarinyar nan ta fitar da mu kunyarki amin".
Maimunaa ta amsa da Amin.
Faran-faran suka gaisa da baƙin da suke gidan, suna ta saka mata albarka har ta yi alkawarin za ta kawo musu dabino da bagaruwa gobe, ta sanar da Halima gobe da sassafe za su zo su ɗauke ta su tafi gidan ƙunshi.
Washegari da safe Mukhtar ya ɗakko ta suka je suka ɗauki Halimatu suka tafi ƙunshi, ya ajiye su a wajen ya biya kuɗin ya tafi, idan aka gama musu zai koma ya ɗauke su, suna shiga Maimuna ta samu keɓewa da me ƙunshin, ta faɗa mata kar ta yi wa Halima me kyau, dole nata ne zai fi kyau, sannan idan da yadda za ta yi ta yi kokari ta malala mata lallen a kan ƙunshin saboda hannun ya caɓe.
Haka kuwa aka yi aka tsantsarawa Maimuna ƙunshi me kyau kamar ita ce amarya, aka yi wa Halimatu jeka na yi ka, ƙarshe aka lalata shi hannun duk ya damule, har sai da Maimuna ta ga rashin jin daɗi a fuskar Halima, amma ta maze ba ta ce komai ba, aka yi musu gyaran kai, sannan ta kira shi ya zo ya ɗauke su, suka sauke Halimatu a gida ya kai Maimuna gida.
Da Halimatu ta faɗawa maman kawarta Maimuna ta ce ta siya mata magunguna sam ba ta yarda ba, masifa ma ta dinga yi ta ce "Ban da son zuciya irin na Hanne kishiyar ce za ta yarda ta gyara kishiyarta? Sam ban yarda da kishiyar nan taki ba Halimatu sai kin yi takatsantsan, maza ungo ɗari biyar ɗin nan ku siyo min madara".
Suka siyo, ta tarkato magungunanta da su gumba ta juye a roba ta zuba mazarar ta dama ta ba ta ta ce ta shanye, sannan ta siya kifi da dadddare ta dafa shi da magani ta ba ta ta cinye, ta ce "Halimatu idan ta ba ki wani abun kar ki sake ki sha, ki ce ba sai kin sha ba, idan Allah Ya sa me bayarwa ne ya ba ki ɗan canji sai ki aiko na dinga siya miki".
Halimatu ta ce "To an gode" Amma a ranta dam ba ta ji cewar wai Maimuna za ta ha'ince ta ba.
Ranar party ta zo, tare suka je gidan kwalliya, nan ma dai ƙarawa me kwalliyar kuɗi ta yi ta ce tata ce za ta fi kyau ta yi wa Halima yar saffa-saffa, amma dayake Haliman ta fita kyau duk da haka sai kwalliyar tata ta fi kyan gani, sai da aka zo saka kaya sannan aka ga abin da Maimuna ta yi, kalar kayanta iri ɗaya ne da na Mukhtar, na Halimatu kuma kala da ban, wani less ne ba wani me tsada ba kuma ta zaɓa mata kala mara kyau, ita kanta Halima a fuskarta sai da ta nuna ba ta ji daɗi ba, haka ma Mukhtar ya kada haƙuri ya ce me yasa aka bambanta kala? Ta fara kame-kame kafin ta ce "Ku na yi niyyar Ku yi ankon ashe telan bai fahimta ba shi ne ya yi ɗinkin kayan Haliman da size ɗina, ya yi nawa da size ɗinta, amma ku yi haƙuri don Allah".
Ya ce "Shikanan ba damuwa".
Haka dai suka tafi Halima s sanyaye, shi ma duk jikinsa ya yi sanyi ban da Maimuna da take ta rawar kai, da aka fara gudanar da dinner kuwa har dai da ta ba shi mamaki, don idan ba ka sani ba za ka rantse ita ce amaryar, sun yi anko kuma kwalliya da adonta ya fi na Halima, ga shi yadda take shisshigewa tana riƙe shi kamar ita ce amarya, Halima dama tana da kunya, kuma ba ta da ƙawaye masu buɗaɗɗen idon da suka zuga ta, don haka ta zama kamar yar kallo a wajen, kunya ma ta dinga ji tana sunkuyar da kai, amma Mukhtar duk abin da yake yi hankalinsa yana kanta, tausayi take ba shi, haka aka yi dinner aka tashi ran Maimuna fess, a ranta tana ayyana yanzu ma kika fara shaƙa.
***