JODAH

04

by @sadisakhna


 

  _____👑 *JODA* 👑_____ 

 

              

 

 

 

Na  

 

*Sadi-sakhna* 

 

Ƴar mutan Jama'are 

 

 

 

 

 

 

THE TRIO OF TALES  

(3⃣ minds, 3⃣stories,1⃣Journey)  

 

 

 

 

*HarÆ™a ta (4)*👑 

 

 

 

 

 

Ƙulli biyu sukayi na kayansu,É—aya na sakawa É—aya kuma na amfani,sauran abubuwan da basu zama wajibi ba suka zabi su barsu a wajen.  

 

 

 

ÆŠauka musu kayan yayi yayinda ita kuma ta durÆ™usa ta É—auki Joda,wacce har yanzu take cikin baccinnata mai kama dana mutuwa. 

 

 

 

zani tasaka ta É—aureta É—aram a bayanta,yanda ko wani abu yafaru bazata rabu da bayannata ba. 

 

 

 

Fitowa sukayi daga cikin bukkar tasu suna sanÉ—a a hankali har suka samu damar barin sansanin bayin,kasancewar tsakiyar darene shuru babu wani hayaniyar sawun mutane,sai kukan Æ™wari da dana mujiya kawai mutum yake jiyowa. 

 

  

 

Juyowa yayi ya É—an tsaya Aminatou ta Æ™araso inda yake,kasancewar ya É—anyi gaba itakuma tana binsa a baya. 

 

 

 

"Nayi magana da Abbas Abokina yayimin kwatancen wani Mutum mai kwale kwale jiya da daddare,yana tsallakar da mutane masu irin halin da muke ciki,munyi sa'a zai yau zaije kai kaya babban jirgin da zai kai gabar bakin yankin daular Songhay,daga nan saimu shiga nahiyar ko Allah zaisa mu tsira. Saidai hanyar dazata fiddamu daga nan cikin masarauta zuwa gabar kogi itace babban tashin hankali,saboda akwai dakaru ta ko ina suna jira,dan haka inaso ki kula sosai kuma ki É—aga Æ™afa muyi da hanzari mu fita, ki kula sosai Aminatou sannan ki dunga addu'a a cikin ranki" 

 

 

 

ÆŠaga masa kai tayi cikin nuna alamar ta gamsu da bayaninnasa,kama hannunta yayi suka cigaba da tafiya har suka iso bakin ganuwar ganin inda zasu haura. Anan gizo yake saÆ™ar dan tsallakawa batareda an gansu ba abune mai matuÆ™ar wuya,gashi garin a zagaye yake da Æ™ofar shiga guda biyu kacal,kuma kowanne lokaci akwai dakaru masu tsaron shiga da fitar kowa, Babu wanda yakeda iko fita sai ya nuna Khatimin izini,idan mutum bashida shi daidai yake da É—an leÆ™en asirine,idan kuma bawa ne to guduwa zayyi kenan. 

 

 

 

Can gefe da idan babu kowa suka Æ™arisa,alamar mutane suka gani a wajen maza guda uku. Suna Æ™arisowa har jikin Aminatou yafara bari saita kalli ashe abokan Kamaluddeen ne. 

 

 

 

Tun safiyar ranar suke aikin huda matattakala a jikin ganuwar,sunyi nasarar yin yanda mutum zai kama ya haura,idan suka nasarar taimakawa musu suka gudu a daren zasu maida laka su toshe alamar. 

 

 

 

Kamaluddeen ne yafara takawa,saida yakai tsakiya suka miÆ™o masa kayannasu ya jefasu ta baya, É—ago da Aminatou sukayi yakama hannunta yajata sama,cikin kulawa ya taimaka mata ta sauÆ™a ta can bayan. 

 

 

 

Ganin ta sauÆ™a lafiya tana jiransa yasa ya É—an tsaya suyi bankwana da abokannasa,wanda suka bada ransu sukayi kasada wajen ganin sun taimaka masa ya gudu.   

 

 

 

"Nagode Muku bansan da wanne baki zan cigaba da gode muku ba Allah ya tsareku a wannan wajen ya shiga lamarinku" 

 

 

 

"Bakomai kamal kayi sauri kaje tsayuwar nan tamkar kana jawo wani shiga hatsarinne bayan wanda yake gabanku,maxa ka tsallaka ku tafi Allah yatsare,idan kun isa lafiya kayi mana aiken wasiÆ™a" 

 

 

 

Jinjina kai yayi ya tsallaka,su kuma suka fara rufe ramin matattakalar da sukayi musu. 

 

 

 

Dirgawar dayayi yabada sauti mai Æ™arfi kasancewar tsakiyar darene gari yayi tsit,hakan ne yabada tasiri wajen ankarar da dakarun dasuke nesa dasu kaÉ—an. 

 

 

 

Da sauri kuwa suka zare mashin su da kwari da baka tareda darara tsawar tambayar waye a wajen. 

 

 

 

Jikin Aminatou ne yafara rawa,ga tasaka dukkan hannyenta ta rirriÆ™e Joda wacce take É—aure gam a bayanta,jaka É—aya kamaluddeen yayi nasarar É—auka tareda nausawa jejin dayake gabansa da gudu hannunsa yana riÆ™eda na Aminatou wacce itama take É—aga Æ™afafunta da dukkan Æ™arfinta tana miÆ™a su gaba. 

 

 

 

A bangaren su abbas kuwa jikinsu ne yayi sanyi laÆ™was jin dakarun bayan masarautar sun kama su Kamaluddeen. Banda salati na nema su fatan tsira babu abinda sukeyi. 

 

 

 

Gudu sukayi iya gudu, gaba É—aya dajin ya karafÉ—e da amsa amon dogon nishinsu wanda yake fitowa sanadiyyar gudun da sukeyi wanda yafi Æ™arfin zuciyar dake cikin gangar jikinsu. 

 

 

 

Jikinsu ya gaji laÆ™was amma basuda alamar sararawa da gudun da sukeyi,domin wanda suka bibiyarsu domin farautar rayuwarsu suma basu sarara ba. 

 

 

 

Ganin Æ™arfin Aminatou yafara Æ™arewa yasa ya dawo bayanta,gashi goyon Joda yayi mata nauyi a bayanta,kuma babu halin su tsaya ya karbi goyon saboda bibiyarsu a da akeyi. Idanuwanta sunyi zuru zuru numfashinta sai Æ™wacewa yakeyi tana fixgoshi,amma zuciyarta taÆ™i bawa gangar jikinta damar hutawa,domin a halinda take ciki babu abinda zuciyarta takeso face tseratar da rayuwar baiwar allan dake bayanta wacce batasan a wanne mataki take ba na rayuwa. 

 

 

 

Ganin sun kusa cimmasu yasa wani badakare zare kwari da bakar sa ya saita bayan Aminatou inda joda ke É—aure. 

 

 

 

Hakan ya farune duk akan idon Kamaluddeen cikin zafin nama ya tare bayannata kibiyar ta cakeshi a tsakiyar bayansa,daidai sunzo bakin gabar tudun da suke hawa a hankali, zafin harbin yasa ya faÉ—a jikinta suka faÉ—a gangaren kamar an mirgino Durom daga kan tsauni. 

 

 

 

Sunkai wasu daÆ™iÆ™u suna gangarawa har suka iso Æ™arshen gangaren.  

 

 

 

A hankali take buÉ—e idanuwanta wanda sukayi dusu dusu saboda juyewar da kanta tayi,wata Æ™ara takeji a cikin kunnenta mai matuÆ™ar sauti wacce ta hanata jin wani sautin bayan wannan. 

 

 

 

Hannunta ta saka tana bubbuga kunnen harta samu Æ™arar ta ragu kuma kallonta yafara daidaita. Jini ta kalla a hannunta kaman anyi mata lalle dashi,hakan yasa ta juya gefenta da sauri ta kalli inda kamaluddeen yake kwance ya kifa kansa da Æ™asa,bayansa da sauran itacen kibiyar a tsaye wadda ta karye a sanadiyyar gangarowar da sukayi. 

 

 

 

Jijjiga shi takeyi tana girgiza kanta,hawaye yanata kwarara a kumatunta wanda sukasha fodar Æ™asa fururu. 

 

 

 

Ganin Æ™arfinta ya gaza isa wajen jijjiga mijinnta yasa ta waiga gaba da bayanta gefe da hagun taga ko masu bibiyarsu basu saduda ba,amma sai taga wayam da alama sun Æ™yalesu da suka ga sun faÉ—a ramin. 

 

 

 

Sunce goyon Joda tayi daga bayanta,yarab ta zube Æ™asa kamar matacciya. Bata damu da hakan ba dan dama tasan tana cikin wannan halin ta goyeta. Fasihmman data taba hancinta taji numfashi yana shiga da fita. Bayan wannan babu abinda yasameta banda É—an zafi da jikinta yayi sai kuma gurjewa da hannayenta sukayi kaÉ—an. 

 

 

 

Ci gaba tayi da jijjiga shi tana Æ™iran sunansa da dukkan Æ™arfinta,har hakan yayi sanadiyyar jawo hankalin wasu maza da suke jawo kwale kwale daga cikin gabar tekun dake gabansu. 

 

 

 

Tahowa sukayi domin su ga mai yake faruwa. Bayan sun Æ™arisa wajen suka kula da Aminatou wacce take jijjiga mijin ta tana kuka,gefe guda kuma da Joda wacce take kaman ta mutu. ÆŠaga kai sukayi suna kallon Dogon tudun da suka gangaro zuwa Æ™asan tsaunin inda bakin tekun Naija yafara, Abinda yabasu mamaki sosai domin wajen ba Æ™aramin nisa ne dashi ba,in za'a sauÆ™o yawanci zagayowa akeyi,amma su waye ya razanasu haka da suka faÉ—o ta wajen. 

 

 

 

Wanda yafi É—ayan manyanta ne ya tsugunna ya kalleta,itama su É—in take kalla da yanayi mai wahalar fassaruwa. 

 

 

 

"Bansan ku suwaye ba,ballantana nasan ku masu cutarwa ne ko kuma masu taimako,amma koma mai zakuyi mana da farko ku ceci rayuwar mijina,yabada rayuwarsa ne domin ya kare tamu,bazan iya jure rashin shi ba,idan da sauran rayuwa a jikinsa to ku taimakeni ku ceci rayuwarsa" 

 

 

 

Cikin kuka da kiÉ—ima take yimusu maganar ba a cikin nutsuwa ba. 

 

 

 

"Ya isa haka ki nutsu ba cutar dake zamuyi ba,Kai Yusha'u É—auko mata ruwa tasha tukunna" 

 

 

 

"Ahah ku bar ruwan banajin Æ™ishirwa,ku fara dubamin shi dan Allah" 

 

 

 

"Baiwar Allah ki nutsu naga Æ´arki a gefenki itama bata motsi kaman babu rai a jikinta ko kuma ta samu matsala,amma ta iya mijinki kikeyi?" 

 

 

 

"Ahah ita dama haka take bata motsi sanda muka taho,ta faÉ—a doguwar suma tsawon sati guda kenan" 

 

 

 

"To amma naga kaman tana motsa yatsanta tunda mukazo hala baki kula bane inaga kinata mijinkin kaÉ—ai" 

 

 

 

Jin bayanin sa yasa tayi saurin juyawa kaman an zabureta ta kalli Joda,daidai lokacin da yatsunta na hannu suka motsa. 

 

 

 

"Innalillahi ai kuwa hakane,Joda ta tafara motsawa Joda ta zata tashi da izinin Allah,Aban Joda ka tashi kagani Allah ya taimake mu munyi nasarar tseratar da ita" 

 

 

 

Tana cikin sambatun wanda aka Æ™ira da yusha'u ya dawo ta Jakar fata a hannunsa wacce take É—auke da ruwa. MiÆ™a mata yayi saida ya lallabeta kan mijinta yana raye kuma zasu masa magani kafin hankalin ta ya É—an kwanta. 

 

 

 

Wata hanya suka bi bayan sun É—aukeshi,ganin zasu bace mata yasa ta É—auki Joda itama tabi bayansu,duk da jikinta rawa yakeyi saboda rashin Æ™arfin jiki,amma haka ta dage tana binsu a baya har suka iso wata bukka a tsakanin wasu bishiyoyi,an yayyanke tsirran wajen yabada É—an wadataccen fili a cikin duhuwar jejin,ga iskar kusada ruwa tana kaÉ—awa. 

 

 

 

Kwantar dashi sukayi akan gadon da akayishi da itace sai aka shimfiÉ—a fatar dabbobi akai.  

 

 

 

Nuna mata waje sukayi da zauna itama ta shimfiÉ—a Joda a gefenta,hankalin ta gabaÉ—aya ya rabu biyu,ta rasa wanne daga cikinsu zata maida hankalin ta kai. 

 

 

 

Wanda saurayin ya Æ™ira da Baba YaÆ™ub shine ya maida dukkan hankalinsa akan kamaluddeen,an É—au lokaci kafin yasamu nasarar cire masa kibiyar ya É—aure ciwon. Shikuma Yusha'u yakawo mata Kifi taci da kuma ruwa.  

 

 

 

Alwala tayi ta gabatar da sallahr Asuba data azahar harma da la'asar,Æ´ar nutsuwa ce tafara ziyartar zuciyarta data tuna iyalannata suna a raye. 

 

 

 

"Gafara barkanki dai" 

 

 

 

"Gafaran ka dai baba"  

 

 

 

Ta faÉ—a tana É—an sakin murmushi na Æ™arfin hali. 

 

 

 

"Sannu da Æ™oÆ™ari haÆ™iÆ™a kinga rayuwa a yau É—in,amma Allah ya kare na gaba. Mijinki yana raye,nasamu nasarar cire kibiyar datake allon kafaÉ—arsa na dama,Amma zancen gaskiya banida Magani mai Æ™arfi wanda zai kashe gubar da take jikin kibiyar dukka. Gobe zamu kama hanyar zuwa Daular Songhay da asuba,idan babu inda zaku nufa zamu tafi daku inada tabbacin acan zamu samu magani. Amma idan ba'ayi gaggawa ba ina tsoron faÉ—amiki da zai iya rasa hannunnasa na dama,idan kuma yazoda hatsari gubar zata iya shiga zuciyarsa ya mutu. 

 

 Batun Æ´arki kuma itama na dubata,maganar dakika faÉ—a hakane ta faÉ—a doguwar suma ne,amma ta alama wannan mirginowar da kukayi yayi nasarar Tashin Æ™waÆ™walwarta daga baccinda tayi,idan anyi sa'a nan da wasu sa'o'i zata iya farkawa". 

 

 

 

Labarin yazo mata da fuska guda biyu,na daÉ—i da kuma akasinsa,amma duk da haka alhamdulillah kawai zatace.  

 

 

 

Hawayene suka fara ziraro mata,tana yimasa godiya kuma tana hawaye. 

 

 

 

"Nagode sosai Baba,amma bansan kaima dame zan biyaka ba,inaga kuma maganin dazannemo idan nashiga garinda bantaba jin wani nawa ma yaje ba" 

 

 

 

"Indai wannan ne karki damu,kina neman taimako ne nikuma na taimaka miki, batun magani kuma idan munje zan kaiki ne ga É—an uwana,wanda muka gaji ilimin magani dashi,kuma yafini sani da ilimi ma nasanin maganin. Zan roÆ™eshi ya taimakamuku. Tunda ni ba mazauni bane kullum ina cikin ruwa wajen neman Abinci." 

 

 

 

Shuru tayi jimmm kaman bata yarda da abinda yace ba,domin kirkin daya nuna mata a wannan zamani irinnasu abin yayi yawa. Ya kulada hakan sai yacigaba dayi mata Æ™arin bayani. 

 

 

 

Kar hakan yabaki mamaki,tunda natashi zuciyata bata aminta da zaluncin da masu mulki sukeyiwa Bayi da marasa Abin hannunsu,hakan yasa na zabi zaman Ruwa fiyeda zama cikin mutane,ni bazan cutar dake ba,amma banida tabbacin baki kariya É—ari bisa É—ari daga wasu ba,Fasihmman daya kasance kuna É—auke da hatimin bauta a jikinku,ana gani za'a san ku ba Æ´antattu bane."  

 

 

 

"Na gamsu da bayaninka to amma babu yanda za'ayi? Allah yagani banason cigaba da rayuwar bauta, badon komai ba sai dan banason a rabani da iyalina ko kuma na gagara basu kulawa,ka taimake ni dan Allah. Sannan banason na zama baiwar gidan sarauta zuciyata bazata iya yin hakan ba" 

 

 

 

Shuru yayi jimm shi kansa data bashi labarin rayuwarsu ya tausaya mata,amma hanyar dazai shiga da ita ta Æ™ofar daular Songhay ne batareda an ganesu ba yake tunani. 

 

 

 

"To bazance miki ahah ba akwai mafita amma bansan ko zatayi miki ba. Nidai bana buÆ™atar baiwa,kuma ni ba mazauni bane,amma hanya É—aya itace ki amsa ke baiwar ÆŠan uwana ce wanda zan kaiku wajensa neman magani. Ta hakane kawai Masu binciken Æ™ofa zasu buga miki Hatimin shi É—an uwannawa kuma su baki damar na kaiki gidansa,amma inba haka ba zasu gane gudowa kukayi kuma ina tsoron hatsarin dazaku shiga sai yafi wanda kuka fito" 

 

 

 

Shuru tayi a ranta,wato dai bazata taba tsallake Æ™addararta na zama baiwa ba,to amma dai yafi zaman cikin masarauta ko ba komai,sannan idan yanda Baba Yakub yake da kirki shima haka yake to inaga ai batada matsala,zata samu damar kulada iyalanta sannan kuma ayi musu magani. 

 

 

 

"Bazan tilastaki ba saikin bini ba,idan kinada inda zakuje to zan baki kuzuri na duba miki wanda zasuyi ta wajen su tafi dake" 

 

 

 

Ita kuwa wa take dashi,ba inda tasani sai inda tafito,idan tabari suka kubce mata batada masaniyar dawa zata haÉ—u,ga rayuwar mijinta yana Æ™arewa,idan Kasancewa baiwa yazama Æ™addararta zata karba kawai idan shine yafi zama mata alkhairi. 

 

 

 

"Ahah babu inda nasani dazan dosa, Na baka amanar rayuwarmu sannan zan bada Æ´ancin danake tunanin nasamu amatsayin Fasihye na lafiyar mijina dakuma kariya na rayuwar Æ´ata da tawa" 

 

 

 

Jinjina kai yayi,alamar ya karba kuma ya nuna mata haÆ™iÆ™a tayi zabi mai kyau,daga nan suka fara shirye shiryen nausawa cikin ruwan Babban kogin a gobe. 

 

 

 

Da dare yayi komawa bukkar tasu tayi ina Kamaluddeen yake kwance,gefe kuma ta shimfiÉ—a Joda itama tana nata  baccin. Gashashshen tsuntsune a gabanta wanda Yusha'u yakawo mata,Æ´ar cinyar tsutsun ta yaga ta tauna a bakinta,bayan ta gama ci tasha ruwa,matsawa tayi jikin bangon bukkar zata jingina,caraf idanunta yagano mata gangar jikin Joda ta fara jijjiga. Da hanzari kaman wanda aka harbata ta nufi wajenta tana rirriÆ™eta. Yayinda bakinda yake karanto dukkan wata addu'a da tazo kanta. 

 

 

 

Sunyi kaman daÆ™iÆ™a Talatin a haka kafin jikinnata ya shika lakwas kaman an zare mata laka. Sai kuma gumi ya keto ya rufeta shirkif kaman an watsa mata ruwa. 

 

 

 

Itadai Aminatou tana tungume da ita tana kallon abun mamaki,tana so taje ta Æ™ira Baba Yakub amma kuma tana tsoron kada ta tafi wani abu ya sameta.  

 

Fatar idonta ce fara rawa a hankali a hankali saita buÉ—e idon. Ƙiƙƙiftasu takeyi alamar sunyi mata dusu dusu bata gane mai take kallo,alamun jijiyoyin idon sunyi sanyi sakamakon tsawon lokacin data É—auka a kwance. 

 

 

 

Hannun Aminatou karkarwa yafara ganin Æ™wayar idanun Æ´ar tata a buÉ—e bayan tsawon wani lokaci yana rufe. Hannun takai ta shafi fuskar Joda  tana kuka mai haÉ—e murmushi ,wanda itakuma kallonta takeyi da alamun son tuno mai yake faruwa. 

 

 

 

Bakinta ne yafara motsi da alamun tanason buÉ—eshi tafaÉ—i wata kalmar. DaÆ™yar ta samu damar tunkuÉ—o iska daga cikin huhunta ta fito waje,yayinda take tabb da fita kuma ta datseta da labban bakinta tareda furta "Ummmm.......mahh"  cikin dashashshiyar murya,kalmomin suna fizga kaman mai koyon magana. Idonta kuma ya tsaya a kan fuskar Aminatou cak.