JODAH

03

by @sadisakhna


 

_____👑 *JODA* 👑_____ 

 

              

 

Na  

*Sadi-sakhna* 

Ƴar mutan Jama'are 

 

 

 

 

THE TRIO OF TALES  

(3⃣ minds, 3⃣stories,1⃣Journey)  

 

 

 

*HarÆ™a ta (3)*👑 

 

 

 

"To amma idan mukayi nasara fa,zamu tseratar da rayuwar Æ´ar mu,idan da kwananta a gaba zata tashi fah,sai muka bari aka binneta a gobe,baka tunanin zamu rayune tamkar ranmu ya zare daga jikinmu. " 

 

 

 

Shuru yayi yana nazarin maganarta,idan har mace mai tsoro kamarta zata iya yanke irin wanann hukuncin to inaga shikuma.... Kuma gaskiyar ta tunda sun gagara samun mafita wannan ce kaÉ—ai mafitar duk da tanada matuÆ™ar haÉ—ari. Kuma yasan babu kyau,to amma yazayyi kare iyalansa shine nauyi na farko daya É—oru akansa. 

 

 

 

ÆŠaga mata kai yayi alamar ya gamsu da maganar tata,duk da Æ™waÆ™walwarsa  alamun bata gama yarda da hukuncin da zuciyarsa takeson yankewa ba. 

 

 

 

"Yanzu to ta wacce hanya zamu bi kenan,abinda akwai kasada sosai,banason saka rayuwarku a haÉ—ari" 

 

 

 

Da mamaki ta kalleshi,ya yarda kenan. 

 

 

 

"Muje aban Joda ko inane,indai har Æ´ata zata rayu a wajen batareda an farmaketa ba a shirye nake danaje wajen ,kuma na shirya jure duk wani kalubale na hanyar tafiya zuwa wajen. Ban kawo haka a rainaba amma banajin zuciyata zata iya ganin binneta a gobe,idan naji tsoron tafiya dan kada akamani ma to banida tabbacin rayuwa a goben bayan an zartar da wannan zalincin a gareta" 

 

 

 

Yanda take maganar kaman tazare sai hakan yaÆ™arawa kamaluddeen jin tsananin tausayinta, ji yake inama yanada iko,inama shi É—ane da zai iya tsayawa iyalansa,ba matsoraci ba kuma rago wanda guduwace mafita a gareshi.  

 

 

 

****     **** 

 

 

 

Ƙafarta ta É—ora akan cinyar matar tana gyara mata,can kaman wani lokaci yarinyar da bazata wuce shekaru goma ba ta zare hannunta ta zabgawa matar mari wacce zatayi shekara hamsin koma fi a duniya. 

 

 

 

Rike wajen marin tayi,duk da ba yaune ita ko wani daga cikin bayin yake samun wulakanci daga wajen Æ™aramar gimbiyar ba amma wannan ne karo na farko dataji mari ya sauÆ™a kan kumatunta daga wajenta. 

 

 

 

"Ke wacce irin marar hankalice Jahila,cewa nace fah ki sakamin jan fenti shine zaki sakamin baÆ™i,mayya kika maidani komai,to kisaka harshenki ki lashe yanzunnan" 

 

 

 

Kallon farcen yarinyar takeyi wanda tashafa mata baÆ™in fenti da aka haÉ—ashi daga wani sashe na jikin bishiya bayan an Æ™ona shi. Abune mai tsada daba kowo ke iya siyansa ba sai Æ´an wane da wane,domin daga Masar ake kawoshi.  

 

 

 

Karkarwa jikinta yafara ganin tozarcin da jikar cikinnata takeyimata a kawai domin tana baiwarta. Bakinta tasaka tana lashe abin É—aya bayan É—aya saida tayi farce huÉ—u ta fixge Æ™afarta cikin tsiwa. 

 

 

 

"Tsaya tsaya haka ni karki shafamin cuta da wari,jeki É—auko ruwa ki zuba miski ki wankemin" 

 

 

 

Tashi matar tayi da rawar jiki ta wuce wasu bayi guda biyar da suke tsaye kowa da abinda yake hannunta na biyan buÆ™atun Gimbiya Meerah wacce itace Æ´a mace tak a wajen Sunkia Maryama matar Sarki Abdujalal Sunni Ali na Daular Songhay ta biyu. 

 

 

 

Kasancewar anyi maza uku aka sameta sai hakan yabata damar cin karenta babu babbaka,kuma an raineta da raina kowa ta taka kowa,domin itadin takai tama wuce tsaranta sai na gaban gaba. 

 

 

 

Ko daÆ™iÆ™a uku bata cikaba sai gata ta dawo da kwarya mai dauke da ruwa a cikin yana zuba Æ™amshi. 

 

 

 

Kama kafar Gimbiya Meerah tayi kaman ta riÆ™e kwai karta sake yafaÉ—i haka tafara wanke mata kafar tana gogewa da wani farin Æ™yalle. Ita kuwa sai kallonta take tana yatsina karamar fuska. 

 

 

 

"Nuratu....ko batanan" 

 

 

 

"Gani ranki ya daÉ—e" 

 

 

 

Da sauri wata yarinya da kaÉ—an zatafi Gimbiya Meerah don bata wuce shekara shabiyu ba. 

 

 

 

"HaÉ—amin ruwan wanka,sauran kuma kiyimin shirme irin na wancan lokacin,na kula ku Æ´aÆ´an bayinnan kunnenku a toshe yake,kuna daÉ—ewa baku iya abuba,wanann karon idan bakiyi daidai ba sai na saka anyi miki bulala ashirin ba goma ba. 

 

 

 

Girgiza jikin Nuratun yayi jin hukuncin da Gimbiya Meerah ta ambata zata saka ayi mata. Kallon kakarta Inna Mairo wacce take wankewa Gimbiya Meerah Æ™afa,ita tun tashinta bata san kowa ba sai Kakartata, Ubangidan mahaifiyarta ne yayi mata fyaÉ—e wanda Æ™arshe ta mutu a haihuwarta,ganin babu abinda zayyi da jinjirar yasa ya mikata ga Inna mairo ta raineta, sannan yakarbi kuÉ—inta a wajen Sunkia Haleema tunda itace uwargijiyar Inna mairon. Sai hakan yasa ta zama baiwa mafi Æ™anÆ™anta a sashen. Tanada shekara biyu aka haifi Gimbiya Meerah tare suke wasa ta É—auketa kamar yayarta,amma tunda tafara girma tagane matsayinsu ba É—aya ba,kuma komai ita idan tayi ba'a yimata faÉ—a saidai a sauÆ™e akan Nuratu ce tayi,sai hakan yasa halayyar ta suka fara sauyawa. Kuma bugu da Æ™ari yayunta ma suna riritata,komai take buÆ™ata shi suke mata. Sannan Sunkia Haleema itama tafito ne daga masarautar Mali,daular kuÉ—i da iko. itace Ta biyu bayan Sunkia Madina YaÆ´anta Biyu ne a Duniya,Gimbiya Hareesah wacce itace gimbiyar da ake ji da ita a kaf faÉ—in daular,saboda tanada kyau izza dakuma É—umbin baiwa ta ilimi,yanzu haka tana Birnin Jodan acan take karatu na Madarar mulki da tafiyar da sha'anin sa,makami ce ita mai zaman kanta da ake kaifata domin nemowa dukkan masarautar suna ,duk wani buri akanta uwarta ta É—ora,kasancewar ita aminiyar Musso Aimaanah ce,kuma tayi mata alÆ™awrin itace zata zama Sarauniyar gobe ta mali,Gimbiya meerah kuma so ake a haÉ—ata da Kaita Hamad É—an Musso maleekan. sai kuma Gimbiya Meerah. tanason Æ´aÆ´anta,kullum burinta su zamo sune a sama su taka kowa yanda suke so. Wannan yataka muhimmiyar rawa wajen sauya halayyar Meerah gabaÉ—aya. 

 

 

 

Duk lokacin da su Nuratu suka baro sashensu na bayi suka zo aiki zuciyar ta take cunkeshewa,babu wani da take gani mai muhimmanci a rayuwarta kaman Inna mairo. Abin yanayi mata ciwo idan taga Meerah tana cimata mutunci amma babu wanda zai nuna bacin ransa ma akai ballantana ya hana. Mutum goma ne a sashen Meerah,Inna mairo ce Babba kuma kusan ita tayi rainonta. Sai masu matsakaicin shekaru guda Takwas sai kuma Nuratu itace Æ™arama kuma Jikar Inna mairo. 

 

 

 

Yau tayi nasara ta haÉ—a ruwan yanda Meerah takeso,Mata hudu ne suka tattaro kayan wankanta suka shiga banÉ—aki,ita kuma Nuratu tabi inna Mairo zasuje suci abincin rana kafin su dawo,yamma har tayi da kyar take tafiya saboda yanda cikinta ya fafe. 

 

 

 

Babbar masarauta ce mai matuÆ™ar girma kamar gari guda,ita kanta Nuratu tunda suke bata taba fita waje ba,rayuwarta gabaÉ—aya ta Æ™are a cikin masarautar, Domin a bayi sai matsayinka yakai kafin za'a baka damar fita,wanda yawanci ma maza ne suke fitan. 

 

 

 

Kamo hanya sukayi zasuje inda ake raba abinci,jikinsu a sanyaye suke tafiyar,sun san zuwa yanzu kam an gama rabawa bazasu samu ba. Meerah ta hanasu tafiya firr,kuma ta sani sarai samun abincinsu na lokaci ne. 

 

 

 

"Inna shin wacce irin rayuwa ce taketake wakana a waje,shin irin tamu ce ko kuma ita dabance da wannan?" 

 

 

 

"Ehh to bazan ce miki ga wacce tafi ba,ko a wajen ma idan ke baiwa ce to duk É—ayane,saboda É—abi'a ce ta É—an adam idan yanada dama ya dama. Wani lokacin har gwara nan zaki samu wani mai kyau kici daga inda kike aiki idan ya rage,amma a waje sabanin hakane saboda shi kansa mai gidanki ba lallai ya Æ™osheshi sosai ba ballantana ya baki" 

 

 

 

"Inna shin iya abincine abinda idan bawa yasamu shikenan an gama masa komai,ina kimarsa da darajar sa a matsayin sa na shima É—an adam ne?, ni kaÉ—ai nasan yanda nakeji a raina idan Gimbiya meerah tanayi miki walaÆ™anci,koba komai ai kin fita" 

 

 

 

Tsayawa da tafiya inna mairo tayi cakk kafin tajuyo ta kalli Nuratu da fuska mai É—auke da rashin alamar wasa. 

 

 

 

"Nakula ke har yanzu yarinya ce baki gama sanin a wacce duniya kike rayuwa ba ballantana kisan a wanne matsayi kike. To ki shiga hankalin ki in kinaso mu rayuwa cikin kwanciyar hankali zamaninmu ya shuÉ—e a haka. Kada ki taba damuwa da halinda zanshiga bama a wajen Denti meerah ba koda a jaririn da aka haifa yau ne. Domin na daÉ—e da HaÉ—iye zuciyata,bana ma jinta bare ta kaini ga shiga matsalar da bazan iya fitar da kaina ba" 

 

 

 

Suna tafe inna Mairo tana nusar da Nuratu rayuwar da suke ciki har suka iso wajen rabon abinci,kaman yanda suka tsammata kuwa an gama raba busashshiyar gurasar da mutum zai gabjeta ko babu ruwa. To su basu samu ba. Kallon banza mai rabon abincin tayi musu,Æ™atuwar matace hannun ta riÆ™eda wani Æ™aton ludayi na itace wanda take juya miya a cikin wata tukunyar kasa dake kan murhu. 

 

 

 

"Tsabar WalaÆ™anci bakai zaka ciyarda kanka ba,amma kazo ka karbi abunma sai kaga dama tukunna. To ya Æ™are saiku jira na gobe." 

 

 

 

Kallon miyar dake kan wuta Nuratu tayi da kuma uwar gurasar da take cikin wata babbar Æ™warya,amma kuma matar tace musu wai babu abinci saidai su dawo gobe. Meyasa kowa bashida tausayine wai. 

 

 

 

HaÉ—iyar yawu tayi saboda yunwar da take mintsininta. 

 

 

 

"Dan Allah baaba Sahura ki É—an bamu wlh yunwa mukeji tun safe bamuci komai ba,kuma aikine mukayi uwargijiyar mu ta hanamu tafiya shiyasa,gashi can dayawa kin ajiye mai zakiyi dashi" 

 

 

 

Cikeda Æ™ukewa hawaye yana taruwa a idanunta tayi maganar. 

 

Aikuwa kaman jira baaba Sahurar Take ta juyo kanta kaman zata cinyeta. 

 

 

 

"Lallai yarinyar nan dama ana faÉ—in kin fiye rashin kunya da shiririta ashe da gaskene,to innaga dama daga yau bazan Æ™ara baki abinci ba naga yanda zakiyi ko zaki Æ™wata kai" 

 

 

 

Kirjinta ne ya buga dummm jin abinda baaba Sahura tace, inkuwa haka ta faru to kashinta ya bushe,kallon fuskar inna mairo tayi wanda itama bataji daÉ—in furucin Nuratun ba. 

 

 

 

Saurin zubewa tayi akan gwiwoyinta tana roÆ™on Baaba Sahura tareda haÉ—a hannayenta waje É—aya tana murzawa. 

 

 

 

"Dan Allah kiyi haÆ™uri baaba sahura wlh ba haka bane yunwa nakeji shiyasa" 

 

 

 

Ta Æ™arisa maganar tana fashewa da kukan ban tausayi. Kallonta baaba sahura tayi tana kanne ido É—aya da kuma É—aga kai alamar takama,saidai kuma ta alama taji daÉ—in roÆ™on da Nuratu tayi mata domin fuskarta ta É—an sarara. 

 

 

 

"Shikenan tunda kin roÆ™a na janye magana ta" 

 

 

 

Ajiyar zuciya Nuratu ta sauÆ™e kafin ta tashi akan gwiwoyinta tana kaÉ—e kasar dake kan gwiwarta. Har sunyi niyyar juyawa zasu tafi baba Sahura ta cillowa nuratu gurasa guÉ—a É—aya,bata iya ta cafke ba sai ta faÉ—i a Æ™asa. Kallon gurasar tayi da take kwance a cikin rairayi ta kuma kalli baba sahura wacce tayi kaman bata aikata komai ba na rashin daidai. Saima juyawa da tayi ta cigaba da aikin gabanta. 

 

 

 

Tsugunnawa Nuratu tayi cikin sanyin ta É—auki gurasar kana ta fara Æ™ade Æ™asar dake jiki tana kallon inna Mairo. 

 

 

 

Itama kallonta takeyi da alamu masu wuyar fassara,tafiya ta farayi zuwa hanyar sansaninsu,ganin haka yasa Nuratu raba gursar biyu tabi inna mairo a baya da sauri ta miÆ™a mata. 

 

 

 

Juyowa tayi ta karba suka fara tafiya. 

 

 

 

"Keee keee ku waÉ—annan masu tafiya ku biyun kuzo nan" 

 

 

 

Juyowa sukayi a tare suna kallon mai maganar, Gimbiya Asma ce matar Yerima Kabeer babban É—an sarki Abduljalal mai jiran gado, bazata wuce shekara goma sha Bakwai ba don aurene akayi mata da wuri irinna tsarin gidan sarauta. Itama Æ´ar sarki ce daga yankin Masarautar Ghana,wanda suma suna da madafin iko,shiyasa take jinta da mulki da taÆ™ama,sannan take taka wanda taso saboda jin itace Sarauniyar garin ta gaba. Duk da mijinta hankalinsa ba iya ga kanta ya tsaya ba harma da bayin dake gefensa,kuma duk wacce ta É—au hankalin mijinta bata barinta haka saita illata ta,shiyasa sunanta yake kaÉ—a duk wata hantar bayin dake masarautar.  

 

 

 

Juyawa su inna mairo sukayi suna kallonta,tafiya take cikin takama jikinta sanye da wata doguwar riga da jan saÆ™i mai tsada,wuyanta cikeda zinare, tsohon cikin dake cikinta yaÆ™arawa suffarta É—an cika,idonta cikeda baÆ™in kwalli kasancewar tana É—an haske sai yataimaka wajen yiwa fuskarta gwarjini. 

 

 

 

Bayan ta bayi ne guda uku,gefe da gefe sai kuma ta tsakiya a bayanta wata tariÆ™e lema akanta domin kare mata hasken rana. Da alama tafito zagayawa ne. 

 

 

 

"Ke Æ™aramar kizo nan zan aikeki tsohuwar masarsuta ki karbomin saqo  

 

 

 

Zaro ido Nuratu tayi ta kalli inna mairo. Dan harga Allah duk wanda ya kalli fuskar nuratu to kuwa yaga alamar gajiya da galabaita sosai. Fasihmman data ambaci tsohuwar masarauta inda iyayen sarkin suke,can ne masarautar kafin a gina wannan a dawo, kuma akwai tafiya mai É—an tazara tsakanin sabuwar da tsohuwar, iya kafin mutum ya fita daga da'irar masarautar ma ya nufi can tafiyace mai zaman kanta. 

 

 

 

Ganin inna mairo batace da ita komai ba yasa idanuwan data zaro É—in suka fara zirarar ruwan hawaye,saurin kama gefen zaninta tayi ta goge mata saboda karsu kula. Ita kanta tasan aikan da aka saka É—iyar tata yayi mata yawa,domin ko ita akace taje ta dawo a yanzu an gamata da aiki ballantana kuma Æ™aramar yarinya kamar Nuratu,to amma shin ya zasuyi?. 

 

 

 

Wata dabara ce ta faÉ—o mata,da sauri taja hannun nuratu ta Æ™arisa gefe kaÉ—an da Gimbiya asma,wacce take wani yatsina fuska tanayi musu kallon kamar takalli kashi. 

 

 

 

"Ran Gimbiya ya daÉ—e nace idan babu damuwa ni zanje miki aikan,yarinyar batajin daÉ—in jikinta" 

 

 

 

Ta Æ™arisa maganar tana haÉ—a hannayenta biyu tareda langabar da kanta gefe. 

 

 

 

"Ai na ganki nace tajemin aiken,bake nayi niyyar aikaba ita nayi niyya,idan taje a hanya mala'ikun ajalinta su É—auketa,ina ruwana da jinyarta. Tukunna ma yaushe bawa a masarautar nan yafara maida yawunsa idan aka bashi umarni. Sa'ar ki É—aya wannan maganar taki kin furtata ba'a fusace nake ba,da saina sakata zuwa da dawowa sau goma" 

 

 

 

Saurin durÆ™usawa tayi jikinta yana rawa tana bata haÆ™uri,ganin hakan bazai kaita ba yasa ta tashi da sauri ta tura Nuratu gaban gimbiya Asmah akan ta aiketa,ita kuma tayi gaba da sauri. 

 

 

 

Aikan magani ne da aka aiko mata daga garinsu,bataso ta aiki babba tana tsoron karya bsta mata shiri,shiyasa tana ganin Nuratu tasaka a ranta itace daidai da aikennata. 

 

 

 

Jiki babu Æ™wari haka ta karbi bayanin gun wanda zataje ta nufi hanyar fita daga masarautar,har haÉ—a hanya take saboda tsabar gajiya da yunwa. 

 

 

 

Har tazo wuce ta wani waje taji an cafko hannunta zuwa bayan katangar. Har ta gigice zata kwaÉ—a ihu taji muryar ummannata. 

 

 

 

"Ke dan Allah kiyi shuru,hungo ruwa maza sha,ga tsagin gurasata ma maza haÉ—a dukka ki cinye in kina tafiya a hanya,sannan kiyi sauri karki tsaya a ko ina,daga kin karbo mata kuma maza ki dawo gida kinji?" 

 

 

 

ÆŠaga kai tafi dan maganar bazata fito ba tacika bakinta da gurasa tana binsa da ruwa. 

 

 

 

Da kallon tausayi inna mairo take binta harta gama ci tasha ruwan,ajiyar zuciya tayi kafin ta kama hanyar fitan. Ba kaman É—azu ba yanzun da É—an kumarinta.