Chapter 3
*MIJIN KANWATA..*!
_(k'addarata)_
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty❤️*
*HIJABS CORNER BY JANAFTY*
*Muna da Hijabai masu kyau da inganci, ɗinki cikin kwarewa da* *mabambanta design, muna aikawa da kayanmu ko'ina a Nigeria, muna maraba da masu siyan ɗaya ko sari.*
****, tuntuɓa ta wannan lambar*
*KADUNA/ZARIA*
*Bojuwa herbs*
*By*
*Surayya Dee.*
****.*
*Sanyi flusher!*
*Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.*
*Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*.
*Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.*
*Tightening set na hade mace ta dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*.
*Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.*
*Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.*
*Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.*
*Tuntubeta a wannan lambar*
*****
*Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.*
*Nation wide delivery*.
*Page 3*
Sai da yayi wanka yayi Sallar Isha"i ya saka madaransa da Furansa cikin karamin Fridge din Dake Falon nashi kana ya fito Domin ganin ya"yan nashi Sanye yake da Tattausansun Riga da wando na barci masu ruwan Duhuwa na kamfanin PJM,hannayensa Cikin aljihun wandon Barcin ya sauko kasa da Magajiya yaci karo Tana ta Safa da marwa Tsakanin Kitchen da Kayattacen bangaran makeken Dining din cin abincin Dake chan yammah da Falon.
Har ya sauko bata ma Lura dashi ba Magajiya mai aikinsu ba yarinya bace a kallah a shekaru zata bama arba"im baya Daga garin kargi take Mijinta Rasuwa yayi kuma bata taba Haihuwa ba kuma Mijin nata shine mai kula da Dabbobin Maimartaba alokacin bayan Rasuwarsa Magajiya ta Dawo Karkashin kulawar Fada cikin Hadiman Uwargidan Sarki Fulani Shime bayan Haihuwan Aliyu Wasim kenan da Shi sulaiman din ya Bukaci Samun mai taimaka ma Sunaira awanchan Lokacin Maimairtaba yabada Umarnin a basu Magajiya.
Tun achan baya akwai Girmama juna a tsakaninsu dagashi har sunaira suna mata kallon Uwa ce shiyasa take jin Dadin Zama dasu Tayi kukan Rashin Uwardakin iri Hajiya Sunaira,Ammh ko ayanzu bazata Dora komai game da Sabuwar uwar Dakin nata ba abu Daya ta sani bata da kwarammiya da Yawan mgana kamar Sunaira a kowani Fanni suna da bambamci Dabi"u da kuma Hallaya.
Ta duka tana Jera Filet din saman Dining din taji mganarsa Daga sama.
"Magajiya Barka da aiki..!
Yafada cikin kyakyawan Sautinsa da Hanzari ta Juyo tana kallonsa Lokaci Daya ta maida kanta kasa tare da dan Rankwafa Tana Fadin"Barka da Fitowa Sarakin Maimairtaban Kargi..!
Haka take Kiransa daman dan Murmusawa yayi kafin yace"Magajiya bana son Sarakin nan fa..Maimartaba Kadai ke iya Kirana na amsa..Sunana Sulaiman kuma don Allah ki Daina Ramkwafamin in zamu gaisa nan fa Gidana ne..Ba Fadar Sarkin na Kargi ba!
Ya karishe Fada Muryansa da alamun Zolaya ammh bai nuna saman Fuskarsa ba Kasa ta karayi da kanta kafin tace"Amin afuwa Ranka ya Dade..Bana iya kiran sunan mai garin Kargi gabadayane..Sunan yana Daraja da Kima awajena..!
Bai mata mgana ba illah kafada Daya Daga Daidai Lokacin da Samira ta Fito Daga Dakinta wani kallo yayi mata mai Cike da Tsana da gargadi Daya sata Zubewa tana mai barka da Fitowa kallo Daya yayi mata ya kauda kai Daidai sanda Magajiya ke Fadin"Saraki nan Zakaci abinci ko na Haura maka dashi saman Dakin ka ne..?
Kansa ya Girgiza yana Fadin"Am ok..Fura zan shan kafin na kwanta Ina yaran nan suke..!?
Magajiya tace"Mai sunan Hajiya tayi barci Tun dazu Datagama Rigima Hajiya ta mata wanka sai ta samu Barci..Mai sunan babban Mutum kuma yana Dakin nasu yana kallon yan aljanun nan nasu..!
Jim yayi yana kallonta batare da yayi mgana ba Har zai ce wani abu sai ya Fasa ya wuce ya Fara Taka Lallausan Cafet din kasar Italian Dake malale atsakar kayattacen Falon Dayaji kayan More Rayuwa.
Bayaso yayi mgana saboda yar aiken Hajiyarsu dole ya Fara Kafa Kafa da ita Domin bashi da ikon korarta faruwar hakan kamar ya siyan ma kansa Tikitin Fadan Hajiya ne da kuma Kudirinta akansa Da Fara Kokarin Tabbatar dashi.
Dakin su Wasim din daya zama Mallakinsu tun dawowarsu gidan,Wafiyya Dakin Magajiya take kwana Hatta Wasim din ma wani Lokacin sai dai shi ya fita Sakin jiki kuma baida Rigima ita ga ta yarinya sannan ga Kiyuwa da Rigima kala kala bata iya kwana batajita Lafe jikin Mutum ba.
Koda ya shiga Dakin Wasim barci ya kwasheshi nan Tsakar Falon ga Talabijin nan a kunne ana Haska Cartoon din yara,gabansa kayan wasa ne su Ninja da superderman,da Bindogogi Daga gani dasu ya ke wasa kafin Barci ya Daukesa Tsausayinsa da Tsausayin Ya"yansa ya kamasa Allah Sarki Mutuwace mai Tonon asiri da ba domin Mutuwa ba da yanzu Wasim suna tare da Mahaifiyarsu tana basu kulawa shi kanshi da Rayuwarsa bata zama a Tagayyare ba
Ya kara Tattabar ma kansa Hasashen su Maimartaba akansa ba Daidai bane in suna Tunanin sun kakabamai auran Yayar matarsa saboda sun yi mai gata to wlh kara Gurgurta rayuwarsa sukayi,Domin shi dai bai ga amfanin hakan ba matar da bata wani da amfani acikin Gidan da Lokacin Datake nan da batanan duk Daya yaransa sun wuni Cikin Kadaici su kwana cikinsa Tana chan yawonta da sunan wai aikin asibitin gwannati aikin banza aikin Wofi Shidai Wlh an gama Kasheshi ba Tun yau ba ya Dade da Sanin ya Juyama Rayuwar jin Dadi baya Tun sadda Sunaira ta bar GidAn Duniya.
Cicciban Wasim dim yayi ya Rumgumesa yana kokarin kokuwa da Rauninsa Na Lokaci kafin ya maidasa kan gado,Kayan Jikinsa ya Ciremai ya isa ga karamin Durowansu ya Zaromai kayan barcinsa ya sakamai Barcinsa yayi nisa shiyasa bai Farka ba ya Dade yana Shafa kansa yana Tofamai addu"a ya Dade adakin kafin ya Fito sai da ya Ragemai Hasken Dakin ya karamai karfin A.C saboda garin akwai Zafi sosai Tunda yaga bai ga Wafiyya ba,Tana Dakin wanchan yarinyar mai girman kan tsiya alhalin shi kuma bai Tabataka Kafarsa zuwa Dakin ba Tun bayan Daya tashi ana Sunaira ya koma nata din Har Abada
Falon ya Sake Fitowa bai ga Magajiya ba yana shirin Zuwa Kitchen kenan sai gata ta fito Tana ganinsa ta Rabe gefe kanta a kasa tace"Yallabai wani abu kake Bukata..?
Kansa ya shafa yana Fadin"No..Wasim yaci abinci kafin ya kwanta..?
Magajiya tace"Eh Hajiya ta basu Tea Shida mai sunan Hajiya kafin ta Fita..!
In sukace Hajiyanan wani Haushi ke kamasa bai ce komai ba ya kada kai ya wuce har zai koma sama sai ya Fasa ya Karkata aqalan Tafiyarsa zuwa Dakin da abaya yake zame masa Wajem shiga da yin komai nasa na Rayuwa wani Lokacin sai ma ya manta yana da Dakin barcinsa a sama Sunaira Tana da kiyuwar Hawan Bene shiyasa sanda zai yi ginin ta Dingamai Complain shi kuma yana son Rayuwa a upstair domin tun yana Gida asama yayi Rayuwa,shiyasa bayan Tarewarsu Sunaira bata yarda ta Bisa saman sai ya shammaceta saidai shi ya Biyota ahaka ahaka duk ta Kwashe Rabin kayansa zuwa Dakinta Shi kanshi Daga baya mantawa mayake da Turakar tasa yafi Jin Dadin Rayuwa kusa da Noory dinsa tafi su.
Lokacin Daya Tun kari Dakin gabansa Sai da ya Fadi yaji wani sanyi na Shigarsa,Rabonsa da Dakin tun bayan Lokacin Rasuwar Sunaira Daya maida Dakin wajen kwanansa man yake komai,baya Fita ko"ina ya wuni aciki ya kuma kwana kayan sunaira su suka Zamemai abun Farincikinsa dasu yake kwana yake dashi Sai da Maimairtaba da kansa da Abbansa suka zo har tsakar Dakin suka Tallabeshi atare suka Fita dashi zuwa Falo suna Faman Lallashinsa da ban baki alokacin baya cikin Hayyacinsa Hawaye kawai yake domin yasan wannan Hakurin da ake bashi na Rashi ne ba na wani aabu.
Tundaga Lokacin aka saka aka kwashe komai na Sunaira aka kai gidan Iyayenyta aka Fitar da duk abunda Zai Tunamai da ita ballatana Har ya kallah yaji Rauni.
Harta kayan Dakin Lokacin da Sunaima Zata tare an sauyasu ammh har alokacin yanajin yana da alaqa mai Girma da Dakin Domin sun Zuba wata Rayuwa mai Wahala mantawa shida Sunaira acikin Dakin nan.
Lokacin Daya Dora Hannunsa Saman Handle din Kofar ya Turata ta Bude ya shiga,an Rage hasken Dakin Duhu yadan mamaye ganinsa Hannunsa na Rawa ya Lalubi makunnun Hasken da Daman ya Haddace mazauninsa ya Kunna Haske ya Gauraye Dakin Gabadaya
Wani yam yam yake ji acikin Jikinsa Lokacin Dayake bin Dakin da kallo Duk da an sauya Zaman komai acikin Dakin shi a idanuwansa yana Hango komai acikin Muhallinsa ne yana Hango kansa shi da sunaira akan Tsakiyar makeken gadon Royal din Dake Dakin Asatin dazata Fara wannan Ciwon ciwom Dayayi Sanadiyar barinta Duniya.
Yana kallon Abun kamar acikin magaji ne sanda suka gama Farantama juna rai ya Dauketa kamar yar Tsana Duk da Tana dan Jiki suka Shige Tiolet achan din ma kafin suyi wanka sai da suka kara Zuba wata Soyayyar kafin siyo wanka su Fito yana kallon Sanda ya Direta gaban Madubin Dakin kam karamar Kujeran Dreesing mirror.
Shi ya Dauko mata Handryer dinta Ya jona mata ya Fara Taimaka mata ta Busar da gashinta itama ta rantse sai ta Busar mai da nashi gashin yana ta bari ammh Taki mikewa tayi shi ya koma ya Zauna ta Rika saka Hannunta Cikin sumarsa kamar Tana Tafiyam Tsutsa Lokaci Daya tana Busar mai da gashi nokewa mata yake ganin da gayya takeyimai yasa ya Mike yana Rike Handery din hannunta Lokaci Daya yana kallon kyakyawan Fuskarta yana Fadin"Stop it Noory..Ina jin wani iri..!
Tana yarfamai Dogon Gashinta a Fuska Tana Fadin"Saboda mene Sarakina.?
Alokacin Duk duniya ita kadai ke Kiransa Saraki yaji sunan Har Tsakiyan kansa Lumshe ido yayi kafin ya Bude yana Fadin"Wani iri nake ji..In kika Cigaba da min Allah zan kara Kwakuleki ne kin sani ko..?
Dariya ta kyalkyallce dashi bai biye mata ba ya kwace abun hannunta ya kashe ya maidashi Cikin Wata Dirowa ya sungumeta gabadayanta Har Towel din jikinta na Zamewa yana Fadin"Muje na ganki..Sai kiji Dadin Dariyan Dakyau..!
Kan gadom ya Direta ya Bita ya Danne yana aika mata da sumba ko ta ko"ina,Dariya take alokacin Fararan Hakoranta suna bayyana Kiran sa sunansa take kamar koyaushe in tana son Rokonsa"Haba nawan..Sulaiman haba sulen Sunaira..Kada kamin haka Haba Abban Wasim da Wafiyya Sarkin Goben Kargi haba yallabaina Ranka ya Dade na..!
Take Fada alokacin Tana Dariya Shima Dariyan yake yana kallonta yana Fadin"Kin mamta baki Kira Inna da Baba ba..!
Mintsinansa tayi a Damtsen hannunsa yadan Saki kara Dariya ta saka kafin ta sunne kan Kirjinsa tana kara Sakin Dariyanta Kanta ya shafa yana Fadin"Ina Bukatar karin wasu ya"yan..Mai sunan Fulani nake so da Maimairtaba..!
Tana jinsa sanda ya Fara Chanza Tashar itama Tallabosa Tayi Tana Fadin"Nima zan tayaka Sarakina..Ina so na samo.mai sunanka ne na saka masa sunanka in ya Girma na Zaunar dashi na Fadamai Tarihin Sunan wanda yaci Sulaiman Gwarzon Sunaira ne har Gidan Aljannah..!
Alokacin Dagashi har ita basu san da Zanen kaddaransu ya Harbo Gefen Mahaifarta ba basusan Cikin da suka so su samu ba yana makale da ita agefen Mahaifa Domin Allah shi ya riga ya gama Nashi namu ne mutane muke Wahalar da kanmu wajen Shirmenmu Farincikin da suka kasance shine na Karshe a wannan Ranar bayan kwana Daya ya Tafi Lagos wajen Taron yadda Harkan kasuw Zata Bunkusa Taro ne yaan kasuwa Kasashen Duniya gabadaya Kamfononi da ma"aikata da manyan yan kasuwa yanachan yaji Kiran Waya kiran wayar da ya Zama Barazana ga Rayuwarsa na Labarin Sunaira ta yanke jiki ta Fadi a Bandaki Jini ya yanke mata tana asibitin Garkuwa Dake kaduna Likitoci sun Tabbatar da Ciki agefen Mahaifarta in ana son Tsira da Lafiyarta sai anyi aiki an maidashi Cikin maHaifa aikin da akayi shi da kwana Daya Sunaira ta amsa Kiran Mahallaci a Hannunsa Tana Rike da Hannayensa Idanuwanta tana kallonsa Suka ida Kafewa Ta amsa Kiran Allah akan idonsa da Idon Iyayenta da yan"uwanta kan Idanuwam Hajiyarsu da Abba da Fulani Har Duniya ta Nade bazai manta da wannan Ranar ba.
Sulaiman ya kasa Controling din yanayinsa da wannan Raunin Hawaye sun Jigamai Idanuwansa yadda baya ganin gabansa Da Rarrafe ya karisa Gaban gadon yana kaallon yarsa wacce tana da Shekara Uku aduniya Sunaira tatafi ta barta, bata ko gama Shan Dimin Mahaifiya da kowani D"a yake sha ba Mutuwa ta Raba Tsakaninsu yana kaallonta sai dai Tana Rikidemai me Tana komai ma Sunaira da irin kyakyawan Mirmishimta akoda yaushe.
Baisan sadda ya fada kan gadon ba ya Tattaro Wafiya cikin Jikinsa ya kamkameta Cikin Dashewar Murya ya Saki kukansa da amon Muryansa Hawaye na Zuba Daga kwarmim Idonsa baya Cikin Hayyacinsa yasa har baisan irin Rikon da yayi ma Wafiya mai Zafi bane sai da yaji Mutsu mutsunta tatashi Tana Neman kwantan kanta,ayadda yake wannan kukan duk bawan Mai imanin Daya gansa sai ya Tsausayamai Domin Magidanci mai ji da komai Rayuwa kamar Sulaiman Aliyu Sulaiman kwamce yana kuka kukan zucci Dana Sararin tabbas abun a Tsausayamai ne kuma aduba Rauninsa
Chan sama sama yaji kukan Wafiyya shi ya Dawo dashi Daga Hayyacinsa ya Zabura ya Mike zaune ya Rikota yana Lallashinta Fadi yake"Shiii...Sorry Hajiyata Nine..Daady ne..Baba ne..!
Gabadaya ya Rude baima san abunda yake Fadi ba ita kuwa tasan jikin Babanta da Muryansa yasa ta kara Lafewa tana Sauke Nunfashi Kwantawa yayi ya Dorata saman Kirjinsa yana Lallashinta Har barci ya Dauketa Tana Sauke Numfashi bazai iya Katse mata wannan barcin nata ba yasa ya gyara mata zama akan Kirjinsa nasa shi kuma ya Kurama Rufin Dakin ido Komai Daki Daki yana Dawo mai kamar Alokacin komai ke Faruwa
Barci barawo me ya sace shi bayan Tsawon Lokaci daya Dauka bai Runtsa ba da asuba kuma Kukan Wasiyya ya Tadashi Daga barci ta Fara Rigima ya Mike a kasalance ya Fice Dauke da ita Zuwa Dakin Magajiya ya isketa Tatashi Har ta Dauro alwala bai ce mata komai ba ya mikamata Wafiyya ya Fice tana Binta da kallon tsausayin Domin jiya da Daddaran taje Daukan Wafiiyya ta kawo ta wajenta ta kwanta Ta ganta Kan jikin Uban suna barci Tsausayinsu ya kamasu ta koma Daki tana Rokon Allah ya Tallafama wannan bawan Allah ya Dubi Rauninsa.
Sanda ya Fito Daga Dakin Magajiya yana kallon Samira na lekensa ta Kofar Dakinta Data Bude kadan ya ganta sai yayi kamar bai ganta ba Yunwa yake ji ya kwama bai ci komai ba Rabonsa da abinci tun Breakfast din Safe,Sama ya Haura ya shiga wanka a gurguje koda ya fito har an Tada Salla a wasu masallatan Farar Jallabiyansa ya saka da Hulansa Tabani kaji Hadisi ya Dauki Carbi Daman ya Dauro alwalansa ya Sauko Zuwa maaallacin Dake Tsallake inda yake Sallah yana Fita Haraban Gidan ya ci karo da Megadi yana shimfida Darduma nan gaban Dakinsa zai Tada Sallah yana ganinsa ya Shiga sosai kai Domin yasan yayi Fadan Salla acikin Gida ya Rika zuwa Cikin jam"i.
Kallo Daya yayi masa ya kauda kai bai cemai komai ba ya Bude karamar Kofa ya Fice sum sum Megadin ya Namnade Darduman yabi bayansa Sani ba anan yake kwana ba yana Hayin banki ne inda yake zaune da Matarsa da Dansu Daya.
Sulaiman bai dawo gidan ba sai bakwai na safe yana cikin masalllaci yana ta Tasibihi yana shigowa ba kowa afalon ammh har an Shirya Dining din da abun karyawa Allah Sarki Magajiya bata gajiya da Hidimansa Data yaransa Tun bayan Rasuwar Sunaira Wlh itace Bangonsa.
Sama ya Haura,bai samu natsuwa ba sai da yasha Furansa yaji Dama dama wanka ya karayi ya shirya Cikin American suit masu ruwan Toka ya matse Wuyansa da Tie ya Dauko Karamar Jakar Briefcase dinsa da Wayoyinsa ya Nufi kasa yana Tafe yana Laluban Lambar sani yasan Halinsa sai ya Zauna yana Jiransa.
Wayar ta shiga Daidai Lokacin Daya iso Tsakiyar Falon Sani ya Daga Kiran Alokaci Daya yana Fadin"Yallabai ina kan adaidai ne ganinan karisowa..!
Kwafa kawai yayi ya Datse Kiran yana ayyana Sani ya gama Rainasa Wlh sai dai shi ya Dinga jiransa kullum kamar wani Sa"ansa..!
Ya taka keman zuwa Dakin Wasim sai ga Magajiya ta fito Rike da Hannun Wasim Cikin Shirin makaranta goye da Jakarsa da Lunch Box dinsa Wafiyya ma Ma cikin kayan makarantar ta Command Childreen School,Tarkacen Jakarta na Hannun Magajiya.
Suna ganin Abbin nasu suka Saki Magajiya Harda Wasiyya Dake hannunta ta Fara mika hannu ta Saketa suka Nufeshi Shima kasa ya Durkushe ya ware musu hannu suka Shuge Wasim Dake da Wayau shi ke Fadin"Oyooyo Daddy..!.
Wafiyya da mganarta ta yara take Fadin"Daaddi..Toyoyo..!
Ta kwaikwayi Wasim Rumgumesu yayi yana jin kaunarsu na Ratsashi Cikin Muryansa sanyinsa yace"Gud Mrnin my Sweet Childreen..!
Yake fada yana Dagosu Daya bayan Daya yake basu Peck a Kumatunsu
Cikin Soyayya yace"Kun yi Breakfast..!
Wasim ya Daga kai kafin ya kalli Magajiya Dake gefe kanta na kasa yace"Magajiya ta bamu tea da Egg Daddy..!
Mikewa yayi yana Dauke da Wasiyya yana Fadin"Ehhyye..kun ci Dadi Hajiyata kema kinci Egge din..!
Kai ta gyadamai Tana Shafa sumar kansa Kallon Magajiya yayi kafij yayi mgana ta Fara gaisheshi ya amsa Cikin Kulawa
Kallonta ya karayi yana Fadin"Sannu Magajiya Nagode kwarai..!
Kanta na kasa tace"Ba godiya Tsakanimu Ranka ya Dade..Wlh bazan Taba Biyanku Tarin Alherinku gareni ba..Allah ya Jikam Hajiya karama Allah yayi mata gafara..!
Amsa mata yayi da amin kafin yace"Ba wata Hajiya karama Magajiya..babba da karamar duka Noory ce kin ji ko..?bana so ma karajin kin ce Hajiya karama..!
Kai ta gyada Kafin tace"Afuwan Insha Allahu zan Kiyaye..!
Kai ya kada yana Fadin"Zan fita wajen aiki..Daganan zai kai su makaranta Fatan komai ya kamallah?
Magajiya tace"eh yallabai..Sai dai kai Zaka Fita baka ci komai ba..?bai Damu ba yace"No karki Damu am ok...Nasha Furata dazu..kuma in naje office zan sha Tea in naji yunwa..!
Batace komai ba Domin ba Huruminta bane bata sake mgana ba Wayarsa yake Dubawa Lokaci Daya yana Sakin tsaki yana shirin mgana Sani ya shigo Falon kamar an jehosa yana Faman Sosa keya gaban sa ya Zube yana Fadin"barka da safiya Yallabai..Amin afuwa wlh ban samu abun hawa akan Lokaci bane ayi min afuwa Ranka ya Dade..!
Hararansa yayi Lokaci Daya ya Dauke kansa Sani yasan Laifinsa yasa ya Karisa ya Riko Jakar Wasim da Lunch Box dinsa Data Wasiyya ya Rike Hannun Wasim yana Fadin"Babban Mutum barka da Safiya..!
Wasim na Dariya yana Fadin"Sani...Sani..!
Wafiyya dake hannun Sulaiman itama ta Fara Zillo Tana Dariya Tana Fadin"Chani..Chani!
Sani ya juyo yana Fadin"Na"am Hajiyar Allah..Da Girman kujeranki..!
Sai bangalamai Dariya take tana Mikomai hanmu Sulaaiman ya kallah yaga ya Hade ransa kamar bai Taba Dariya ba sai ya kama kansaya juya suka gaisa da Magajiya.
Sun fara takawa zasu bar Falon Sulaiman yajuyo yana Fadin"Magajiya ina ita wannan yarinyar da Sani ya Daukota Daga Kargi..?
Sani naji ya waigo yana Fadin"Yallabai Samira kenan ai.!
Kallonsa da Sulaiman yayi ne yaaasa yayi Saurin jan hannun Wasim suka Fice Daga Falon Magajiya ta rakasa da yar Dariya Sani ai surutunsa yafisa ma karfi indai shine.
Kanta Sulaiman ya koma yana Fadin"Naga ke kadai ke ta Wahala Magajiya..ga aikin kula da yaranan ga kuma ma gida..ita ban ganta tana wani abu ba?
Kan Magajiya na kasa tace"Tana Taimakamin da kula da yaran Wani Zubin Yallabai..!
Kai tsaye yace"Wani zubin..?daman zama tazo yi..?Ina Lura da ita bata da wannan amfani koda yake ai tanayi abundaya kawota Munafunci da Saka Ido..Koda Hajiya ta kawota bashi Zai Hana naci mata Mutumcin ba Indai bazata gyara ba ai da sunan aiki aka kawota ba Hutu ba..!
Ita dai magajiya kanta na kasa batace komai ba Har ya Fice Daga Falon yana Zabgan Fada.
Yana Fita Samira ta Fito Daman Tana Labe wani kallo tabi magajiya Dashi kafim tace"In kikace zaki bibiyi Rayuwata agidan nan..Bani ce zan shiga Uku ba kece domin ba Kargi ma Zaki koma ba sai da aneni Dangin masu Dattin Hula..Ni Hajiya ta kawoni kuma Umarninta nake bi acikin Gidanan ki kula ki kuma kama Girmanki kafin na Fadamata abunda kike shirin yi..Tsohuwar banza kawai..!
Tafada tana sakin Tsaki Kafin ta wuce tana wani kada Jiki kamar mazari,Da kallo Magajiya ta Bita dashi batace komai ba,Domin bata da tacewa Tun zuwanta Gidan banda Rashin Da"a babu abunda Take shukamata in anyi mgana tace Hajiya to daman ai sai ita kuma gaskiya ta Fada Hajiya Zabba"u bata kyashin cin Zarafin duk wanda ya shuga Harkanta Shiyasa data Fahimci hakan ta kama kanta da Samiran Tana jin Dadin zama da Yallabai bazata so wani abu ya Gifta ba.
Sun gama shiga Motar yau da 4matic dinsa zai Fita dukkansu shida ya'yan nasa Gidan baya suka shiga riverse sani yayi tare da Hon megadi ya wangalemusu get suka Fita sai dai basu kai Fita ba Saboda mai adaidatan daya Tsaya gaban get din Sunaima ta Fito Daga Ciki ta Bude Jakarta ta Dauko kudinsa ta basa ya Tafi saidata Juya ne taga Motar tsaye Tana Jiran ta kauce.
Gefe ta koma Tana kallonsu suka wuce Fuu kamar zasu tashi Sama Glassan Tintied ne Shiyasa bata ga yadda su Wasim suke ta Ihun kiran sunanta ba.
"Anty...Anty....!
Harda wafiya Dake kan jikin Uban Tana Tsalle tana Fadin"Anty Radam a abakinta shi kam ta iya Kira,Sani kam sai da ya maganta ya juyo yana Fadin"Ranka ya Dade...Hajiya fa suka gani kaji suns Ihun kiran Anty..!
In motar ta tanka to sulaiman ya Tanka Wayarsa ma ya Fiddo yana Laluban Habib yaga Kiranss da Safe Lokacin yana wamka yayi bakam Daga sani har yaran,har suka gama kiran sunan Anty suka Hakura.
Har cikin makaranta yakai su kamar yadda ya saba Wafiyya tana Nurseey 1 ne yayinda Wasim ke primary 1 kowa ya saba Daman Sulaiman ke kawo su kuma Baya Tafiya shi da Sani sai ya Damka kowamnensu ajinsu hannunsu malamansu da Jakansu da Lunch Box dinsu da tunsuna Rigima in ya kawosu zai tafi har suka Saba in zai Tafi suna mai Bye bye abaya Tare da Sunaira wani Lokacin suke kawo wasim ko kuma in ya makara ita ta Tuka Mota ta kaishi Lokacin ba"a Saka Wafiyya ba sai bayan Rasuwarta aka Sakata,Daganan kamfani suka wuce.
Sunaima kuwa Duk da Ranta ya bata shi din ne acikin Motan bata damu ba Tunda shi din bawai ya Dameta bane,Megadi na gaisheta ta amsa mai Cikin Kadahan dinta,ta shige Cikin Gida Tagaji jiyanan sun karbi yan Haihuwa da yawa bata samu ta Runtsa ba Tana shiga Falon da Sallama suka Hada ido da Samira dataji Sallamarta ta Fito Zuruf kamar an jehota,Kallon kallon sukayi ma juna Batacema Sunaima ba itama batacemata ba Motsi Sunaima Taji a Kitchen yasa tasan Magajiya na Ciki chan ta Nufa suka gaisa ta mata sannu da dawowa duk da tasan da yaran ya Fita sai da ta tambayeta ta tabbatar mata da cwaa Yallabai ya tafi kaisu mkaranta kafin ya wuce wajen aiki.
Fitowa tayi zuwa Dakinta Tana kallon Samira Dake Tsaye afalon har lokacin Tana Nazarinta Sunaima ko barayinta bata Kallah ba,domin bata da Lokacinta Bata shiga Gonarta ba jira Take sai ta shiga gonarta Tayi mata Fata Fata da Zataa gane Shayi Ruwa ne.
Dakinta ta shiga hijabinta kadai ta Cire Da Uniform din da komai ta shiga Tiolet Daman kayan sun yi Datti warin Jini suke yi suna Bukatar wanki yau din nan Allah ya Taimaketa bata da aiki yau da gobe,Sai jibi zata koma na Safe.
*******
*ABUJA..*!
_Area:GARKI..._
Da misalin karfe 10:00am na safiya.
Tana daga cikin Tiolet din Dake Makeken Bedroom dinta mai kama da aljannah Duniya,Taji wayarta Tana ta Ringing din neman Dauki,Tasan bazai wuce Hajiya Salame ba da suka Fara mgana ba Dazu da Safe,Sadiya Tanaga ta wuce makaranta Shiyasa bata jita ta Shigo ba.
Saddiqa kuma tana Shashen Falmata shiyasa bataji Motsinta ba.
Agurguje ta gama wankan ta fito Dauke da Babban Towel ajikinta Tana Digan Ruwa da komai ta Nufi wayarta Dake ta saman neman Dauki Ganin sunan Hajiya Salame yasa ta Murmusa Ta Daga Tana Fadin"Kin cika Gwazzaba..Kina kira na ina Wanka ne..!
Dagachan Bangaran Hajiya Salame Diya ta kusa da Karshen a wajen Maimartaba Sulaiman Sarkin Kargi da Hajiya Fulani kuma sa"ace ga Hajiya Zabba"u domin Duk Tare suka tashi Lokacin suna yanmatanci ita Zabba'u aka bama Aliyu ita kuma Salamen aka Aura mata Yaron kanin Maimairaba Mai rasuwa Alhaji Hashimu Tana zaune agarin jos Tunda dan siyasa ne itace Uwar Laila da ita kadai ta Haifa agidan Duniya shiyasa ta riga taga gata kuma Take kan ganin gatan.
Yatsina Fuska Tayi tana Fadin"To kema da wani abu kike..Yaya fa baya garin wankan Sassafe haka alhalin kinsan mun fara mgana..?
Hajiya Zabba"u ta zauna gefen gadon tana Fadin"Wlh bari kawai Fita Zanyi..Nayi shooping akwai abubuwana da suka kare ne..Da Sadiya nace tajemin to ta shiga makaranta suna da Test..!
Hajiya Salame tace"Shikenan ya muka kwana kan mganar mu..?dazu d kikaji na kashe kiran Kawar Laila ce tazo..!
Hajiya Zabba"u tace"Ok..Ai daman na Fadamiki wannan karon ba Gudu baja da baya..Laila kamar ta auri Sulaiman ta gama Wannan alkawarina ne Salame..!
Hajiya Salamatu tayi kayattacen Dariya kafin tace"Ko kefa Zabba"u tun tuni fa kina da wannan Damar kika Zauna haka kina tsorin Yaya da Maimairtaba..Kinsane da yadda Laila Taki kowa tun farko sai sulaiman akan shi har Dan Sarkin Gombe taki..Da Farko in nayi shuru to yanzu gabar mu ne In lokacin marigayiya matarsa taci nasara wannan Tsohuwar da batasan komai ba bazata ci galaba akanmu ba yanzu ta ina zAmu fara..!?
Hajiya Zabba"u tace"Ta inda aka hau tana nan za"a sauka..!
Gobe zan shirya na Tafi kargi in mun yi mgana da Abbansu ya barni zan je na samu maimairataba da kwararan Hujojjinmu da muka Tara wanda na Tabbata bazai taba Gujemusu ba bama shi ba hatta Sarakin da Mahaifinsa basu isa suce wanu abu ba wannan karon..!
Hajiya Salamatu ta saka Dariya kafin ta Tsagaita Tana Fadin"Nasan zaki iya..In takama ma Harda kukan ko Zabba"u..?
Hajiya Zabba"u tace"Keda kikasan komai..In nagama nawa Maimairtaba in ya Neme ki sai ki cike bangaran daya rage ke da Laila..!
Hajiya Salame tace"Ina nan ina jiran Damar..Itama Laila ai ta shiryama hakan ai aski yazo gaban goshi da yardan Allah nan da wata Daya Laila ta zama Halastataciyar mata ga Sulaiman auran da Maimairtaba zai Daurshi a Fadarsa da Hannunsa..!
Hajiya Zabba"u tace"Insha Allahu..!
Daga haka suka cigaba da mganarsu kafin su yanke kiran da Karkashi Hajiya ta shafamai ta shirya Cikin wani Ubansu Leshi da mayafinsa ta Dauki Jalarta da wayarta da Atm dinta na Banki ta Fice Daga Dakin Falon ta Ratsa zuwa Shashen Falmata Domin ta Sanar da ita zata Fita.
*Janafty*