Chapter 2
*MIJIN KANWATA..*!
_(k'addarata)_
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty❤️*
*Bojuwa herbs*
*By*
*Surayya Dee.*
****.*
*Sanyi flusher!*
*Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.*
*Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*.
*Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.*
*Tightening set na hade mace ta dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*.
*Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.*
*Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.*
*Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.*
*Tuntubeta a wannan lambar*
*****
*Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.*
*Nation wide delivery*.
*HIJABS CORNER BY JANAFTY*
*Muna da Hijabai masu kyau da inganci, ɗinki cikin kwarewa da* *mabambanta design, muna aikawa da kayanmu ko'ina a Nigeria, muna maraba da masu siyan ɗaya ko sari.*
****, tuntuɓa ta wannan lambar*
*KADUNA/ZARIA*
*Page 2*
*A.S.KARGI ENTERPRISES*
_03:00PM_
Wani katon allo ne kafe da sunan A.S.KARGI ENTERPRISES akan wani katon Bulding mai girma da Fadi mai kama da wata alkarya guda Ginin yana Tsakanin kan Shararan Titin nan ne na Garin Kaduna wanda zai Dauke ke ka Shatalele har zuwa UTC sai dai Ginin Babban Ma"aikatan yana kan Titi ne kafin akai Utc.
A.S.KARGI ENTERPRISES babban Ma"ikata ce datayi suna kuma tayi Fice ma"aikata ne da ake Sarrafa Fata zuwa wani nau"in abun amfani da Bukatar kamar su jaka,Takalmi da sauransu.
Ma"aikatan Tana da Tarin ma"aikata kama Daga yan Gida Nageria zuwa ma"aikatan Kasashen Ketare sannan kayan su kaya ne mai inganci da Nagarta Tunda yawancin Kayan aikin su suna yin Odar su Ne Daga kasashen Ketare,A.s.kargi yayi suna sosai saboda Ingancinsu da Nagartasasu shiyasa kaf kasar Nageria ba wanda baisan da zaman kamfanin ba,Duk da wannan karamin ma"aikatan ne wanda D'a Daya Tilo Wajen ma mallakin Ma"aikantan ke Kula Dashi Shekaru Biyar da suka gabata Babban Ma"aikatan Tana garin Abuja Inda Alhaji Aliyu Sulaiman ke da Alhakin Kula da Ragamar wajen Sboda Jajircewarsa da kuma Saninsa kan abunda ya shafi kasuwanci suna da kyakyawan Hulda da Sauran Kamfanoni Saboda nagartansu da yadda suke Tafiyar da kasuwancinsu kan gaskiya da kwarewarsu kan abunda suka karanta uwa uba ga kyautatama kanana da manyan Ma"aikata.
Acikin babban Office din Dayafi kowani Office girma acikin ma"aikatar koda duba da yanayin yadda aka kawata Office din da komai na More Rayuwa kamar dakin mace kama daga Kujerun karban baki karamin Fridge,Tibin bango,A.c,cafet,harda karamin Tiolet in Bukatar hakan tataso.
Zaune yake Daga chan Karshen Office din kan Kujeransa na Iko Kansa na Duke ne yana Faman Rubuce Rubuce kan Tarin Fayel din Dake gabansa Sanye yake Cikin American Suit Baki da Fari ya Daure Wuyansa da Tek Tik baki,Fuskarsa Tana Duke ne shiyasa bata Fito sosai ba sai dai Sumar kansa Da Masu aski suka gyarata Daga ganin yadda Sumar take zaka Fahimci ma maamallakin Gashin baya son Tara suma in baya Cireta Duk Sati to tabbas yana Sansareta Duk bayan kwana Goma.
Agogon Fatan na kamfani Rado Dake Daure a Tsitsiyan hannunsa na Hagu yakai Duba,Karamin Tsaki yaja batare daya Dago kansa ba ya jawo Wayar Telephone din Dake gabansa ya Dandana Wasu Lambobi ya saka a kunni Jim kadan naji Wata Murya Cikin Zati da Haiba yana Fadin.
"Lazifa ki fadama Sani yaje makarantar su wasim ya Daukesu zuwa Gida....!
Daga haka bai jira abunda za"a cemai ba ya Sauke wayar yana dan kara gyara Zamansa Cigaba yayi da aikin dake gabansa Cikin gaggawa kamar wanda yake cikin sauri ko Hanzari.
Yaji Sanda aka Bude Kofar Office din nashi aka shigo bai batama kansa Lokaci Wajen Dagowa ba sanin kowaye Shi kadai ne ke shigomai Office batare da Sakatariyarsa Ta Kirasa ta Sanar dashi ba shi kadai ne ke Shigomai kai Tsaye ba iya Office ba Harta a Rayuwarsa kai Tsayen yake Shigomai.
SAIFULLAHI KARAYE,Aboki kuma Amini Guda Daya daya ke dashi aduniya shi da Saifullahi ba yan"uwa bane asali ma basu taba sanin juna ba sai baya baya nan sun hadu ne a awata Jami"ar Nottngham lokacin Dayaje Hada Degree dinsa na Biyu kan kasuwanci kamar yadda shima Saifullahi yaje sai dai sabanin shi da Mahaifinsa ya Turasa shi Saifullahi Tallafi ne Daga gwannatin kano saboda Hazakarsa da Baiwarsa yasa Gwannati ta Dauke Nauyin karatunsa Tunda suka Hadu suka Fahimci sudin sun Fito Daga kasa Daya Nageria kuma sun Fahimci gabadayansu Abunda yakai su ne agabansu kuma Dukkansu din ba baya ba kwari ne Wajen Sanin Abunda suke karanta har suka gama Karatunsu kunne Doki suke wajen Kokari da Hazaka.
Kuma bayan sun dawo Gida Shi yayi Sanadiyar Dawo da Saifullahi kusa dashi alokacin da Mahaifinsa ya Damkamai amanar kula da wannan ma"aikatan aransa yaji ba wanda zai Tayasa ko Tallafa masa ya cika Burin Mahaifinsa sai Saifullahi lokacin Da ya kai sa gaban Maimartaba da Mahaifinsa sun yaba dashi tun kafin ma su ga Takardunsa,sun zo ma"aikatan sun Hada hannu da karfi Shi amatsayinshi na Shugaba Saifullahi mataimakinsa Cikin Shekaru Biyar sai gashi sun Zarce Tsara acikin Tsararrakinsu Ma"aikatansu ta samu Cigaba da Riba mai yawan da ba wanda ya Taba Tsammani hakan yasa Saifullahi ya Zama Dan gida kuma dan Dangi acikin Tarin iyalan Maimartaba Sarkin Kargi.
Yana jinsa ya zauna kan Kujeran Dake Fuskartansa ammh bai sa ya Dago Daga abunda yake yi ba Saifullahi ya kallesa sosai yana so ya Fahimci meke Damunsa Saifullahi Dogon Namiji ne mai Zati da haiba daka gansa kaga Bakanon Daya jiku da Wahala da Neman na kansa.
Gyara zamansa yayi kafin yayi gyaran Murya yana Fadin"Agogo baka ji Shigowata bane..?
Kansa na Duke kamar bazai tankasa ba sai chan yace"Naji..Sai yaya..?
Yafada Cikin Dakakkiyar Muryansa mai Cike da Zati da Haibarsa na koda Yaushe.
Saifullahi ya shafa dan gemunsa Daya Tara kamar na Rashin kunya yana Kokarin Danne Dariyansa yace"Yau ma kace Antyn taka ta bata maka Rai kenan kafin ka fito..!?ko aiki ta sakaka ne Dan kaninta..?
Yafada yana kokarin Danne Dariyan Dake neman kwacemai,Bai Dago ba kuma bai yi mgana ba illah Dakatawa da yayi da Rubutun da yake yi saman wani Fayel na dan Lokaci kafim ya cigaba Lokaci Daya yana Taune lebensa na kasa Daga gani mganar ta sosai inda kemai kaikayi.
Ganin yayi banza dashi bai ce komai ba yasa ya kara fadin"To ni dai Allah ya Huci Zuciyarka..Antynmu bata kyauta mana ba Haba don Allah sai ta Rika bata maka rai haka ake Rayuwa Fisabillahi..!?
Yafada yana yar dariya kadan Kamar bazai ce komai ba sai kuma ya Tattara Fayel din gabansa ya Rufe Lokaci Daya Ya Turesu gefe ya Dago da kansa da kyau yana kallon Saifullahi Dake kokarin Danne Dariyan Dake Cinsa..!
Cikin Danne giransa tare da Tattare naman goshinsa yace"Saifu an taba Sharara maka mari..?
Saifullahi ya waro ido yana Fadin"Mari kuma KARGI..?
Yafada yana bayyana Razanansa da mganar wanda aka Kira da Kargi na Kallah daidai Lokacin daya Mike Tsaye ingarman jikinsa na kallah Cikakken Bahaushe kuma Bazazzagi Domin ga Tsawon da Girman nan na asalin Zazzagawam da suka Fito Daga Taatson Kargi ta Fanni Uwa da uba.
Bakin Namiji ne mai cikar kamala kyakyawan ne sosai domin ya Dace da Tsararriyar Fuskarsa mai Dauke da Manyam Idanuwansa da matsakaicin Hancinsa ba bai cika Tsawo ba yana da cikar gashin Gira dana Ido sannan Yana da Manyan idanuwa masu Saka ma Duk wanda ya kalla dasu mazari masu Daukeda wani kyalli acikin su.
Fuskarsa Tana da dan Fadi kadan inda ta Dace da Bakinsa dan karami Tattausa kamar baya tauna abu dasu sai Zagayen Sajensa Daya Zagaye Bakinsa dashi wanda ke karamai Kwarjini da Haiba da kuma Zati Hade da bayyana Natsuwarsa akoda yaushe.
*SULAIMAN ALIYU SULAIMAN KARGI* wanda aka fi sani S.A KARGI Amtsaayin Managing Daractor na Kamfanin Mahaifin nasa Wato A.S.KARGI ENTERPRISES,shine D"a na Farko Kuma Namiji kwara Daya Tal Cikin Jerin ya"ya goma da Allah ya bama Alhaji Aliyu Sulaiman Kargi Kuma Shime maso soyuwa Wajen Mahaifiyarsa Hajiya Zabba"u kuma Shalele ne sanyin Idaniyan Duka Dangi ne kuma Saraki ne wajen Wanda yaci Sunansa Wato MAIMARTABA SULAIMAN SARKIN KARGI wanda shi ya Haifi Mahaifinsa Alhaji Aliyu Kargi Daya kasance da na Hudu ajerin ya"yan da Allah ya azurtama maimartaba dasu.
Kuma Uba yake ga Tilon ya"yansa WASIM da WAFIYYA da Sanyin Idaniyarsa Masoyiyarsa da har yau har gobe bai Daina Kukan Rashinta ba.
Sai da ya isa Fridge din ya Bude ya Dauko Ruwa mai sanyi ya Bude ya sha Rabi kafin ya maidashi Inda ya Daukosa,Ya juyo yana Sauke Nunfashi Sama sama Lokaci Daya yana Fadin"To ka iya bakin ka Tun kafin hakan ta Faru dakai..Wlh zan iya marinka lokaci Daya na Hada maka da manyan Ashariya in baka iya bakin ka ba In kana ganin bazan iya ba Just Tary me an see..!
Yafada Lokaci Daya yana zama kan kujeran Ikon Daya tashi Saifullahi ya Jinjina Kai kafin yace"Zaka iya Allah ya Taimaki Saraki..Ammh dai kasan Zagi bai Dace ga jikan Sarkin Kargi ba ko..?
Karamin Tsaki yaja yana Fadin"Sai dai Sarkin Karaye..!
Saifullahi na Dariya yace"Abun har da Zagi ne..?
Sulaiman ya Muskuta Lokaci Daya yana Kokarin Rage Tamkewar Tek tie din Dake Wuyansa yace"D"ansu yaja musu..Ka iya bakin ka in kana son tsira da Mutumcinka..?ya batun Ganawar mu da kamfanin Dasuki Ventures..?
Saifullahi yace"Shigowata fa mganar ta kawani..Sun nemi mu saka musu Ranar da zamu zauna Meeting din..!
Kai Tsaye sulaiman yace"Ka gaya musu Ranar Monday..Zamu Hadu dasu a inda na Fadamaka..!
Saifillahi ya Jinjina kai kafin ya samu Zarafin mgana Wayar Sulaiman Dake gabansa ta Dauki karan neman agaji.
Daga yanayin yadda yayi sanda yaga sunan mai Kiran Saifullahi baya Bukatar wani karin bayani yasa Cikin Dan Tausasawa yace"Hala Hajiya ce..!
Dakai Sulaiman ya amsa mai Yana kokarin Gyara zamansa Kafin ya Daga Wayar Hajiya ai bata Kiran banza Shi fa ba Domin kada yayi Sabo ba Dayace Kiran Hajiyarsu kaf bana Alheri bata Kiranka sai da wani abu babba ko Mutuwa ko kuma ta Kira ta Fadamaka abunda zai hanaka sukuni Hajiya Zabba"u Jarumar macece kamar mijinta a tsaye take kan Mijinta da ya"yanta bata Daukan Reni ko Kadan.
Dakyar ta samu amsa Sallamar Daya Rangadamata yana kokarin Gaisheta ta katse shi Daga chan bangaran.
"Ba gaisuwarka na Kira naji ba Saraki.."
Tafada cikin Kaushinta akoda yaushe Ido ya Runtse kafin ya Bude Cikin Tautausawa yace"Meya faru hajiya..?
Cikin bayyana Bacin ranta tace"Yanzu nayi mgana da Samira ta Fadamin Tunda wannan Tsohuwar guzuman matar taka ta Fita Jiya da Daddare da sunan Zuwa wajen aikin da take Fadi har Yanzu Karfe uku na Rana ta wuce Saraki bata dawo ba kana Sane da hakan..!?
Ta tambayeshi Cikin Kaushin Murya a muryanta sam ba wasa ballatana Sausauuaci.
Miyau ya Hadiye dakyar yana kallon Saifullahi Dashima yake kallonsa Shifa Daman yasan Za"a Rina ba abanza Hajiyarsu ta turo Wanan Munafukar Samarin ba Shifa Daman Tun Sanda ta bashi Umarnin ya Tura Sani Direbansa ya Dauko mata ita Daga Kargi wajen Fulani yasan Za"a Rina C.I.D hajiyar ta sakamai agidansa Saboda ta Rika samun Labaran abubuwan Dake Faruwa ai shi ya Shiga Uku ya Kade har ganyensa gashi Abba baya nan ya Tafi Lagos kan ganawa da wasu kamfonin da suke son saka Hannun Jari da kamfaninsu.
Sumarsa kansa da aka Saisaye ya shafa kafin yace"Bansani ba Hajiya Tun safe ina Office..!
Cikin Fada tacigaba da Fadin"To daman ina zaka sani..?tunda aka Dauki wacce bata dace dakai ba aka likamaka Saraki..Samira ta Fadamin koda yaushe ta Fita aiki sai sanda Taga Dama take dawowa ita ke auran kanta ko kai ke auranta..?ina da list din Duka Shedule din aikin su na asibitin Datake aiki In aikin Safe gareta 2pm na rana suke mika aikin ga masu zuwa yammah in na Rana ne karfe 6pm zata mika aikin ga masu Aikin Dare in kuma aikin Dare gareta Karfe 7am na safe zasu mika aikin Ga Ma"aikatan Safe na Ranar ammh ita sai Ta kai wani Lokacin kafin ta dawo Cikin Gidan Bata wani abu da Zai Nuna tasan Ita Matar aure ce!
Ta karishe Fada Cikin kumfar baki to me zai ce..?Koshi Da yake Mijin nata ai baisan komai game da ita kanta ba. ballatana aikinta ammh Hajiya Har komai ma ta sani Lalle nema.
Bai da tacewa Illah "Hajiya kiyi Hakuri don..!
Bai karisa ba ta katseshi Cikin Tsawa Tana Fadin"kada ka kara cemin nayi Hakuri Saraki..Abaya na Dade ina Cijewa da kalmar Hakurin da Mahaifinka da Maimairtaba suke Jinginamin ammh banda yanzu..In abaya nayi Hakuri ka Zauna da Sunaira Ta Chanchanci hakan ne..Ammh Wlh Tallahi kaji na Rantse maka Saraki wannan karon bazan zuba ido na bari akara Salwarta da Rayuwar D'ana ba.Tunda Iyayenka suka Aura maka wannan Tsohuwar bada izinina da Shawara na ba nayi Shuru bazan ja da mganarsu ba sai dai ka sani wannan karon Mutuwa ce kadai Zata katangeka Daga Auran LAILA..!
Tana gama Fadin haka bata jira cewarsa ba ta Datse kiran Tana Faman Cigaba da kai kawon Datake yi a Tsakar Kayattacen Bedroom din nata Atsaye take domin a kallah Farko in kayi mata zaka Fahimci haka Jin Dadi da Hutawa sun Boye shekarunta sai dai kana ganinta kasan bata da Rauni kuma tana da matukar Jajircewa.
Hajiya Zabba"u Aliyu Kargi kenan Mata ta Farko kuma Uwargidan agidan Alhaji Aliyu Kargi wacce ake kiran da Hajiya Tana da abokiyar Zama mai suna Falmata ita din yar Maiduguri ce Aliyun ya aurota Daga baya wacce kowa da kowa ke kiranta da Hajiya karama.
Har ta Datse kiran bai Dauke Wayar Daga kunnensa ba,Mganar ta gama Shigarsa ita kemai amsa kuwwa acikin kunnuwansa.
Saifullahi ya kallesa Cikin Nazarinsa kafin yace"Me Hajiya tace Kargi..?
Haka suke kiran juna wani Lokacin da sunayen garinsu asalinsu.
Sai Lokacin ya Sauke ajiyar Zuciya Lokaci Daya ya Sauke Wayar daga kunnensa ya kalli Saifullahi yana Fadin"Hajiya tasan komai..Infact ma Wannan yar aikin Data saka aka Daukota Daga Kargi yar Leken asiri ce ita take kira Tana Fadamata Halin da ni da Gidana muke ciki can u juzt Imaging Hajiya tasan Harda Lokutan aikin Yarinyar nan mai Son girma fa..!
Saifullahi ya gyara Zamansa yana Fadin"Ba abun mamaki bane..In Hajiya tasan hakan sai me kuma tace..?saboda nasan ba shikenan ba..!?
Sulaiman ya Furzar da iska Daga bakinsa kafin yace"Tace min in tayi Hakuri a baya Lokacin SUNAIRA yanzu bazata Saurari kowa ba..!
Saifullahi yace"Uhm ina jinka..!
Sulaiman ya Runtse ido kafin yace",Ta gayamin ta kara gayamin bayan ta Rantsemin.._Mutuwa ce kadai Zata gatangeni daga Auran yarinyar nan LAILA.._!
Saifullahi ya kuramai ido yana kallonsa na dan wani Lokaci kafin yace"Daman ai kasan haka Zata Faru..Nidai kai mun sani Shurun hajiya baya na nufin ta Hakura bane..Kuma ita kanta Lailan koran manemanta da Rushe auranta da dan Wajen Baba Lawali ai kai take jira..Ta kuma san Kila a wannan gabar Zatayi nasara..Duk da Lokacin Marigayiya Sunaira ta rasa wannan damar..Banda wannan karin Damarmaki ne a abude Sulaiman bama Dama Daya ba..!
Kamar allon magiji haka Sulaiman ke kallomsa Kafin yace"Na sani Saifullahi..Nasan haka zata Faru..!
Saifullahi yace"Ina mafita..?
Sulaiman ya Taresa da Sauri yana Fadin"Babu mafita...Bazan iya auran Laila ba Wlh bantaba kallonta da wani mtsayi face kanwata kamar su Sadiya take..!
Saifullahi yace"Auranta shine mafitanka..Hajiya bazata Tsaya ba..Kuma ina ganin a wannan gabar Ko Abba da mai Mairtaba bazasu iya Tsaidata ba..!
Sulaiman ya Tallafe kumatunsa yana Fadin"Tabbas..Domin Maimartaba ya Fadamun zuwa na karshe wajensa..Na Lallaba Hajiya sun kara mata Laifi akaro na Biyu..na Tabbata wannan karon ko su bazasu bijera ma Bukatarta ba..!
Saifullahi yace"Nima nayi Tunanin haka..Sai dai akwai Hanya guda Daya da zata Kubutar dakai..!
Da Sauri Sulaiman yace"Fadamin ita Saifullahi..kasanni kasan Tsarina Wlh bazan iya Zama da mace Fiye da Daya ba..Tun bayan Rasuwar Noory na Fidda Rai da aure saninka ne nima fa su Maimairtaba ba Shawara dani sukayi ba wajen auramin yarinyar nan ba..Inda sun Fadamin nan take zan Gayamusu bamj dace da juna ba,ba Daya suke da Norry ta ba Hallayarsu ba Daya ba Ta Kowani bangare suna da Bambamci nasan in baka manta ba yarinyar dana bama Shekaru Hudu aduniya Da kunninka da kunnena Ranar da Sunaira ta Cika kwana arba"in aka Daura mana aure Abba ya Mtsa mu shiga mu gaida Inna munji Sanda Take Fadan taya y Kaddara Zata kaita auran wanda Take gogayar Shekaru dashi..!take kallonsa mtsayin kaninta..?ni ne wai Yarinyar nab da son Girma Zata kalla tace kaninta.?
Ya karishe Fada yana nuna kansa Cikin Bacin rai.
Saifullahi yace"Coool Down..Tunda munsan Tana son Girma..mu Barta da Girman kai ka zauna akanin nata mu samo mafita..Ka Daidaita da matarka Sulaiman..Kila Faruwar haka ya Rufe Damar da Hajiya ta samu ayanzu Wajen Tusa maka auran Laila..!
Wani irin kallon kama Rainamin Wayau Sulaiman kemai kafin yace"Ni in zama kaninta..?Bansan kana shan kwaya ba sai yau Saifu..!
Saifullahi yace"Tare muke shan..Kai bakasan abun arziki ba kankantar zai makale maka ne..Kai da in kuka Hada kanku da girman nata da komai Zaka Lamkwasata ta koma kasanka sai yarda kayi da ita Namiji ne fa kai Duk Girman kanta tana da Zatin Ka ne..?ta isa taja da Namiji..!duk kamewarta ai Mutum ce Tana da Kwayoyin Halitar Bukatar Namiji atare da ita..!
Tsaki Sulaiman ya saki kafin yace"Ni da ita?ko ka manta Yayar matatace Sunaira..?
Saifullahi yace"Nasani..!
Sulaiman yace"Kuma kake fadin na je na Nuna mata Girma na..Hala ce maka akayi ni yanzu ma ina da wata Sha"awa ne...Mtseww Tun bayan Rasuwar Noory komai ya Tsayamin kamar tatafi da duka kuzarina ne..!
Saifullahi yayi Dariya yana Fadin"Yanzu Sunaira ta Shude a Rayuwarka Sulaiman..Sunaima itace K'ADDARANKA yanzu..!
In kana son komai ya Daidata sai ka Bude Zuciyarka da Hannayenka ka Rumgumi kaddaranka..!
Sulaimam ya juya kawai kujeraansa na Iko Tana Juyawa dashi Bayason ma ya karajin mganar Saifullahi domin abun bama mai yuyu bane,Yarinyar da ta gama Rainasa wai kaninta..?agidan Ubanta ya zama kaninta tasama ya Kunduma Baba zagi..Shekaru hudu ya bata ammh Tana mai kallon kasa da ita Gata da Girman kai sai abunda Taga Dama take yi ba Tun yau ba yasha Jin Noory tana Complain kam Taurin kan yayar nata Tun Tana da Rai alokacin Tabe baki kawai yake acikin Ransa yana Fadin Duk wanda ya aureta shine za"ayi ma Jaje ashe ashe Alokacin Zanen kaddaransu yana Hade gashi yanzu shine acikin Jajen Tsumutsumu.
Kafin Saifullahi yayi niyar Bude baki yayi mgana Sakariyar Sulaimam Lazifa ta Bude Kofar Office din ta Shigo da sallama Saifullahi kadai ya amsa mata Cikin Ladabi ta Ramkwafa Tana Fadin"Ranka ya Dade..Sani Direba ne yazo yana son ganin Yallanbai..!
Jin haka yasa bai jira cewar Saifullahi ba ya Juyo yana Fadin"Send Him in..!
Kai ta Jinjina kafin ta Fice Tana wani Taku Daya bayan Daya Dukkansu da kallo suka Bita Saifullahi ya Dagamai gira yana Fadin'Ga wata fa..In Laila bataa maka ba,sai ka Raka da Sakariyarka da nasan ka Dade da Fahimtar she is in love with u..!
Sulaiman ya Tattare Fuskarsa kamar yaga kashi kafin yace"Jira nake ta kasa Hakura ta Furta..She wil Fired aranar Wlh..!
Yafada yana Bubbuga kafarsa saman Tattausan Cafet din Dake Office din Dariya Saifullahi yayi daidai Lokacin da Sani amintattacen Direban Sulaiman ya shigo matashi ne mai jini ajika Dukawa yayi yana gaishesu Saifullahi ne kadai ya amsa banda Sulaiman daya katse shi da Fadin"Ina su Wasim..?ina fatan ka kaisu gida ka Damka su hannun Magajiya..?
Yafada yana Duba agogon Hannunsa ganin Har La"asar ta Kusa.
Sani Cikin Sadda kai yace"Yallabai koda naje na Iske Antynsu tazo Daukansu nayi nayi ta bari na kaisu Gida Taki yarda Daga karshe ita ta bani Umarnin dawowa kamfani ita kuma ta Daukesu suka wuce gida..!
Tunda ya Fara mgana Sulaiman ke kallonsa Yana Jin bacin ransa na Karuwa Cikin Dan Sauta Murya yace"A ina ta Dauke su Sani..?
Cikin dan In ina yace"a..Adaidaita Ranka ya Dade..!
Mikewa yayi a Fusace yana Buga Teburin gabansa da karfi sai da wasu Fayels suka Zube a kasa Lokaci Daya Cikin Hargowa yake fadin"Wani irin iskanci ne wannan sani..?kamata a rika Yawo da ya'yana acikin adaidaita duk Tarin arzikin dana mallaka..Kana sane ba iya wannan ma"aikatan ba Ina da Kamfanin Sarrafa Madara na S.A.KARGI YOGHOURT, AND FURA dana gina shi da gumina ace duk tarin arzikin nan nawa ya"ya na suna yawo acikin Adaidata sani kana ganin kamim adalci kenan..?
Ya karishe Fada Cikin bayyana Bacin Ransa Sani Cikin rawan jiki yace"Wlh Yallabai nayinayi da ita ta shiga na karisa dasu gida taki yarda..Tace na dawo kamfani kana Bukata ita zata karisa dasu..!
Sulaiman ya watsamai wani kallo yana Fadin"Wato itace ma mai baka Umarni..?ita ta Dauke ka aiki ne Sani..?nace ita ke Biyanka albashinka Duk wata ko ni..?
Sani da kansa ke kasa Cikin Rawan jiki ganin megidansa nasa cikin Bacin rai yace"Amin afuwa Ranka ya Dade..Naga Antyn suce..Kuma Hajiya fa Matarka shi..!
"To hell with Hajiya..Da Anty su din Gabadaya sani bar gabana kafin Raina ya baci na zageka Wlh..Har kai zaka Fadamin matatace..?kafini sanin haka ne..?
Nace kafini sani ne..?
Yafada cikin Hargowa har yana kokarin baro inda yake zuwa gaban sani Da sauri Saifullahi ya Mike ya kalli SaniDake Durkushe yana Fadin"Allah ya huci zuciyarka Ranka yallabai ayi hakuri..!
Hakurin Dayake basa ji yake kamar yaa Mangaresa Hararansa kadai yake yi ganin haka yasa Saifullahi kallonsa yana Fadin"Sani tashi kaje abunka..Jeka Jirasa a waje..Wannan Fushin ba naka bane..!
Da hanzari sani ya Mike ya Fice yana Sauke Numfashi da Oga Saifullahi ya Kwace sa da yau megidansa nasa ya Zazzagamai na Zazzagawan nasa.
Yana Fita Saifullahi ya juyo kan Sulaiman Dake faman kokuwa da bacin Ransa yana Fadin"Ina Ruwan Sani da zaka rufeshi da Fada..?umarni ta basa kuma yabi..In kana son gaskiya kamar yadda Zaka bama Sani Umarni yabi haka itama Zata bashi..kuma bakaji me yace ba Antynsu ce fa?kaima in da kara ai Antynka ce..!
Yafada yana Danne Dariyansa Sulaiman ya Juyo yana kallonsa aransa yana Daidaita manyan Ashariyan da zai Shimfidama Saifullahin ne.
Saifullahi Daya Fahimci haka sai ya Daga hannu yana Fadin"Nifa kadaina kalloma haka..Tattara wannan Angry din naka ka bari in ka koma Gida Antnynka nachan na Jiranka..!
Sulaiman bai ce komai ba ya wuce zai shiga Tiolet din dake Office din Saifullahi na Dariya yace"Yauwa Kargi don Allah ka siya adaidata Tunda naga Anty naka tafi kwarewa ahaawanta sai ka Daukan mata Direba Shikenan ba damuwa acikin haka..!
Sulaiman kamar bazai Tsaya ba sai kuma ya Dakata ya Juyo Fuskarnan Tamau yana kallon Saifullahi kafin yace'"Baka fahimta ba..Aini ya"yana na Damu dasu..Ba ita ba..Ba adaidaita ba ko bayan a kori kuran awakai zata shiga ko akwalan Dan mutanen Kargi..!
Daga haka ya Tura Kofar Tiolet ya shigo ya bankota da karfi yabar Saifullahi da Dariya shima Ficewar yayi zuwa nashi Office din yana Faman Tunanin yaushe ne Kargin nasa zai Daina Gujema kaddarasa Daga shi har Sunaima din..?
Yana ji ajikinsa Kaddaran Data Hadasu mai karfi ne da bazata Rabasu Cikin Sauki ba..!
*******
*A Daran...*!
_7:00pm_
Area:Malali Gra kaduna..!
Ta fito katon Haraban Gidan kenan tana Kiciniyar saka Dogon Hijabin Data ke Sanyawa Tana Rufe Jikinta In zata tafi wajen aiki ta makara kamata yayi Tun 6:pm tana asibiti ammh Rigiman Wafiyya yasa bata samu Damar Tafiya akan Lokaci ba
Yau Wafiyan tana jin Rigima ne Tunda Ta Daukosu Daga makaranta suka Dawo Gidan ta yi musu wanka ta basu abinci Wasim yana ta wasansa bayan ya gama ta kunna musu Cartoon suna kallo Banda Wafiyya Dataki barinta ko nan da man chan in Tiolet zata shiga Tana Biye da ita in kuma Tace Zata ijiyeta sai ta Fara kuka.
Ta Tattaba Jikinta ba alanun Rashin Lafiya tasan rigimar ta ce tatashi,Yau din Anty take da ita sosai haka ta Nanike mata yarinyace yar shekaru uku duk inda ta saka Kafa Tana Rike da ita Tana Kiran sunan ta Anty.
Wasim shi ya fita wayau shekararsa Biyar da wani abu shiyasa bai Cika Rigima ba Tunda ta dawo suna Dakinta bata Fito ba Abinci ma Magajiya ce ta Biyosu dashi Kuma har Lokacin bata Huta ba Tana Wahala kan yaran ko kayan makarantasu Data wanke a compound din Tsakar Gidan Wasiyya kin yarda da tayi Magajiya ta Riketa tayi Tare sukayi wankin Duk ta Jika Jikinta Sai ta gama ta sunkuceta sukayi Dakinta Tana ganin Sabuwar mai aikin da akawo Daga Kargi Samaira Tana Lekensu bata bi ta kanta ba daman ita Tun zuwan Samira bata yarda da ita ba tasan akawai manufar zuwanta bata taba Bita kanta ba Tana jira wata Rana ta Shiga Gonarta ne ta gane bata da wayau.
Allah ya taimaketa bayan ta mata wanka ta bata madaranta Sai ta samu Barci itama wankan tayi a gurguje ganin ta makara ta gama Shiryawa kenan Wasim ya kawo mata Tarkacen Homwork dinsa na makaranta bazata iya Ture Aikin ya"yan nata ba yasa ta Zauna ta koyamai tare sukayi aikin basu barta ta Fita ba sai da ta Kira Magajiya ta Dauke hankalin Wasim kana ta Fice Jaka a hannu Hijabi ma haka ko Sallar mangariba bata yi ba ta bari sai ta isa asibitin tayi achan Tunaninta Daya na yadda Zata samu abun Hawa a wannan Daran
Tana Fitowa da Samaira ta Fara Cin karo kamar wacce ke gadin Lokacin Fitarta,tana kuma ganinta ta koma Cikin Dakin da aka Sauketa Tun zuwanta Sunaima ta tabe baki bata Damu ba ta Fice zuwa Haraban Gidan
Sai da tagama Daidaita kanta kana ta Karisa suka gaisa da Megadi ya Bude mata karamar Kofa ta Fice yana mata Fatan dawowa Lafiya Lokaci daya yana mamakinta Duk Tarin Motocin Dake Haraban gidan Tunda yake da ita Tun kawota gidan amtsayin matar yallabai bai bata ganinta a Mota ba sai dai adaidaita,Gaskiya hakan ba Dacewa bane Tunda Yallabai yana dashi hakan kamar bata sunan Asalinsa ne da nasabarsa.
Sauri take ta Zabgawa ganin anguwan tsit daman ai haka take ba Jama"a,Sai Wurgar Manyan Motoci na alfarma bama Adaidaita balle ta saka Ran hawa ta isa da wuri daman in ta samu sai dai da Rna in sun shigo da pasinja ammh ba irin wannan Lokacin ba.
Tafiya take yi har tayi nisa Gajiya Tayi ta Dakata Tana kallon Siririn agogon mata na gayu Dake Hannunta 7:20pm har ta wuce kanta ta Dafe Tana Tunanin mafita domin tamakara yau bataje wajen aiki kuma batasam Wani Lokacin zata bata kafin tasamu abun hawan ba.
Yana gaban Motan yau bai shiga baya ba Ransa ne abace yasa kwata kwata baya Cikin natsuwarsa Wayarsa yake Tabawa Hankalinsa baya saman Hanya Sani kuma na Faman Tukinsa Cikin kwarewa.
Sun karyo kwnaar Layin Kayattacen Gidan nashi Ya Dago kansa yana Fadin"Sani wai ba mai amotar ne da kake Tafiya sannu sannu..?mintinmu nawa da baro kamfani har yanzu bamu kawo gida ba..!
Yafada daidai Lokacin da Idanuwansa Cikin Haskem Lantarkin Daya Zagaye ko"ina na gidajen Dake wajen ya Haskomai Fuskarta Tana Tsaye Gefen Titi Tana gyara zaman jakarta Tana kuma kallon Titi sosai kamar tana Jiran wani abu.
Wani Takaichi da Malolin abu ya Taso ya Rufeshi Daman yana Cikin Bacin rai sai ta karamai har bai ji sanda Sani ke faman bashi hakuri ba.
Bakincikinsa Daya sai an dangatashi da ita In banda Salon Cin Mutimcin mene wannan..?yarinyar nan ba karamar mara Mutumci bace ya gama Lura da ita Tsaf.
Dauke kansa yayi kamar bai ganta ba Har suka Gotata Sani Ne ya ganta sai yadan Rage Gudun Motar yana Fadin"Yallabai kamar fa Hajiya nagani Tsaye bakin Titi..!
Wani kallo Sulaiman ya sakarmai Dayasa ya Take Motar bai Shirya ba.
Hon Sani ya Zuba Megadi ya taso ya Bude get din suka Sulala Ciki kusa da Mota Kirar 4matic suka Tsaya Ko Jira bai yi abudemai ba ya Bude da kansa ya Fito ko kafin megadi ya kariso yana gaishesa ya Rika ya Bude Gidan baya ya Dauko karamar Jakar Briefcase dinsa da Madaran youghourt na kamfaninsa a leda da Tambarin kamfanin,Dazu kafin ya baro kamfani yayi ma Habib waya manager sa mai kula da Kamfanin nasa yace ya bama Daya Daga Cikin aget dinsu ya kawoma Madara DA Fura Office guda Biyu ya Dauki Daya ya bama Saifullahi Daya domin duk kwanan Duniya bai kwamciya bai sha Madaran nan da Fura ba.
Sama sama yake amsa gaisuwan na Auwalu maigadinsa kafin ya Fara Taku zuwa Kofar da sadasa da Babban Falon Gidan nashi Sai kuma ya tsaya Cak kafin ya Juyo yana kallon Sani Cikin Kaushinsa yace"Kaje ka Dauketa...!
Sani Dayaji abun kamar Daga Sama yace"Ita wa..?
Hararansa Sulaiman yayi kafin yace"Bansani ba!
Yafada yana juyawa ya Cigaba da Tafiya Sani kansa ya shafa yana Dariyan Dramansu da ogan nasa ai ba yau suke Tare ba yasan Halinsa Ciiki da bai
Juyawa yayi ya shiga Motar ya sake Ficewa Daga Gidan Tana nan inda suka Barta bata samu adaidaita ba Agabanta ya Tsaya kafin ya Sauke Glass din Motar yana Fadin"Hajiya barka..Shigo muje..Yallabai yace nazo nakai ki..!
Tsam tayi tana kallonsa Yallabai.?
Dazu fa ta gansu sanda suka wuceta Domin ai ta gane motar bakar Prado ta Zamani ganin basu nuna sun ganeta ba yasa ta kauda kanta da ace Tana da wani Zabi bazata shiga Motarshi ba ammh Tuna bata dashi yasa ta Bude Gidan gaba ta Zauna Tana cema Sani Tagode Daganan bata kara mgana Har yakai ta Bakin asibitin tace ya Dakata ta Sauka wannan Shine karonta na Farko Data Taba Shiga Motar tasa.
Shi kuwa yana Taka Kafarsa da bakaken Sawun cikin Takalminsa na Fatar daminsa yana ayyanawa aransa "Ko bakomai Saboda Noory..Ammh ba Domin Halinta ba..!
Haka yake fada har ya Taka Matattakalan Hawan saman Bene Inda Jerin Dakinsa yake Tun a baya kafin Rayuwa da kaddara ta Juya Da rayuwarsa ahaka.
*Bojuwa herbs*
*By*
*Surayya Dee.*
****.*
*Sanyi flusher!*
*Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.*
*Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*.
*Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.*
*Tightening set na hade mace ta dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*.
*Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.*
*Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.*
*Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.*
*Tuntubeta a wannan lambar*
*****
*Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.*
*Nation wide delivery*.
*Janafty*