💦BARIKI TAFI GIDA 💦

Chapter 1️⃣

by @aishayakubuahmad811

💦BARIKi TAFI GIDA💦



writer✍️ 
Aisha yakubu  Ahmad







Bismillahir rahmanir raheem 💧









page1️⃣












ASHNAH POV……. 









Zaune take tayi tagumi ta kurawa jaririyar da take hannun ta idanu tana zubar da hawaye, tayi nisa a cikin tunanin da take yi , dan tayi nisa acikin tunani wanda batasan lokacin da hawaye yake zubowa daga idonta bah, tana tuna baya, kuka ta sake fashe wa dashi, tana cewa me yasa , me yasa Ahmad ya mata haka , me ta masa da ta chan chan ci wulakanci , indai wannan ce soyaya to bata fatan ta sake soyayya a rayuwarta, tama cikin wannan tunani aka banko kofar dakin da take zaune, “ ina  kike mara mutunci “ wani mutumi ya fada wanda a shekaru ba ze wuve shekara 47 ba , amma saboda wahalar rayuwa idan ka ganshi zaka yi tunanin ya bawa shekara 50 baya. 

Dogo ne ba laifi fari ne sol kana ganinsa kaga mahaifin yarinyar da take zaune tayi tagumi tana zuba kuka , “ baba dan allah kayi hakuri kawai take cewa duk uwar masifar da yake surfawa, wata mace ce ta shigo ɗakin tare da zubewa tana ƙara bashi haƙuri , ammma ko kallon ta beyi bah, kana ganin ta kuma kasan mahaifiyar yatinyar ce saboda tsananin kamannin da suke yi da juna, akalla zata yi shekaru 35 da biyar , duk ita fatar ta duk ta koɗe alamun tana shan wahala amma hakan be hana bayyanuwar kyawun matar bahh, bude baki tayi zata sake bashi haƙuri yace, “ idan kika sake kika sake cewa tak anan to a bakin auren ki “ jin haka ya saka yarinya da ke kuka cewa , “ Ummi dan Allah kar ki ƙara magana , kuma yanzu zan bar gidan kamar yanda baba ya buƙata , amma dan Allah karki bari sanadiyya ta auren ki ya mutu zan bazan taba yafewa kaina bah “, tana gama faɗin haka tashiga haɗa kayan ta , zani ta ɗauka ta goya jaririyar sannan ta saka hijabi , miƙewa tayi zata fita  , har ta kai kofa sai kuma ta ɗan dakata ta juyo ta karewa gidan kallo kafin tasaka kai ta fice a gidan , mamanta na kiran ta “ Ashnaahhh, Ashnahhhh………………🥹




Ku biyo ni domin jin yadda zata kasance 




Daga alƙalamin ✍️
AISHA YAKUBU AHMAD