💦BARIKI TAFI GIDA 💦

Chapter 2️⃣

by @aishayakubuahmad811




💦BARIKI TAFI GIDA💦




writer✍️
Aisha Yakubu Ahmad






join my whatapp group via this link:  ***






or join my arewapen via this link also: https://www.arewapen.com/book?id=6a404d02013c3441d19e0400







Bismillahir rahmanir raheem









page2️⃣











ALH MUSA POV………






“ Ku tabbata kun kashe ta “ shine abunda wani

mutumi yake faɗa, a kishingiɗe yake zaune akan 
two seater ya miƙe ƙafa , kana ganin sa kasan 
ya jiƙu da nera , dan daular da ke cikin falon ma 
abun kallo ce ,wani mutum ne aƙalla ze yi 
shekara hamsin a duniya , baƙi kakkaura gemu 
ya cika fuskar , a kammale yake , dan kallon 
farko idan kayi masa zaka basa wasu siffofi 
masu kyau daga yadda yake abu , kamar dai 
yadda mutane suka sheda ;Alh Musa , mutum 
ne me kirki me taimakon talakawa , me adalci , 
baya ƙyamar yan uwansa, gashi da son zumunci………..


wannan kenan 💧 


HAJ ATIKA POV ………………..




Zaune take ta ƙurawa TV ido , sallama akayi 
daga waje , amsawa tayi ba tare da ta miƙa 
kallonta ga wanda yayi sallamar bah ,wani 

matashi ne fari tas , sanye yake da glass a idon 

sa, yana da matsakaicin tsayi ,ɗago da dara- 
daran  idanun sa yayi, Masha Allah kawai na iya 

furtawa , zan wani irin kyakyawa ne , irin mazan 

da ake cewa one in million , to shine wannan 

matashi da na gani .Sanye yake da black 

armanis wanda sukai bala’ in amsar jikin sa , 

faffaɗan kirjinsa na kalla wanda ya ƙoshi da gym 

ga fatarsa da ke zuba kyalli kamar me yin 
skincare , tafiya yake kamar baya son taka ƙasa

ƙarasawa yayi yace “ hajja ina kwana “ dubana 
na ƙara kaiwa gareshi , saboda yadda muryar 
 shi take da taushi amma a ɗan dake take , ta 
irin mazannan da suka ƙoshi da training. miƙewa

 yayi ya ƙarasa dining , siririn tsaki yaja tare da 
miƙewa ya fita daga fallon cikin sassarfa………..


wannan kenann 💧 




ASHNAH POV ………………..


Tun bayan fitowarta daga gida takr tafiya 

batasan inda takr wurga ƙafarta ba , tafiya take 

tana share hawaye ,dubana na kai gareta , 

kyakyawar yarinya ce , black  beauty ce  amma 

saboda wahala da take sha fatarta ta dafe ta 

sake komawa baƙa , tana da dara- daran idanu ,

 amma a lumshe suke alamu name jin bacci , 

dogon karan hancin ta ne ze fara jan hankalin ka  

da ya zarce be sauka a ko’ ina ba se dan 

ƙaramun bakin ta da ya sake ƙawata fuskar ta 

…………..




💦ku biyo ni domin yin yadda zata kasance 💧


Daga alƙalamin ✍️
Aisha Yakub Ahmad