BURIN ZUCIYA Chapter 4
*BURIN ZUCIYA❤* *Arewapen@ayshadansabo*
©️ _Ayshat D'ansabo_ _lemu_ 🖊️
*Free page 4*
Yau tunda Surayyah ta tashi da farin cikin dawowar Uncle B ta tashi,duk da cewa ta san ita da ganinsa zai iya kaiwa nan da 2 days haka ma,domin tasan Kaduna zai sauka gida.
Tana daga kwance a ɗakinta wayarta na riƙe a hannunta tana karatun wasu Novel's wanda tagwayen marubuta suke yi,kumallon mata da mulki ko saurata na Ummy shatu da phertyma zarah take karantawa.Sosai take jin daɗin labaran sai da ta kammala Page's ɗin da aka wuce ta,kafin ta shiga group ɗin Ɗaurin Ɓoye na safiyyah huguma,shima nan ta karance Page ɗin da aka turo.Sosai labarin yake mata daɗi yana taɓa zuciyarta,wutsiyar raƙumi na Billyn Abdul shine ta karanta daga ƙarshe.tana shirin aje wayar sai ga kira ya shigo,ganin sunan Anty Rash Abuja daya bayyana bisa screen ɗin wayar yasa Surayyah sakin murmushi tana ɗaga wayar bayan ta saka shi a hands free take faɗin.
"Mutanan Abuja sai yau kika tuna dani Anty Rasheeda? "
Daga ɓangaren Rash ta furta."Ke har kina da bakin yin ƙorafi Surry? Lallai wuyanki ya isa yanka har na ganki a Abuja,zuba ido muke amma shuru kin kyauta,bayan babu inda kike zuwa kun gama service free kike,maimakon ki zo Abuja muyi chilling ɗinmu amma kin kasa mayyar gida kawai. "
Dariya Surayyah take sosai jin yadda Anty Rash ke zubo ƙorafi,kafin ta tsaida dariyar tana faɗin. "Afuwan Anty Rash,in dai Abuja ne ina tafe In Sha Allah soon.Baba ne baya so na zo ni kaɗai,amma tunda uncle B zai iso 9ja a yau,in dai yazo Zaria zan bishi Kaduna daga nan sai muzo Abuja tare nasan dole zai zo Abuja ɗin."
Rash ce ta furta. "Alright to Allah ya kawo shi lafiya,kice za mu shana sosai idan tare kuka taho don Uncle B yayi ne akwai sakin bakin aljihu idan aka fita."
Duka suka sanya dariya a tare kafin su kama wani hirar Rash na sanar ma Surayyah cewa za ta yi tafiya zuwa Dubai,amma one week kawai za ta yi ta dawo 9ja.Sallama sukai da juna Surayyah ta aje wayar tana sauke ajiyar zuciya,a fili ta furta. "Anty Rash rigima, Anty Rasheeda daru,kina sha'aninki yadda kike so."
Falo ta fito ta tadda Mummy a zaune tana amsa call,sai ta nufi seater ta zauna tana ɗaukar remote ta sauya tasha zuwa Zeeworld tana kallo,sai da Mum ta gama wayar Surayyah ta juya suna fuskantar juna take faɗin.
"Mum yanzu muka gama waya da Anty Rash fa,sai ƙorafi take min naƙi zuwa Abuja,yanzu haka ma wai jibi za ta wuce Dubai,rayuwar Anty Rash anya babu alamar tambaya a kanta kuwa?Mum sam bakwa son tuhumarta inda take samun manyan kuɗi tana yadda taga dama,sam ɗabi'un Anty Rash bana jin daɗinsu ta sauya sosai."Surayyah ta ƙare maganar tana sauraran jin me Mum ɗin za ta ce,sai taji tana faɗin. "Surayyah ni kaina ina mamakin yadda take kashe kuɗi,ga harkar Samari da take taƙi fidda miji muyi mata aure,duk da cewa an mutu an bar mana rufin asiri amma yadda Rash ke kashe kuɗi yana ɗaure min kai,sai dai da anyi magana sai tace Hisham ne yake mata komi,naji maganar tafiya Dubai ɗin Sameera ta sanar min Hisham ne ya biya mata kuɗin don taje ta saro kaya,kin santa da son juya kuɗi,shiyasa wani abun muke kauda kai tunda tana neman nata."
Surayyah ta sauke ajiyar zuciya ba don ta gamsu da maganar Mum ba ta furta."Haka ne kuma,to Allah yasa mu dace.Za ni Abuja idan Uncle B yazo,sai muce tare idan zai je Abuja mu tafi tare ko? "
"Eh tuh hakan yayi,yanzu mukai waya da Haidar ai,yace min jirgin ƙarfe uku na yamma zai iso."
Surayyah ta murmusa tana faɗin."Allah ya saukesu lafiya,ai duk na ƙosa in ganshi Mum,nasan ya sake fresh da kyau ƙasar ya amsheshi tun last zuwan da yayi ya sauya baki ɗaya,duk wacce ta aure shi wallahi ta more uncle B yayi ne."
Murmushi kawai mum tayi tana faɗin."Ke dai Surayyah baki rabo da shirme,wai ya kukai da Safiya ne jiya akan zancen ki da Aliyu? Naji yau ta kira Babanku sun jima suna magana,sai ya ce min idan ya dawo za mu yi magana. "
Surayyah ta ɓata rai tana turo baki cikeda shagwaɓa tace. "Wallahi Mum ni sam ba zan iya auren Aliyu bane,nayi mata bayani ne yadda zata fahimce ni.Ta kuma fahimce ni sosai,kawai ki tayani addu'a Mum Allah yai mini zaɓi na gari kafin wata biyun da Baba ya ɗibar min su cika. "
"To Auta Allah ya yi muku zaɓi ke da ɗaukacin Yaran musulmi baki ɗaya."
Cewan Hajiya Ayshatu tana mai tashi ta nufi ɗakinta yayin da Surayyah ta amsa da. "Ameen. " Tana maida duban ta ga TV ta cigaba da kallonta hankali kwance .
⚡⚡⚡⚡⚡
*KADUNA*
Sanye yake cikin sky blue gezner wanda akai wa ɗinkin da ya dace da shaddar sosai,kanshi babu hula sai gashinsa daya sha gyara yana kwance luff.Ya yi kyau sosan gaske,sashin Hajiya ya nufa domin yi mata sallama sabida tafiya za su yi zuwa katsina wajen wani ta'aziya na abokin aikin su daya rasu.
Humaida da Farha ya tadda zaune a falon suna kallo,sallamarsa suka amsa idanun Farha na kansa.Sosai shigar da ya yi yai mata mugun kyau,wani sabon sonshi take ji na sake fisgar zuciyarta ta.Kallo ɗaya yai wa sashin da suke ya ɗauke kai yana jefawa Humaida tambayar ina Hajiya take? ta bashi amsa da cewa tana ɗakinta,bai sake tankawa ba ya nufi corridor da zai sada shi da ɗakin Hajiya.
Da sallama ya murɗa ƙofar ya shiga tana zaune a bakin gado tana shafa man zafi a ƙafarta dake mata ciwo,ta ɗago idanunta ta sauke akan shi tana amsa sallamar Abdallah,ya samu bakin gadon ya zauna kusa da ita yana faɗin.
"Hajiya barka da hutawa,ƙafar ce dai har yanzu? Gaskiya ya kamata cikin watan nan ki sake fita checkup Saudia,ina ga wannan karon tafiyarmu Umrah zai zo ɗaya ina so in ɗauki hutun 2 week's haka."
Hajiya ta saki murmushi tana fadin. "To Allah ya nuna mana Abdallah,amma da sauƙi fa bawai wani ciwo yake can ba,yanzu sai ina wannan ɗaukar wanka haka?"
Ta ƙare maganar cike da zolaya,hakan yasa Abdallah sakin murmushi yana faɗin. "Katsina muka nufa Hajiya,gaisuwar mutuwar da nake sanar miki za mu na abokin aikinmu da ya rasu."
"Au! Au!! Anyi haka na manta ne ai,to Allah ya tsare hanya ai musu gaisuwa Allah ya yi masa gafara."
Cewar Hajiya idanunta a kan Abdallah daya miƙe yana amsawa da. "Ameen Hajjaju sai mun dawo."
Hajiya tayi masa a dawo lafiya ya fito yana ciro wayarsa dake ringing,sunan Rayyan ya gani ya ɗaga wayar yana sanar masa cewa gashi nan bisa hanya.Koda ya fito falon bai kuma kallon su Humaida ba ya nufi hanyar fita,Humaida ce ta furta."Adawo lafiya Ya Abdallah. "
Hannu kawai ya daga mata yana ficewa baki ɗaya,yayin da Farha ta bishi da ido tana ji a cikin zuciyarta anya ko za ta iya yakice soyayyar Ya Abdallah a cikin zuciyarta kamar yadda ta sha alwashi?Humaida ne ta zuba mata harara tana faɗin. "Tirr! Wallahi,ke dai Farha ba za ki taɓa zama mai aji ba,ina jiya kika gama kuka da cewa za ki barsa amma dubi yanzu ya shigo ko kallon ki baiyi ba,ke kuma kin saki ido da baki kina binsa da kallo tamkar za ki cinye sa mitsuww..!"
Ta ƙare maganar da jan tsaki haushin farha na kume ta,Farha ta sauke ajiyar zuciya tana duban Humaida take faɗin."Hmm! Humaida ba za ki gane bane, Ya Abdallah shine BURIN ZUCIYAta,soyayyarsa yayi ƙarfin da bazan iya yakiceshi cikin sauri ba."
"Aiko kina da sauran shan takaici a gaba. "
Cewar Humaida tana ƙoƙarin barin falon ma baki ɗaya.
Ta bar Farha zaune tana tuno maganganun su da Abdallan na jiya,tambayar kanta take ko wace mai sa'ar ce ta sace zuciyarsa alhali su gasu suna ta bibiyarsa amma ko kaɗan basa gaban shi.
⚡⚡⚡⚡⚡
*ABUJA*
Sameera ce zaune a cikin falon dake down stairs,fruit take sha da Fauziyya ta yanka mata.Sosai take jin daɗinsa hankalinta na kan wayarta suna magana da wani business partner ɗinta da suke harkar gwal da shi,sallamar Ralsy ƙawar Rash ce yasa ta maida dubanta ga ƙofa tana sakin murmushi tare da faɗin.
"Oyoyo Raliya,yau kece a gidan,kwana biyu ina tambayar Rasheeda ke,sai ta shaida min wai kunje umrah da su Hajiyarku."
Ralsy ta ƙariso takai zaune cikin seater fuskarta ɗauke da smile take faɗin."Wallahi kuwa Anty Sameera wannan karon duka gidan muka tafi,yau 2 days kenan da dawowarmu,ina mutumiyar ne?"
Anty Sameera ta sake sakin murmushi tana faɗin. "Husnah,wallahi bata jima da fita ba tana gidan su Ayrah,ita sam inba skull bata son zama shiru sabida ba ta da abokin wasa anan."
Raliya ta sake murmusawa tana faɗin. "Ayyah! To ita ƙawar tawa tana ciki kenan ta barki ke ɗaya a falon,ko kuwa na tako zero ne?"
"Aiko bata jima da shigewa ba,tana nan Ralsy."
Cewar Sameera tana maida hankalinta kan wayarta yayin da Ralsy ta miƙe ta nufi hanyar ɗakin Rash.A kwance ta sameta tayi ɗai-ɗai bisa bed,sanyin AC da ƙamshin ɗakin ya ratsa ko'ina.Tana sanye cikin pitted gown daya matseta sosai,hankalinta na kan wayarta tana chat da sabon saurayinta Fahad wanda basu jima da haɗuwa ba.Muryar Ralsy da ta jiyo tana sallama yasa ta tashi zaune tana faɗin.
"Oyoyo ƙawar kirki,ashe da gaske za ki zo ɗin yau."
Ralsy ta ƙarisa shiga ta zauna kusa da Rash,idanunta fes akan Rash wacce Ralsy taga ta sake cika jikinta kullum na sake buɗewa.Mutane na ganin tsabar hutu da jin daɗi ne yasa ta yin ƙibar,duk da cewa ƙibar ba wani mai yawa bane ƙugunta da kirjinta ne dai suka cika sosai.Hannu Rash takai ta rufe idon Ralsy ganin yadda take binta da kallo,kafin ta furta.
"Ke kallon fa? kamar baki sanni ba."
Ta ƙare maganar tana cire hannunta daga fuskar Ralsy ɗin,Ralsy ta aika mata harara tana faɗin."Rash kinga yadda kullum kike sake zama big lady sai wani uban kyau da fresh kike ƙarowa,miye sirrin ne ko duk ƴan mazan ne ke baki tarin kulawa haka?"
Baki Rash ta kai bisa kunnuwan Ralsy tana raɗa mata wasu kalamai,suka sanya dariya suna tafawa kafin Rash ta kashe ido tana fadin."Ralsy ba za ki gane bane,Hisham na matuƙar bani kulawa,sannan ga Shushu a gefe guda,ke yau 5 day's ma nayi wani kamun mun haɗu a cafe naje shan shayi."
Rash ta ƙare maganar tana sakin smile yayin da Ralsy ta saki dariya tana fadin. "Shegiya ƙawata, wallahi baki da kyau,Rash wai kuma har yanzu kina nufin Anty Sameera ba ta soma gano kina tarayya da mijinta ba? Nifa ina jiye miki tsoran randa Allah zai toni a sirinki. "
Harara Rash ta watsawa Ralsy tana faɗin. "And so what idan asirin namu ya tonu?Aini yanzu Ralsy bana shakkar uban kowa ma yasan alakar dake tsakaninmu,tunda dai duka ni da shi mun cika BURIN ZUCIYARmu,mun riga da mun zama abu guda,abinda bai riga ya faru ba shi kake tsoro ƙawata,kuma in banda abinki ai sakacinta ne ya janyo har hankalin mijinta ya dawo gareni,har yayi nasarar ɓata mini rayuwa don haka bani tsoran tasan komi wallahi,zuciyata ta riga ta gama ƙeƙashewa."
Rash ta ƙare maganar tana jin ciwo a can ƙasan zuciyarta,tana tuna irin kamewarta ada amma sai da Hisham yayi nasara a kanta.Ba kuma komi ya jawo hakan ba illah sakacin Sameera,abubuwa da yawa daya dace ace ita matarsa ita ya kamata ace tayi masa saita dinga sakar mata ragamarsu.Ta barta kara zube tana yin yadda ta so,tayi shiga duk irin wanda take so,tana gilmayya a tsakaninsu ba tare da ko sau ɗaya ta taɓa nuna mata rashin dacewar hakan ba. Buga kafaɗunta da Ralsy tayi ne ya dawo da ita hayyacinta,tayi firgigit tana zubama Ralsy idanunta.
"Rash miye da tunani kuma?
Cewar Ralsy ɗin tana tsare Rash da ƙananun idanunta,Rash ta murmusa tana faɗin. "Babu komi kawai ina tuna baya ne Ralsy rayuwata ta da kafin ta lalace a yanzu,rashin iyaye masifa ne Ralsy domin inka rasa su komin kusancinki da ɗan Uwa ba lalle ya tsare mutuncinki ba,sam ƴan Uwana basa nuna damuwarsu akan irin rayuwar da nake,ina harka da samari kala kala amma basu damu dasu bibiyi wace irin rayuwa nake da su ba,basu taɓa matsamin in fito da mijin aure ba,gashi yanzu idanuna sun gama buɗewa zuciya da gangar jikina sun gama sabawa da maza,Rash yanzu haka jibi za mu bar ƙasar kuma da Hisham za mu fita,amma Anty Sameera bata san hakan ba,nace zani sarin kaya nan take ta amince,Hisham ya sanar mata cewa ya biya min kudin ticket."
Ta ƙare maganar tana tashi ta nufi hanyar fita domin kiran fauziyyah ta kawo wa Ralsy abin motsa baki,Ralsy ta bi bayan Rash da kallo tana jinjina rashin tsoro da buɗewar idanu irin na ƙawarta.Duk iskancinta bata taɓa barin ƙasa tare da Namiji ba,iyakarsu hotel's ɗin Abuja,amma ita Rash bata damu ba bayan tasan irin dangantakar dake tsakaninta da Hisham ɗin.Sai dai tunawa da tayi Hisham ɗin shine ummul aba'isin zaman Rash ɗin duk abinda ta zama a yanzu yasa ta kauda zancen,Rash ɗin ce ta dawo bayanta fauziyya ce ɗauke da tray,ta aje tana gaida Ralsy tare da juyawa ta fice.Rash ta zauna tana faɗin."Bismillah,ƙawata ga mutuminki samosa nan."
Ralsy ta fara da zuba lemun coconut ta kai cup ɗin baki ta kurɓa,ta aje tana duban Rash tana faɗin.
"Gaskiya Rash kibi a sannu tarayyarku da Hisham ya isa haka nan,ki bar mata mijinta please Rash."
Dariya sosai Rash tayi tana faɗin."Dallah!Banza ke kin cika tsoro,wai ke tausayi take baki ne? Hmm! Sai ma kinga yadda yake min Yarinya,rannan fa har cewa yayi ya rasa mai nake sha na fita daɗi."
Suka kwashe da dariya Ralsy na faɗin."Gaskiya Hisham shu'umi ne Rash,amma wannan rayuwar ya kamata mu barta haka muyi aure kuma."
Rash ta saki dariya tana faɗin."Hakane ƙawata nima BURIN ZUCIYATA kenan wallahi"
Daga haka salon hirar nasu ya sauya ya koma kan harkar business,Ralsy na sanar mata za ta fara shigo da takalma da bags ne ita daga Italy,ita kuma Rash na bata labarin irin kayan da za ta yi order tare da nuna mata sample's na wasu daga ciki, dukkansu suna da rufin asiri bawai suna iskanci bane don kuɗi,suna yi ne kawai sabida sabo,domin Ralsy ɗiyar minister ce Ubanta ya rufu ya tada kai,yayin da Rash ita kuma Ubansu ya bar musu rufin asiri sosai domin yayi tashen kuɗi kafin ya rasu.
Sai wajen biyar da rabi suka fito,Rash na taka mata har gurin mota,sai da tabar cikin estate ɗin kafin Rash ta juya zuwa cikin gida.
Daidai lokacin Sameera ta kuma sakkowa,ta dubi Rash tana faɗin. "Har Raliya ta wuce ne babu sallama? Ni tunda na haye sama bacci ya sace ni ban jima da tashi ba."
"Eyyah! Aiko ta wuce Anty Sameera."
Cewar Rash tana yin gaba za ta wuce ɗaki,Sameera ta kirayi sunanta hakan yasa ta dawowa da baya.
"Rasheeda ɗakin Dadyn Husnah zabki taimaka ki gyara,yau kasala nake ji wallahi na rasa miye matsalata,sannan ki ɗauki jakan da ya saba tafiya da ita ki haɗa masa kaya wanda zai iya isansa kwanaki biyar haka."
Kallonta Rash tayi tana faɗin."Okey Anty wata tafiyar kuma zai kuma yi kenan?gaskiya Ya Hisham baya zama sosai yanzu."
Rash ta ƙare maganar cike da shagwaɓa,Sameera ta saki smile cike da ƙaunar mijinta take faɗin."Wallahi nima ƙorafin da nai masa kenan,sai ya nuna shi ma ba don ana nemansa da gaggawa ba zai jima bai sake fita ba."
"To Allah ya kaishi lafiya,bari in je inyi yadda kika ce ɗin,nima tun yau zanyi shirina sabida jirgin yamma zanbi zuwa Lagos,washegary sai mu tashi zuwa Dubai. "
Cewar Rash tana yin gaba Sameera ta bita da kallo zuciyarta na cike da tarin tambayoyi akan Rash wanda ta kasa tinkararta dasu.......✍🏻