BURIN ZUCIYA(Short Story)

BURIN ZUCIYA Chapter 3

by @ayshadansabo

*BURIN ZUCIYA❤* *Arewapen@ayshadansabo*

©️ _Ayshat Ɗansabo_ _lemu_ ✍🏻

*Free page 3*

A hankali bakinsa ya motsa ya furta. "Please Farha leave me a lone,bana buƙatar hayaniya."

Kallonsa take cikin ido zuciyarta na sosuwa da salon wulaƙancinsa,har lokacin idanunsa na kanta hakan yasa ta janye nata tana faɗin. "Au yanzu ni ce mai hayaniyar Ya Abdallah? Any way laifina ne da zuciyata kullum take tare da kai,amma kai ko kaɗan baka taɓa tausayamin ba Abdallah,miye aibuna da ka kasa so na? Nima ba nice na ɗaurawa kaina sonka ba Allah ne ya jarabci zuciyata da ƙaunarka."

Ta ƙare maganar tana sakin kuka.Hakan ya karya zuciyar Abdallah,domin ya tsani yaga mace na kuka. Maganar da tayi na cewa Allah ne ya ɗaura mata son shi ya karya zuciyarsa,musamman da a yanzu zuciyarsa ke kan azabtuwa da soyayyar Yarinyar da yai wa gani ɗaya,amma ta mamaye ilahirin zuciyarsa.Cikin murya ƙasa-ƙasa yai magana yana faɗin.

"Seat."

Ba musu ta koma ta zauna tana dubansa tare da ƙoƙarin tsaida hawayenta,kallo ɗaya yai mata ya ɗauke kansa yana faɗin.

"Farha kamar yadda kike ji aranki kina so na,haka nima nake jin son watanki a cikin zuciyata,impact ma gara ke kina ganina kuma nasan kina yi,ni har yau wacce aka jarabci tawa zuciyar da ƙaunarta bata ma san ina yi ba,don haka Farha kiyi ƙoƙarin cireni a mind ɗinki,domin ni ba zan yaudareki da kalmar so ba,don ban taɓa jin wani feeling akanki na daban ba,na ɗaukeki a matsayin Humaida ce acikin zuciyata,don haka karki yaudari kanki,Allah ya baki wanda ya fini,amma ni Abdallah ban taɓa ma kaina sha'awar nayi auren zumunci ba."

Ya ƙare maganan yana miƙewa tare da yin taku ɗaya biyu,zuwa gabanta.Hankicin dake hannunsa ya miƙa mata ba tarebda ya yi magana ba,tasa hannu ta amsa.Bai sake cewa komi ba ya kwashi wayoyinsa da car key ɗinsa ya bar garden ɗin,ba tare da yabi takan magazine ɗin da ta sameshi yana dubawa ba.Wani kuka ne na tausayin kanta ya ƙwace mata,tabbas Abdallah ba zai taɓa sonta ba tunda har a yau ya iya gaya mata ga da ga baya ra'ayin auren zumunci bare har yayi ra'ayinta.Ya iya furta mata watanta yake so ba ita ba,tabbas ya zama dole ta tirsasa zuciyarta yakiceshi a ranta ta rungumi samarinta masu matowa a kanta.Share hawayen idanunta tayi wanda har fuskarta ya sake yin ja abinka da fara,jiki a sanyaye ta fito daga garden ɗin domin komawa cikin gida. Motarsa ta hango yana barin gidan baki ɗaya,koda ta shiga kai tsaye ɗakin Humaida ta nufa ƙanwarsa da ya kasance ita ce age mate ɗinta masu shekaru ashirin da ɗaya.Dukkansu a halin yanzu deegree garesu har service sun kammala.

Babu kowa a cikin ɗakin hakan yasa ta faɗawa bisa bed tare da lumshe idanunta,zuciyarta na cigaba da jin raɗaɗi da ɗacin kalaman Abdallah.Ƙofar toilet aka buɗe wata budurwa kyakykyawa ta fito da alamu alwala ta ɗauro,ta sauke ganin ta akan Farha dake kwance kafin ta furta.

"Hey! Farha,what's wrong with u? kika zo kika zube a gado kamar mara lafiya."

Farha ta buɗe idanunta ta sauke akan Humaida tana faɗin."Ni da Yayanki ne Humaid, Ya Abdallah ba zai taɓa sona ba,yau ya sanar dani hakan ido cikin ido."

Ta ƙare maganar muryanta na rawa yayin da Humaida ta saki murmushi tana faɗin: "Dama ni na san sai wannan ranar tazo Farha,shiyasa tunda daɗewa na kwaɓeki da na ga kullum zurma kanki kike akan sonsa shi kuma ba kya gabansa.Ya Abdallah ya sha faɗin cewa bayi ƙaunar auren zumunci amma kin sani kika cigaba da yaudarar zuciyarki,to gashinan ya sanar dake wata yake so bake ba.Sai ki cireshi a ranki tunda bashi ne autan maza ba,kuma kina da samari masu aji kamarsa."

Har Humaida ta ƙare maganar idanun Farha na kanta,ko kaɗan ba tayi mamakin kalamanta ba,domin ba tun yau tasan Humaida na jin haushin yadda ta liƙe ma Yayanta. Maimakon tayi magana kawai sai ta míƙe ta shige toilet itama,Humaida ta nufi inda pray mat yake ta shimfiɗa domin gabatar da sallar magriba da ake ta kira.

⚡⚡⚡⚡⚡

*ABUJA*

Sakkowa take daga matakalar benan tana riƙe da hannun husnah,dukkansu sanye suke cikin shiga na alfarma.Sun yi kyau sosai barin ma husnah da ba inda ta baro kyawun Ubanta,gashinta ya sha gyara an kama jelarsu da band masu kyau. Sameera na sanye cikin gown na lace mai shegen kyau da tsada,kallo ɗaya za kai mata kasan cewa matar manya ce da masu gidan rana suka zauna musu.Madaidaicin mayafi ne bisa kafaɗarta,sai hannun hagunta da ke ɗauke da hand bag ɗinta.Ɗakin Rasheeda ta nufa kai tsaye tana jaye da hannun husnah har lokacin,a kwance ta sameta bisa bed daga ita sai dogon shimi rabin cinyoyinta farare tas duka suna a waje.Hannunta riƙe da waya tana latsawa,sallaman Sameera ya sa ta tashi zaune tana faɗin.

"Anty Sameera har kunyi shirin zuwa birthday party ɗin kenan? "

Sameera ta saki smile tana faɗin."Yes dubi ƴar taki mana ki ga shigarta tayi kyau kuwa?"

Rash ta dubi Husnah tana ware mata hannu, Yarinyar ta isa gareta ta shige jikinta.Rash ta dubi Sameera tana faɗin."Komi yayi Anty sai dai bari in ɗan sa mata jan baki kaɗan."

Ta ƙare maganar tana sauka ta nufi gaban dressing mirrow ɗinta wanda ke cike taf da tsadaddun kayan kwalliya,zuwa haɗaɗɗun designer's performs.Red ɗin janbaki na oriflame ta ɗakko ta saka ma Husnah,nan da nan kwalliyar ya sake inganta,takai mata kiss a forehead tana faɗin.

"I luv u so much my princess."

Husnah tayi dariya tana faɗin."Luv u too Anty Rash,zan kawo miki tsarabar ƙatoton cake."

Duka suka sa dariya kafin Sameera ta dubi Rash tana faɗin."Rash idan Hisham ya sakko ki sanar dashi mun wuce,yasan da fitar but yanzu bacci na baro shi yana yi bani son tada shi.Na san yanzu zai tashi tunda anyi magriba,sai mun dawo tunda ba za ki ma Maman Ilham kara kije ma Ilham birthday celebration ba."

Ta ƙare maganar tana yin gaba Husnah na biye da ita,Rash ta ɗaga murya tana faɗin."Sai kun dawo,yau sam bani jin fita ne Anty."

Sameera na barin gidan bai fi da mintuna goma ba,Rash ta fito ta haura zuwa sama.Kai tsaye ɗakin Hisham ta nufa,ta murɗa ƙofar tare da sanya kanta ciki.Sanyi da ƙamshin ɗakin suka bugi hancinta,bashi ciki sai ta nufi bakin bed ɗin ta zauna tana ƙarewa ɗakin kallo.Sameera na matuƙar ƙoƙari wajen gyaran ɗakin mijinta,ko da yaushe za ka samu ko'ina fes yana tashin ƙamshi.

Ɗaure da towel ya fito hannunsa na riƙe da wani ƙarami yana goge sumar kansa,da alamu wanka yayo idanunsa ya sauke akan Rash yana sakin murmushi kafin ya furta.

"Baby har Sameera ta fita kenan tunda naga kin hayo nan ko? "

Wani farr...!Tayi da idanu kafin ta kaɗasu tana faɗin."Yes sun fice babu jimawa."

Ta ƙare maganar tana miƙewa ta isa gare shi,idanunsa fes akan cinyoyinta da ƙirjinta dake waje.Domin shimin jikinta duka tsayinsa bai ƙarisa cinya ba,towel ɗin hannunsa ta amsa tana tayashi goge jiki,yayin da yake faɗin.

"Rash jiya fa kin rikitani sosai,har kinsa na kasa jin daɗin Sameera sam,me kike shane na gyara da yafi nata ne kike rikitani ko yaushe?"

Murmushi ta saki tana kai bakinta bisa kunnuwarsa,banji me ta raɗa masa ba,gani kawai nayi ya janyota zuwa jikinsa suna sakin dariya kafin yakai bakinsa kan kirjinta yana kissinga.Ita kuma hannuwanta na yawo a jikinsa cike da ƙwarewa a shaiɗanci,wanda rainonsa ce shi ya koyar da ita komi har idanunta suka buɗe.Cikin muryarsa daya sauya yake faɗin,

"Rash muyi ko da round ɗaya ne, kin riga da kin taɓoni,ba zan iya komi ba saina gamsu."

Zare jikinta tayi daga nasa tana jifanshi da wani shu'umin kallo,kafin ta ɗage rigarta tana masa nuni da ƙasanta.Kallo ɗaya yai ma wajen ya gane nufinta,bata da tsarki period ɗinta yazo kenan.Hakan ya sashi jin takaici sosai,amma da yake tasan kanshi sai ta dawo jikinsa tana sake rikitashi da salonta,wanda ya kasa daurewa suka nufi bed ɗinsa.Sosai ta gamsar dashi ta hanyar da tasan za ya gamsu matuƙa,shimin jikinta ta mayar tana sauka daga bed ɗin ta nufi ƙofa tana faɗin.

"Sweety na tafi sai ka sakko Dinner."

Tashi yayi shima ya nufi toilet domin yin wanka,koda ya fito jallabiya ya saka ya tada sallah.Haɗa magriba da isha'i yayi duka a lokaci guda, sabida suna can suna shaiɗanci har lokacin isha'i tayi.

Sameera basu shigo gidan ba sai ƙarfe tara na dare,tuni har Rash da Hisham sunyi dinner abinsu inda suka ciyar da junansu.Hankalinsa na kan kallon labarai a tashar BBC world news,yayin da Rash hankalinta ke kan wayarta.Ta sauya shiga zuwa riga da wando na bacci masu kauri,nan falon Sameera ta zube tana zama kusa da Hisham har jikinsu na gugar juna.Yayin da Husnah ta nufi inda Rash take,tana nuna mata abinda suka zo dashi.

"Anty oyoyo,har kun dawo?"

Cewar Rash kenan tana ɗaura ido akan Sameera,da ta zame mayafinta sosai rabin jikinta na jikin Hisham ɗin.Ta dubi Rash ɗin tana faɗin.

"Kin ganmu sai yanzu,wallahi abu yai kyau kinyi missing."

Rash ta saki smile tana faɗin."Bakomi ba dai next month bane babyna za ta yi nata,so time ɗin ne za mu warwasa,zan haɗa mata haɗaɗɗen birthday party ko my princess."

Ta ƙare maganar tana duban Husnah dake ta murna,jin abinda anty Rash ɗin ke cewa.

"To Allah ya nuna mana."

Cewar Sameera tana maida dubanta ga Hisham,wanda sam bai sanya bakinsa cikin hirarsu ba.Tashi Rash tayi taja hannun Husnah suka nufi ɗakinta,Hisham ya bi mazaunanta da kallo yana kai hannu ya rungumo Sameera zuwa ƙirjinsa yana cusa kansa a samansu.Sai ƙarfe 10pm suka nufi sama,domin shirin kwanciya bacci.

⚡⚡⚡⚡⚡⚡

*ZARIA*

Ƙarfe goma Surayyah ta gama shirin kwanciya bacci,Babansu ya aiko Mum tayi kiranta.Ta zura hijab ta fice zuciyarta cike da addu'ar Allah sa dai lafiya kira da dare haka,bayan tayi sallama ya amsa mata ne ta shiga tana mai zama kusa dashi kamar yadda ya yi mata nuni da hannu.Ta dube shi tana faɗin.

"Baba gani."

Alhaji Mahmud ya aje cup ɗin hannunsa da yasha ruwa ya fuskanceta sosai,tare da kiran sunanta kafin ya cigaba da faɗin.

"Abinda yasa na kiraki Auta,akan maganan Aliyu ne Yaron ya matsa yana tsananin son ki,har ya tinkari Mahaifinsa da maganar aurenki yake son yi idan an bashi dama.To sai dai ni sanina dake shine har yanzu mamanki ta sanar min baki nuna kulawarki a kansa ko meyasa? Shine na kira inji dalili domin ni kaina Yaron ya kwanta min banga wani aibu a gareshi ba.Surayyah na gaji da zaman ki haka babu aure,mutanan Unguwa da dangi sun fara gutsiri tsoma akan hakan,ana cewa kina koran samari duk wanda yazo sai ki kore shi,to na gaji ki sanar dani miye aibun Aliyu,ko kuma kina da wani tsayayye ne da kukai alqawarin aure da shi?"

Ya ƙare maganar da jefa mata tambaya.Surayyah wacce tunda Baba ya fara magana zufa ya fara wanke mata fuska,zuciyarta ya cika da ruɗani da matsanancin jin zafin Aliyu.Sai da Baban ya sake magana cikin tsawa sannan ta buɗe baki cikin rawar murya tana faɗin.

"Yi haƙuri Baba,babu wani da mukai alƙawarin aure dashi."

"Naji sanar dani aibun Aliyu da ba za ki bashi dama ba."

Alhaji Mahmud ya furta hakan cikin dakiya tare da tsuke fuska,Surayyah ta sake yin ƙasa da kanta tana jin wani abu ya tokare mata a ƙirji.Lokaci guda tsanar Aliyu ya mamaye zuciyara,cikin rawar murya take faɗin.

"Baba don Allah ka yi haƙuri ba zan iya faɗin komi a yanzu ba,amma gobe zan je in sanar da Anty Safiya."

Ta ƙare maganar tana jin hawaye na biyo fuskarta wanda ta rasa na miye ma? Tsabar yadda kanta ya kulle da lamarin Aliyu.Muryar Baban nasu ta jiyo yana faɗin.

"Alright,to Allah shi kaimu lafiya,sai dai ina so ki sani wannan karon bazan ɗaga miki ƙafa ba,idan har Aliyu ne baki so to ki fiddo mijin aure ki turoshi gareni.Na baki nan da watanni biyu kacal,bayan naji gamsasshen bayani na dalilin da yasa baki son Aliyu.Idan banji abinda ya gamsar dani ba to ki sama zuciyanki baki da miji sai shi,maza tashi ki je ki kwanta. "

Cikin gudu-gudu Surayyah ta fito daga ɓangaren Babansu tana sakin kukan da take riƙewa."Meyasa Aliyu zai mata haka bayan duk irin kashedin da tai masa akan ya fita daga rayuwarta? Akan me zai je ya turo Mahaifinsa alhali ba itace ta bashi izinin yin hakan ba? Tabbas ya tabbata Aliyu ba ita yake so ba yayi hakan ne don kawai ya cika Burin Zuciyarsa a kanta."

Tana shiga ɗakin gado ta faɗa tana jin zuciyarta na sake ɗaukar zafi,haushi da tsanar Aliyu tare da duk samari masu zuwa mata da son cika burin zuciyansu ya mamaye ruhinta.Ta ina zata fidda mijin aure nan da watanni biyu alhali daga samarin har magidantan da BURIN ZUCIYA iri ɗaya suke zuwa mata.Kuka ne ya ƙwace mata tana sake jin tsanar maza na ratsa zuciyarta,dole taje wajen Anty Safiya gobe domin ita kaɗai ce za ta iya sanar ma dalilinta na ƙin Aliyu bayan ya bayyana BURIN ZUCIYARSA a kanta.

Duk yadda taso yakice damuwa don ta samu bacci mai daɗi abin yaci tura,baccin ma sai dai ɓarawo ya saceta shima tana yi tana farkawa.Daga ƙarshe ma tashi tayi ta ɗauro alwala misalin ukun dare ta shiga nafilfili,tana kaiwa Allah kukanta tare da neman zaɓinsa.

Washegary sai ƙarfe goma na safe ta farka daga baccin da ta samu ya ɗauketa bayan sallar asuba,cikin hanzari ta nufi toilet tayo wanka da brush ta fito ɗaure da towel.Gaban mirror ta isa taja stool ta zauna tana shafa mai,kwalliya kaɗan tayi ma face ɗinta ta goga lipstick red.Sosai tayi kyau,ta nufi closet ɗinta ta fiddo Riga doguwa na atamfa da akai wa yankan A shape.Ɗinkin ya yi mata kyau,ta feshe jikinta da turaruka masu sanyin ƙamshi.Ɗaura ɗankwalin tayi irin ɗaurin ture kaga tsiya ɗinnan,ta fito ta nufi kitchen kai tsaye domin zubo abinda za ta ci.Ganin ba abinda take so akai ba yasa ta soya Irish da egg ta juye a plate tare da haɗa tea ta fito falo ta zauna tana cin abincin,sai dai kuma hankalinta na gidan Baba Lawal duk ta ƙosa taje ta samu Anty Safiya akan maganar Aliyu.

Sha biyu dot ta fito sanye da hijab hannunta riƙe da ƙaramin hand bag na Gucci,tai ma Mummy sai ta dawo ta fito gidan tana takunta cike da nutsuwa har ta fito bakin titi.Ta ɗan jima kafin ta samu abin hawa ta shiga,ta sanar dashi tudun wada layin mora zai kaita.

Koda ta isa gidan tsit babu motsin kowa da alama Yaran duk suna skull,kai tsaye falon gidan tayi wa tsinke tana ƙwala sallama.Anty Safiya ta fito tana amsa sallamar,ganin Surayyah ce yasa ta kama baki cike da zolaya take faɗin.

"Ashe ma matar ƙani ce,yau wata rana anzo gidannan da wuri haka."

Surayyah ta saki smile tana zama a cikin seater take faɗin."Anty Safiya kenan yanzu ɗin ma wallahi da dalili,ƙanin naki dai shi ya tadoni domin yana shirin ɓallo ma kansa ruwa don bazan ce ni zai ɓallowa ba."

Ta ƙare maganar cike da matuƙar nuna jin haushinta,hakan yasa Anty Safiya saurin zama tana tambayarta lafiya dai ko? Surry ta sanar mata yadda sukai da Babanta jiya,ta ƙare maganar da faɗin.

"Wallahi Anty Safiya ba zan taɓa auren Aliyu ba,nasan na so shi a baya amma banda yanzu,da na riga na gane Burin da ke cikin zuciyarsa a kaina."

Idanu Anty Safiya ta tsurawa Surayyah har ta dasa aya kafin ta furta. "Duk naji Surry,amma sanar dani miye burin zuciyar Aliyu a kanki da kike faɗi?"

"Aliyu jikina yake so bani ba Anty Safiya,sabida ya sha gwadamin sai dai muyi soyayyar shan minti,amma na nuna sam ni ba zan iya ba.Kullum ya zo wajena burinsa ya kai hannunsa jikina,bashi da aiki saina lallaɓani akan in amince ya dinga taɓa jikina.Ba zan iya auren Namijin da tun a waje ya nuna jikina yake so bani ba,ya ɓullo da maganar aure ne don ya cika burin zuciyarsa ba wai don yana min so na tsakani da Allah ba."

Surayyah ta ƙare maganar tana hawayen takaici,wanda hakan yasa jikin Anty Safiya yin sanyi.Sai taji ma kunyar Surayyah duk ya lulluɓeta,ace wai ƙaninta da suka fito ciki guda ne ke neman ɓata ma Surayyah rayuwa.To ɓata mata rayuwa mana,domin duk saurayin da zai nemi ya dinga shafaki yana tsotse-tsotse da jikinki ai ɓataki yake,koda bai kusanceki ya kwanta dake ba.Dafa Surayyah tayi tana bata haƙuri tare da bata tabbacin ta kwantar da hankalinta za ta yi magana da Aliyu.

Bata wani sake jimawa ba ta baro gidan Anty Safiya,ta nufi saloon domin tana son a wanke kai ayi mata calaba......✍🏻