HASKE A DUHU

60

by @hijjartabdoul06

**********Daddy na zaune ya yi shiru komai baya yi masa daɗi. Kawai de gashi nan gashi nan ne yana zuwa office amma be san abinda yake yi ba. Yana zaunen nan Fa'iza ta shigo ta yi shirinta tsaf zata wuce office.

"Dad kuɗi aka ce wai ka dena bani. Na je wurin accountant a bani yace ba haka ba".

Kallonta ya yi batare da yace mata komai ba. Sai ya watsar da ita ya cigaba da abinda yake yi na kallon jarida da kuma shan tea. Mug ɗin ya ɗauka ya kurba ya ajje.

"Daddy magana nake yi maka, kuɗi yanzun nake so, account ɗina ya yi ƙasa".

Laura ta shigo tana kallonsa sannan ta kalleta. Sai kuma ta kalla Mami dake zaune tana lissafi ita kuma.

"Alhaji wai kana ji Fa'iza na yi maka magana?

Mami ta ce, "Kamar de baki san abinda ake cewa ba ko? Ina sati biyu da suka ce aka ce maki ga abinda Fa'izar ta yi".

"To sai ka yi me kenan?

"Sai aka yi me kike tambaya?

Mamin ta faɗa cike da mamaki tana kallonta. Tsaki ta yi kawai, tana kallon Alhajin.

"Na ce baka ga Fa'iza tana magana ba ne ko me?

"Ka yi mata abinda take so, shine magana, kana da kuɗi idan baka bawa ƴar ka ba me zaka yi".

Daddy kallonsu ya yi daga ita har ƴar na ta.

"Daddy please".

Ƙafa ɗaya ya daura akan ɗaya yana jingina da jikin kujera bayan ya naɗe jaridar hannunsa.

"Shi wannan yaron da kike so. Ina kika san shi? Ya aka yi kuka hadu? Daga ina yake?

"Daga rana irin ta yau, kada na sake ganinki kin sa ƙafa kin fita a cikin gidan nan. Ni ba uban banza ba ne, ba kuma uban da zai bari rayuwar yar sa ta lalace ba ce. Kuɗi ya sa bana kula da tarbiyyarku, neman kudi yasa ban damu da ku ba sai de kawai na baku ku kashe. Na barku da uwarku, ashe itama bata san abinda take yi ba.....

"A'a Alhaji idan ban kula da ƴa ta ba, da waye zan kula....

Tashi ya yi tare ka daka mata tsawa kamar zai dake ta.

"Ni kike faɗawa haka?

"Ina faɗa kina faɗa?

"Ni ka ke yiwa tsawa haka?

Itama ta faɗa tana nuna kan ta. Jinjina kai ya yi sosai yana kallanta.

"Ka ga Alhaji, tunda waccar abar ta shigo gidan nan shikenan ka dena min abinda nake so, ka dena so na. Kawai ka sallame ta koma inda ta fito, tunda de...

"Sa'ar kike faɗawa haka? Ƙanwar tawa?

Ya faɗa yana zabga mata mari sosai a kuncinta.

"Ni kikewa faɗa haka? Ni?

Ya faɗa yana sake kallonta.

Sai ya yi dariya kaɗan.

"Laura baki da mutunci. Baki da kunya".

Ya faɗa sosai yana girgiza kan sa.

"Dana yi me?...

"Da ki ka hada baki da Sadam, a cutar da ɗan uwana Ishaq".

Ya faɗa sosai alamar kamar jira yake ta zo ta taƙale shi faɗa. Cike da borin kunya ta ce.

"Ai naga de ba son shi ka ke ba, ɗan uwan naka da ka ke cutar da shi....

Wani marin ya sake zabga mata.

"Na yarda na cutar da ɗan uwana da kai na, ba ruwanku wannan ahalina ne. Amma ban yarda kowa waye ba ya zalunce shi".

Ya faɗa yana tsalleketa ya wuce ta bishi da mamaki tana kallonsa. Ta yi tunanin idan ya ji zai ji daɗine me yasa toh?

Daddy kam hauka cewa ce kawai be yi ba a kwanakin nan, gaba ɗaya ya rasa me yasa komai yake neman tarwatsa masa zuciya. Shi kan sa be san da cewar yana son Ishaq har haka ba, sai da kwanakin da ya bude companynsa aka zo da zummar wai a haɗa hannu da shi domin cutar da shi. Kawai kallon abin ya yi, batare da ya yi magana ba. Har yanzun kuma be yi maganar ba. Ya sani, yana son kan sa, amma ba kamar irin wannan ba, ya sani ya cutar da shi a baya, ya yi masa abubuwa da dama da ya sa shi zama wani iri, amma tabbas ba zai taɓa bari wani wai ya cutar da Ishaq ba. Zai je ya nemi gafarar Kawu domin ya sa masa hannu a wannan takardar ya haƙura ya janye zai yi dukkan wasu ladabi da ya ce domin muddin Kawu zai sa masa hannu a takardun sa fatansa ya ƙare Ishaq daga mumman hali irin na Sadam. Sadam ɗan ƙwaya ne, Sadam zan iya yin komai domin ya ga ya ci riba a duniyarsa. Sadam mugu ne, kuma tantiri ne bashi da alƙibila....

Yana wanan tunanin ya iso office ɗin sa, suna isowa ya same shi a zaune office ɗin sa yana kallon sa yana yi masa murmushi. Shima Daddyn murmushin ya yi masa kwatankwacin irin wanda ya yi masa.

"Me ya kawo ka?

"Abinda ya kawo kwanaki shine a yanzu ya kawoni".

"Banda sauran alaƙa da ta rage a tsakaninmu. Kuɗin Proff na rigada na tura masa abinsa. Ba wanda yake bina ko da sisin kwabo ne. Banda share na kowa a cikin wannan Company idan bana mutum ɗaya ba tak. Dan haka zaka iya tafiya bana hada dukiyata da gurbatacciyar dukiya ka gane?

Ɗan murmushi ya yi sosai ya ce, "Amma ai na ji labarin irin yarda ka ke yiwa ɗan uwanka....

Shima Daddyn murmushin ya yi masa mai kyau ya ce.

"Me bakin ka ya ce? Ɗan uwa? Wasu ƴan uwan, suna yin faɗa, a tsakaninsu har su dena magana su yi gaba ta shekaru da shekaru, amma hakan ba wai yasa basa san junansu ba".

"Kai a yanzu kana so ka ce min kana son Ishaq kenan?

Wani murmushin takaicin Daddy ya yi ya ce.

"Ko duka dukiyata zata ƙare wajen kula da shi, to tabbas zan yi hakan ko da kuwa zan koma kwana a titi ne batare da ya sani ba".

Jinjina masa kai ya yi sosai yana kallansa tare da tashi.

"Zamu gani, tsakanin ni da kai waye mai nasara".

Shima Daddyn yana jinjina kai.

Ya ce, "Ko da ace ka yi nasara a yanzu, a gaba ba zaka yi nasara ba. Ina maka fatan alkhairi".

Fita ya yi daga office ɗin sa, Daddy ya dafe kan sa. Me yasa haka? Me yasa ya ji yana ƙaunar Ishaq? Me yasa? Daman yana son shi ne?

"Ya Allah".

Ya faɗa sosai yana zare hularsa, kafin ya zauna yana kunna TV sai ga shirin da aka haska a kwanaki na buɗe Companyn sa. Ware ido ya yi sosai yana kallon Ishaq ɗin da yake bayani. Wallahi da haushi yake ji ya cigaba amma a yanzu sai fuskarsa har wani murmushin zallar farin ciki take yi. Tabbas ya sa wahala a rayuwarsa, ya sha wahalar da shi be sha ba. To mema ya tsira da shi na daga cikin rayuwarsa? Da me zai iya bugar kirji ya ce ya tsira? Ina kuɗin da yake taƙama da shi?

A hankali ya sauke ajiyar zuciya kawai yana zaro wayarsa.

"Ga Fa'iza tare da wasu maza".

Kulle idan sa ya yi kawai sosai, wato da yace kar ta sake fita shine ta sake fita ko? Shikan wanne irin abu ya aikata a rayuwarsa har haka?

Kulle idan sa ya yi sosai yana jin zuciyarsa na zafi da bugawa, kafin ya tashi yana fita kawai daga office ɗin batare da ya yi komai ba.

************Mami shiru ta yi sosai tana jin Daddy, kenan itama ta tafka kuskure ne ko me yake so yace mata? Ina yaran ta? Tunda ta taho bata ji daga gare su ba. Da sauri ta ɗauka wayarta tana lalubo numbernsu amma bata shiga ba, idan hankalinta ya yi dubu to ya tashi, ina yaran ta haka? Da sauri ta danna kiran numbernsa. Amma be daga ba, da ta sake kira ne, ta ji an daga.

"Yarana nake so ka haɗa ni da su".

"Kin bani ajiyar su ne?!

Ya faɗa a daƙile yana kashe wayarsa. Dafe goshinta ta yi sosai tana jin rikicewa na samuntae. Nan take ta sayi ticket, Allah yasa ta samu ta yi saurin shiryawa ta wuce Abuja. Acan ta same su, koda ta je gidan hanata shiga aka yi, abin ya so bata haushi amma de ya daure ta roƙe su suka barta ta shiga.

Sanda ta je ta iske Fahima rungume a jikin wani, sai da zuciyarta ta buga ganin wannan abin.

"Fahima?

Ta faɗa da mamaki sosai tana kallonta. Sai kuma ta ƙarasa ganin mutumin sai wani lallashinta yake yi, ita hankalinta ne ma gaba ɗaya ya tashi ya yi masifar kaiwa nesa.

"Ke?

Ta daka mata tsawa ganin suna shirin kissing juna bama su sanda da ita ba. Ai bata yi wata wata ba ta kwasheta da mari.

"Irin tarbiyyar da na yi maki kenan Fahima? Fahima ke ce kuwa? Daman haka kike? Tun yaushe hakan ya kasance? Fahima....

Kuka Fahiman ta sa sosai tana durƙushewa a wurin Mami. Mami gaba ɗaya ta rikice ta kasa samun natsuwa, yarinyarta? Har cikin gidan ubanta?

"Mami ki....

Mutumin zai yi mata magana ta ɗaga masa hannu.

"Bana son jin komai daga gareka. Yanzu ka fice....

Shiru ya yi yana kallon Maminta, ashe daman haka take da faɗa? Sun sum ya kwashi jiki ya fice. Ɗago ta ta yi ta sake zuba mata wani marin.

"Baki da hankali ne? Shi fa namiji ne Fahima?

"Ina can hankalina a kwance kuna nan kuna kulawa da kan ku ashe bansani ba wulaƙanta kan ku kuke?

"Fahima ni??

Rasa abin cewa ta yi kawai ta dafe goshinta. Yarda take maganar da ƙarfi ne yasa kowa dake cikin gidan sanin ana abu a cikin sa. Hakan yasa matar Babansu fitowa.

"Wannan kuma daga ina?

"Maminmu ce".

Taɓe baki ta yi sosai ta ce, "Ohhh, kunga ku fitar min da ita daga cikin gidan nan, bana san sake ganinta. Kuma kada ta sake dawowa".

Ta faɗa tana kallon Mami. Mamaki ne sosai ya ishe Mami, ganin Fawwaza ta dawo daga wani wurin kana ganinta zaka san a buge take sosai. Kallon Mami ta yi kawai da idan ta dake a juye sannan ta wuce takalmi a hannunta. Sanin da ta yi mata da, bata shan komai, bata bin maza, bata yin komai sai de ta fi ta yi chilling ɗin ta ta dawo. Amma de bata duk wani abu da ya sabawa shari'a why now?

Tana ji tana kallo aka riƙeta hannu bibbiyu aka watsar da ita a titi, saura ƙiris mota ta bugeta. Mami ji ta yi wasa abubuwan na bin fuskarta tana taɓawa ta ji hawaye ne. Dagaske kuke take. Kawai ta saki kukan sosai ga dukkan ƙarfinta.

Yayinda a cikin gida Fahima ta kalli matar Baban na su da suke cewa. Umma jin haka ita Fawwaza ke faɗa kuma haka Babansu yace su ke ce mata.

"Amma baki yiwa Mami adalci ba kin san da haka ?

"Ni kike faɗawa wannan maganar?

"Ke uwata ce da ba zan faɗa maki ba?

Ta faɗa tana kallonta da idan ta dake cike da hawaye sosai. Matsowa ta yi kusa da ita ta wanka mata mari sosai. Fahima ta sa hannu zata rama Baban su ya fito da yake kallon komai ta window.

"Ashe iskanci na ki har cikin gida ki ke yi bansani ba?

"Ni fa Abbah ba abinda na yi, ban taɓa kwana da wani ba. Kawai kai duk abinda aka ce maka mun yi sai ka yarda?

"Fahima? To ko nima zaki dakeni bansani ba? To dakeni".

Ya faɗa yana sake ƙara sowa.

"Aikin da aka saki baki kammala ba ko? Kika taho rungume namiji acikin gidan ubanki".

Cewar Matar Baban na su.

"Zahira rabu da ita ta dakeni".

Sunkuyar da kanta kawai ta yi tana shigewa cikin gidan na su, tana zuwa ta shige ɗakin su kawai ta rufe ƙofa ta sulale ta saki kuka sosai tana haɗe kai gwiwa.

Zaituna ta ce, "Wai ba zaka iya zama ba. Sai kin tanka mata ku yi ta samun matsala da Abbah".

Tana kuka sosai ta ce, "Taya zan yi hakan? Taya zan iya ganin na zama Yar aiki a cikin gidan ubana Zaituna, me yasa ba zaki bani haɗin kai mu samu mu mata shegen duka ba".

"Sai abin ya sake dawowa kan mu ko?

Taɓe kawai Zaituna ta yi tana tashi ta ce, "Zan wuce nikam ina da class, zan bi ta kofar can da bata sani ba. Should in case an zo nemana ki ce na fita compound baki san inda nake ba".

Ta faɗa tana yaga mayafi. Share hawayenta Fahima ta yi ta ciro kuɗin da ke cikin bra ɗin ta ta miƙa mata.

"Ki yi sauri ki dawo".

Jinjina mata kai ta yi ta fice da sauri. Kafin a hankali ta kifa kan ta a cikin gwiwarta tana sakin kuka mai tsuma zuciya sosai. Basa cin abinci a gidan ubansu sannan duk wani gyaran gida sune suke yi na cikin gidan su. Masu aiki basa komai daga ci sai kwanciya, shi fita su nemo ace sun yi karuwanci, su kan ya za su yi? Da wanne baki zata fara cewa Mami ta yi haƙuri? Me suka aikata sukam?.....

**********Sahal sai da ya tabbatar da ya cika alƙawarin da ya ɗaukarwa kan sa. Domin de shi da Raudah sun zama abu guda ne. Tun sanda suka yi asuba Raudah ta koma bacci, yayinda shi kuma be rintsa ba kawai yana kallon ta ne. Sai kuma ya tashi raya daren da salloli. Sai lokacinne ya samu ya ɗan jima bacci shima a kusa da ita ya je ya rakube kamar mai tsoron taɓata, dan ko kallonsa ta ƙi ta yi kuka fuskar ta sosai take a ɗaure. Alamar fushi ne take yi da shi.

Motsin da ya ji ne yasa shi bude idan sa a hankali ya ganta yarda ta ke juya ƙafa tana tura baki kafin ta buɗe idan ta tana sakin kuka. Wato to de banzar kwanciyarta take so ta yi amma babu hali. Duk yarda ya so kar ya yi murmushi sai da ya murmusa sosai. Aka ce kowa ya tuba dan wuya.

"Munafiki".

Ta faɗa masa a hankali tana kallonsa da hararan sa cike da gunaguni.

"Wai ni ina son ki".

"Ko ina so anan?

Bude ido ya yi, yana buɗewa ta maida nata ƙasa tana zabga masa harara tana ɗauke kan ta ta kuma sake kumbura baki.

"Ki ka ce me?

Cike da masifa ta ce, "Kar ka sake cewa kana so na".

Ta faɗa saboda irin kalaman soyayyar jiya da ya ringa zuba mata yana lallashin abinsa. Be san sake ɓata mata rai suke ba. Ita babbar damuwarta ma, da wanne idon zata sake kallonsa?

"Yi hakuri ba zan sake ba shikenan?;

Ya faɗa zai riƙota.

"Kul bansaka ba, ban ce maka ba zan iya tashi ba. Daga rana irin ta hau kar ka sake taɓa ni. Tunda baka da mutunci baka da kirki".

"To Raudahna".

Hararansa ta yi sosai tana sake kumbura baki. Duk wannan abun na tsananin kunyarsa domin ta kasa haɗa ido da shi. Sai de a kalli bakinsa a harare shi.

"Sai me kuma?

"Aww jira ka ke na ce sai wani abun ka ce ba zaka yi ba? Daman na takura ka ka ke taimaka min ashe bansani ba?!

Cike da tsantsan mamaki sosai ya ware ido.

Ya ce, "Walalhi ban haka ne ba. Ki yi haƙuri dan Allah".

Murguɗa masa baki ta yi, sai kuma ta sakar masa kuka sosai.

Dafe kan sa ya yi kawai yana kallonta. Sai kuma ya ga ta juya, ba'a ɗau lokaci ba ta cigaba da bacci. Ohh daman gaba ɗaya bori ne yake damunta.

Kiran wayar da ake yi ne yasa shi saurin mayar da wayar silent yana ɗaukar wayar ya fita da waje, ya duba tarin calls ɗin numbern ta yi daga jiya kawai zuwa yau, anyi kira ya fi ɗari. Yana cikin kallon numbern da tunanin waye me wannan kiran, wani kiran ya sake shigowa.

Wayar ya kara a kunne domin jin waye ne yake mata wannan kiran haka...